Join Our WhatsApp Group

ILIYA DAN MAI KARFI Complete Hausa Novel Document by ILIYA DAN MAI KARFI


ILIYA DAN MAI KARFI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14275



ILIYA DAN MAI KARFI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Ahmad Ingawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 70.85 kb

File Type: txt

Views: 1824+

Download: 418+

Last download: 3 days ago

Description/Story: ILYA DAN MAI KARFI-01

ABUN AL'AJABI 1

A wani gari can cikin kasashen Gabas, an yi wani ana kiransa SAHABI, da matarsa wai ita MURJANATU.

Suna zaune cikin gidan gona Ba wadansu wadatattu ba ne sosai, amma kuma ba matalauta ba ne. Suna da yan dabbobi da gonaki. Abin da dai ya rage musu jin dadin
zaman duniya shi ne rashin magaji kawai. Allah bai nufe su da samun da ba.

Shekara da shekaru suna ta neman haihuwa, amma ba su samu ba. Ran nan kwanci tashi, sai Murjanatu ta samu ciki. Wai kada ka so ka ga irin murnar da Murjanatu da Sahabi suka yi. Tun cikin yana da wata hudu, Sahabi ya soma tanadin iccen wanka.

Ran nan da rana tsaka, Sahabi yana aiki a bayan gida, cikin gona, sai ya ji an rafsa guda,
Ayyururui... Ayyururui....har sau uku. Sahabi ya jefar da fartanya, ya sheko da gudu cikin gida. Da zuwansa kuwa ya tarar da abin da ya ke fatan ya gani. Murjanatu ta sauka, ta sami da, namiji, santilo. Da ranar ta kewayo, jama'a
suka taru, aka rada wa jaririn suna ILIYA.

Ana nan har yaro ya kusa ISA yaye, sai rashin lafiya YA same shi, kafafuwansa duka biyu, da hannu guda, suka shanye. Shikenan ya zauna a
haka, har ya girma. Daga kan dan gadonsa ba ya iya fita ko ina, sai dai a fitar da shi. Iyayensa suka yi bakin ciki kwarai, suka hakura Wata rana iyayen Iliya sun tafi gona, ba kowa gidan sai shi kadai, kan gadonsa, yana ta tunanin yadda duniya take, yana kulle-kullen abubuwan da zai yi, da yana da kafafu. Kwatsam, sai ya ji anyi sallama, Salamu alaikum, salamu alaikum! Sai Iliya ya amsa, Alaikas Salamu.

Kowane ne ya shigo! Sai ga wadansu mutane su uku, suna sanye da tufafi irin na Larabawa, sun yi shigar alhazai. Ko wannensu yana rike
da doguwar tasbaha, yana ja Suka zauna. Iliya yayi musu maraba, suka amsa masa da murna
Iliya ya dubi mutanen nan dakyau, ya ga ba irin mutanen da ya saba gani ba ne. Sai yazaci ko irin mutanen nan ne da ya kan ji ana cewa suna bi gari gari suna wa'azi.

Malaman nan suka tambayi Iliya ko akwai wani abinci yabasu su ci. Iliya ya ce Ba za'arasa ba, ku duba, inda duk kuka gani, ku dauka ku ci. Bana iya tashi, balle in duba muku." Suka tambaye shi abin da ya same shi. Ya ce, "Wurin nan da kuka ganni tun da aka haife ni a nan nake. Ban taba leka ko kofar gida ba.

Ko bayan daki ma sai ankai ni. Allah Sarkin jin kai! Ashe malaman nan ba mutane bane Mala'ikune aka aiko su jarraba Iliya, kuma su warkar da shi. Sai dayansu ya debo ruwa cikin kwarya, ya yi addu'a ya ba Iliya, ya ce, Wanke
fuskarka da Jikinka. Iliya ya karba da hannunsa
mai lafiyar, ya wanwanke. Kamar kiftawar ido, sai ya ga jikinsa sarai, kamar ba nasa ba. Kafafunsa da hannunsa shanyayyu duk sun mike, har in ba wanda ya sani ba, ba wanda zai zaci Iliya ya taba samun wata tawaya.

Ya miko kafafuwansa kasa daga kan gado, ya gurfana gaban malaman nan, ya yi musu godiya Cikin murna yaje ya dauko madara ya durkusa ya ba su. Wannan yakurba, ya mika wa wancan, har ya kewaya dukansu. Sa'a nan babbansu ya mikawa Iliya ya ce, Kaima karba ka sha Iliya.

