Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR LAILA MAJNUN Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR LAILA MAJNUN


HIKAYAR LAILA MAJNUN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 5050



HIKAYAR LAILA MAJNUN

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Yusuf Abdullahi A Jibaga ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 26.55 kb

File Type: txt

Views: 828+

Download: 155+

Last download: 1 day ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

HIKAHIKAYAR LAILA DA MAJNUN

maimaici ne√

Hikayar Laila da Majnun an ba da ita kimanin
shekaru dubu da suka wuce, kuma an bayar da
ita ta fuskoki da dama, to amma dukkan
fuskokin sun hadu akan ginshiki daya, watau
tsarkakkiyar soyayya ce tsakaninsu. Ga irin
hikayar da muka rairayo:

Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah dan
kabilar Banu Amar. Qays ya kasance mai fasahaf
da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da
soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad an fi kiran
ta da Laila Amiriya, a hankali ya rika nuna mata
soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu. Duk
lokacin da ta makara zuwa makaranta sai
hankalinsa ya tashi ya rasa sukuni, gaba daya
sai ya zuba wa kofa ido ba ya mayar da hankali
ga karatunsa. Wata rana da zuciyarsa ta cika da
bege, ya ji kirjinsa kamar ya fashe, bai san
lokacin da ya rika rubuta sunan Laila a takardar
rubutunsa ba maimakon abin da ake koya
musu. Dalibai da suka ga haka sai suka
hakikance lallai ya yi nisa wajen kaunar ta. Da
haka ita ma Laila ta soma kaunarsa ya zamana
duk makarantar an san su a matsayin masoya.
Shi Qays kamar tun yana yaro k’arami masu
ilmin taurari suka bayyanawa mahaifinsa cewa
zai kasance wanda rayuwarsa za ta fada cikin
wahala da musiba. Suka kara da cewa idan ba
a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa. Tun
daga wannan lokacin mahaifinsa ke samo masa
lak’ani da magunguna da addu’oi. Yayin da ya
data sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai shi
Dimashka karatu inda anan ne ya hadu da Laila.
Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban kabilar
Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa
ga maciji da kabilar su Qays. Laila da Qays suka
zama tamkar jini daya tsoka daya idan bai ga
daya sai ya kama rashin lafiya, amma Qays abin
na sa ya fi tsanani, domin kuwa har wakoki yake
rubutawa masoyiyarsa yana karanta su a ko’ina.
Daya daga wakokin da yayi mata ita ce:
Na so ki ya mai kyau dan gaske
Wane wata ko tauraro mai haske
Kin shiga ruhina kin mammallake
In babu ke to ni kuwa na hakkake
Ba za ni rayu a duniyar nan ba
A makaranta aka rinka gulmar su ana nuna
Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan
ka yi masa abu ka ce masa ya yi hakuri don
Laila, shikenan zancen ya wuce. Da dalibai suka
gano lagonsa, suka rika dauke masa kayan
rubutu suna cewa ya basu domin darajar Laila.

Ba musu sai ya ba su. Maubin (malamin)
makarantar ya damu kwarai da irin wannan
al’amari. Musamman da ya ga Qaysa wanda
yanzu sunan ya bace ya koma Majnun Laila
(Mahaukacin Laila) ya rubutawa iyayensu
takarda yana fadakar da su halin da ‘ya’yansu
ke ciki. Iyayen Laila suka cire ta daga
makarantar aka kirawo wani kwararren malami
yana koya mata karatu a gida. Ciwon so ba shi
da magani! Maimakon hakan hakan ya yi
magani sai ya dada rikita al’amari. Majnun ya
daina karanta komai kullum sai kuka sai waka,
duk abin da ya gani sai ya ga yana masa gizo
da kamannin Laila. Nan da nan sai ya soma rera
wakar so gare ta.
Mahaifin Majnun ya zo takanas ya dauke shi
zuwa wajen likitoci da ‘yan tsibbu da bokaye da
sauran masu da’awar magani duk abin ya zama
tamkar wutar kara ana yayyafa mata fetur.
Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo
domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin
Laila amma duk a banza. Wani daga baffaninsa
ya ce masa, “wai kai Qays me ka gani a jikin
Laila da ka nace mata haka? Ka zo mu je na
nuna maka mata dubu wadanda suka fit a kyau
da kyan fasali da asali da mulki da dukiya da
sarauta ka zabi wadda ta yi maka.” Majnun ya
dube shi ya girgiza kai ya ce, “idanun Majnun
Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.”
Ya daga hannu sama ya ce, “Ya Allah! Na san
ba ka yi kyakkyawa a duniyar tamkar Laila ba.
Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da
suka zo duniya shan iska. Ya Allah alk’awarinka
bay a tashi, na tabbata daga kan Laila ba zaka
sake wata kyakkyawa ba. Ya Allah ka ba ni
Laila!”

