Join Our WhatsApp Group

DAKAKKIYAR ZUCIYA 1 and 2 Complete Hausa Novel Document by DAKAKKIYAR ZUCIYA 1 and 2


DAKAKKIYAR ZUCIYA 1 and 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17932



DAKAKKIYAR ZUCIYA 1 and 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 19, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 99.79 kb

File Type: txt

Views: 1602+

Download: 409+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: ★DAKAKKIYAR ZUCIYA★!!!
Abdul'aziz sani mad akin giñi
Littafi Na Daya (1)
Part A.
A WANI ZAMANI CAN BAYA MAI TSAWO DAYA
SHUDE,A BIRNIN KISRA ANYI WANI SAURAYI
MAI
SUNA SHUBAIRU IBINI HAURAS.Shubairu ya
kasance dan kimanin shekaru talatin da uku
kuma
Allah yayi masa baiwa da yawa.Abu na farko ya
kasance kyakkyawa na gaban kwatance domin a
gaba daya birnin Kisra babu wani 'da namiji mai
irin kyawunsa.Abu na biyu shine yana da tarin
ilmi na addinai kala kala har guda tamanin da
uku.Abu
na uku yana da wata irin baiwa wacce mutane
suka kasa gane asalinta domin tana kama da
tsafi
wasu kuma su kirata da suna TSATSUBA.Ita dai
wannan baiwa yanayinta shine ko da Shubairu
baisan mutum ba bai taba ma ganinsa ba da
zarar ya kalli fuskarsa zai iya ganin duk abinda
ya faru
ga mutum a rayuwarsa tun daga kuruciyarsa
kawo
izuwa girmansa har abinda ya aikata a wannan
rana.Idan kuwa ya dafa kan mutum da hannunsa
na hagu zai iya ganin irin daukakar da mutum zai
samu ko kaskanta nan gaba a rayuwarsa.Wani
abin mamaki shine duk da yana da wannan baiwa
bazai iya gayawa mutum abinda zaiyi ya kare
kansa ba daga abubuwan sharrin da zasu same
shi.Shidai Shubairu bai kasance dan kowa ba a
cikin birnin Kisra,ma'ana shi ba dan sarakai bane
ko attajirai ya kasance maraya don tun yana yaro
dan shekara shida iyayensa suka mutu a lokacin
da suka fita bayan gari kiwon dabbobinsu yan
fashi
suka kawo musu samame.Bayan yan fashin sun
kashe iyayeyn Shubairu sai suka fara kokarin
sace
dabbobin nasu su gudu dasu.Bisa sa'a saiga
dakarun sarki Kuzzaru sun fito kewaye.Koda
sukayi
arba da yan fashin sai suka fatattake su suka
gudu.Dama a wannan lokaci iyayen Shubairu sun
fito kiwo ne tare da Shubairu kuma wani iko na
Allah yan fashi basu kashe shi ba.Shidai
Shubairu
tunda yaga an kashe iyayensa saiya fado kasa
daga kan rakumi ya rinka tsala kuka.Bayan
dakarun sarki Kuzzaru sun kori wadannan yan
fashi sai sukaga kyakkyawan yaro na gaban
kwatance zaune a kas bisa ciyawa yana ta
kuka.Shugaban dakarun wanda ake kira da
Huzaika
ya tunkaro Shubairu yana mai kura masa idanu
cikin alamun tausayawa.Koda Shubairu yaga su
Huzaika sun durfafo shi saiya tsorata ainun ya
yunkura zai ruga da gudu.Cikin hanzari Huzaika
yace dashi tsaya yakai wannan yaro kada ka guje
mu domin mu ba masu cutarwa bane a gareka
mun kasance dakarun sarki Kuzzaru mai mulkin
wannan birni na kisra.Koda jin wannan batu sai
Shubairu ya koma ya zauna ya cigaba da yin
kukansa.Da isowarsu Huzaika daf da gawar
iyayen
Shubairu sai suka cika da mamaki domin
dukkansu sun gane Mahaifin Shubairu wanda ke
kwance a mace.Domin shine yake kai madarar
shanu a gidan sarki kullum da sassafe ana
