Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR TUFFA UKU Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR TUFFA UKU


HIKAYAR TUFFA UKU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 4475



HIKAYAR TUFFA UKU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 23.68 kb

File Type: txt

Views: 556+

Download: 114+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01. HIKAYAR TUFFA UKU

Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan abubuwa.
Wata rana da dare, daga cikin ranaku,

a cikin birnin Bagadada, lokacin da Halifa Harun Al'Rashid da Wazirinsa Ja'afarul Barmakiyi ke mulki, Halifa ya aika cikin dare aka kira masa waziri Ja'afaru da sarkin fada Masruru.

Ya ce musu, "Ina so a cikin wannan dare mu canja kama, irin ta fatake, mu shiga cikin birni, mu tambayi talakawa a kan yadda suke ganin mulkinmu a kansu, duk wani hakimi, ko wakili ko mai unguwa da muka ji talakawa na kuka da shi, sai mu tube shi."

Ja'afaru da Masruru suka ce, "Mun ji, mun dauka!"

Suka yi shiga irin ta fatake, suka shiga cikin birni. Suna cikin tafiya cikin wani kwararo, sai suka ga wani tsoho, shekaru sun yawaita a kansa, yana dauke da wata

tsohuwar koma ta kamun kifi, yana tafe yana wake-wake. A cikin wake-waken nasa sai suka ji yana cewa: "Koyaushe mutum ya kai kara zuwa gare su, sai su wulakanta shi, koda shi yake da gaskiya. Idan haka ne kuwa,

kasancewar ran talaka a cikin kabari shi ne ma fi kyawon zama."
Yayin da Halifa ya ji wannan waka ta dattijo, ya dubi Ja'afaru ya ce, "Dubi wannan talaka, ka ji wannan waka tasa? Lalle akwai abin da ke damun sa a cikin zuciyarsa."

Halifa ya gabata a gaban tsoho ya ce, "Ya kai wannan tsoho, mene ne sana'arka?"

Tsoho ya ce, "Ya shugabana, su ce sana'ata. Ni talaka ne, na fita daga gidana tunda tsakar rana na nufi kogi kamun kifi, har zuwa wannan lokaci da na dawo, Allah bai nufa na kama wani abu da zan ci ni da iyalina ba, domin bakin cikin wannan abu, nake gurin mutuwata."

Halifa ya ce da shi, "Ko za ka koma tare da mu zuwa ga kogin Dujillati, ka jefa komarka a ciki, bisa ga arzikina, komai komarka ta debo a cikin kogin zan saye shi dinari dari, ka sami abin da za ka ci da iyalinka?"

Tsoho yayi farin ciki da jin wannan magana ta wannan farke. Baisan sarkinsa bane' Ya ce, "Na yarda, ya shugabana."

Suka dunguma suka nufi kogin Dujillati, da suka isa, tsoho ya warware komarsa, ya jefa bisa ruwa, ta nutse kasa, ya jirkita ta, sannan ya jawo ta. Koma ta fito da akwati dake sarki me cika alkawarin saiya biya' kudin wannan akwati babba mai nauyi. Yayin da Halifa ya gan shi, ya dubashi shi, ya same shi nannauya. Ya ba masunci dinari dari, ya tafi yana murna.

Masruru ya dauki akwati tare da Ja'afaru suka nufi gidan Halifa. Da suka isa, suka kunna fitila, aka ajiye akwati saiya ciro mab'alli Halifa. Ja'afaru da Masruru suka karye murfin akwati suka tarar da kubba a ciki, an rufe ta da jan gashi. Suka yaye gashin, suka tarar da mayafi karkashinsa,

suka yaye mayafin, suka tarar da shimfida karkashinsa, suka yaye shinfidar, sai ga yarinya a kwance, kai ka ce narkakkiyar azurfa ce don kyau. An yanka ta gunduwa-gunduwa, ta kasance matacciya.
Yayin da Halifa ya ga wannan yarinya da irin kisan da aka yi mata, sai hankalinsa ya tashi, hawaye ya karyo masa yana gudana a kan kundukukinsa.