Iliya ya karba ya sha Jim kadan, daya daga cikin malaman ya ce wa Iliya Yaya ka
ke jin jikin ka yanzu ??

Iliya yace, Na ji wani sabon karfi ya zo mini, har
ina jin kamar kasa ba zata iya daukata ba.
Sai babbansu ya ce wa Iliya yakara kurban madarar Bayan da Iliya ya kara shan madaran sai malamin ya ce, To, Iliya, ka gaskata TSARKAKKEN SARKI ALLAH Ka bi umurninsa, ka yi dukkan abinda ya hore ka da shi, Za ka fifita daga dukkan mutanen kasar nan. Za'a ji sunanka ko ina cikin duniya.

Komai wahala, kome hatsari kada ka yanke kauna ga Ubangijinka. Kuma wannan abu tabbatacce ne kuma rubutacce ne, cewa ba za ka mutu a wurin yaki ba kome tsananinsa.

Duk cikin duniyar nan ba wanda zai sami nasara akanka, sai mutum daya tak.
Ana kiransa da WARGAJI.
Za ka hadu da shi, amma ko kadan kada ka yi fada da shi.

Yanzu ka dauki aniya, ka tafi Birnin ƘIB......ILYA DAN MAI KARFI-02

Duk cikin duniyan nan ba wanda zai sami nasara a kanka, sai mutum daya tak. ana kiransa Wargaji, za ka hadu da shi, amma ko kadan kada ka yi fada da shi. Yanzu ka dauri aniya, ka tafi Birnin Kib, kada ka ce za ka tsaya ka bata karfinka a gona, ko a lambu, ko a daji."

Suna kare magana, sai Iliya ya nemi malaman nan ya rasa. Ya dimauta. hankaiinsa ya tashi, domin bai san dalilin da za shi Birnin Kib ba. Ga shi kuwa malaman sun bace balle ya tambaye su. Ya ga abun duk kamar cikin mafarki Zuwa can, hankalinsa ya dawo, ya yi godiya ga Ubangiji, ya nufi gona wurin iyayensa. Ya tarar da su, sun yi aiki, sun gaji, suna kwance, suna ta sharar barci. Ya yi sallama, ba su farka ba. Sai ya matsa. ya dauki gatari. ya dubi wani katon reshen kuka ya sare Cikin inuwarsa kuwa iyayensa ke kwance. Da karar saran, da ta faduwar itacen duka ba su sa iyayen Iliya sun farka daga barcinsu ba. Sai ya dauki sauran gatarorinsu ya kafe su a jikin itace, ya koma wani wuri ya Boye, yana dariya. Ya ce a ransa, "Idan sun farka za su yi aiki, ba su ga gaturansu ba, ai sa nema."

Can da zafin rana ya buge su, sai suka farka firgigit Suka duba sama, suka ga an sare reshen kukar, suka yi mamaki. Don sun tabbata sare wannan ice cikin dan lokaci haka, sai dai kamar katta goma. Suka duba ba su ga kowa ba, sai gaturansu kafe ga itace. Suka yi, suka yi, su cire, suka kasa. Da Iliya ya ga sun kasa sai ya fito yana dariya, ya sa hannu daya ya cire musu gaturansu. Ganin Iliya haka, sai suka bar mamakin sare ice, da na kafe gatura. Suka koma mamakin Iliya Duk wuri ya yi tsit, da uwar Iliya da ubansa suka kafa masa ido kuri, amma ba su gane shi ba sosai. Don kuwa sun san irin halin da suka bar shi a gida. Uban dai sai dubansa ya ke daga kasa har sama. Can suka gane dai dansu ne, Iliya, ya zama haka. Sai uban ya ta da kansa sama, ya yi wa Allah godiya.

Saboda mamaki iyayen Iliya suka kasa ce masa kome. Sai Iliya ya durkusa gabansu, ya ba su dukan labarin abin da ya faru. Ya kuma nuna musu zama irin nasu ba zai yi masa ba. Ya ce an umurce shida ya taf Birnin kib.

Iyayensa suka yi ta murna ganin dansu ya Mike amma kuma suka yi juyayi, da bakin ciki saboda rabuwa da shi. Iliya ya sake durkusawa, ya tausasa murya, ya ba iyayensa hakuri, ya yi musu magana mai dadi, yadda ransu zai yi dan sanyi. Sa'an nan ya roke su gafara, ya yi ban kwana. Tun daga nan wurin ya kama hanya zuwa Birnin Kib.

