Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

WARE BAIKO Complete Hausa Novel Document by WARE BAIKO


WARE BAIKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 136408



WARE BAIKO

Reading Time: 11 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 8061929616, 08033933642, 09032409668, +227 90795939

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 690.97 kb

File Type: txt

Views: 685+

Download: 2068+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: [6/28, 1:46 PM] Sis Asma: BISMILLAH

🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮


1️⃣

Official



By
AsmaBaffa
Copy By Zainab Butalawa

Littafan Dana rubuta

GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MA'AIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
ME MAGANI
TUBABBIYA
HADIN KAI
RASHIN SA'A
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
TA GYARU
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA
DANGIN RABI
DUNIYATA AMNA
MAFARKIN FARIDA
WARE BAIKO.....


INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA SABON NOVEL DINA KAMAR YANDA MUKA FARA LAFIYA ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA TARE DA NI DA KU FANS ALLAH YA BAMU LAFIYA DA TSAWON RAI MAI AMFANI.

WANNAN NOVEL BANA KUDI BANE DAN NISHADINKU FANS ALLAH YA BAR KAUNA

DAN ALLAH A DINGA ZUBA SHARHI MUNA RAKASHEWA KAMAR YANDA AKA SABA🤣

WANDA SUKE GROUPS DINA DA WANDA NAKE GROUPS DINSU DA MA WANDA BAMA GROUP DAYA DUKKAN MASOYA NOVELS DINA INA MIKO GAISUWA INA DANNO MUKU GODIYA ME TARIN YAWA.

WANDA NA BATAWA RAI A YAFE MIN NIMA DUK DA NASAN AN FITAR MIN DA NOVEL DIN KUDI NA YAFEWA KOWA 🤣

WARE BAIKO KACOKAN SADAURKARWA NE GA KAWATA 'YAR ARBARKA
🌹AIDA MAMAN TASNIM🌹


Page Dinku ne manya manya

UMMI DEEJAT
AUTA
BESTYNBEELAT
MAMAN SAMHA
UMMUN SADDEEQ
MOMCY
MAMAN SADIQ
FANCY HONEY
RAHMA



Gudu take Yaya Sulaiman na binta da katuwar bulala Yana tsula Mata,ihu take tana gudu cikin masifa Sulaiman yace wallahi kinji na rantse sai kinje makaranta,Yar iskar yarinya kullum sai da duka za a raka ki school,Bata fasa gudun ba shima Bai fasa binta Yana duka ba tana haki Hadi da ihu Tace wallahi bazan je ba nace muku bana son makaranta bana so amma baza ku saurareni ba,Ni da Makaranta bama mutunci ba kawaye bane bana sonta.

Zanci ubanki cewar Sulaiman mutane suna ta kallonsu wurin 10am lokacin da a ake rakata da bulala makaranta in da sabo mutane sun Saba gani sabo da basa ganin budurwar a mai hankali shi yasa bata Shiga safgar kowa itama ba a kulata.

Shaffff....Sulaiman ya shabda Mata bulala again a Haka ya rakata har School,tana wallahi bazan Gane komai ba,na fada muku bani da kwakwalwar karatu ko wanne iri ne,ni karatu baya shiga kwakwalwata bazan Gane ba tana fadan Haka har ta shiga aji,Malam Yana ciki ko kulashi Bata Yi ba ta fada ciki da kalar tafiyarta wata iri ta saki jiki wani shakwaf sannan ta rankwafa gashi ko Ina jefa kafarta take haka take tafiya ita ba tafiyar maza ba kuma baza ace tafiyar mata take yi ba babu Wani gwalli ko yanga.

wuri ta samu ta zauna Jakarta tana saman cikinta hijab din ya karkace gefe,a jikin window ta zauna ta bude tare da zura kanta waje tana kallon compound,Malaman sun rigada sun Saba da halinta ba Wanda ke kulata Haka Malam ya gama darasinsa na mathematics

Zai fita ta juyo ta zabga Tsaki tace Sannu sai kaje ka Nemo X din da kanka,kullum kuce 2a-2b = 2ab find x waye zai nemo muku x din ita x din gidan wa take tafiya? Kullum a,b,s suna aji suna hutawa a saman allo ita x da kullum ake cewa a nemota Ina take tafiya ko yawon banza ita take tafiya? Idan mutuniyar arziki ce tayi zamanta a aji mana mu dinga kallonta,Malamin Takaici yasa ko kulata baiyi ba ya fice abinsa,Yan aji suna ta Dariya Amma ko kallo Basu isheta ba sabo da bata da kawa a makarantar,A babban kauyen nasu ma kawarta Daya ce Sakina Shekarunsu Daya Amma Sakina ita bata tsaya Wasa ba da wuri ta gama karatun secondary tuni ta Kama sana'a,ita Kuwa Har yanzu a Ss3 take nna ta Mata repeating har takai shekara 21years yanzu a haka,sabo da garinsu babban Gari ne na gaske sai dai Kawai local government din nasu ba a cikin birni take ba a wajen garin Adamawa take shi yasa gaskiya da wayewarsu da ci gabansu sosai kamar ba Yan Kauye ba banbancinsu babu yawa Dana cikin birni.