biyansa
bayan kowane kwana talatin.Cikin matukar
mamaki
Huzaika ya sake duban Shubairu yace yakai
wannan yaro ma'abocin kyawun fuska mene ne
dangantakarka da wadannan mamata? Cikin
shesshekar kuka Shubairu yace IYAYE
NANE.Koda
jin haka sai Huzaika yaji ya kamu da tsananin
tausayin Shubairu don haka saiya durkusa a
gabansa ya share masa hawaye sannan ya rike
kafadunsa yace mene ne sunanka?Shubairu ya
fada
masa sunansa.Huzaika yace daina kuka yakai
Shubairu ka sani cewa yanzu zan dauke ka tare
da
wannan dukiya ta iyayenka na kai ku wajen
sarki.Tabbas sarkina mutum ne mai tausayi dajin
kai don haka nasan cewa bazai bari ka wulakanta
ba.Koda gama fadin haka sai Huzaika ya mike
tsaye ya dauki Shubairu ya dora shi akan dokinsa
shima ya hau kan dokin ya zauna sannan ya
umarci dakarunsa dasu kada wadannan dabbobi
izuwa gidan sarki.Dabbobin dai adadinsu bai
wuce guda ashirin ba.Guda goma sha biyu shanu
ne
kosassu ragowar guda takwas kuwa rakuma ne
manya lafiyayyu.Nan take dakarun suka cika
aikinsu aka nufi cikin gari.Fadar a cike take
makil
da jama'a ana tafiyar da harkokin mulki kamar
yadda aka saba.Sarki Kuzzaru na zaune bisa
karagar mulki fadawa sun kewaye shi a gefen
damansa kuwa matarsa ce gimbiya Lamrisa a
zauna ta caba ado na gaban kwatance kuma
gashi
ta kasance mai tsananin kyawu tamkar ita tayi
kanta.A wannan lokaci gaba dayan mutanen
dake
cikin fadar satar kallonta sukeyi kuma kullum
haka abin ke faruwa domin kowa ji yake kamar
ya
sureta ya gudu da ita.A wannan lokaci sarki da
fadawansa na cikin raha sai hira suke da dariya
cikin nishadi.Ita kuwa gimbiya Lamrisa fuskarta a
murtuke take.Fiye da shekaru goma sha daya
baya
babu wani mahaluki daya taba ganin murmushin
gimbiya Lamrisa.Shi kansa sarki Kuzzaru rabo da
yaga murmushin Lamrisa da dariyarta tun
shekarar
farko da sukayi aure saadda take amarya.Bayan
cikar shekara guda ne da taga bata sami haihuwa
ba ta matsawa sarki Kuzzaru akan shiga neman
magani da bincike wajen bokaye.Abinda binciken
ya tabbatar shine matsalar rashin haihuwa daga
gareta ne kuma har abada ba zata iya haihuwa
ba.A kalla an ziyarci bokaye dari ba daya duk
bayani iri daya sukeyi.Tun daga wannan lokaci ne
gimbiya Lamrisa ta kamu da tsananin bakin ciki
ya
zamana cewa kullim bata da aiki DARE DA RANA
face kuka.Saida ta kwana arba'in a cikin wannan
hali sannan sarki ya samo kanta da kyar da
taimakon bokansa har ta saki jiki ta cigaba da
rayuwa amma fa tun daga wannan lokaci ne aka
daina ganin murmushinta da dariyarta.Babu irin
kokarin da sarki Kuzzaru baiyi ba akan yaga
Lamrisa ta manta da batun matsalar rashin
haihuwarta amma abu ya gagara don haka saiya
hakura ya zuba mata idanu kawai.Ana cikin
wannan zaman fada ne aka ga sarkin yaki
Huzaika
ya shigo dauke da kyakkyawan yaro dan shekaru
shida a hannu.Nanfa kowa da kowa ya kurawa
yaron idanu cikin tsananin mamaki,ba wani abu
bane ya haddasa hakan ba face ganin yadda
kamannin wannan bakon kyakkyawan
yaro sukà zama iri daya dana gimbiya Lamrisa
tamkar itace ta haifeshi alhalin kowa yasan cewa
bata taba haihuwa ba.Sa'adda Gimbiya Lamrisa
