Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

BAYAN RAI Complete Hausa Novel Document by BAYAN RAI


BAYAN RAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 78157



BAYAN RAI

Reading Time: 6 Hours

Added On: 25, Apr 2024

Author: Jeedderh Lawals ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 816 492 9724‬

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 428.02 kb

File Type: txt

Views: 1057+

Download: 1531+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: BAYAN RAI! BY Jeedderhh....


[5/2, 10:39 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕


*JEEDDERH LAWALS*


🐾°•01•°🐾


GARIN KANO
Tafe take cikin natsuwa mai tattare da kwantaccen nishadi a kawatacciyar fuskarta. Budurwace mai kimanin shekaru ashirin da uku zuwa da hudu, ba zaka gane yanayin kalar fatar ta ba, ita ba fara ba, ba kuma baka ba, haka ba zaka kirata da chocolate color ba, a takaice dai tana da wata irin kala ce ta daban. Wani babban gida mai wargajejen gate irin mahadi-ka-ture dinnan ruwan gold take dosa, sai data tsaya suka gaisa da wasu maza biyu dake zaune a can gefen gidan a karkashin bishiyar umbrella a zaune suna hira sannan ta shiga gidan, nan ma sai da ta tsaya suka gaisa da maigadi gidan cikin girmamawa kafin ta bi wata siririyar hanya mai shimfide da grass carpet wadda zata sadaka da ainihin main parlour na gidan.

Cikin siririyar murya tayi sallama falon ta shiga a nutse, kamilalliyar dattijuwa dake zaune a cikin falon tana kallon tashar Saudi 1 idanunta saye da farin medicated glass na kara karfin gani, ta dago ta dubi inda mai sallamar take shigowa bakinta ya motsa a hankali wajen amsa sallamar, fuskarta ta dan washe da fara'ah lokacin da tabi budurwar da kallo yayin da take zama a kan carpet din gefen kafar dattijuwar. Hajiya Karima ta kalleta a nutse tace "Rayyanatu, har kin dawo kenan?" ta gyada kai a nutse kuma cikin girmamawa tace "ehh Ummie, Hajiya Tabari tace tana gaishe ki sosai" fuskarta ta kara washewa da fara'a sosai tace ina amsawa kuwa.... Yara sun kusa dawowa, yakamata ki hanzarta ki dora abinci kafin su dawo koh? Ta amsa da toh Ummie. Har ta mike taji Hajiyar na cewa.., "Modibbo yace yau sakwara yake son ci, don haka sai a cire shi cikin namu abincin ki mishi nashi, kin dai san irin yadda yake son sakwarar shi tayi" ta koma ta kara rusunawa tace "Ehhh Ummie, za ayi in shaa Allahu" Ummie tace to madallah.

Dakin da aka ware mata ta fara shiga ta cire kayan jikinta ta sanya wasu sannan ta shiga kitchen din, ta duba time table na abinci ta ga jallof rice ne da farfesun kayan ciki ne abincin daren yau, don haka ta hau shirye-shiryen komi. Ta fereye doya ta dora bisa wuta, sannan ta fito da kayan ciki daga cikin freezer ta wanke su tas ta dora akan wuta bayan ta zuba wadatacciyar albasa da citta, ta kuma dora shinkafa. Doyar na dahuwa ta sauke ta ta dauko turmi ta fara aikin kirbi, kafin kace me! ta hada zufa sharkaf. Ta dan dakata tayi tsaki a fili tace "haka kawai a dinga saka mutum yin wahalar banza, yanzu haka duk wahalar dakan wannan da nasha nasan a banza zata tashi tunda ba wani ci za ayi ba, don dai kawai halin mugunta da son a wahalar da mutum, an san ba za aci abu ba amma sai a saka shi girka abu mai wahala..." Ta kara jan wani tsakin da yafi na dazu tsawo..., "aichhh! I cnt really understand wat's in dix guy's head, he's a total jerk... Very selfish...!" daga kan wannan da za tayi sai idanunta biyu cikin nashi... Tsaye yake a kofar kicin din ya harde hannayenshi biyu a kirji sanye da shadda bugaggiya dinkin Abacha sai dai kanshi babu hula, akwai alamun ya dan jima a wajen babu mamaki duk zagin da ta dinga auna mishi sun shiga kunnuwanshi. Gabanta ya bada sautin dararasss!! kamar fadowar gini, ta zaro wasu dara-daran fararen idanuwa tass kamar madara, ta shiga motsa dan karamin bakinta amma sautin maganar taki fitowa......




