Join Our WhatsApp Group

RANA DA WATA Book 2 Complete Hausa Novel Document by RANA DA WATA Book 2


RANA DA WATA Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11713



RANA DA WATA Book 2

Reading Time: 0 Hours

Added On: 21, Nov 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 65.95 kb

File Type: txt

Views: 593+

Download: 180+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: RANA DA WATA
Littafi na biyu 2
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih Usman
Post:- Shuraih 99%
Part A
.
.
Lokacin da su tsohuwa shafhila suka shafe rabin sa'a suna tafiya a wannan daji mai dauke da mugayen maridai masu cin bil'adama, sai suka zo wucewa ta gaban wata katuwar tukunya wadda aka girke ta da wasu manyan itatuwan wuta suna ci ganga-ganga
.
Yayin da suka ga haka sai sabitul agadawur yayi masu nuni da hannunsa alamar kowa yayi shiri da barin yin wani motsi
.
Tsohuwa shafhila tana ganin wannan katuwar tukunya,sai hantar cikinta ta kada, sai ta koma tsakiyar wannan ayari, tana mai tsananin lura da sauraren dukkanin wani motsi dake tashi a wannan lokaci
.
Ahaka har suka shafe rabin sa'a suna tafiya batare da sun hadu da wani abu na cutarwa ba,
Kwatsam ba zati ba tsammani sai suka ga wadansu maridai masu tsananin yawan gaske sun tare masu hanya ba damar wucewa
.
Su dai wadannan maridai sun Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% kasance dogayene suna da tsawo wanda ya kai kamu arba'in, idan mutum ya tsaya a gabansu sai kaga kamar wani tsauni ne a gabanka
.
Koda su tsohuwa shafhila suka ga wadannan maridai, sai wani wanda yafi kowa tsoro acikinsu ya kurma wani uban ihu da dukkanin karfinsa saboda tsabar kidimewa da razana da yayi sa'adda yaga wadannan maridai
.
Lokacin da wannan matsoracin yayi wannan ihu, sai gaba dayan wadannan maridai suka juyo tare da barin wawason da suke akan wadansu mutane shida da suka kamo, suna juyawa ai kuwa sukayi arba da ayarin su tsohuwa shafhila
.
Take sai wani maridi dake kusa da wannan mai tsoron yai saurin sa hannunsa mai kamar shafcecen shebur ya dauke shi ya jefa abaki yana taunawa,
.
Sa'adda maridin ya dauki she, sai ya kasance kamar ya dauki wwani dan karamin tsuntsu ne, al'amarin daya dugunzuma su tsohuwa shafhila da su sabitul agadawur kenan.
Ai nima shuraih Shuraih 99% sai da na tsorata ainun
.
Suka kidime kowannnensu jikinsu ya kama karkarwa maridin daya jefa matsoracin nan abakinsa ya taune, ya hangame baki yana wata irin hamma wadda ta haddasa wata guguwa ta bayyana mai karfi tana daukar duk abinda ba shi da kwakkwaran nauyi
.
Sannan yace da wata irin murya mai kamar rugugin hadari,
"Hakika wadannan mutane sunfi duk wadanda muke kamawa zakin nama,saboda haka mutafi dasu a kowacce rana mu ringa karyawa da su har su kare"
.
Lokacin da su tsohuwa shafhila suka ji haka, sai gaba danysu hankalinsu ya tashi, nan take sai manyan sadaukai da jaruman dake tare da su, suka zaare takobi da niyyar su afkawa wadannan maridai ayi ta takare
.
Koda ganin haka sai daya daga cikin maridan ya bushe da dariya yana mai tsuntsirewa akas, sannan yasa hannu ya rarumi mutum goma daga wadannan Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% sadaukai da jarumai yai wurgi da su, bisa ga dole kowa ya nutsu aka daina samun masu taurin kai a cikinsu
.