tayi arba da yaro Shuhairu sai ta cika da
tsananin
mamaki kuma nan take taji ta kamu da tsananin
son sa a cikin zuciyarta.Lamrisa dai bata san
sa'adda ta mike tsaye ba ta taryi Huzaika ta
mike
hannu zata karbi Shubairu tana murmushi.Al'ama
rin dayai matukar baiwa kowa
mamaki kenan a cikin fadar aka bude baki ana
kallonta.Kawai sai akaji sarki ya daka mata
tsawa.Cikin razana ta tsaya cak ta kame kamar
gunki.Sarki Kuzzaru ya mike tsaye ya tako
kafafunsa yazo har gaban sarkin yaki Huzaika
fuskarsa a murtuke ba sassauci.Gaba daya
mutanen fadar saida suka tsorata domin kowa
yasan cewa idan ran sarki ya baci kowa sai yaji
ba
dadi.Duk da cewa ya kasance mutum ne mai
saukin kai,hakuri,tausayi da jin kai.Kai wasu ma
daga cikin jama'ar dake fadar tuni jikinsu ya
kama karkarwa saboda tsoron kada sarki ya
fusata ya
doka dirkar gini da hannunsa fadar ta rushe gaba
daya kowa ya hallaka tunda ya kasance
gagarumin
Sadauki mai karfin Allah ya isa.Sarki Kuzzaru ya
dubi sarkin yaki Huzaika a fusace yace yakai
dirkar
birnin Kisra a ina ka samo wannan kyakkyawan
yaro kuma mene ne dalilin da yasa ka shigo
dashi
nan fadata?Koda jin wannan tambaya sai sarkin
yaki Huzaika ya risina cikin biyayya yayi gyaran
murya sannan yace ya shugabana dazu bayan na
fita zagaye da safe tare da dakaru don tabbatar
da
tsaron gari kamar yadda ka umarcemu dayi
kullum sai kawai muka hango wadansu yan fashi
suna
kokarin kada wadansu dabbobi izuwa cikin
daji.Nan take muka sukwani dawakanmu izuwa
kansu ai kuwa suna hango mu sai suka tarwatse
suka ruga izuwa cikin jeji.Muna isa inda
dabbobin
suke mukayi arba da gawar mutane biyu,mace da
namiji.Namijin dai ba wani bane face Lunzaru
mai
kawo madarar shanu nan fada kullum da
safe,macen kuwa matarsa ce mahaifiyar wannan
yaro wanda muka tsinta zauna a kas kusa da
gawar tasu yana ta sheka kuka.Ya shugabana na
sani cewa kai mai adalci da jin kai ne bisa haka
ne na dauko wannan yaro tare da dabbobinsa na
kawo su gareka domin yaron yana bukatar
taimako
tunda yanzu ya zamana maraya.Sa'adda Huzaika
yazo nan a labarinsa sai kawai yaga hawaye ya
zubo daga idanun sarki cikin sanyin jiki sarki ya
sumbaci goshin Shubairu sannan ya karbeshi
daga
hannun sarki yaki ya mikawa Gimbiya Lamrisa ya
dubeta cikin murmushi yace karbi wannan yaro
yake matata yau kin sami mai kore miki bakin
cikin daya addabi zuciyarki tsawon shekaru goma
sha daya.Koda jin wannan batu sai fadar gaba
daya ta rude da shewa masu kade kade da bushe
bushe suka kama aikinsu.Ita kuwa gimbiya
Lamrisa saita rungume yaro Shubairu ta fashe da
kukan farin ciki ta ruga izuwa cikin gidan
sarautar.Sarki Kuzzaru ya koma kan KARAGAR
MULKI ya zauna sannan ya share hawayen dake
bisa kumatunsa ya dubi jama'ar dake cikin fadar
gaba daya yace yaku jama'ata kuyi sani cewa a
yau ina cikin tsananin farin ciki haka kuma ina
cikin matukar bakin ciki.Ba komai ne yasa nake
wannan farin ciki ba sai domin a yau ne matata
gimbiya Lamrisa ta fita daga cikin kuncin bakin
ciki na tsawon shekaru goma sha daya.Tabbas
wannan yaro da aka kawo zai kawar mata da
kewar