Ya waiwaya zuwa ga Ja'afaru cikin fushi mai tsanani, fushin da bai taba yin irinsa ba, ya ce da shi, "Ya karen wazirai, Wallahi ka cancanta da na kashe ka a cikin wannan lokaci. Kana wazirina har a kashe mutum, a saka a cikin akwati a jefa cikin kogi cikin zamanin mulkina. Kuna so wannan laifin kisa ya ratayu a kaina? Wallahi!

Babu makawa in bincika al'amarin wannan yarinya, duk wanda aka samu ya kashe ta, in kashe shi, in saka mata hakkinta."

Hankalin Ja'afaru ya tashi, domin bai taba ganin fushin Halifa kamar irin wannan ba. Halifa ya dube shi ya ci gaba da cewa, "Da girman saduwata ga dangin Halifofi na daga Banu Abbas, idan ba ka zo mini da wanda ya kashe wannan yarinya ba, in saka mata gare shi, Wallahi sai na rataye ka a kofar gidana, kai da mutum arba'in na daga 'yan uwanka!"

Ja'afaru ya ce, "Ka jinkirta mini zuwa kwana uku, ya Sarkin Musulmi!" Halifa ya ce ya jinkirta masa.

Ja'afaru ya fita daga gidan Halifa, ya nufi cikin birni yana mai bakin ciki, yana cewa a cikin ransa: Ina zan san wanda ya kashe wannan yarinya, har in hallara shi gaban Halifa? In na hallara masa wani wanda ba shi ya aikata laifin ba, aka kashe shi, alhakinsa ya ratayu ga wuyana ke nan, ni yanzu ban san abin da zan aikata ba. Ya nufi gidansa.

Ja'afaru ya yi zaune gidansa har kwana uku suka wuce. Rana ta hudu Halifa ya aika zuwa gare shi, yana nemansa. Yayin da ya zo gaban Halifa, sai ya tambaye shi, "Ina wanda ya kashe yarinya?"
Ja'afaru ya ce, "Ya Sarkin Musulmi, ni na san abin boye ne, ballantana na san wanda ya kashe yarinya?"

MUHADU GOBE DOMIN CIGABA02. HIKAYAR TUFFA UKU
(TALE OF THE THREE APPLES)