Batare da bata wani dogon lokaci ba sai wadannan maridai suka tasa keyar ayarin su sabitul agadawur zuwa wani katon kogon dutse wanda dama anan ne suke aje duk wanda suka kamo
.
A lokacin da aka kaisu wannan wuri sai suka iske wadansu jarumai majiya karfi su hudu a daddaure da wata katuwar igiya wanda sai mutum dari su hadu ba tare da sun iya koda tsinka rabin ta ba
.
Maridan suka kebe ayarin su tsohuwa shafhila daban ba tare da sun hada su da wayannan zaratan jarumai ba , sannan suka mirgino wani katoton dutse suka toshe hanyar da ake shigowa wannan katon kogo
.
A wannan lokaci ne nadama da dana sanin wannan tafiya tazo wa gaba daya ayarin, tsohuwa shafhila tafi kowa razana da kasancewar wannan lamari, take ta tuna Shuraih Usman Shuraih 99% mai typing yayanta wadanda suke tsananin gaba da junansu wadanda saboda ta samu hadin kansu ne ta sayar da dukkanin kadarorinta ta taho da niyyar ta sama masu hanyar da zasu san cewa sufa yan uwa ne na jini
.
Kuma su hada kansu wuri daya ba tare da sun kara nuna tsana da matsananciyar gabar dake tsakaninsu ba
.
Kashe gari da safe sai ga wadannan maridai sun shigo , suka debi mutun dari daga yarinsu tsohuwa shafhila zasu tafi dasu koda suka zo kan tsohuwa shafhila sai wani maridi ya kura mata ido yana kallonta
.
Al'amarin dayai matukar tayar mata da hankali kenan, batare da yace da ita komai ba sai kawai suka fita tare da wayannan mutane da suka deba a matsayin kalacin su na wannan safiya
.
Yayin da wadannan zaratan jarumai dake daure cikin igiyya , suka ga tashin hankalin da su tsohuwa shafhila suka shiga sakamakon zuwansu wannan waje da suka Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% fidda rai da ci gaba da rayuwa, sai daya daga cikinsu wanda ake kira da suna zahakim yai magana da murya yadda duk wanda yake kogon dutsen zaiji ya fara da cewa
.
"Yaku wadannan mutane ku sani da zaku yadda da wata shawara da kuwa mu da kuu din nan mun kubuta daga sharrin wadannan maridai"
Yayin da tsohuwa shafhila da sabitul agadawur da sauran mutanen da ke tare da su , sai tsohuwa shafhila tayi saurin amsa masa tana mai cewa
.
"Me zai hana mubi ko wace irin shawara ka zo mana da ita koda kuwa hakan daidai yake da halakarmu gaba daya, kasancewar zamanmu a cikin kogon dutsen nan shima halakane"
.
Koda zahakim yaji wannan bayanni daga bakin tsohuwa shafhila sai yayi murmushin karfin hali yace da ita, Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%
.
"Mu hudunnan da kuke gani yau kwananmu tara a cikin wannan kogon dutse, kuma wadannan maridai sun kasa cinyemu ne saboda dalili daya, nalura akwai wani maridi daga cikin su wanda yana da matukar tausayi da jinkai, baya sin ganin ana halaka mata ko kadan, atakaice ma zai iya bujirewa sauran maridan ya yakesu idan suka dage akan cewa lallai sai an halaka mata a wannan kogon dutse
.
A gaban idonmu yazo ya kubutar da wasu mata dake tare damu a lokacin da aka kamamu, kasancewar wannan dabi'a ta wannan maridi, ina mai tabbatar maku da cewa lallai zai dawo garemu ayau dinnan da dare, saboda wannan tsohuwar da kuke tare da ita
.
Sai ku kwance mu tun yanzu domin da zarar ya shigi muyi masa kwab daya mu halakashi, sannan mu tsre kafin gari ya waye munyi masu nisan da ba zasu taba cimmana ba"
.
Koda zahakim yazo nan a zancensa Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% sai gaba daya suka amince da wannan shawara tasa , sai kuwa suka taru gaba dayansu kowannensu ya zare takobin da ke tare dashi, suka kama aikin yankan wannan katuwar igiya da aka daure wadannan zaratan jarumai
