Join Our WhatsApp Group

HATSABIBIN TSIBIRI Complete Hausa Novel Document by HATSABIBIN TSIBIRI


HATSABIBIN TSIBIRI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 44142



HATSABIBIN TSIBIRI

Reading Time: 3 Hours

Added On: 27, Nov 2023

Author: Safiyya Mrs J Moon ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08132166848

Book License : Paid

Category: Adventure novels

File Size: 237.12 kb

File Type: txt

Views: 1233+

Download: 641+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: [1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIRI.
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association (AWA)

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1

(Hatsabibin tsibiri kagaggen labari ne, ba'ayi shi dan wani ko wata ba in anci karo da abinda ya yi daidai da rayuwarka/ki alkalami ne ya zo da salon. Labarin zaiyi nutso ne cikin wata rayuwa mai ban al'ajabi na matsafa tare da wata ƙasaitacciyar masarauta da magajinsu ya shigo da salon da tun ginuwarta tayi hannun riga da lamarin. Duhu, Haske, Ƙarya,Gaskiya, Zalinci, Tausayi, Halarci,Butulci, Sadaukarwa, son mulki bakin rai bakin fama gami da tasirin riƙo da Addini duk na ƙunshe cikin tafiyar Mrsjmoon a cikin wannan labarin na Hatsabibin tsiri.

Ya Allah ka lamuncemin na rubuta abinda zai amfani al'umma. Allahumma Amin.

*Littafin baki dayansa sadaukarwa ce ga aminaina masu dubun karamci a gareni wato Khadija Candy da Rahma Kabir, Allahu ya ja wannan zumunta har zuwa gidan Aljanna mu zamo makwaftan juna Alfarman sayyidul sadati Manzon Allah S.A.W. Amin.*

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Allah ka karo dubun salatai marasa irga ga masoyinnan naka, shugaban Halittu baki ɗaya abin alfaharin salihan bayi, jagoran mabudin alkhairai, Abul Fad'imatul Zahra'u Sayyiduna Muhammadur Rasulullah S.A.W.

Page 01

Tekun Kabobo.

Teku ne mai faɗi da tsawo wanda ya ke cikin k'ungurmin dajin da ke yammacin Hatsabibin tsiri kuma gabashi da Masarautan birnin Mungaye.

Ruwan Tekun na da abin al'ajabi domin da safe zuwa rana kalansa blue ne amma idan marece ya shiga sai ya koma fari k'al wanda mai gani kan iya hango halittun da ke rayuwa a ƙasanshi na shawagi dan k'asansa na dauke da halittun da ke rayuwa a ruwa nau'ika daban daban, kama daga Kadoji, Kifaye da sauransu haka yashi da tsirrai koraye duk suna bayyana a fili ga duk wanda ke iya kawo ziyara da yamamcin.

Duk wannan girma da Tekun ke da shi gami da yawan ni'ima ya zamo hange daga nesa ga Fulani makiyaya domin basa iya isa gab'an shi balle tsautsayi ya kai dabbobinsu su shan ruwansa, hasalima basa biyo hanyar sai bisa makuwa inda suna farga da dimuwan da sukayi zasu sanja hanya tare da kare hanyar da dabbobin zasu isa zuwa gab'an Tekun domin jugewa samun asara dan duk wanda ya yi kuren isar bisashensa bakin Tekun zasu afka ciki tamkar waɗan da aka tura. Hatta da mafarauta ba kowa ke shiga dajin Tekun ya dawo lafiya ba sai in har ya kai kwaro wurin tsafi tamkar irin tsirarun jama'ar Hatsabibin Tsibiri. Sai kusan shekaru biyu da ya gabata Gimbiya Lina d'iya ga Sarki mai mulkin Hatsabiban Tsibiri ta maida Tekun muhallinta shi ya janyo matsafan sukayi nesa da Tekun domin girmama muradin mafi soyuwar Gimbiyarsu.

***
Guguwar iska ce ta turnik'e sararin samaniya dajin ya koma bak'ink'irin tamkar ruwan sama na daf da sauka domin ba sautin da ke tashi sai gunjin fitar iska wanda guguwar ta ke kad'awa da mugun k'arfi gami da tashin duk abin da taci karo da shi zuwa sararin samaniya, abin mamaki har da ƙananun duwatsu iskan sama ta ke yi da su tamkar ledoji. Ƙara gami da rugugi kawai ke tashi abinda ya haddasa rud'ewar tsun-tsayen da ke saman bishiyoyin da suka kewaye Tekun soma neman wurin tsira.