rashin haihuwa domin nasan cewa zata reneshi
kamar yadda zata reni dan cikinta.Dangane da
bakin cikin da nakeyi kuwa shine wannan talaka
nawa da yan fashi suka kashe wato mahaifin
Shubairu ya kasance masoyina na kwarai,a
duniya
ban taba samun mutum MAI KAUNATA ba
kamarsa.Tabbas akwai sirri mai karfi a tsakanina
dashi amma kuma ban isa na jawo shi jikina ba
shi yasa bakusan alakar dake tsakanina dashi
ba.Jin ya mutu ne na zubar da hawayena domin
nasan cewa na rasa masoyi wanda bazan taba
samun kamarsa ba.A iya sanina da Lumzaru ban
taba sani cewa yana da aure ba bare ma nasan
cewa yana da 'da.Ko shakka banayi yana boye
wannan kyakkyawan da nasa ne domin inda wani
ya taba ganinsa da tuni labarinsa ya cika
gari.Bisa
dalilin faruwar wannan al'amari daya faru a yau
na
tsintar wannan yaro na bayar da hutun kwana
bakwai a kasata kowa ya zauna a gida ya
huta,sannan kuma na bayar da umarni a sallami
dukkan tsofaffun fursunoni a dukkan kurkukun
kasar nan wadanda sukayi shekaru uku da
tsarewa.Haka kuma na shirya walima ta kwana
bakwai kullum dare da rana anan fadata domin
taya farin ciki bisa samun wannan yaro kuma ina
gaiyatar kowa da kowa,talaka da mai kudi,bawa
da basarake ban bambance ba.Koda jin wannan
batu
sai fadar ta sake rudewa da shewa mutane suka
kama farin ciki.Kamar yadda sarki Kuzzaru yayi
alkawari haka al'amura suka kasance wato saida
aka shafe kwanaki bakwai ana shagalin walima
dare da rana a cikin birnin kisra a gidan
sarauta.Talakawa,attajirai,sarakai da sauran
jama'a
kuwa suka rinka cincirindo a cikin gidan sarki
saboda yawan jama'a idan mutum ya dubesu sai
yayi zaton cewa mutanen duniyar ne kaf suka
taru
amma duk da wannan yawa na jama'a saida
abinci
da abin sha ya wadace su kai almajirai ma saida
suka daina barar abinci a tsawon wadannan
kwanaki bakwai.Daga wannan rana gimbiya
Lamrisa ta cigaba da renon yaro Shubairu ta
kaunace shi ainun tamkar itace ta haifeshi,dare
da
rana tana tare dashi babu abinda ke raba su.Duk
wani gata na duniya babu irin wanda Lamrisa
bata nunawa Shubairu ba,kullum idan tayi masa
wanka
sai ta caba masa ado irin na yayan sarakai.Kai
saboda tsananin son da Lamrisa ke yiwa
Shubairu
saida tasa wani gwani masassaki ya sassaka
gunkinta dana Shubairu wanda yayi matukar
kama
dasu aka ajiye gumakan biyu a tsakiyar katon
falon dake bangaren turakarta.Babu abinda zai
dada
baiwa
★littattafañ hausa
mutum mamaki face yadda gaba dayan mutanen
gari ke girmama Yaro Shubairu ya zamana cewa
ana kiransa da suna YARIMA.Shi kansa sarki
Kuzzaru nan da nan ya shaku da Shubairu yaji
kamar dan cikinsa ne amma duk sa'adda ya tuno
da cewar Shubairu bazai taba gadonsa ba sai ya
cika da tsananin bakin ciki ya kulle kansa a cikin
turakarsa yayi kuka ya more.Kullum idan sarki
zai
tafi fada tare da Shubairu yake tafiya,kuma wabi
abin sha'awa shine shiga iri daya sukeyi kuma ko
yaushe Shubairu na zaune daf dashi bisa karagar
mulki.Shi kansa Shubairu ya tsinci kansa a cikin
sabuwar rayuwa ta daula har ya rinka jin kamar
bai
taba rasa iyayensa ba saboda sa'adda iyayen
nasa
ma ke raye bai taba samun irin wannan daula ba.
