Join Our WhatsApp Group

AUREN KWANGILA Complete Hausa Novel Document by AUREN KWANGILA


AUREN KWANGILA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39498



AUREN KWANGILA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 19, Sep 2023

Author: Ashanty Love ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 728.5 kb

File Type: txt

Views: 3982+

Download: 1703+

Last download: 6 hours ago

Description/Story: AUREN KWANGILA!




1








Littafin






SUMAYYAH ABDULKADIR
Babbangoro2015@yahoo.com
Takorikabara@gmail.com

SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, masu jimirin bin rubutuna daki-daki shekaru dai-dai har goma sha biyu!Tun daga kan SIRADIN RAYUWA har zuwa yau da Allah ya hada mu a AUREN KWANGILA, yabawarku da karfin gwiwar da nake samu daga gare ku ne ya sa har muka kawo yau. Ina rokon Ubangiji ya hadamucikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.


GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a gidan rediyo ba tareda iznina ba, ban yarda a juya shi ta kowacce siga ba ko rubuta shi a social media, yin hakan zai gurfanar damu gaban kuliya kuma abin tuhuma ne daga Lawyer na barrister Sadiq R Wali. Wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan ayyukan sa.


MANUFA
Manufar littafin tana cikin littafi na 3 da na 4. Don haka kada kayi korafi ko sharhi har sai ka dangana da karshen labarin. Taku har abada; Takori



