Join Our WhatsApp Group

MATSATSUBI Book 2 Complete Hausa Novel Document by MATSATSUBI Book 2


MATSATSUBI Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33908MATSATSUBI Book 2

Reading Time: 2 Hours

Added On: 02, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 177.7 kb

File Type: txt

Views: 1091+

Download: 870+

Last download: 1 day ago

Description/Story: MATSATSUBI 2

Lokacin da su Jafar suka fada cikin shafi na goma sha shida KUNDIN TSATSUBA, wato bayan iskar cikin KUNDIN ta zuƙe su, sai suka tsinci kansu a cikin sararin samaniyar wata sabuwar duniyar, kuma a ƙudundune cikin wata irin gagarumar guguwa mai tsananin ƙarfi. Saboda ƙarfin guguwar sai da ya zamana cewa ta tale hannayensu da ƙafafuwansu. Gashin kansu ya tsefe sama kamar taron tsintsiya. Idanuwansu suka gwale, ƙofofin hancinsu da bakunansu suka ƙara girma, banda ihun azaba babu abinda suke yi.
Kwatsam sai suka ga wata surar fuskar
bil'adama a samansu wacce ta saje da kalar gajimare. Bakin surar ya wangame yana mai ƙyaƙyata musu dariya. Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin razana da fargaba kenan. Mazalish ta fara ƙoƙarin haɗe hannayenta biyu waje guda don tayi tsafi, amma sai abu ya gagara, domin ta kasa haɗe hannayen nata, saboda tsananin ƙarfin guguwar. Fuskar ta sake wangame baki a karo na biyu ta ɓarke da mahaukaciyar dariya mai tsananin firgitarwa, sannan ta ce,
"Nice GUGUWAR MASIFA, kuma nice GUGUWAR BALA'I, duk wanda ya ziyarceni sai na kai shi cikin mahallaka dubu. Kaicon ku waɗannan baƙi masu karambani, yau za ku san cewa karambaninku ya janyo kun tsokano tsuliyar tashin hankali irin wanda baku taɓa gani ba,kuma ba ku taɓa jiba."
Kafin wani daga cikin su Jafar ya iya buɗe bakinsa yace wani abu tuni wannan fuska ta bi jikin guguwar sun zama iri daya. Kawai sai Guguwar ta kanannaɗe su ta riƙe to da su ƙasa,
daga sararin samaniya, cikin tsananin gudu saida suka zo tsakiyar wata ƙatuwar teku, sannan Guguwar nan ta saki su Jafar ta ɓace.
Koda Jafar, Yelisa, Gulzum, Mashrila da
Mazalish suka ga an sake su za su faɗa cikin tsakiyar teku mai tsananin girma da faɗin da ba'a iya ganin ƙarshen tsawonta da faɗin ta sai duk suka rafka ihu. Kafin su tsunduma cikin tekun sai wani ƙaton, jibgegen kifi ya wangame
bakinsa suka faɗa ciki. Kawai sai kifin ya rufe bakinsa ya yi nutso izuwa ƙarƙashin ruwa ya ci gaba da tafiya abinsa.
Lokacin da su Jafar suka faɗa cikin bakin kifi suka biyo ta cikin maƙogwaronsa, sannan suka ratsa ta cikin hanji, tuni gaba ɗayansu sun fita
daga hayyacinsu, basu isa cikin kifin ba sai bayan tafiyar daƙiƙa ɗari uku da arba'in. A matuƙar galaɓaice suka faɗo ƙasan cikin kifin suka zube shararaf kamar tulin tsummokara, da ƙyar suka miƙe zaune sannan suka fara kalle-kalle cikin firgici da mamaki.
Jafar ya ƙare nazarin kayan cikin kifin tsaf sannan ya ce, "Yau kuma a tsakiyar shuke-shuken teku aka watsomu, yanzu ta ya ya zamu iya fita daga wajen nan nikam banga alamar akwai wata hanya ba."
Koda jin wannan batu sai aljani Gulzum ya bushe da dariyar ƙarfin hali sannan ya ce,
"Amma dai ka cika daƙiƙi kuma kidahumi(lallai ma Gulzum anyi ɗan iska😂😂😂ku ji pah,wai Jafar mutumin nawa yake kira daƙiƙi🙄🙄🙄,toh in akwai daƙiƙi a cikin su ai bai wuce Gulzum ba,ko ya kuka ce😂😂), wa ya gaya maka cewa nan acikin shuke-shuken
