Join Our WhatsApp Group

DOCTOR SHAZIM Season 1 Complete Hausa Novel Document by DOCTOR SHAZIM Season 1


DOCTOR SHAZIM Season 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 132889



DOCTOR SHAZIM Season 1

Reading Time: 11 Hours

Added On: 20, Dec 2023

Author: Khadija M Abdulwahab ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KING AND QUEEN WRITING CHAMBER

Author Phone : 09132289761 KO 08133650574

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 668.32 kb

File Type: txt

Views: 754+

Download: 816+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: ✍

👨‍⚕️ Doctor Shazim👨‍⚕️
     
Daga alƙalamin

KHADIJA ( M ) ABDULWAHAB

KAINAAT... ✍ 

*_KING AND QUEEN WRITING CHAMBER_*

Proud to my first novel

Ina alfahari da  kasan cewar wannan littafi na farko agareni 📚 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma ɗaukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi.
Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏

✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️

Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin   nan ba ta kowace hanya, ba tare da an nemi izni a wurina ba.
idan kunne ya ji jiki ya tsira!

Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin mutuncin wani ba,  duk   wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi arashi ne. 

Season one
Free

Episode 1_2

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_

12 June 2003

_Ƙarfe 12:30 Am

Yanayin sanyin da gari yayi, da iskar da ke kaɗawa wanda ya haddasa ganyayyakin bishiyu yin rangaji, tare da ba da wata sassanyar iska.
Yadda sauran ruwan saman da ƙasa bata gama shanyewa ba, da wanda yake gudu acikin kwalbatoci zai tabattar maka da lallai damuna ta kama.

Shiru anguwar take sai kace ba kowa a cikin ta saboda yanayi na dare haɗi da damuna, duk da daman ba'a cika samun mutane na kai kawo a cikin irin waɗannan anguwannin ba ko da kuwa da rana ne, sai hasken bulbs daya haske anguwar haɗe dana street lamps  kaɗai ake gani.

Anguwace irin ta masu faɗa aji a cikin ƙasa, domin kuwa daga shahararrun yan kasuwa sai manya a gwamnati ke a cikin ta.

Motace ta shararo da gudu daga kwanar dake hannun dama a cikin anguwar, yayin da wasu ba ƙaƙen motoci guda huɗu ke biye da ita.

Gudu motar take sosai har ta fita daga cikin anguwar ta hau babban titi, still wa ɗannan moticin na biye da ita a baya
Daga irin gudun da mamallakin motar ke yi zaka san cewa yana gudu ne tsakanin rayuwa da mutuwa.
ta mirror ɗin motar yake hangen fitilar motocin da ke binsa,
yana gudu motocin na bin sa har suka hau kan titin da zai fitar da kai daga garin, gudu suke har suka fita daga garin,
in ban da salati da neman ɗauki daga ubangiji babu abun da mai motar nan ke yi.
domun shi a yau ya san tashi taƙare, saboda ya galabaita a dalilin dukan daya sha, tukin neman ga garar sa yake, ƙarfinsa ya kusa ƙarewa, dubawa yayi ta cikin mirror motar amma bai ga alamun waɗannan motocin ba, tunani ya fara to ko ya tsre masu ne, amma duk da haka bai fasa gudun da yake ba, wani mummunan Bugun da yaji an kaima ma motar shi ne yasa shi fahimtar ce wa kenan wata hanyar suka bi amma suna biye da shi mirror ɗin motar ya kalla, amma sai yaga ba waɗan cen motocin ba ne, wata ƙatuwa truck ce ke binsa yanzu saɓanin waɗancen motocin, ba shiri ya karya kwana ya faɗa cikin daji, gudu kawai yake amma ba wai ya san inda yake dosa ba ne, tsintar kansa kawai yayi a bakin wani ƙaton rami mai zurfin gaske, dole tasa shi taka birki ba dan ya shirya ma hakan ba sai dan baya da wani zaɓi, kawai ya sadakat kwanan shi a yau sun ƙare.
bai gama wannan tunanin ba yaji me truck ɗin ya kaima motar shi wani mumunan bugu wanda ya haddasa mashi buguwar kai nan take ya suma.
Sake ja da baya me truck ɗin yayi ya kaima motar wani bugun wanda yafi na ɗazun, nan take motar tayi cikin ramin, ko karar faɗawar ta ba'a ji saboda tsananin zurfi irin na ramin .
parking me truck ɗin yayi a bakin ramin tare da leƙa ramin ta hanyar hasken motarshi daya bari a kunne.
wani irin ramine me zurfin gaske, wanda tsananin zurfin shi zai sa ka kasa ganin abunda ke ƙasan ramin.