Halifa ya juya wurin dogarawa ya ba su umurni
su rataye Ja'afaru da 'yan uwansa. Tausayi ya
kama mutane, wasu suka fara kuka. Dogarawa
kuwa suka zabura domin cika umurnin Sarkin
Musulmi
Daga nan sai ga wani saurayi kyakkyawa, mai
kyawawan tufafi, ya keto daga cikin mutane da
gaggawa, ya zo ya durkusa a gaban Halifa. Ya
ce, "Ya Sarkin Musulmi, ni ne na kashe wannan
yarinya da kuka gani a
cikin sunduki. Kashe ni a madadinta, domin
daukar mata fansa."
Yayin da Waziri Ja'afaru ya ji zancen wannan
saurayi, da abin da ya bayyana daga zancensa,
ya yi farin ciki da kubutar ransa da na 'yan
uwansa, sannan kuma ya yi bakin ciki da
hukuncin da za a yi wa wannan saurayi. Halifa
ya yi umurni da a rataye wannan saurayi tunda
ya yi ikirari. Dogarawa suka cafe saurayi za su
rataye shi.
Daga nan sai ga wani tsoho mai yawan shekaru,
ya ratso ta cikin mutane yana kuka. Ya zo ya
durkusa a gaban Halifa ya ce, "Ya Sarkin
Musulmi, kada ka kashe wannan saurayi ba da
alhakinsa ba. Ni ne wanda ya kashe yarinya, a
kashe ni maimakonta."
Saurayi ya ce, "Ya Halifa wannan tsoho ya tsufa
da yawa,rudewar tsufa
ce ta sa shi yin wannan magana. Ni ne na kashe
yarinya, a kashe ni maimakonta, ku biya
alhakinta da ni."
Tsoho ya ce da saurayi, "Ya dana, kai yaro ne
kankane, yanzu ka fara sha'awar duniya. Ni na
girma na koshi da duniya, na fanshe ka na
fanshi Waziri Ja'afaru da 'yan uwansa, babu
wanda ya kashe yarinya sai ni. Domin Allah na
roke ku, ku gaggauta kisasi da ni."
Halifa ya dubi saurayi da tsoho ya ce, "Wanene
daga cikinku ya kashe yarinya?"
Saurayi ya ce, "Babu wanda ya kashe ta sai ni,
don haka a kashe ni."
Tsoho ya ce, "A'a, ni ne na kashe ta, don haka ni
ne ya kamata a kashe."
Da Halifa ya ji haka, sai ya ce a rataye su duka
su biyun. Waziri Ja'afaru ya ce a'a, mutum daya
ya yi kisan kai kuma a rataye biyu, wannan
zalunci ne ya Halifa.
Saurayi ya ce, "Da girman wanda ya daukak
sama, ya shimfida kasa, ni ne na kashe yarinya,
na sanya ta a cikin sunduki, na jefa sundukin a
cikin kogin Dujillati." Ya siffanta abin da aka
samu a cikinsundukin
majeranta. Halifa ya gasgata saurayi, ya kuma
tabbata shi ne ya kashe yarinya. Halifa ya yi
al'ajabi a kan wannan al'amari, ya tambayi
saurayi dalilin kisan yarinya.
Saurayi ya ce, "Ka sani ya Sarkin Musulmi, cewa
wannan yarinya matata ce, 'yar baffana. Wannan
tsoho shi ne ubanta kuma baffana ne. Na aure
ta tana budurwa, na sami zuri'a da ita 'ya'ya
uku, dukkansu maza. Ta kasance tana so na,
matsanancin so, tana yi mini biyayya iyakar
biyayya, da dai ba ta taba bata mini rai ba.
Ranar farko ta wannan wata, sai ta kwanta
rasahin lafiya mai tsanani. Na nemo masu
magani kala daban-daban, suna ba ta
magunguna har ta fara samun sauki. Ran nan
na shiga dakinta, sai ta ce da ni, tana son wani abu, domin tana
marmarinsa. Na tambaye ta menene shi? Ta ce
da ni, tana marmarin cin tuffa. Na ce zan siyo
mata.
Da fita ta daga dakinta, ban zame ko'ina ba sai
kasuwa wurin neman tuffa. Na zagaye kasuwa
duka amma ban samu ko daya ba. Na dawo
cikin gari ina cigiyar tuffa koda daya ta kasance
dinari daya in siya, amma ban samu ba. Na
kwana cikin wannan dare ina mai tunani.
Da gari ya waye na kara fita cigiyar inda zan
sami tuffa. Na hadu da mai sayar da 'ya'yan
itace, na tambaye shi tuffa, ya ce mini, tuffa ta yi
karanci yanzu, ba lokacinta ba ne, ba a
samunta ko'ina sai a cikin gonar Sarkin Musulmi
ta Basara.
Da na dawo gida, na shiga wurin matata, sonta
ya daukaka a gare ni. Na yi nufin tafiya Basara
wajen neman tuffa, daga nan Bagadada kuwa
tafiyar kwana goma sha biyar ne, amma ban
gaya wa matata ba, sai dai na fada mata zanyi
tafiya ta kwana talatin. Muka yi bankwana da
ita.
Na shirya na kama hanya, ina ta tafiya ba dare
ba rana, har kwana goma sha biyar, na isa
Basara. Na tafi wurin
mai kula da gonar Sarkin Musulmi, na siyo tuffa
guda uku, kowace daya a kan dinari daya. Na
juyo zuwa gida, na yi wasu kwanaki goma sha
biyar kafin na iso.
Bayan na iso gida, na shiga dakin matata na ba
ta tuffar guda uku, na fada mata inda na samo
su, da kuma kudin da na siyo su. Ba ta nuna