ƙarƙashin ruwa muke? To ka duba da kyau ka gani. Nan a cikin cikin kifi muke, tabbas rayuwarmu na cikin mugun hali domin ko zafin dake cikin kifin nan bai kashemu to kuwa yunwa da ƙishirwa sa kashemu, nan da kwanaki da baza su gaza biyu ba."
Koda jin wannan batu sai gaba ɗayansu hankalinsu ya dugunzuma kowa ya rasa abin da ke masa dadi.
Daga can sai Yelisa ta dubi Mazalish ta ce,
"Wai ke ina taƙamarki ta tsafi take? Me yasa baza ki cece mu ba daga cikin wannan masifar da muke ciki?"
Mazalish ta ce, "Ai kin san cewa gaba da gabanta ko? Inda tsafina zai iya cetonmu da tun kafin guguwar nan ta jefomu cikin tekun zamu kuɓuta."
Jafar ya mike tsaye ya duba gaba da baya ya jinjina kai ya ce, "Kai amma fa Ubangijin da ya halicci wannan kifi ya cika abin tsoro, ku duba fa ku gani sam-sam ban iya hango ƙarshensa.
Wai shin yanzu mene ne abin yi?"
Mashirila ta miƙe tsaye daf da Jafar suka fuskanci juna sannan ta ce, "Ni ina ganin babu abinyi face muje ƙarshen bindin kifin nan baza mu kasa riskar ƙofar da yake fitar da abin da ya ci ba, sai mu fita ta wajen."
Gaba ɗayansu suka yarda da wannan shawara don haka sai suka kama tafiya acikin cikin kifin suka nufi inda jelar kifin take a sahu guda.
Gulzum ne akan gaba sannan Jafar, Mazalish,Yelisa da Mashrila, sai da suka yi tafiyar sa'a guda sannan suka iso bindin kifin inda suka ga ƙofar da suke nema, nan take Gulzum ya zura
kansa ta cikin ƙofar da niyyar fita. Koda kifin ya ji wani irin raɗaɗi a bindinsa sai ya yi ta juyi yana mai ƙaraji. Gaba ɗayansu suka rikito suka hau tsinawa a cikin kifin, a haka suka yi ta ƙoƙarin fita amma abu ya gagara. Ƙoƙarin nasu ne ya gigita kifin yai ta juye-juye har ma ya fita da gudu sai daya iso gaɓar tekun sannan ya yi kakarin amai ya amayar da su gaba ɗaya don ya huta da azabar abin da ke kartarsa aciki, ai kuwa yana gama amayar da su ne ya koma cikin tekun ya nutse, kafin daya daga cikinsu ya sake dawowa haiyacinsa tuni guguwar nan tazo ta kanannaɗesu tayi sama da su tana mai ƙyalƙyala dariyar mugunta. Guguwar ta ci gaba da gudu ɗauke da su Jafar a sararin samaniya
har tsawon lokaci sannan ta sauko ƙasa ta watsar da su a tsakiyar wani makeken jeji.
Jeji ne mai yawan bishiyoyi, duwatsu, tsaunika da ƙoramai abin gwanin sha'awa sai wanda ya gani. Koda su Jafar suka tsinci kansu a wannan wuri sai suka cika da farin ciki don tsammanin cewa sun shigo wuri mai ni'ima wanda babu abubuwan tashin hankali a cikinsa. Abin da basu sani ba shine sunyi gudun gara sun faɗa gidan zago domin bala'in da ke cikin wannan jeji ya ninka na faɗawarsu cikin cikin kifin sau arba'in.
Nan fa su Jafar suka mimmiƙe tsaye suka isa bakin wata ƙorama kowa ya tsuguna ya jiƙa makoshinsa, sannan suka fara zuba ruwan ajikinsu don su ji ɗan sanyi, sakamakon ɗumamewar da jikinsu yayi a cikin kifi. Ai kuwa suna gama yin hakan kenan suka ga waɗansu abubuwa kamar manyan duwatsu sun kewaye jejin gaba ɗaya. Abubuwan suka rinƙa matsowa a hankali, ashe waɗannan abubuwa ba