dariya yayi me sauti da amo tare da cewa yanzu kam nasan zan samu cikwan kuɗina domin wannan sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba.
komawa yayi cikin motar shi, anan yasamu wayar shi na ringing  ɗaukar wayar yayi
boss  shine sunan daya bayyana a jikin screen ɗin wayar,  picking call ɗin yayi tare da sa wayar a handspree  tun kafin yace wani abu me kiran nashi yace " Ina fatan kagama dashi? "
answer ya bama boss  ɗin da cewa " ai wannan tashi ta ƙare sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba,  dan a yanzu yana can ya gana da magabatan sa"
"amma naji daɗin jin haka" boss   ɗin ya faɗa .
"amma boss ya kake ganin za'ayi da matar shi da yaran shi ?" me truck ɗin ya tambaya.
"Kar ka damu da wannan big boss.   zaiji da komai , yanzu dai katuraman da account number ka domin natura maka Sauran kuɗin aikin ka "
"thank you so much boss" me truck ɗin ya faɗa. boss ɗin ya ce
"don mind" Kit ya kashe wayar
account number ya turama boss tare da yima motar key ya bar wajen

WANNAN KENNAN.

🌹~ _Kainaat_ ~ 🌹

Gida ne matsa kaici shi ba ƙarami ba shi kuma ba babba ba chan sosai ɗan dai dai.
gida ne namasu rufin a siri kuma yan boko naji da faɗa.
Painting ɗin gidan ya kasance white and blue color ne, haka ma get ɗin gidan blue and white ne.
daka shiga compound ɗin gidan zaka fara cin karo da ɗakin mai gadi daga hannun hagu Sai parking lot daga hannun dama wanda ke ɗauke da rides masu kyen gaske da tsada na fashion a ƙallah za su kai guda 5 a parking lot ɗin.
Sai garden mai kyen gaske ga suke suke masu ɗaukar hankali.
Sai boys quarters dake bayan part ɗin masu gidan.
Masha Allah na furta a ya yin da nayi arba da parlorn gidan wanda aka ƙawata shi da furniture's masu kyen gaske da tsada, komai na cikin parlor onion and pitch color ne, daga gefen daman parlor twin up stairs ne me kyau
Sai kitchen dake gefan hagu wanda yake haɗe da store kusa da shi kuma dining area ne mai ɗauke da chairs guda 7,Sai wani ɗan corridor daga gabas ɗin parlor mai ɗauke da 4 bedrooms, daga chan kuma up stairs ɗin ya kasu kashi 3,part ɗin matar gidan dake haɗe dana yaranta ke hannun hagu Sai na me gidan dake hannun dama sai chan gaba na yaron gidan ne namiji. daga part ɗin dake hannun hagu naji anata kwala Kiran Aaimah! Aairah!! Aairah!!!.
Wata kyakyawar mace ce tafito daga ɗaya daga cikin  bedroom ɗin  ta nufi wanda ke kallon nata ta na cigaba da Kiran
" Aaimah " da "Aairah".
Fara ce sosai tana da jiki ba sosai ba ita ba rammama ba Ita ba mai ƙiba ba a kalla zata kai kimanin shekara 50 . jikin ta sanye yake da sleeping dress riga da wando masu santsi yana yi da Pakistan dress pink color. ba ƙaramin kyau suka yima surar jikinta ba.
"Kun kuwa san ƙarfe nawa" ta faɗa yayin da take tura ƙufar bedroom ɗin ta shiga.
Masha Allah na faɗa domin kuwa bedroom ne me kyan gaske, komai na cikin sa ya kasan ce pink and white color ne , yaji kaya masu kyan gaske bawai cike yake da kaya ba.
bed ne sai bed side drawers, sai dressing mirror gefen shi kuwa wardrobe ne wanda clothes set ne ciki sai jikin ƙofar shigowa kuma jere suke da ƙofar bathroom sai wani ɗan corridor inda ya kasan ce laundry basket ne da shoe rag ne sai bag hanger , bags ne masu kyau na gayu dana school kowace bag set biyu ce kuma color ɗaya.