alamun farin ciki ba ko kadan da wannan kokari
da na yi. Ta karba ta ajiye su yashe a kasa.
Bayan 'yan kwanaki kadan ta warke sarai daga
rashin lafiyarta.
Ran nan na fita kasuwa, ina zaune a cikin
rumfata ina cininki. Daga nesa, sai na hango
wani bakin mutum a cikin rana, da tuffa a
hannunsa. Da ya zo ta
gaban rumfata zai wuce, sai na ce a zuciyata,
ina wannan bakin mutum ya sami tuffa a cikin
wannan gari wanda na zagaye ko'ina ban samu
ba? Bari in tafi ya fada mini inda ya siyo, idan na
tashi saye nan gaba ba sai na sha wahala ba.
Da ya zo dab da rumfata, sai na yi sauri na fito
na tare shi, na ce abokina ina ka siyo wadannan
tuffa, idan na tashi siya in tafi can in siyo?
Sai bakin mutumin nan ya yi dariya ya ce mini,
"Masoyiyata abar begena ce ta kai mini su har
gida. Ta ce mini lokacin da ba ta da lafiya,
sakaran mijinta ya tafi har Basara ya siyo mata
su, guda ukun nan a kan kudi dinari uku."
Lokacin da na ji zancen wannan bakin mutum,
ya Sarkin Musulmi, duniya ta yi mini baki kirin,
na ji babu wanda na tsana a raina kamar
wannan mutum da matata, maciya amana.
Amma ita ce mai babban laifi tunda har gida
take isko shi. Nan take na rufe shagona, na nufi
gida a fusace.
Da zuwana na tambayi matata, "Ina tuffar da na
siyo miki guda uku?" Ta ce da ni, ba ta sani ba,
ba ta kuma san inda suke ba. Tun daga nan
na gasgata zancen
bakin mutumin nan, bana tsaya na yi wani
dogon bincike ba. Idanuna suka rufe da
tsananin fushi da kiyayya.
Na tashi na dauki wuka, na hau bisa ga kirjinta,
na yanka ta da wukar. Na yanke kanta da
gabobinta, na yi mata gunduwa-gunduwa. Na yi
gaggawa na rufe ta da mayafi, na kunsheta a
cikin shimfida, na sa ta cikin kubba na rufe, na
sa kubbar a cikin sunduki. Da dare ya yi na
dauki sundukin na dora shi a kan alfadarata, na
tafi na jefa shi a cikin Bahrul Dujillati, babu
wanda ya sani, domin lokacin 'ya'yanmu sun tafi
gidan baffana.
Bayan na jefa sundukin a cikin kogi na dawo
gida,sai na tarar da a cikin 'ya'yana daya ya
dawo gida yana kuka. Na tabbata bai san abin
da na yi wa mahaifiyarsa ba, sai na tambaye shi, me yake yi wa
kuka? Ya ce mini, "Na dauki tuffar da ka siyo wa
mama, lokacin da ta shiga wanka, na fita ina
wasa da su a hannuna zan je gidan kaka, sai na
hadu da wani bakin mutum ya kwace su daga
hannuna ya ce ina na same su? Na fada masa
babana ne ya siyo wa mamata su lokacin da ba
ta da lafiya, duk daya a kan dinari daya, kuma
har Basara ya tafi neman su saboda sonta da
yake yi. Ya mangare ni, ya tafi da su. Ina jin
tsoro kada mama ta gane ni ne na dauke su ta
buge ni."
Yayin da na ji zancen dana, sai na tabbata lalle
bakin mutumin nan shi ne ya yanka zancen
karya game da matata. Na kashe ta a kan
zalunci, ba tare da ta yi mini wani laifi ba. Na yi
kuka, kuka mai yawa.
Ina cikin wannan hali, sai ga wannan tsoho,
mahaifin matata, ya rako sauran 'ya'yanmu. Na
labarta masa ga abin da ya kasance ga 'yarsa,
ya zauna a gefena yana kuka, ba mu gushe ba
muna kuka har tsakar dare. Muka yi zaman
makoki a wannan dare.
Bayan kwana hudu sai muka ji ana shelar
ratayewar Waziri Ja'afaru da 'yan uwansa, shi
ne muka zo, sai muka samu wannan labari. Ina
hada ka da girman Allah, ya Halifa, ka gaggauta
sa a rataye ni, domin biyan kisasi ga matata, ni
ina jin tsoron yin shari'a da ita ranar lahira."
Koda saurayi ya gama labarinsa, gaba dayan
jama'ar dake wurin idonsu ya cika da hawaye,
hatta Halifa sai da ya zubar da hawaye. Halifa
ya ce, "Na rantse da Allah ba ni kashe kowa face wannan bakin
mutum, funafuki, annamimi."
Halifa ya juya ga Ja'afaru ya ce, "Na ba ka
kwana uku, ka kawo mini bakin mutumin nan,
idan ba haka ba zan rataye ka, da 'yan uwanka
mutum arba'in." Jama'a duk suka watse.
Waziri Ja'afaru ya koma gida yana mai bakin
ciki, yana cewa a ransa, "Ta yaya zan iya nemo
wannan bakin mutum cikin dubban mutanen da
ke wannan birni? Na rantse da Allah ba zan fita
daga gida na neman kowa ba, Allah da ya kare ni daga halaka yanzu
shi nake roko ya kara yi mini mafita." Ya yi
zamansa gida har tsawon kwana uku bai fita
ba.