duwatsu ba ne wadansu irin maridai ne masu tsananin girma, tsawo da faɗinsu ya wuce ƙima. Ƙaramin cikinsu shine wanda tsawonsa ya kai kamu ɗari, faɗin ƙirjinsa kuwa ya kai arba'in. Koda ganinsu sai hankalin su Jafar ya dugunzuma suka rasa abin yi, kawai sai Gulzum yayi tsalle sama ya kama reshen bishiya ya fara tsalle-tsalle da nufin guduwa, caraf ɗaya daga cikin maridan ya kamo Gulzum a cikin tafin hannunsa, maridin ya ɗago hannunsa ya saita Gulzum dai-dai fuskarsa ya ƙare masa kallo sannan ya ƙyalƙyale da dariya. A lokacin ne maridan gaba ɗaya suka tsaya ƙyam a waje ɗaya, wannan wanda ya kama Gulzum dama
shine mafi girma sai ya sauko da Gulzum ƙasa ya ajiyeshi kusa da su Jafar suma ya ƙare musu kallo sannan ya sake bushewa da dariya.
Daga can kuma sai ya waiga ya dubi
'yan'uwansa ya ce, "Ya ku ahalil Bauzuls yau fa mun fito farauta a sa'a domin munyi tsintuwar abin da muka daɗe muna nema shekara da shekaru wato jinsin aljan da mutum." Ko da jin
haka sai Jafar ya sha gaban Gulzum ya ɗaga kai sama ya dubi wannan maridi mai magana ya ce,
"Ya kai wannan basamudan maridi me yasa kuke neman jinsin mutum da aljan har tsawon lokaci, amma baku samu ba sai yau. Shin kana nufin mutane da aljanu basa shigowa dajin nan ne?" Sa'adda Jafar yazo nan a zancensa sai
maridin yasa dan yatsansa guda a cikin
kunnensa na hagu tamkar ansa guga a rijiya yayi susa.
Sannan ya sosa kunnen dama ya dubi Jafar ya ce, "Ya kai wannan karamar halitta me kake cewa ne wanda ban ji ba? Ina son ka sake maimaitawa." Koda jin haka sai daya daga cikin maridan ya zaro wani ƙaho dake saƙale a ƙugunsa ya ajiye shi a gaban Jafar tamkar ya ajiye ƙaton kwale-kwale. Ya ce da Jafar yasa bakinsa a bakin bututun ƙahon sannan yai magana. In ba haka ba kuwa sarki ba zai ji muryar sa ba. Koda Jafar ya doshi wannan ƙaho sai ya fuskanci cewar ai ƙofar dake bakin ƙahon ma takai faɗin ƙatuwar rijiya. Kawai sai ya zura kansa gaba ɗaya a cikin ƙahon ya
maimaita maganar daya faɗi ɗazu. Ai kuwa sai nan take muryar Jafar tayi kauri kuma ta cika jejin gaba ɗaya da amsa kuwwa. Al'amarin da ya janyo tarwatsewar namun dajin dake wajen
kenan, gaba ɗaya duk suka kama gabansu.
Sarkin maridan ya yi murmushi mai kama da kukan jaki ya ce, "Ba komai ba ne yasa muke neman jinsin aljan da na mutum face maganin wata masifa data addabe mu shekara da shekaru, ya ku waɗannan ƙananan halittu kuyi sani cewa dani da jama'ata mun fi shekara dubu sittin acikin wannan daji kuma tunda muke zaune a nan bamu taɓa ganin jinsin mutum da aljan ba, sai sau ɗaya tsawon waɗannan shekaru. A halin yanzu akwai wata cuta da take addabarmu kuma mun kasa samun maganinta, wannan cuta itace ta rashin haihuwa, matanmu ko sun sami ciki baya zama,kai koda ya tsufa sai dai rana guda aga ya ɓace. Gaba ɗayanmu nan mu dubu ɗari bakwai ne da saba'in da bakwai. Tsawon waɗannan shekaru dubu sittin bama haihuwa kuma bama mutuwa, wato dai bama raguwa kuma bama ƙaruwa, kimanin shekaru ashirin da biyu baya wani hatsabibin aljani yazo nan neman wasu abubuwa na sirrikan tsafi. Sunan wannan aljani SHAMHARU, lokacin da yazo mana mun rufar masa gaba ɗaya don mu hallakashi amma muka kasa. Bayan ya tilasta mu mun samo masa abubuwa biyar da yake da buƙata sai muka roƙe shi da ya taimaka mana bisa cutar data addabemu ta rashin haihuwa.
Nan take ya sanar damu cewa ba zamu fara haihuwa ba har sai mun samo jinin bil'adama kimanin cikin kwanson kabewa babba guda uku da kuma jinin aljan cikin ƙaramin kwanson kabewa. Idan muka haɗa wannan jini guda biyar