turus ta tsaya ganin ta kwance har yanzu akan bed, " Aairah lafiya kike kuwa da baki tashi ba ina Aaimah take Ita ma, ko yau baku zuwah school ne iye. "
Ƙarar buɗe ƙofar bathroom taji juyawa tayi, wata kyakyawar budurwa ce ke tsaye jikinta ɗaure da towel iya gwiwarta jikin ta sai raɓar ruwa yake, alamar wanka tayi,  fara ce Ita ma kamar mahaifiyar ta tana da dogon gashi har ƙugunta, ga matsakai tan idanu masu ɗauke da brown eyeball da zara zaran eyelashes, hancinta ma ɗan dai dai dogon bamai yawa ba sosai, ga small mouth me ɗauke da pink lips, tana da shape mai ɗaukar hankali sannan tana da tsayi amma ba sosai ba chan. masha Allah kawai zamuce, akalla zatai kimanin shekara 18 a duniya.
"Ok kintashi kenan Aaimah ce kenan bata tashiba."
"Wallahi mom  tunɗazu nake tashin ta amma taki tashi wai Ita batagaji da bacci ba."
"Tafi ke ki shirya, rabu da Ita yanzu ai zata tashi ba dan halinta ba " mom ta faɗa a lokacin da ta ƙarasa jikin bed ɗin , "Aaimah! Aaimah!! wake up, its time for school , ko kina sone kuyi late ne iye autar mom . "
"Uhm uhm uhm haba mom wai miyasa kike cema Aaimah auta nifa" Aairah tafaɗa yayin da take buga ƙafa tan turo baki haɗe da rike ƙugu.
ai kuwa nan Aaimah ta tashi tana ma Aairah dariya harda gwalo, dama duk abunda mom ke faɗa tana ji, tashi ne kawai bata yi ba
"mom  kinganta ko dariya take man harda gwalo"Aairah ta faɗa sai wani turo baki take da hura hanci. "Ke da'alla  rabu da Ita, ai kema autah ce"
mom ta faɗa  tana dariya ganin yarda Aairah kema Aaimah dariya harda tsalle, "oho dai ai ni aka fara cemawa" mom ta katse ta da cewa
" To ya isa haka maza kushirya
ABIE na nan yayi shirin tafiya , kunsan dai yau zai koma wurin aiki abuja."
"to shikenan mom gamu nan zuwa" har suna haɗa baki wurin faɗin haka.
fita Mom tayi daga bedroom ɗin haɗe da jawo masu ƙofa, ta shi Aaimah ta yi ta nufi bathroom tana faɗin my twin sister dan Allah kifito man da uniform ɗina kafin na fito"Aairah ta ce " to sannu mom kinji koh"
"haba twin sister dan Allah fa nace" Aaimah ta faɗa tana lan gwabar da kai , Aairah ta ce " hmmm sai shegen daɗin baki kamar ta Allah"
" Pls twinee" Aaimah tasake faɗa
"shikenan ba dan halinki ba"Aairah ta faɗa tana ya tsine fuska,murmushi Aaimah tayi tana faɗin "yawwa twenny Ni na san nafi kowa Sa'ar Yar uwa a duniya shiyyasa nake alfahari dake baki sani ba fah irin daɗin da nake ji Idan naganki kusa dani ba" , baki kawai Aairah ta saki tana sauraron ƙar yar da Aaimah ke shirga mata. "wallahi Aaimah kin bani ki rinƙa jin tsoron Allah , ko kunyar ƙarya ba kyaji " gwalo Aaimah tayi hadi da jawo ƙofar bathroom ta shige, dariya kawai Aairah tayi haɗi da girgiza kai tana faɗin " Allah ya shirya ki Aaimah da karya"
wurin dressing mirror ta wuce Vaseline ɗin dove ta shafa tare da farar powder kaɗan ta shafa a fuskar ta sai kwalli da tasa ma eye's ɗin ta, wurin wardrobe ɗin su ta wuce buɗewa tayi , kaya ne masu yawan gaske komai set biyune, wurinda hijaban su suke daban haka ma sleeping dress ɗinsu da ban suma dogayen riguna da atamfofi wurinsu suma da ban haka ma uniform ɗin su na school dana Islamiyya,