AUREN KWANGILA-1
January, 1996
K
yakkyawan gidan ginin zamani na nan a tsakiyar hamshakiyar unguwar Asokoro cikin babban birnin tarayya, Abuja. Ba shi da girman da ya wuce kima, amma fasahar da aka zuba wajen gina shi abar kwatance ce, sannan hawa daya ne babu hawan bene (flat house). Ainahin ginin gidan a tsakiyar gidan aka yi shi, inda furanni suka zagayeshi suka yi masa rumfa har samansa, rufin da aka yiwa gidan brown ne ire-iren rufunan gidajen kasashen ketare. Kamar yadda rufin gidan yake brown haka fentin gidan ma yake ruwan madara da ruwan kasa (milk&brown). Daga can gefen dama na gidan an gina guest rooms wato dakunan saukar baki wadanda maigidan yayi su ne musamman don saukar ‘yan uwansa dake Kanon Dabo idan sun zo. Gidan ya kawatu da furanni kala-kala dogaye da gajeru masu sanyi da kamshi da kyawun gani hadi da kayatarwa a harabar gidan da kewayensa. A kasa kuwa ‘grass carpet’ ne sun kwanta sun yi lumm, masu taushi da sanyi hadi da sanya nishadi a zuciyar mamallaka gidan.
Da ka shigo get din gidan dakin maigadi za ka tadda a baryar dama, daf da get din. In ka kara yo gaba kadan rumfar adana motoci ce, ga su na a jere sai numfashi da sheki suke yi, mulmulallu kuma kosassu rufe cikin tamfol, adane reras cikin rumfar ba tareda kowacce ta gogi ‘yar uwarta ba, samfur din kowacce daban dana ‘yar uwarta, motoci ne da wadanda suka ci suka tada kai ke yayi a wancan zamanin.
Wannan kayataccen gida dana bata lokaci wajen wassafo muku, mallaki ne na Professor Dr. Hamza Dakata, wanda ke rike da mukamin (parmanent secretary) na ofishin shugaban kasa mai ci a wancan lokacin, shekara ta alif dari tara da casa’in da shidda wato (1996).
Matar gidan, Hajiya Maryam Hamza Dakata, na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da suka kawata falon. Saboda girmansa kujeru saiti uku ya ci ba tare da kowanne seti ya san da zaman dan uwansa ba. Wato a kowacce kusurwa ta falon akwai setin kujeru kala daban da ‘yan uwansu, haka kilishin da ke shimfide a kasansu (carpet) kala daya yake da setin kowanne setin kujera. Sai aka yi labulaye mai ratsi da kalar dukkan kujerun falon.
Idan ka dubi Hajiya Maryam sai ka ji kamar ka sace ta ka gudu sabida kyau da iya ado. Kai ba za ka ce ita ta haifi yara maza guda hudu da ke zagaye da ita tana koya musu aikin makaranta na yi a gida ba (homework). Kallo daya za ka yi wa yaran ya ishe ka kimanta irin hutun rayuwar da suke ciki su da iyayensu, domin dukkaninsu girmansu ya haura shekarunsu.
Babban, wanda ke amsa sunan Abdul’azeez shekarunsa goma sha uku. Yana amsa sunan “Yaya Azeez” daga bakin kannensa. Sai mai bi masa Isma’el da kannen sa biyu ke kira “Ishma” shekarunsa tara. Daga Isma’el sai Usman shi kuma shekarunsa bakwai a duniya tsiransu babu yawa. Hajiya Maryam ta jima bata kara haihuwa ba bayan haihuwar Usman, sannan ta haifi autan ta Haleem wanda har yanzu bai kai ga shiga makaranta ba, dan shekaru uku.
Lokaci zuwa lokaci Hajiya Maryam kan daga kai ta dubi agogon bango, sai kuma ta sauke ta ci gaba da nunawa Azeez aikin makarantarsa (home work), da gani za ka fahimci dakon wani abu take (jira); tana tsammanin shigowar maigidanta ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya ci a ce ya shigo gida tun dazu shi da ba ya kai wa magriba a (office) in ba da wani kwakkwaran dalili ba. Idan hakan ta faru ma zai yi waya ya gaya mata. Amma yau shiru.
Usman ya sosa mata inda ke mata kaikayi da cewa.
“Wai Mammah ina Daddy ya je ne har yanzu bai dawo ba? It’s almost past eight fa (takwas har ta wuce)”.
Hajiya Maryam ta yi ajiyar zuciya, “Kada ku damu. Bari in lalubo shi a waya, watakila aiki ne ya tsare shi”.
Ta shiga latsa wayar hannunta, wadda a lokacin (mobile) ake kiranta, rike ta sai masu kambun susa, ta kai a kunnenta, amma har ta yi burarinta ta gama Daddyn bai dauka ba. Ta kira ya kai sau goma ba amsa. Cikin danne tashin hankalinta ta dubi ‘ya’yan nata wadanda suka tsura mata ido kamar a kwayar idonta suke son gano mahaifin nasu. Sai ta rasa me za ta ce musu, duk suka yi shiru.
Daidai sanda aka murda kofar falon aka shigo, duk suka maida hankalinsu ga kofar don a zatonsu Daddy din ne. Maimakon shi din, mai aikinsu ce, Jamila.