A daidai wannan lokacin Gimbiya Lina na zaune a saman ruwan Tekun Kabobo ta hard'e kafafunta saman kujera mai ruwan zuma tamkar ta hau saman dutse kamar yarda wurin da ta ke zaunen ya nuna babu alamun ruwa mai motsi balle igiyarshi ya wuce da ita ta zamo abin kalacin halittun ruwan.

Ga dai shi ruwan Tekun na tsiri gami da kumfa na gudu cikin murd'ewar igiyoyi sai dai kafin ya iso inda ta ke zaune ya ke sanja hanya ya zagayeta ya nausa gaba inda ke isa tsakiyar Tekun ya rufe dutsen da ke tsakiyarshi ruf zuwa wasu sakonni dutsen ya bayyana tamkar ruwan bai tab'eshi ba.

Murmushi ta saki cike da nishad'in ganin yarda ruwan Tekun ke wasanninsa, jin rugugin ya ƙi ƙararewa sai ta d'aga kai ta tsirawa sararin samaniyar ido na tsawon sekon goma sannan ta sauke kallonta kan fatar jikinta da ya ke bud'e ba sutura sai walwali ya ke yi cikin d'aukan ido tamkar jikin tarwad'a, sake kallon giragizan ta yi da suke k'ara yin duhu sai ta shafi fatar dantsen hannunta na hagu tare da kallon halittan k'irjinta masu ban sha'awa da cika domin ita kanta in ta kallesu suna burgeta saboda zubin da Allah ya yi musu na kyawu gami da jan hankalin duk wanda ya yi arba da su. Shafosu ta yi da hannun dama idanunta lumshe sumar idanunta na d'igar da ruwa na bin saman kuncinta. Girgiza kai ta yi sumar kanta ya yi tsiri sama ya fesar da ruwa sannan ya dawo ya rufe mata fuska zuwa saman k'irjin, ta yaye sumar da hannunta na hagu tare da sake kallon sararin samaniya a tak'aice ta kauda kai gefe cikin had'e fuska.

"Lima kenan, tabbas neman maganarki ya yi yawa, sam bakya son a zauna lafiya, kin addabi'a al'umma tsibiri kin kuma hanani watayawa a can, to ai shi kenan mu zuba mugani, domin jiya ba yau ba, Gimbiya Lina ta tumbatsa matuk'a, zata baki mamaki dan haka bari in nuna miki kaɗan ya ke Gimbiyar da bata kai a ambata mata sunar ba."

Ta furta a hankali tare da jan tsaki mai sauti ta nuna guguwan da tafin hannunta wani haske ya soma fita daga tsakiyar hannunta na nufar iskan, aikam tamkar kiftarwar ido sai ga sararin samaniyar ya washe tangaras, ta sauke numfashi tare da share gumin da ya tsats-tsafo mata a saman goshi sai ta mike a saman ruwar ta yi nutso cikin Tekun, kujerar da take zaune ya zama walk'iya ya b'ace haka ruwan da ke sanja hanya a inda take zaune ya samu damar biyowa na kai da kawon shi.

Bak'ar tsun-tsuwa ce mai yarfin ja a fuska-fuskanta ta baiyana gefen Tekun zuwa can ta bud'e fuka-fukan ta soma shawagi a saman Tekun zuwa kimanin 'yan mintoci sai ta zama bak'in hayak'i ta b'ace.

Gimbiya Lina da ta nutse cikin kogin sai da ta sami kimanin mintoci goma sha biyar sannan ta taso sama ta soma tafiya tamkar tana taka turb'aya dan yarda k'ura ke bin bayan takalmi idan ana tafiya a kan sa to haka ruwan ke tartsi na bin diga-digan Gimbiya Lina, wanda suke farare sol tamkar yarda fatar jikinta ya ke.

Tafiya ta keyi tamkar wacce ke filin gasar sarauniyar kyau dan cikin k'asaita ta ke takun abin da ya bawa mazaunanta da ke cikin siririn pant damar motsawa tamkar ba ita ce mamallakinsu ba dubi da yarda take mara k'iba su kuma gasu da fad'i gami da cika tare da fitar da shape na musanman tamkar wacce aka zana su a jikinta.