WATA RANA da hantsi fada ta cika makil da
jama'a Shubairu na zaune daf da sarki saiga wani
mutum mai siffar attajirai ya shigo cikin fadar.Da
zuwan mutumin saiya fadi gaban sarki ya kwashi
gaisuwa sannan ya dago kai ya dubi sarki yace
ya
shugabana ni sunana Ubairu ibini Lauras kuma
na fito ne daga birnin Mirsa.Na kasance bafatake
mai
tarin dukiya don haka duk sa'adda zan fito
fataucina nakan fito da rakuma dubu dari gami
da
dakaruna mutum dubu hamsin masu tsaron
lafiyata
da dukiyata.Yanzu da hanya ta biyo ni ta kofar
birninka saina yanke shawarar na shigo cikin
birninka na yada zango kuma na baje kolina a
ranar da kasuwarku ke ci.A halin yanzu masu
gadin kofar birninka sun hanani shigowa da
rakuma na da kuma dakaruna,ni kadai suka bari
na shigo shine nazo neman alfarma a wajenka
domin
ka bani izini na shigo da hajata da
dakaruna.Yanzu
haka daya daga cikin masu gadin kofar garin ne
ya
rako ni izuwa nan fadarka domin yaji da bakinka
idan ka amince.Lokacin da attajiri Ubairu yake ta
wannan bayani Shubairu ya kura masa idanu.Nan
take idanun Shubairu sukayi jawur kuma fuskarsa
ta sauya yanayi daga annuri izuwa fushi.Har
sarki
Kuzzaru ya budi baki zaiyi bayanin amincewarsa
akan Ubairu ya shigo da dakarunsa da dukiyarsa
sai Shubairu ya tari numfashinsa yace Ya Abbana
inason na gana dakai a sirrance.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya kama kowa a cikin fadar
domin Shubairu bai taba tsoma bakinsa ba a
cikin
harkokin mulki sai yau.
da fatan xaku gafarcemu na dan rashin postin da
bamayi wannan ya damo Asaline saka makon
rasa wasu littattafan da mukayi da kuma
lalacewar computer mu.
★DAKAKKIYAR ZUCIYA★!!!

Littafi Na Daya (1)
Part B.
BAI TABA TSOMA BAKINSA BA A CIKIN
HARKOKIN
MULKI SAI A YAU.BA TARE DA GARDAMAR
KOMAI
BA SARKI YA MIKE TSAYE YA KAMA HANNUN
Shubairu suka koma can gefe daya inda babu
wanda zaiji abinda zasu tattauna sannan ya
dubeshi yace yakai dana me kake son zaka gaya
mini ne har da ka katse mini hanzari bisa
alfarmar
da wannan bakon attajiri yazo mini da ita?