Yana cikin tafiya, sai ya gamu da wani mutum yana jaye da dan dukushin doki. Iliya ya tambayi mutumin ko zai sayar masa da shi. Abu kamar wasa, mai dukushi ya yarda, suka yi ciniki. Iliya ya san bashi da kudi, amma don kada a kure shi, sai ya sa hannu kawai cikin aljihu, kamar da wasa, sai ya ji kudi a ciki. Ya dauko ya biya doki. Daga nan sai wani tunani ya zo masa, ya ga ya fi kyau ya koma gida, ya kiwata dokin sa'an nan ya sake fita. Sai ya juya ya koma gida.

Iliya yasawa dokinsa suna KWALELE. Ya shiga kiwonsa yana horonsa yadda zai saba da wahala, da jure yunwa. Kafin wata uku dukushi ya cika, ya zama ingarma, wanda ba kamarsa a nan kurkusa. Ya zama sai harbin iska ya ke yi aturke, har ya fi ubangidansa kosawa a tafi.

Da Iliya ya ga lokacin tafiyarsa ya yi, sai ya je wurin iyayensa ya shaida musu. Ya roke su gafara, suka yi. masa kyakkyawar addu'a, suka yi ban kwana da juna Kashegari tun da asuba Iliya ya shirya, ya hau Kwalele, yatafi

GAMUWAR ILIYA DA WARGAJI.

Ilya ya mika cikin daji yana ta tafiya, bai san inda ya ke nufa ba, har dare ya yi masa. Ga gajiya da yunwa, ga kishin ruwa, kuma ga dokinsa ya gaji, yana dai ta tafiya ne kurum. Kwamtsam sai ga wani lambu a gabansa, cike da 'ya'yan itatuwa da furanni masu ban sha'awa. Daga tsakiyar lambun kuma akwai wata alfarwa wato tanti, ta farin alharini, a kafe. Iliya ya sauka ya daure dokinsa, ya je ya leka cikin alfarwar bai ga kowa ba, sai gado na karfe, da shimfidu, da matasan kai. Bai yi wata wata ba, sai ya haye gadon ya yi kwanciyarsa, ya yi ta sharar barci, har gari ya waye. Rana ta sake faduwa, dare ya yi, gari ya sake wayewa, har dai wajen kwana uku, bai farka ba.

A ranar dare na ukun Iliya yana tsakar barci, sai Kwalele ya rika jin wani irin motsi da rugumniya an nufo wajen alfarwan nan Kamar dai hadari ya taso, kasa na motsi kamar za ta tsage. Itatuwa suna ta faduwa, har koguna suna fantsamar da ruwa cikin daji. Sai Kwalele ya yi haniniya da karfi, don Iliya ya farka. Ya yi masa ishara da cewar ya tashi maza ga wani abin firgici nan tafe. Ashe wurin shan iskar Wargaji ne, wanda aka fadawa Iliya kada ya yarda su yi fada da shi.

Can, sai Iliya ya yi firgigi ya tashi. Kwalele yayi masa ishara da ya hau sama ya Boye. Nan da nan Iliya ya haye bisa wani dogon ice, na cikin lambun, ya make. Kwalele kuma ya sami wuri ya Boye shima.

Zuwa can, sai Wargaji ya iso, yana bisa wani doki kato, daga nesa kamar tsauni. Ya sauka abakin kofar alfarwar. Iliya ya dube shi da kyau, ya ga lalle ya isa abin tsoro, don bai taba ganin mutum da girma kamarsa ba. Shi mutum ne mai fadi, ga tsawo, har ya kere itatuwan da ke wurin. Sai ya ga ya jawo wani dogon akwati daga bayan dokinsa, ya dauko wani irin mabudi na zinariya, ya bude akwatin. Sai ga wata kyakkyawar 'ya, jawur da ita, kamar aljana ta fito. Ta ci ado da kaya iri iri na zinari, da lu'ulu'u, da jauhari Tana sanye da wadansu irin takalma na sakakken jan alharini. Fuskar ta sai kyalli ta ke yi kamar madubi Tana da dogon wuya ga idanu dara-dara, hanci har baka, gashin kanta sai tasa hannu ta tattara shi don kar ya zube Kasa.