waɗanda muka samo masa, mu da masu gaba ɗaya, kowa daga cikinmu sai ya lakaci wannan tsumi ɗan kaɗan ya lashe,tabbas idan muka yi haka zamu rinka haihuwa amma kuma zamu rinƙa mutuwa. Da yawanmu tsufa ya fara zame mana cuta don haka muna bukatar mutuwa,babu yadda ba muyi ba akan mu rage yawanmu ta hanyar kashe junanmu amma abu ya gagara
domin duka,yakushi,sara da suka basa tasiri a jikinmu. Yau gashi mun tsinci dami a kala wato mun sameku don haka yanzu, yanzu bada wani ɓata lokaci ba zamu kama ku mu tafi daku
izuwa gidajenmu inda zamu yankaku mu tara jininku acikin kasko guda don hada wannan magani. Mukam wahalar mu da baƙin cikinmu ya ƙare daga yau."
Kafin ɗaya daga cikin su Jafar yace wani abu tuni an damdamƙesu an tafi da su. Nan take maridan nan suka kama kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe suka nufi wani katon dutse mai tsananin girman gaske.
Su dai su Jafar tuni sun sallama rayuwarsu don sun tabbatar da cewa babu mai cewa yanzu mu shi kenan haka ƙarshenmu zai kasance.
Ai kuwa mun sha wahalar duniya a banza kenan,mu ba muyi suna ba kuma bamu sami matsayin komai ba."
Ita kuwa Mashrila sai tace, "Ni kam inda nasan hakane zata faru a gareni da nayi zamana acan garinmu na mutu acikin irin masifar da ta addabe mu."
Mazalish tace, "Ni kam mutuwata anan ta fiye mini alheri akan na rayu a matsayin mayya mai shan jinin bil'adama."
Jafar ya share hawayensa yace, "Ni kam babban abin baƙin cikina shine zan mutu banga abin dake cikin shafin karshe na KUNDIN TSATSUBA ba."(😲😲😲😬😬😬😬😬ho Jafarun mu🤣🤣🤣🤣🤣j jama'a kunji halin mutumin naku ko🤣🤣🤣.)
Ko da jin haka sai Gulzum ya yi tsaki yace,
"Amma dai kai Jafar ka cika banza mara tunani,in banda rashin hankali da hauka irin naka wane ne zai yi fatan ya karance wannan tsinannen littafin.
Kaga mu bala'in da muka sha a baya ma ya ishemu. Ai gwarama waɗannan maridan su kashe mu huta da fargabar sauran masifun dake jiranmu."
Haka dai su Jafar suka ci gaba da
surutai na tausayawa kansu har maridan nan suka iso gaban wannan tafkeken dutse.
Da zuwa sai su Jafar suka ga ashe a jikin wannan dutse maridan suka gina gidanjensu.
Ba wai gini aka yi akan dutsen ba,a'a dutsen aka ƙwaƙule akayi ɗakuna.
Abin mamakin shine,gaskiyar
al'amarin shine da kaifin faratan hannaye maridan akayi wannan gagarumin aiki.
Da zuwa sai aka sauke su Jafar aka ɗaɗɗauresu tamau da igiyoyi ajikin wasu turaku na dutse,daga nan gaba ɗayan maridan suka kewaye wani ƙaton kasko wanda girmansa ya kai a sanya bil'adama dubu a cikinsa.
Nan take aka cigaba da kiɗa ana rera wata irin waƙa mai daɗin sauraro kai kace mutane ne masu nutsuwa suke waƙar.
Jafar ya dubi Yelisa yace, "Ya ke Yelisa haƙiƙa ina mai matuƙar baƙin ciki da ya zamana zamu mutu ba tare da kun cika burin zuciyarmu ba,amma ina jin daɗi cewa zamu bar duniya a tare muna masu kallon junanmu,in ba don nasan mutuwa zan yi ba da nace wannan kiɗan da waƙar sun isa su gusar mana da takaicin duk irin wahalar da muka sha a baya."
Mashrila tace,
"Ya kai abin begena ni kam indai
dai ace kai ne ka rigani mutuwa da tabbas haɗiyar zuciya zanyi na mutu,amma tun da dai tare zamu mutu ba zanyi takaici da nadamar
komai ba.
Kuma babu mamaki mu sake haɗuwa a wata duniyar dabam muyi sabuwar rayuwa."
Koda jin haka sai kishi ya turnuƙe Yelisa suka fara kace nace.