Sa'adda
Shubairu yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar
zuciya cikin takaici yace yakai abbana ai wannan
attajiri wakili ne na babban makiyinka sarki
Farhama na birnin Kairufa.Ina tabbatar maka da
cewa hajar da yazo da ita bisa rakuma dari ba
komai bace face wadansu mugayen aljanu guda
dubu dari biyar wadanda idan har ka bari aka
shigo dasu cikin birninka sai sun hallaka gaba
dayan jama'armu.Sannan ayi maka juyin mulki
ayi
maka kisan gilla a kone dukkan wadannan
kyawawan gine ginenmu.Ya Abbana duk wannan
bayani danayi maka yanzu na ganshi ne akan
fuskar attajiri Ubairu a lokacin da yake gabatar
da
kansa.Ina so ka sani cewa a zahiri idan ka tura
aka duba wannan haja wacce attajiri Ubairu yazo
da ita babu abinda za'a gani face kayayyakin
karafa na dangin zinare da lu'u lu'u amma idan
mai karfin sihiri zai dubesu zai ga cewa wasu
muggun bakaken aljanu neLallai kasan matakin
da
zaka dauka akan wannan al'amari idan kuwa kayi
sakaci lallai karshen mulkinka yazo.Sa'adda yaro
Shubairu yazo nan a zancensa sai hankalin sarki
Kuzzaru ya dugunzuma ainun ya kurawa Shubairu
idanu cikin tsananin al'ajabi.Abu na farko shine
tabbas ya san cewa fiye da shekaru ashirin baya
sarki Farhama nata shirya masa mugun tanadi
don
ganin bayansa amma yana tsallakewa bisa
taimakon bokansa mai suna Zuraita Ibini
Laufur.Abin mamakin shine tunda aka tsinto yaro
Shubairu boka Zuraita bai sake zuwa fada
ba.Alhakin a da can duk bayan kwana uku sai
yazo
ya yiwa sarki bayani bisa abubuwan da yake
hangen zasu iya faruwa nan gaba a cikin
binciken
da yayi.To waishin menene ya hana Boka Zuraita
zuwa fadar a tsawon kwanaki arba'in da
bayyanar
Shubairu?Sarki Kuzzaru ya tambayi kansa a cikin
zuciya kuma ya kasa baiwa kansa amsa.Sarki
Kuzzaru ya sake tambayar kansa yace to wai
shin
shi wannan yaro Shubairu yaya akayi yasan
al'amarin Ubairu?Ni dai a sanina da mahaifin
wannan yaro bai kasance boka ba.A ina Shubairu
ya sami ilmin tsafi?Bayan sarki Kuzzaru ya gama
yiwa kansa wadannan tsauraran tambayoyi a
cikin
zuciyarsa saiya kawo gwauron numfashi ya ajiye
sannan ya dubi Shubairu cikin murmushi yace
yakai dana tabbas na yarda da duk wannan
jawabi
da kayi mini,dalili kuwa shine nasan mahaifinka
mutum ne mai gaskiya da amana kuma nayi
imani
cewa ka gaji halayensa don haka zanyi amfani da
wannan shawara daka bani lallai zan san matakin
dazan dauka a kai.Koda gama fadin haka sai
sarki
ya kama hannun Shubairu yaja shi suka koma
izuwa kan karagar mulki suka zauna.A wannan
lokaci gaba dayan fadar tayi tsit kowa ya
zubaido
kuma ya kasa kunne yaji abinda sarki zai fadawa
attajiri Ubairu tunda ba'a san shawarar da yayi da
yarima Shubairu ba.Bayan sarki Kuzzaru da
Shubairu sun zauna akan karagar mulki sai sarki
ya dubi attajiri Ubairu yace yakai wannan babban
bako ka koma can wajen gari wajen dukiyarka da
jama'arka ku kafa tantuna ku kwana acan lallai
kafin safiya zan yanke hukunci bisa
bukatarka.Koda jin wannan batu sai attajiri
Ubairu
yayi murmushi gami da godiya sannan ya mike
tsaye dan ya juya ya fice daga cikin...


Read / Download DAKAKKIYAR ZUCIYA 1 and 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album