Yarinya ce karama Yar Fara kyakyawa a kalla zata Kai 6yrs,saman bene ta hauro da gudu sanye da Yar gown iya gwiwa me siririn Hannu pink cikin kyakyawan gidan take tafiya da gudu har ta shige wani lafiyayyen bedroom Wanda ya gaji da tsaruwa,tana Shiga tayi Sallama tare da cewa Yaya Nabeel Wai me ya sameka? kyakyawan Matashin Wanda aka Kira da Nabeel Amma kowa yafi saninsa da Lele sabo da Haka Iyayensa ke kiransa, juyi yayi a saman makeken bed dinsa ya sake kankame pillow tare da lumshe Ido ya bude tarrr saman Yar Yarinyar nan da alama kanwarsa ce

Yace Fadila Jeki ki fadawa Mimi da Affa ki basu shawara kice ayi min aure na girma,na Gama degree Ina da aikinyi me Zan jira Kuma, Yar yarinya Bata ganewa ta kyalkyale da dariya tace Yawwa Yaya Nima daga Nan sai a hada da nawa, muyi tafiyar mu tare ko,wanda aka Kira da Yaya ya hade rai yace nine na girma ke yanzu me Kika sani,kunya nake ji kije ki fadawa Affa da Mimi karki sake kice Ni na turo ki shawara Kawai Zaki basu,kice ya kamata a Fadawa su Kawu tunda Kinga sune Yan Uwan Affa sune zasu wuce gaba sai kice a fada musu su wuce gaba ayi auren Nawa,Dariya Yarinyar Fadila tayi cikin maganarta da ba Wani fita take ba sabo da yarinya ce sosai tace Yaya Yar karama ce fa Ni ai Mimi baza su yarda ba

Bazan sake kulaki ba Indai Baki je kin fada ba,Yarinyar Haka ta kwashe da gudu harda faduwa tana cewa Zan fada Yaya,part din Affa tayi ta Iske Mimi a can tana Shiga tace Affa Wai ayiwa Yaya Nabeel aure amma Ni dai bazan fada muku shi yace ba,gaskiya ba shine Yace ba,Dariya ta basu Affa Kuwa Nan take ya hade rai yace shine ya turo ki,na rasa me yake damun Yaron Nan Ina so yayi Ilimi me zurfi amma shi ba yaso shi yasa nace Yan Uwana su Kara maida shi kasar waje karatu Ya koma yayi Masters

an waye yanzu bai Isa ba a sati biyu Inshaallah zai bar kasar Nan Zan samu yan Uwan nawa,har yaushe Nabeel ya girma,har yaushe ya San wani aure me ya sani yaro ayi Masa aure Dan Kawai yaga Allah ya hore mana,a banza Muka Tara kudin yasan wahalar da Muka Sha,Ina laifin ma idan ya Kai matakin masters ya gama a yaso aure da wuri yace ayi Masa amma ko Degree biyu babu comon degree da kowa Yana da shi..

Ka bi a hankali dan Allah ai ba haramun bane Kuma Nabeel ai ya Isa aure akan a barshi Haka ayi Masa Mana ai karatu baya Hana aure,29yrs fa Tunda kaga Yana Haka akwai dalili cewar Mimi,Affa da Bala'i ya tasowa wa Mimi ai dama ke kike lalata shi to wlh ko me zaiyi bai Isa na janye maganata ba karatu zaiyi Likita nake so ya zama,Taya za a kaishi waje a kashe kudi akan ya Zama likita Dan iskan yaron Nan sai yaje ya karanta Engineering ya dawo, Kuma nace Kar ya fara sana'a sabo da Matukar Yana Kama kudi bazai ilimin ba amma karshe sai gani nayi ya hada gwiya da turawa ya kawo motocin aikin titin kwalta gashi Nan yanzu yaje Yana ta faman tara kudi baya Jin magana ta,sai kyale kyale da Hawa motoci Yana Wasa da kudi ga Kanina can Yana Gina Masa tankasheshen asibiti,to idan ba nan ce hanyar cin Abincinsa bafa Haba Affan Fadila ku dinga rage wannan yahudancin Kar ya halakar da ku,Tsaki Yaja tare da furta sai Naga Wanda ya Isa nace ae yace a'a ya fice abinsa.

A bakin kofar Palon ya Iske Lele ya Sha wata kafirar shadda milk ga Uwar suma taci kudi,Baffa ya kalle shi ya tabe baki yace Lele kalleka a haka Kamar wayayye Kamar Dan boko Kalar Ilimi, zubin Doctor Allah ya maka Amma ka Raina baiwarka ka zabi aure ka Isa kasa nayi abinda banyi Niyyar ba,ko da kudinka zakayi wallahi baka Isa ba bare ace Ni Zan maka dole, karatu zakayi kayi shiri Us zaka tafi verysoon bani da arzikin fitar da Kai waje nasan kana da kudi kaima Nabeel Allah ya baka amma Yan Uwana zasu yi,matsa ka bani waje shashasha ba abinda kuka sani sai aure kuyi ta yiwa Mata ciki kuna sakinsu to ba a gidana ba,yaro da Kai 29years kace Aure.

Nabeel har Affa ya Gama Bai ce komai ba har ya tafi ya shiga shirgegiyar motarsa driver Yaja,Nabeel ciki ya Shiga wajen Mimi dinsa.
Nabeel lele Yana shiga wajen Mimi kunya ta lullube shi sabo da Yana da kunya shi kam,Lele meke damunka haka?Kamar zai narke yace Mimi wlh aure nake so ki Masa
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download WARE BAIKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album