Ta yi tafiya har zuwa tsakiyar Tekun sannan ta tsaya jikin k'aton dutsen ta bud'e hannayenta tamkar walk'iya ta rikid'a zuwa balbela fara sol ta tashi sama zuwa wani tsauni da ke kusa da Tekun tana sauka ta yi girgiza ta dawo halittarta na Bil'adam ta yarfe yatsunta biyu saiga sutura ya baiyana a jikinta cikin shigar doguwar rigan yadin karan miski fari da ratsin ja tare da takalmin fata half cover mai launin Sarauta shima fari ta mik'a hannu jan gyale mai yarfin fari ya baiyana saman tafin hannunta ta nad'e kanta da shi ya zauna d'as, ta sake mik'a hannu kwalban turaren Company mai daraja mai suna LOST IN YOU ya baiyana ta fesa tare cilli da shi sama ya b'ace wani kwalban turare fari sol tamkar ruwa ya bayyana ta kai bakinta ta b'alle murfin ta kafa a bakinta ta shanye tas tare da cilli da kwalban ya zama walk'iya ya b'ace ta had'a hannayenta wuri d'aya ta manna a saman goshinta tare da kulle ido tana wani surutai saiga wata budurwa mai kama da ita sak tamkar an tsaga kara ta baiyana cikin shiga mai kamanni da nata, suka tsirawa juna ido kowa da karatun da ruhinsa ke kitsawa masa.

Gimbiya Lina ce ta kawo k'arshen shirun da cewa "Ba kya jin magana ko Lima? Shin wai har sai yaushe zan daina yi miki gargad'i akan shigomin yanki batare da neman izininta ba?"

"Baki isa ba Lina kuma bazaki tab'a isar ba, yankinki ko yankina? Ko kin manta ne in tuna miki? Ni ce mai k'arfin iko sama da ke dan haka kada ki sake yimin tsaurin ido domin zan hukuntaki tamkar uwar gijiya da baiwarta, dafatan kin tuna tazararmu da juna na sanin alkaliman sihiri."

"Oh rigimar na ki ta nan ya b'ullo? To zan barmiki nan amma ki sani duk ranar da kika k'ara binciko inda na ke sai kin raina kanki domin yanzu ba da ba ne, na ga ba ya yi ga ba na baya kam sai tsintar hula sannan ina baki shawara ki koyi yarda ake magana da shugaba kada ki sami matsala nan ba da jimawa ba domin Gimbiya Lina ce gabanki sarauniyar Hatsabibin Tsibiri lokaci kaɗan mai zuwa."

"Haka zalika nima Gimbiya Lima ce a gabanki wacce kowa na tsibiri ke tsoron karo da ita domin bata san wargiba aiki da cika ne takenta ko da kuwa ga jininta ne sannan magajiyar karagar Hatsabibin Tsibiri batare da wasi-wasi ba."

"Na yaro kyau take bata karko amma bari in barki ki gama cika bakin naki sai 'yar nanuniya ta nuna shugaban wani a tsakaninmu ba da jimawa."

Dogon tsaki Lima ta ja tare da kaiwa kafadar Lina duka cikin cewa
"Ke dalla ni rufemin baki ki zauna ki sanarmin da inda kikayi b'atan dabo na tsawon shekara d'aya da rabi, kika barni da jidalin rabuwa biyu duk in Abun ya nemi ganinmu a lokaci d'aya domin bana son b'acin ranshi idan ya gano bakya Tsibiri zai iya sauke fushin a kaina."

"Binciken ki ya bayyana miki inda na je tunda bazaki fita sabgata ba kamar yarda ba ruwana da naki sannan baruwana da fushin Abun dama Mah kika ce to na duba lamarin."

"Idan kin isa ki cire hijabin da kika sanya a tafiyar naki kisha kallon tonon silili kamar yarda na tabbatar cikin jikinki da kika tafi da shi d'an kwanaki talatin da bakwai wanda kika b'oye haihuwarsa kuma fushin Abun ya dad'e bai dameki ba idan kinso kice ba shi ne makyen-kyashinki ba daga sama kika fad'o."

Jim Lina ta yi tana kallon 'yar uwarta zuwa can ta motsa labba ta ce "Lima sharrin da zakiyimin kena, na Haihuwa? A she tsanar naki har ya kai haka? Ni ce fa Linar da ta tsani ak'idarki na bilayi a gidan hutu, shin me yasa zaki jefeni da lamarin da kika san ban taɓa sha'awar aikatawa ba?"

Kinfi kowa sanin ban iya sharri ba domin abin da nake da tabbacin shi na kanyi zantuka a kansu sannan kin fi kowa sanin ina kan gaskiya, tabbas kin bar Tsibiri da ciki dan haka maza sanarmin ko ranki ya b'aci, yanzu na aikaki gaban Abun ba sutura ki fuskanci hukunci."