(Kutttttt😳😳😳 lallai yaran nan a gaishe su,suna gaf da mutuwa amma ta kishi suke😂🤣🤣)

Mazalish ta dubesu ta bushe da dariya tace,
"Haƙiƙa kukan daɗi kuke yi kawai saboda ganin masoyinku a kusa daku yanzu ni da ban san a inda nawa yake ba kuma ban san a inda zan riske shi ba,ai sai dai naci gaba da kuka tunda gashi ma yau zan bar duniyar gaba ɗaya."
A dai-dai wannan lokacin ne suka ga an ɗebo wani garin magani kala biyar an zazzagesu duk a cikin ƙaton kaskon nan.
Daga nan kuma sai wani ƙaton maridi ya dubi sarkin maridan yana
mai tambayar wanda za'a fara kashewa daga cikin su.
Sarkin maridai yai nuni ga aljani
Gulzum.
Koda ganin hakan sai Gulzum ya fashe da kuka yana baiwa Yelisa wasiya cewar,
"Idan ta koma duniyarsu ta nemi iyayensa ta sanar dasu yadda ya kasance kuma ta nema masa gafararsu domin ba'a son ransu ya bar gida ba,ya shiga duniya."
Yelisa ta zubar da ƙwalla don tausayi da sabo tace,
"Ya kai Gulzum ai abin da ya same ka shine zai same ni sai dai muyi hakuri gaba daya."

(😂🤣🤣🤣🤣. Su Gulzum anga mutuwa🤣)

Kafin wani daga cikinsu Jafar yace wani abu tuni ƙaton maridin nan ya suro Gulzum,igiyar da ta ɗaure shi ta tsitstsinke,da hannu ɗaya
maridin ya aza Gulzum a saman ƙoƙon sannan ya ɗaga ɗaya hannunsa ya kaiwa maƙoshin...


Read / Download MATSATSUBI Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

4 months ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album