Ta shigo cikin ladabi ta tsuguna a gaban uwargijiyarta.
“Mammah abincin dare ya kammala, na shirya komai a (dining)”.
Mammah ta nisa, “To sannu da aiki Jamila, muna jiran shigowar Daddy ne kafin mu ci abincin”.
Jamila ta ci gaba da durkuson bata tashi ba kanta a sunkuye. Mammah ta lura akwai magana a bakin Jamila.
Cikin kulawa ta ce “Ya aka yi ne kuma Jamila?”
Jamila ta muskuta cikin matsanancin ladabi, kanta a kasa.
“Na zo in yi muku sallama ne, gobe zan koma gida kauye”.
Gaban Hajiya Maryam ya fadi, don tana jin dadin zama da Jamila, yarinyar na da hankali, tsabta da ladabi. Ta yi masu aiki kala-kala daga garuruwa daban-daban, amma ba ta taba yin mai aikin da ta ke jin dadinta irin Jamila ba. Shekarunsu uku kenan tare tun haihuwar Halim aka samo mata ita daga kauyen Kura. A tsayin shekarun nan ba ta taba yi mata wani abu da ba ta ji dadinshi ba. Yi-na-yi-bari-na-bari da alheri da kyautatawa ke shiga tsakaninsu. Ta daure ta ce.
“Lafiya za ki tafi gida? A sanina lokacin zuwanki gida bai yi ba? Cewa nake yau watanki daya da dawowa?”
Jamila cikin matsananciyar kunya ta ke magana.
“Ki yi hakuri Mammah (yadda take ji ‘ya’yan ta na kiranta), ni ma ba da son raina zan barku ba. Domin hakika ku mutane ne na kwarai wadanda suka san hakkin dan Adam da darajar da Allah ya yi masa komai kaskancinsa. A wannan zuwan nawa gida na samu miji da muka daidaita, iyayenmu suka yi magana da juna. Na yi wa iyayena alkawarin bayan wata daya zan dawo a daura mana aure. Tunda na dawo nake so na fada miki kunya ta hanani sai yanzu da lokacin ya zo”.
Jikin Hajiya Maryam ya yi sanyi. Tabbas duk son da ta ke mata ba za ta hana ta yin aure ba kam a kan neman duniya. Murya a sanyaye ta ce.
“Toh Jamila. Na yi miki murna. Allah ya sanya alkhairi, Ya kuma hada mu da alheri. Jira ni ina zuwa”.
Ta mike ta yi dakinta ta dauko rafar kudi a jakarta, turamen atamfofi Holland guda uku da mayafai da takalma da jaka uku-uku ta zo ta zubewa Jamila. “Ga kudin aikinki na wata uku a gaba, wannan kuma gudumawata ce Allah ya sanya alkhairi, Ya bada zaman lafiya”.
Idanun Jamila suka cicciko da kwallah, ta sa hannu biyu ta karba tana godiya. Ta tashi ta koma sassansu na ma’aikatan gidan.
AbdulAzeez ya dago kai daga kan littafinsa, duk maganganun da suke yana jinsu amma bai dago ba sai yanzu da Jamila ta bar falon, yace,
“Mammah garinsu za ta koma?”
“Eh, aure za a yi mata Abdul’aziz”.
Usman ya ce, “Ba za ta dawo ba?”
Nan ma ta daga musu kai, ta ce, “Eh”.
Damuwa ta nuna sosai a fuskar yaran, don sun shaku da Jamila. Tana kula da su sosai, tana jansu a jiki.
Haleem ya ce, “To Mammah, wa zai dinga goya ni?”
Ta yi murmushi, “ai ka wuce goyo yanzu Haleem. Kada ku damu, za mu samu wata. Addu’a za ku yi Allah ya sa mu samu mai irin halayenta”.
Suka daga hannu duka suka ce, “Ameen”.
Isma’el da bai yi magana ba, sai yanzu yayi dogon nazari irin na yara masu tsinkaye sannan ya ce.
“To yanzu Mammah wa zai dinga yi miki wanke-wanke da sauran ayyukan data ke yi?”
Ta yi murmushi, “Ni zan yi da kaina Isma’el, kuma ba da jimawa ba za mu samu wata...........”
Ba ta kai ga rufe bakinta ba suka ji horn din motar Daddy. Ai a guje, in ba ka yi ba ni wuri, Maryam da yaranta ba ga uwar ba, ba ga ‘ya’yan ba, kowanne so yake ya fara isa ga Daddyn. A tare suka isa daidai lokacin da direbansa ya yi fakin a babbar kofar shiga falon, wadda ta kasance ta gilashi (sliding door) suka taro shi zuwa cikin falon don ta nan yake shiga, sauran mutane kuwa sai dai su zagaya su shiga ta kofar kicin.
Bakinsa kamar zai tsage don fara’a, ya bude hannuwa suka shige ciki har uwar. Da alama cikin farin ciki yake mara misaltuwa. Da alama akwai soyayya da shakuwa mai yawa a tsakanin wannan family. A haka suka shiga falon yana dauke da Haleem. Sai jero masa tambayoyi Isma’eel da Usman suke yi na ina ya je yau bai dawo da wuri ba? Shi da ma babban wato Abdul’aziz magana ba ta dame shi ba, uban ya kamo hannunsa suka zauna tare cikin kujera,
“Come on Babban Yaya. Wa ya taba min kai na ga kamar kana fushi?”