Wani daga kabilarsu ya ba shi shawarar ya
dauki Majnun zuwa Makka ya yi roko a ka’aba
kan Allah ya dauke masa son Laila a zuciyarsa.

Amma saboda tsananin soyayya a yayin da
suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa:
kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka
son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na
tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan
tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . Ya
k’ara da cewa, “Ko Luqman, babban malami
masani na tabbata ba shi da maganin ciwon
so…Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke
tsakanina da Laila. Ya waka wadannan baitoci:
A Makka na ce da shehin malami,

Wai shin wace ke cutar da ni?
Shin laifi ta ke yi to a sanar da ni,
Shehi ya ce “d’ana bi a hankali,
Azaba na nan zuwa can gare ta
Na yi farat na ce masa “a’a na yafe,
Da azaba ta samu Laila ko a gefe,
Ba ni kauna gara ta same ni a lafe,
Da na daina sonta a barci ko fake,
Gara na mutu da ciwon kaunar ta
Sannan ya ce da murya mai raurawa, “Allah ka
ba ni Laila!”

GO BE ZÀMU DAURAHIKAYAR LAILA MAJNUN...2

Yayin da iyayen Majnun suka ga haka kullum
lamarin nasa k’ara lalacewa ya ke yi, sai suka
ga babu mafita face su je su nemi auren Laila
wurin iyayenta. Wannan shine mataki na k’arshe
da suke ganin zai magance matsalar d’ansu.
Suka tashi jakadu na musamman zuwa garin su
Laila suka bayyana musu irin halin da d’ansu
yake ciki game da soyayyar Laila. Sannan
jakadun suka nemi aurenta dominsa. Iyayen
Laila suka amsa da cewa, “mu a wajenmu abin
da Majnun yake yi domin ‘yar mu wulak’anci ne
mai girma. Kuma duk da yake mun san cewa
Laila tana da ra’ayinsa amma ba zamu iya
aurar da ita gare shi ba. A dalilinsa mun cire ta
daga makaranta, mu a wajenmu, mahaukaci ne
kad’ai zai rik’a irin abinda Majnun ke yi.”

Da haka iyayen Majnun suka ji dad'i tunda su a
tsammaninsu idan har ya daina shiririta za su
amince su aura masa ita. Saboda haka suka
shiga tausasarsa suna ba shi shawarar ya nutsu
ya daina abubuwan da yake. Majnun ya amince
da haka, amma da sharadin za a kaishi ya ga
abar k'aunarsa Laila.
Suka shirya suka tafi tare da wakilansa zuwa
garin su Laila. Aka sauke su a wani babban gida
sannan aka kawo musu abinci da abinsha. An
kawata wajen da fitilu masu launi iri dabam -
dabam. Sannan a kunna turaren wuta ko'ina sai
kamshi ke tashi. An jera kasake masu yawa cike
da abinci da fulawoyi masu k'ayatarwa. Zuciyar
Majnun kuwa ta kasa nutsuwa, ji yake kamar
yayi tsuntsuwa ya tafi ga masoyiyarsa. Bai iya
jurewa ba sai ya mik'e a gaban waliyan Laila ya
rika safa da marwa yana rera wadannan baitoci:
Na yi nisan zango don na gane ki,
Ga shi na zo nan ina ta bid'ar ki,
Ina kike ina kika shiga ne in ganki,
Zuciyata tana ta jidali domin nemanki
Ya ki taho abar begena don Allah nunan kanki
Jimawa kad'an sai ga karen da Laila ke zuwa
da shi makaranta ya shigo gidan. Majnun sai ya
ji ya kasa jurewa, ya zabura wajen karen nan ya
rungume shi yana sumbatarsa yana cewa, "Na
ga rabin Laila saura rabin. Ya karen nan mai
baiwa maza je ka ingizo min Laila." Garin
wutsulniyar da kare yake yi da k'afafu ya ture
farantan abincin, suka bata gaban rigar wani
dattijo mai fada aji a dangin Laila. Shi kuwa
gogan naka sai ya d'auki wani tsiron fulawa ya
mak'alawa karen a wuya yana ce masa, "maza
je ka kaiwa Laila ka mik'a min gaisuwata gare
ta." Duk jama'ar wurin suka yi tsit suna kallon
ikon Allah. Wakilan da suka rako shi suka rasa
inda zasu sa kansu domin kunya. Wakilan Laila
kuwa suka cika da fushi iyakar fushi. Wani daga
cikinsu ya fusata ya ce wa Majnun, "Shin bautar
kare ka zo ko kuwa maganar aure?"
Kai tsaye Majnun ya kalli mutumin ya ce,
"wannan karen a wurina ya fi mutum dubu
daraja, domin a jikinsa ina ganin surar
masoyiyata wadda k'aunarta ke d'amfare a
zuciyata dare da rana." Duk wuri aka d'auki
salati. Jama'a suka rik'a zundensa suna cewa
ya haukace. Dattijon nan da aka b'atawa riga da
abinci ya mik'e a fusace ya fice daga gidan. Duk
jama'a ma suka watse.
Da wannan jama'a suka rika rantsewa cewa
haukan nan dai bai rabu da shi ba, sai ma abin
da ya yi gaba. Daga nan iyayen Laila suka fito
kai tsaye suka ce ba zasu aurar da 'yar su ga
Majnun ba. To daga nan sai duk wani fatan
samun nutsuwarsa ya zama sharon gayya, suka
hakikance ba za su iya magance masa matsalar
ba, don haka suka sa masa albarka suka kyale
shi bisa halinsa. Shi kuwa duk inda ya shiga
lungu da sak'o sai ya rik'a cigiyar Laila ko sun
san inda take da yadda zai sadu da ita. A haka
har ya yi kicibis da wani jakada mai aikin raba
takardu. Ya tambaye shi labarin Laila. Jakada
ya ce masa Laila da iyayenta sun tashi daga
garinsu sun koma wani gari mai nisa, daga nan
garin zuwa can tafiyar mil dari da ashirin ne.
Majnun ya shiga yi masa magiyar yana ba shi
sako zuwa gare. Jakada ya amince zai karb'I
sak'on takarda kurum babu wani abu. Majnun
ya zauna yayi ta rubutun shafuka da yawa, har
jakada ya gaji ya ce masa, "wacce irin wasika ce
haka?" Majnun ya ce, "wasikar soyayya ce bata
da k'arshe."