🐾💕💕💕🐾
[5/2, 10:39 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•02•°🐾

Wani irin murdadden mutum ne mai wani irin murdadden hali da fahimtar inda ya saka gaba ke matukar ba mutane wahala, hatta da iyayenshi kuwa. Miskili ne na gaban kwatance.
Ya karasa shigowa cikin kicin din a hankali kuma cike da ginshira, ba zaka taba fadin ga yanayin da zuciyar shi da fuskar shi ke ciki ba, sai ma wani guntun murmushi daya saki wanda siraran fatar lebbanshi ne kadai suka nuna yayi. Ya bude fridge ya dauko ruwan faro ya bude ya daddaka, bai kara kallon inda take ba ya doshi hanyar barin kicin din hannunshi rike da sauran ruwan a cikin robar. Ta bishi da kallo tana marmara idanuwa kamar ta saki ihu har ya gama fita daga kicin din kafin ta sauke idanunta cikin saddakarwa ta maida su kan sakwarar ta dan rankwashi kanta "ohhh! Wat did I jst do? Oh my....!" "....idan kin gama a ajiye min a karamin dinning..." kamar daga sama ta tsinkayi muryar tashi, ta zabura ta mike tsaye, sai kuma ta kara komawa ta zauna dabas. Cikin rawar murya tace "uhhh??.. Toh... Toh..." ya dan saki guntun murmushi ya juya. Ta dafe kai tace waiyoo!! Yau na bani ni kam. Cikin sanyi da rawar jiki ta gama aiyukanta na ranar.
Tana cikin yin wanke-wanke taji hayaniyar yara suna shigowa cikin falon, ta danyi murmushi tace yara an dawo kenan! Ba'a jima ba taji an rungumota ta baya, an kuma rufe mata idanu a lokaci guda, tayi dariya tace Hauwa.... Adam.... A tare suka saki dariya kafin Adam daya rufe mata ido ya saki ya zagayo ta gabanta ya rungumeta yana cigaba da dariyar da yake yi. Ta hadesu gaba daya ta rungume a jikinta na tsawon lokaci kafin ta sake su ta shafa kawunan kowannen su tace "oyaa, magriba ta gabato maza aje a cire kaya ayi sallah, yau sai bayan Isha'i zamu yi lesson ok??" Hauwa tace "toh Anti, amma ai ke zaki ja mu sallahr koh?" tayi murmushi tana shafar kanta "a'ah, aiki nake yi sosai yau, kuje wajen Ummie" a tare suka amsa da toh, suka fita daga kicin din da dan gudunsu ita kuma ta mike ta cigaba da wanke-wankenta.

Bayan sallahr isha'i suka yi lesson kamar yadda ta musu alkawari, a dakin ta baro su suna tilawar Al-qur'ani ta fita falo ta tattara kwanukan da aka yi amfani dasu zata wanke. Kamar yadda tayi tsammani, ba a wani ci sakwarar data kirba da yawa ba. Ta ja wani dan guntun tsaki tana tattara kayan, tace Allah ya isa na wahalar da aka bani. Fita tayi da sauran ta mikawa mai gadi ita kuma ta koma ciki ta kimtsa komi, ta duba agogo lokacin karfe tara na dare. Hijabi ta saka ta fita, a harabar gidan taci karo dashi yana ta kai kawo hannunshi daya saye cikin aljihu da alamun waya yake yi, da yake farfajiyar gidan akwai wadataccen haske sakamako bulbs da aka saka, yadda ya mata kallo daya ya kawar da kai itama sau dayan ta kalleshi ta watsar, kanta mike ta bude gate ta fita.
Makotansu ta shiga wanda tazarar gidaje uku ne a tsakaninsu. Shima babban gida ne mai kyau, masu manya-manyan motoci ne jibge a harabar ajiye motoci, wasu an rufe su ma da tamfol saboda ba kasafai ake hawansu ba. Ta danna kararrawar dake manne da kofar falon aka mata izinin shiga, ta tura kofar a hankali ta shiga falon. Yana ganinta yayi fara'a sosai, itama dan guntun murmushi ta saki ta nemi waje ta zauna suka gaisa a dan tsaitsaye, ta lalubo first aid box a karkashin karamin teburin da yake a tsakiyar falon ta isa gefenshi ta zauna. Hannunshi ya mika mata, ta fara warware bandeji dake a babban dan yatsanshi ta wanke raunin har ya fara kafewa ta manna mishi plaster, nan yayi mata godiya sosai, ta hada kan kayan ta mayar inda suke, daga nan suka yi sallama ya rakata har bakin kofa bakinshi dauke da godiya, murmushi kawai take yi har ta bar falon. A tsakiyar dakinta ta same su sun bararraje suna ta shakar barci, ta ciccibe su daya bayan daya ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu bayan ta shafe su da addu'o'in tsari sannan ta koma nata dakin, bandaki ta fara shiga ta rage mararta ta dauro alwala ta dawo ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga mai rangwamen nauyi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download BAYAN RAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album