Abdul’aziz ya kwantar da kai a kirjin Babansa cikin damuwa.
“Daddy ka yi dare ne duk mun damu. You know we care for you too much (ka san mun damu da kai sosai)”.
Yana shafa lallausar sumar kan yaron, yana murmushi ya ce, “In ka ji shiru alheri kenan. Amma ba zan fadi wannan albishir din da ke bakina ba sai dukkanmu mun ci abinci mun koshi kada farin ciki ya hana ku cin abinci”. Ya fada tare da mikewa rike da hannun Abdul’aziz din. Da, mafi soyuwa a zuciyarsa, cikin ‘ya’ya maza hudu da Allah ya ba shi.
Gabadaya suka hau kujerunsu na cin abinci suka fara ci cikin nutsuwa. Sai da suka kammala suka yi hamdala suka koma bisa kujerun falon, sannan Daddy ya dubesu daya bayan daya yana murmushi ya ce.
“Tun safe muna dakin (meeting) da (President), Ambassadan kasar Saudiyya ne ya yi (retire) kuma cikin ikon Allah ni aka baiwa kujerarsa. So ku soma shiri, nan da sati biyu kacal za mu koma birnin Jeddah da zama”.
Usman da Isma’el suka soma tsalle, amma abin mamaki ban da Abdul’aziz. Shi kamar ma damuwa ya shiga. Daddy na lura da shi ya kara jawo shi jikinsa, “Ya ya dai Azeez? Kai ban ga kana murna ba”.
Ya yamutsa fuska kadan, kana a hankali ya ce, “Daddy I love Nigeria. Bana son matsawa daga cikinta zuwa kowacce kasa. Na fi son in girma, in rayu, in yi karatu a cikinta in tallafe ta watarana. Kowa ya samu ci gaba, sai ya gudu daga cikinta. (I want to be exempted) daga masu yin hakan”.
Daddyn ya tsura masa ido yana al’ajabi, wai yaro dan shekaru goma sha uku ke wannan maganar. Shi ne da wannan ‘patriotism’ din (kishin kasa). Ya san kuma abin da ya fada haka yake har zuciyarsa. Shi din kuma ya kasance wani mutum mai girmama ra’ayin ‘ya’yansa. Ya tattara hankalinsa waje guda wajen baiwa yaron amsa.
“Ba za ka iya taimaka wa kasarmu ba Abdul’azeez sai ka karantu ka gogu kayi koyi da kasashen da suka riga suka gyara nasu kasashen suka ci gaba. Sannan komawarmu kasar Saudiyyah falala ce mai yawa Azeez. Ga ka kullum kusa da dakin Allah ka je ka roki duk abinda kake so. Ga makarantu na musulunci ba irin namu ba. Ga abinci mai albarka ga kwanciyar hankali. Abubuwan alherin suna da yawa, kuma ai ba dauwama za mu yi ba a can zama ne na kayyadadden lokaci. Ka saki ranka ka ji? Mu je mu gina sabuwar rayuwa”. Ya fada yana bubbuga kafadun yaron.
Ga mamakinsa budar bakin Abdul’azeez sai cewa ya yi, “Daddy I’m okey with my life here (ina jin dadin rayuwa ta a nan). Ina son school dina (Regent). Bana so in rabu da ita da abokaina, tunda dama (boarding) nake yi sai in dinga zuwa muku hutu in an yi hutu karshen kowanne ‘term’.
Hajiya Maryam da tun dazu ba ta saka musu baki ba, sai yanzu ta ce, “Abdul’aziz kafiyarka ta yi yawa, duk abin da Daddy ya gaya maka ba ka amince ba ko me?”
“Na amince Mammah. Abin da ya fada, haka ne. Babu kasa irin Saudiyyah. But I love my country, Nigeria (ina son kasa ta Najeriya) anan nake so in rayu”.
Iyayen duka suka dube shi baki a sake. Daddy ya sanyaya murya,
“Za ka iya rayuwa babu mu Abdul’azeez?”
“Zan iya Daddy, na ce maka ai duk hutu ina tare da ku ko in tafi Kano. I just want to live and study in Nigeria (kawai ina so in rayu, in yi karatu a Nigeria ne).”
Ya gyada kai cikin girmama ra’ayin yaron nasa.
“Shi kenan Abdul’azeez tunda haka ka zaba. Mu ma mun amince”.
Sai a lokacin suka ga murmushin Abdul’azeez.
****
Tun a cikin satin Hajiya Maryam ta soma shirin tafiyarsu Jeddah. Damuwarta daya rashin mai aiki. Jamila ta tafi tun a washegarin ranar da suka yi magana. Ta so a ce da Jamila za su yi wannan hijira mai albarka, ita ma ta samu sauyin rayuwa. Ga shi aure ya raba su yadda ba ta da damar sake zama da ita har abada.
Tana zaune a falonta ta kira aminiyarta a nan cikin Abuja, Hajiya Halima. Mijinta (controller) ne na (Custom) ita ta samo mata Jamila. Ta gaya mata tana son mai aiki da gaggawa za ta tafi da ita Saudiyyah an yi wa Baban Halim Ambassada.
Hajiya Halima ta taya ta murna, ta kuma ce babu lokacin da za a je kauye a nemo, amma ga tata nan Habiba jiya-jiyannan aka kawo mata ita. Su tafi ita za ta nemi wata, ta...


Read / Download AUREN KWANGILA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album