Jakada ya yi dariya da haka sannan ya ce, "to
samu waje ka d'iga aya ka bani na tafi." Majnun
ya nad'e takardar ya ba shi. Sannan ya nemi ya
yi masa rakiya kad'an. Suna tafe Majnun na ba
wa jakada labarin abar k'aunarsa Laila shi kuma
yana ta mamaki. Sai da suka shafe mil goma
Majnun na tafiya a k'asa Jakada na bisa
rak'umi. Jakada ya ce masa, "to ka koma haka,
ka yi nisa kwarai da gidanku."

Majnun ya juyo
ya soma tafiya sannan ya juya ya ce da Jakada
da babbar murya, "ya kai k'aunataccen abokina!
Wallahi na yi mantuwar wani muhimmin sak'o
da nake so na rubuta mata!" Jakada ya ce, "to
gaskiya ba zan tsaya ba, sai dai ka fad'a min da
baki na fad'a mata. Majnun ya kowa ya same
shi suka rankaya. Suna tafe yana fad'a masa
sak'on har suka share wasu mil goman. Jakada
ya ce, "ka koma haka kada a neme ka a
gidanku." Ya juyo ya soma tafiya sannan ya
waigo ya ce, "wallahi ba domin kada ka ce na
matsa maka ba da na k'ara maka wani sak'on.
Muhimmi ne kwarai na mance da shi. Jakada ya
ce, "to matso ka fad'a min!" Suka sake
rankayawa yana ta fad'a masa sak'o. Haka
suka yi ta yi har kafin su ankara sai ga shi sun
isa garin da Laila take. Jakada yayi mamakin
irin wannan soyayya, sannan ya ce da Majnun,
"Babu buk'atar kai wa Laila sak'o gare ni domin
kuwa ga shi mun zo garin da take." Da jin haka
Majnun ya cika da farin ciki da murna. Ya fad'i
sumamme don tsananin farin ciki.

ZAMUCI GABA INSHA ALLAHU GOBE"
Whatsapp only
08071051138^ LAILA MAJNUN...3 ^•^

Bayan ya farfad’o jakada ya ce masa, “ba na so
a ganka, domin jama’a na iya kama ka su yi
maka wulak’anci kafin ka ga Laila. Ga wani
kango can ka shiga ka zauna a ciki ka huta
domin ka yi tafiya mai yawa. Zan isar da
sak’onka ga Laila yanzun nan.”
Majnun ya yarda da shawarar jakada ya shiga
kangon nan ya zauna zuciyarsa na harbawa
kamar ta tsage. Sakamakon tafiyar da ya sha
duk yayi futu – futu. Tufafinsa sun yi jawur da
k’ura, gashin kansa duk ya kukkulle, ga
kafafunsa sun yi fato – fato da kura da faso da
kaushi. Ga shi nan dai yarbajila da shi. Duk da
haka, da ya tuna cewar yana garin da Laila ta ke
gaba d’aya sai ya ji ransa ya yi fari fat. Ya cika
da murna da farin ciki, zuciyarsa ta cika da bege
ya rik’a rera wak’a yana cewa:
Na aika sako na wajen masoyiya,
Zuciyata da rayukana gaba daya,
Na mika su dukansu wajenki gimbiya,
Ke ce tawa hakika na fadi gaskiya.
Na sallama miki kaina lahira da duniya.