Wargaji ya kama hannun matan nan suka shiga cikin alfarwa. Ta bude wata jaka, ta fito da teburi ta girke, ta fito da abinci da abin sha. Suka zauna suka ci, suka sha, suka koshi. Sa'annan Wargaji ya hau gado ya kwanta, ta rika yi masa fita. Nan da nan barci ya kwashe shi. Da ta ga ya yi barci, sai ta fito don ta mike kafa, ta kuma debe kewa, cikin lambu. Tana tafe tana rera wata irin waka a hankali, mai dadin gaske, wadda ke jirkita hankalin mai saurarenta. Can sai ta daga ido sama, ta hangi Iliya bisa itace make. Ta dube shi da kyau ta ce. "Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, sauko."
Nan da nan lliya ya sauko da rawar jiki. Ta kama hannunsa suka shiga cikin alfarwar Wargaji yana ta sharar barci. Ta bude bakin aljihunsa, ta saka Iliya ciki. Iliya ya ji kamar an saka shi cikin wata rijiya mai zurfi.

Bayan an jima kadan Wargaji ya tashi daga barci, ya shisshirya, ya dauki yarinyan nan ya saka akwati ya kulle. ya sarkafa akwatin a kucciyar sirdi. Ya kama hanyar gida. Ya doshi wadansu dogwayen tsaunuka da a ke kira "Tsarkakkun Duwatsu" Wannan wuri ba mahalukin da ya taba zuwa gareshi. Babu kuwa mai iya zuwa wurin. Nan ne fadar GIJIGIJI UBAN WARGAJI. Akwai gine gine masu kawa iri iri a' wurin. Akwai dukiya da samun duniya kowane iri a wurin.

Shi Gijigiji ya fi Wargaji girma, da cika, da kasaita, da kwarjini, da cika fuska. Amma ya tsufa ainun, har ya kai ga makancewa. Suna cikin tafiya sai Wargaji ya ga dokinsa ba ya sauri sosai kamar yadda ya saba. Kuma yana tafe yana sassarfa kamar zai fadi. Wargaji ya yi fushi ya buge shi. Sai dokin ya yi ishara, ya ce, "Yi hakuri, ya shugabana. Karfina na in dauke ka kai da uwargidanka ne kadai, amma ba ni da karfin da zan dauki halitta uku."

Wargaji ya dudduba ko ina bai ga kowa ba, sai ya ji aljihunsa da dan nauyi. Ya sa hannu, ya dauko Iliya. Ya dube shi da kyau, ya ce, "Kai Bil'adama, yaya aka yi har kazo nan, har kuma ka shiga cikin aljihuna?" Iliya ko yaushe mai tawakkali ne ga Ubangiji, kuma ba ya da tsoro, ya dubi Wargaji sosai, ba da wani tsoro ko razana ba, ya ce, "Shugabana, uwargidanka ce ta saka ni cikin aljihunka, ya shugabana." Nan da nan Wargaji ya cika da hushi, ya dauki akwatin nan da matar ke ciki, ya yi jifa da shi bisa wadansu duwatsu a tsakiyar wani kogi, ya ce, "Zauna nan, mutuniyar banza, Aljana ba. Nan za ki yi ta zama har ranar tashin kiyama."

Wargji ya dauki Iliya ya rungume a gabansa kan doki, suka ci gaba. Zuwa can Wargaji ya huce, ya tambayi Iliya kasarsu, da garinsu, da labarinsa duka dai. Iliya kuma ya kwashe labarinsa tun daga farko har karshe ya fada masa. Nan take sai soyayya ta kullu tsakaninsu. Suka ci gaba da tafiya suna ta labari kamar abokai.Amma kafin su isa gida, sai Wargaji ya fada wa Iliya cewa idan sun isa gida, zai kai shi don ya gai da Gijigiji, wato ubansa. Ya fada masa idan Gijigiji ya miko hannu don su gaisa kada Iliya ya mika masa hannu, Ya ce masa da sun isa, akwai makera a kofar gidan, Iliya yayi maza ya saka karfe a wuta, idan Gijigiji ya miko hannu su gaisa, ya mika masa karfen nan a maimakon Hannunsa. Ilya ya ce to, suka ci gaba da tafiya, har suka kawo kofar fada. Iliya ya cika da mamakin irin ginin wurin, watau yadda aka yi shi da farin dutse, aka yi masa zane iri iri. Daga ciki kuma ko ina ka duba sai kujeru da shimfidu. Hatta tagogin gidan na madubi ne ga labule launi iri daban daban, ga fitilu ko ida. Da dai sauran kayan daula da ni'imomin duniya.

Zuwa can Gijigiji ya fito ya tsaya a kofar zaure don ya yi wa Wargaji barka...


Read / Download ILIYA DAN MAI KARFI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album