Zanci gaba03. HIKAYAR TUFFA UKU (TALE OF THE THREE
APPLES)

Koda saurayi ya gama labarinsa, gaba dayan jama'ar
dake wurin idonsu ya cika da hawaye, hatta Halifa
sai da ya zubar da hawaye. Halifa ya ce, "Na rantse
da Allah ba ni kashe kowa face wannan bakin
mutum, funafuki, annamimi."
Halifa ya juya ga Ja'afaru ya ce, "Na ba ka kwana
uku, ka kawo mini bakin mutumin nan, idan ba haka
ba zan rataye ka, da 'yan uwanka mutum arba'in."
Jama'a duk suka watse.
Waziri Ja'afaru ya koma gida yana mai bakin ciki,
yana cewa a ransa, "

Ta yaya zan iya nemo wannan
bakin mutum cikin dubban mutanen da ke wannan
birni? Na rantse da Allah ba zan fita daga gida na
neman kowa ba, Allah da ya kare ni daga halaka
yanzu shi nake roko ya kara yi mini mafita." Ya yi
zamansa gida har tsawon kwana uku bai fita ba.
A cikin kwana na hudu, Waziri ya kira alkalai da
shaidu, ya yi wasiyya ga 'ya'yansa da iyalansa, ya yi
bankwana da su, yana kuka suna kuka. Daga nan
sai ga manzon Halifa ya zo da sakon Halifa na
nemansa yanzu-yanzu. Manzon ya ce da shi, "

Halifa
ya yi fushi mai tsanani, kuma ya rantse wannan rana
ba za ta wuce ba face kana ratayayye, kai da 'yan
uwanka arba'in, muddin ba ka zo masa da bakin
mutumin nan ba."
Yayin da Waziri ya ji wannan sako na manzon Halifa,
sai ya sake fashewa...


Read / Download HIKAYAR TUFFA UKU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album