.
Sai da suka shafe fiye da sa'a biyar sannnan suka smau nasarar tsinke duk igiyar da aka daure su, take kowannensu ya mike tsaye sukayi wata doguwar mika, zahakim kasancewarsa musulmi sai yai godiya ga Allah daya kubutar da shi daga wannan dauri, ya kuma rokon ubangijinsa daya kubutar da shi daga sharrin wayannan maridai masu cin naman mutane
.
Haka kuwa akayi bayan dare ya raba sai ga wannan maridi ya mirgino wannan katon dutse da aka rufe kofar shigowa kogon ya shigo ciki, sannan ya maida ya rufe yana yan dube dube,
.
Adai dai wannan lokacin zahakim da sauran jaruman dake Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% tare dashi, suka zare takobins dake tare da su suka yunkura da tsananin shammata, kafin wannan maridin ya ankara , sai kawai yaji sun kai masa sara da dukkan karfinsu
.
Take sai zahakim da wadannan jarumai sukaji kamar sun sari karfe , su duk suka zube a kas, wannan mariidi yasa hannu ya dauko tsohuwa shafhila daga inda take, sannan ya zahakim da bille can gefe daya
.
"Nazo a gareku ne ba da niyyar na cutar da daya daga cikinku ba, ku sani daga yau zan kauracewa wannan daji da muke ciki, na rantse da iyayena babu abinda zai same ku muddin kuna tare dani, sai na kubutar da ku bazan bari daya daga cikin yan uwana su samu sa'ar sake kamaku ba
.
Hakika maridan nan yan uwana sun cutar dani saboda sun kashe matata dana fi so aduniya fuye da komai,
Akan wannan daliline na daura damarar kubutar da duk wata mace kasancewata ina mai tsananin Shurraih Usman inkiya Shuraih 99% tausayawa rayuwar mata , kuma zan taimaka maku sai inda karfina ya kare " yayin da su tsohuwa shafhila dasu jarumi zahakim suka ji wannan batu, sai wani farin ciki mara adadi ya lullubesu, nan take gaba dayansu kowa yasa ran zai samu biyan bukatar abinda ya fito nema
.
Daga nan babu wanda ya kara cewa komai sai kawai wannan maridi ya ture wannan mulmulallen dutse da ake rufe kogon
Sannan ya fara fita daga bayansa tsohuwa shafhila ta biyo bayansa,
Sannan gaba dayan sauran mutanen da suka rage suaka bi bayansu zuwa waje suna masu tsananin lura da kowane motsi da ke tashi a wannan waje
.
. *** .
Lokacin da huzainu ya tabbatar da muddin yayi sake tofa wannan runduna ta sadaukai masu siffa irinta zuhaisa zasu iya gamawa da shi farat daya, sai ya fusata da fushi irin wanda bai taba yin irinshi ba take Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% duk wani gashin jikinsa ya mimmike, dantsensa suka dada kumbura kamar zasu fashe, yai wata kururwa da tsananin karfin muryarsa, wadda gaba dayan dajin ya girgiza da amsa amon wannan kururuwa ta sa
.
Sannan huzaini ya sake daidata rikon takobinsa yaci gaba da saransu babu ji babu gani, aduk lokacin daya yunkura ya sari daya daga cikin sadaukan , sai dai kawai kaga ya tsarge ta gida biyu,
.
Dada yawaita suke da zarar ya kashe su, haka nan ma sadaukan masu siffa irinta zuhaisa dada karuwa suke fiyeda farko
.
Da zabbabu yaga abin ya nemi yafi karfinsa, sai ya kasance aduk lokacin daya yunkura yasa takobi dakai sara a tsakiyar sadaukan, sai yayi kalmar shahada tare da kai saran a tare
.
Sai ya kasance duk wadda ya sara bata da wowa, haka nan kuma babu wadda zata tashi ballantana ma su dada yawaita awannan lokacin