uniform ɗin school ta ɗako masu set biyu itada Aaimah wurin bed ɗin su ta koma da kayan a hannun ta domin ta shirya.
shaf shaf ta shirya cikin uniform ɗin ta masu ɗan karan kyau, riga ce da skirt, rigar white color ce, skirt ɗin wanda ya kasance iyakarsa gwiwarta pink color sai sock's fara me ratsin pink daga sama sai top wacce itama ta kasan ce pink color sai Yar baby hijab it kuma white color ce, wurin corridor ɗin su ta nufa shoe da school bags ɗin su ta ɗauko masu, white color ne takalman snikers sai school bag pink color.
"Sis kin ɗauko man nima uniform ɗin" Aaimah ta faɗa wacce fitowar ta kenan daga bathroom. amsa Aairah ta bata da "Eh Amma fa kiyi sauri ki shirya kona tafi wurin Abie na barki" wurin dressing mirror Aaimah ta nufa tana faɗin" sorry karki damu yanzu zan shirya ki bani 5 minute insha Allah " shaf shaf itama ta shirya cikin nata uniform ɗin Masha Allah
Itama ba ƙaramin kyau tayi ba saboda itama Aaimah kykyawa ce sosai a bun da kawai Aairah zata nuna mata tsayine shima ba wani finta tayi ba sosai ka mannin su ɗaya da Aairah tsayinne dai kawai banbancin su shima sai insun jera zaka fahimci hakan.
Snickers ɗin ta itama ta saka tare da amsar bag ɗinta dake hannun Aairah
a tare suka fita daga bedroom ɗin direct part ɗin Abie suka nufa, hannun su cikin na juna suka shiga parlor  ne mai matuƙar kyau,  dan yafi na down stairs kyau da haɗuwa domin ya ƙawatu da expensive furniture's, komai na cikin parlorn sky blue ne da fari.
wani kykyawan matshin tsohone wanda Akallah zaikai ki manin shekara 60 a duniya, yana da haske shima sosai, zaune yake akan 2 siter
" abie " kenan
tea yake sha wanda mom  ta haɗa mashi, sallama sukayi tare da ƙarasawa ciki suna faɗin "abie  ina Kwana antashi Lafiya "suka faɗa yayin da suke samun wuri kusa da abie suka zauna,
"lafiya lau alhmdllh my daughters ina fatan kuma kuntashi lafiya" "Alhmdllh abie " suka faɗa, Abie ya ce
"to Masha Allah haka ake so"
"amma Abie zaka tafi yau shine baza ka yi breakfast damu ba" Aaimah ta faɗa tana turo baki
"Sorry my daughters duk da ma laifin kune tunda tun ɗazu ya kama ta ace kuntashi amma kuka yita bacci gashi ni kuma sauri nake, ai daya ke bajima wa zanyiba wannan time ɗin, zandawo very soon kunji koh."
"shikenan abie Allah ya dawo da kai lafiya"da ameen abie ya amsa tare da kai cup ɗin tea bakin sa.
"to uwayen surutu atashi aje ayi breakfast time na kurewa, abar shima abie ya samu ya gama nashi breakfast ɗin karya makara "mom  ce ke magana wacce fitowar ta kenan daga bedroom ɗin abie hannun ta riƙe da jakar kayan shi da zaiyi tafiya da Ita
"Uhmmmmm haba mom dan Allah kibari muƙara sa yin ban kwana mana" Aairah ta faɗa tana turo baki, dariya kawai Abie ke masu
"Kinci gidan ku nace kutashi kuyi breakfast yana chan baba larai tashirya maku,  nima abarni nayi ban kwana da mijina"
"ah mom sai kice mutashi soyayya ta motsa, to bari muyi ta kanmu," Aairah ta faɗa tareda yin dariya
"Kunci gidan ku...


Read / Download DOCTOR SHAZIM Season 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album