Daga nan sai gajiya ta kama shi, ya ji yana so
ya kwanta. To amma sai ya rika tunanin shin a
wanne bangare Laila take? Domin baya so ya
kwanta inda k'afarsa zata rika kallon jihar da
take domin a wajensa hakan cin amanar kauna
ne. Zai iya shurinta bai sani ba. Ya tsaya yana
tunani, shin tana gabas ne ko yamma ko kudu
ko kuwa arewa? Duk inda ya sa kansa sai ya
tuna kila a wannan bangaren take, sai yayi
maza ya sake waje. Daga baya dai sai ya samo
igiya ya daura a kafarsa ya samu gini ya daura
kafar, yana zamana yana reto kamar jemage. A
wannan yanayi kuma bai fasa rera mata wak'a
ba yana cewa:

Hajjina da Umarata na wajenki,
Makka ta da Madina sune ganinki,
Baitil Mukdis wurina murmushinki,
Arzikina duk ni dai in ga dariyarki,
Na sallama kaina gaba wurinki
Kishin ruwa na damunsa amma babu ruwa a
kurkusa, haka ya hakura wutar bege na hura shi,
tana kone masa sassan jiki da zuciya.
Jakada ya yi sallama k'ofar gidansu Laila ta fito,
ya ce mata, "na yi kokari da gaske domin na yi
miki magana, game da masoyinki Majnun wanda
ban taba ganin tamkarsa ba a fagen so." Ya
kwashe labarin duk yadda suka yi ya fad'a
mata. Sannan ya kara da cewa, "yanzu haka na
bar shi a bayan gari domin gudun kada a
wulak'anta shi idan jama'a suka ganshi." Da
Laila ta ji haka sai tausayinsa ya kama ta. Ta
tafi wajen uwar goyonta ta ce mata, "me yake
faruwa ga mutumin da ya yi tafiyar mil dari da
ashirin a kasa ba tare da ya huta ba?"

Tsohuwa ta ce, "wannan mutumin ba zai rayu
ba mutuwa zai yi."
Laila na jin haka sai ta ji ta shiga damuwa, ta
sake ce mata, "babu wani magani?"
"Magani daya ne a sanina. Dole ya sha ruwan
saman da aka ajiye shi akalla shekara d'aya,
kuma dole ruwan ya zamana maciji ya sha daga
gare shi. Sannan ya daura igiya a kafarsa ya
zamana kansa na kallon kasa zuwa wani lokaci.
Idan ya aikata hakan watakila zai tsira da
ransa."

Da ta ji haka sai ta yi tagumi tana cewa,
"wannan magani akwai wahalar samu, kai ba
ma zai yiwu ba." Ta d'aga hannu sama tana
rok'on Allah ta ce, "Ya Allah mai kulla soyayya,
mai bayarwa mai hanawa ka taimaki Qays
Majnun ya samu wannan magani." Ta shafa
sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "soyayya bata
da magani sai ita kanta."

Allah da ikonsa, Majnun na rataye da kafarsa a
sama ga kishirwa na addabarsa sai ya kwance
igiyar ya tafi neman ruwa. Bai samu ruwa ba sai
wani tsohon kasko a wani lungu. Ya tarar wani
zabgegen maciji na shan ruwan. Ya kore shi
sannan ya kafa kai ya shanye ruwan gaba daya.
Ya samu waje ya zauna yana wake - wakensa.

Da gari ya waye Laila ta shirya abinci mai rai da
lafiya ta kirawo kuyanga a boye ta fada mata
komai sannan ta nemi ta kai wa Majnun inda
yake a bayan gari. Kuma ta bata sakon a fada
masa cewar ita ma tana nan tana kaunarsa
kuma tana son ganinsa, amma da zarar ta samu
dama zata zo ta ganshi. Yayin da kuyanga ta je
wajen sai ta tarar da mutane biyu. Daya ya hada
kai da gwiwa kuma duk ya rame ga kansa nan
duguzunzum, dayan kuma mai kiba jawur da shi,
sai dai ya manyanta. Kuyangar ta dube su duka
biyun ta ga babu wanda ya cancanci Laila ta so
shi. Ita kanta ma ta ji duk basu kwanta mata a
rai ba, balle kuma Laila. Duk da haka domin cika
umarni sai ta...


Read / Download HIKAYAR LAILA MAJNUN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album