"Zama bak'ar guguwar da kika zo a cikinsa ki b'acemin da gani ko in illataki sannan ki sani na wuce gaban barazanarki, jiya ba yau ba ce Lima na sake sanar da ke wannan kalman kuma ki saita harshenki kada ki fusatani na aikata miki abinda zai taɓa min domana ( rai)."

"Kome zakiyimin bazan kauce ba sai na san gaskiyan da kika b'oye kuma shi ne dalilin da yasa na rufa miki asiri ban sanarwa Abun labarin bakya cikin Tsibiri ba domin ina son na soma hukuntaki kafin ya yi miki
nashi."

"Saboda na zama karyan maza irinki ba, mara yiwa kanta amfani?"

"Lina in magana kike son faɗamin kin makaro domin kaf sirrikanki a tafin hannuna suke dan haka ki biyoni mu koma tsibiri ko infasa kwai kowa ya san halin da kika kasance na yin cikin da baida sahihin uba sannan da ƙarfi akayi miki kika b'oye wanda yayi saboda kina yiwa jama'a bakin cikin samun ganimar jinin shi."

"Ko yanzu lokaci bai k'ure miki ba maza tafi ki tona asirin domin ban shirya komawa Tsibiri yanzu ba ko wannan ganin da kikayimin wani dalili ya sanyani fitowa duniyar tsirrai dan haka yanzu zan koma dausayin sanyi na cigaba da rayuwa tare da hallitun ruwa masu amana."

"Aikam kin gama komawa k'asan Tekun Kabobo Lina tunda ke ba aljanar ruwa bace haka ban san ta inda kika haɗa dangi da 'yan ruwa ba."

Dariya Lina ta bushe da shi tare da zama a saman wata kujera mai haske da ta bayya gabanta tamkar kiftarwar ido wanda haskenta ya kashewa Lima ido ta k'are da tafin hannunta tana ja baya, hannu Lina ta kai ta rik'o hasken tamkar igiya haka ya shige tafin hannunta sannan Lima ta samu damar dauke hannayenta daga saman fuskanta ta zubawa Lina ido wacce ke cin kayan lambu da suka bayya gareta cikin wani container mai d'aukan ido shima.

"Lina banda tsafi da muka gada kin koma ruwa biyu ce?"

Bata amsa ba illa murmushi da take dokawa cikin jijjiga kai.

"Wani Aljani kika samu ya baki sa'a irin wannan? Ko shi ne wanda ya yi miki cikin?"

"Lima idan baki daina ambatar cikin nan ba zan sab'a miki."

"Zamu sab'awa juna dai Lina domin baki isa b'oyemin halin da kika fad'a ba kuma duk takunki ban k'yaleki sai kinyimin bayanin inda kika b'oye ko rayuka su b'aci."

Kayan marmarin ta watso mata cikin fushi Lima ta yi sauri daga hannu suka tsaya cak batare da sun iso inda ta ke ba haka basu sauka k'asa ba. Numfashi su sauke a tare sannan suka ja baya ko wacce rai a haɗe zuwa can suka juya baya sannan suka juyo da makamai rik'e a hannunsu cikin gaggawa ko wacce ta nufi 'yar uwanta da nufin halakawa. A ta ke k'azamin fad'a ya b'arke tsakaninsu, guguwa ya turnik'e ya rufesu ruf baka ganin kowa cikinsu sai fitar sautin takubba tare da walk'iyar hasken sukan da suke kaiwa juna. Bayan wucewar mintoci goma sha biyar sautin ya d'auke gami da washewar guguwar, wurin ya koma babu su sama ko ƙasa.

Takun ingarman doki ne ya ratso saman tsaunin da ya sanya itatuwar tsaunin soma fad'uwa ƙasa zuwa can wani gabjejen Sadauki ya bayya zaune a saman dokin ya iso ya tsaya a daidai wurin da Lina ta zauna yana bud'e k'ofofin hansa sai kuma ya diro ya shafi dutsen gefen da ta jingina da shi ya sunsuna ya soma waige-waige sai ya juya da hanzari sai ya kaiwa inda Lima ta tsaya duka sauti ya fita dum! Ya ja tsaki sai kuma ya zabura ya hau saman dokinsa ya nausa cikin tsaunin da mahaukacin gudu dokin na sakin haniniya wanda ya hargitsa k'ananun haluttun tsun-tsaye.

***
Lima ce ta soma bayyana jini na zuba a gefen kanta zuwa can itama Lina ta bayya dafe da kafad'arta jini na bin hannunta, a tare suka kalli juna ko wacce ta shafi inda taji ciwo a take ya koma babu alamun rauni suka sake kallon juna ko wacce taja...


Read / Download HATSABIBIN TSIBIRI

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album