Kai nafa gaji da typing, amma dai barin dan kara jajircewa Shuraih Usman Shuraih 99%
.
Koda zabbabu ya fahimci haka sai ya dada zage dantse yana mai kai sara a kowane yanayi cikin kwarin guiwa da jarumta , cikin wani dan kankanin lokaci,
.
Sai daya kasance zabbabu ya samu nasarar kashe da yawa daga cikinsu sa'adda huzainu yaga irin yadda zabbabu yake kashe su, yana karanta wata magana da ambata wata kalma da baya fahimtar komai yake fada, da tafiya tayi tafiya sai huzainu ya rika ambatar kalmar da yaji zabbabu yana ambatawa a lokacin da yake kai sara ga wannan sadaukai masu siffar zuhaisa
.
Ai kuwa sai yaga shima yana samun nasarar tsargesu suna kamawa da wuta su kone kurmus su zama turbaya ba tare da wata ta samu sa'ar tashi ba
.
Huzainu da zabbabu suka kasance suna masu tsananin kai sara da suka cikin zafin nama da sadaukantaka, bayan dakika dari biyu da hamsin, sai ga shi huzainu da zabbabu sun samu nasarar kashe gaba Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% dayan sadaukan babu wanda ya tsira daga cikinsu
.
Zabbabu ya dubi huzainu yana mai murmushi, kafin daya daga cikinsu ya damar cewa daya komai, sai kawai sukaji an kyalkyale da dariya, take huzainu ya gane muryarta, zuhaisa ce nan take ta bayyana a gabansa tana mai nuna sa da yatsa
.
"Kada kayi tsammanin ka samu nasara ka gama da wadannan sadaukai dana hada ka da su kayi zaton cewa ka rinjaye ne, wannan ya kasance shine mataki na daya daka haye daga cikin matakai miliyan dubu dana dauka a kanka
.
Ina mai rantsuwa da darajar iyayena, a karo na gaba ba zaka samu nasarar tsallake matakin da zan dana maka ba koda zaka hada kai da duk jaruman duniya gaba dayansu"
.
Yayin da zuhaisa tazo nan a zancenta, sai kawai ta bace ba tare da saurari wani lafazi daga dan uwanta huzainu ba,
.
.
Yo anan zan tsaya Daga naku Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%
Mamallakin shafin hausaebooks
Da keffians News Teller
Sai mun hadu a part 2RANA DA WATA
Littafi na biyu 2
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih Usman
Post:- Shuraih 99%
Part B
.
.
Lokacin da zuhaisa ta bace sai zabbabu ya dubi huzainu yace dashi,
"Yakai jarumi huzainu hakika ba karamar kiyayya ke tsakaninka da wannan yar uwa taka ba , kasancewar naga tana neman halakaka ta kowwace hanya .
.
Ina mai kyautata zaton ta hada kai da manyan bokaye hatsabiban gaske, saboda haka nake shawartarka daka biyoni izuwa kasata wadda can na tabbata zuhaisa bata da ikon shigowa har can da niyyar ta cutar da kai"
.
Koda huzainu yaji haka sai yace da zabbabu
"Yakai zabbabu ka sani bana shakka kojin tsoron duk irin makircin da zuhaisa zata shirya mani, ka sani zuhaisa ta kasance tun muna yara kanana bama ga maciji da ita, har izuwa lokacin da kowannenmu karfi yazo masa daga nan kuma sai muka shiga farautar juna da son hallaka juna
.
Hakika zuhaisa ta kasance azzaluma mara tausayi Shuraih Usman inkiya Shuraih 99% ko kadan wannan shine dalilin daya sa ba ma shiri da ita sam, saboda na zamo mutum mai sanyin rai da taimako ga mutane mara gata a kasarmu, hatta mahaifiyarmu bata jin dadin irin wannan matsananciyar gaba dake tsakaninmu, amma na daukarwa kaina alkawarin duk lokacin da zuhaisa ta sake zuwa gare ni a bisa mummunar aniyarta a kaina , sai na halaka ta ba zan taba bari taci gaba da rayuwa ba muddin tana nan kan bakarta"
.
Daga nan suka kama tafiya cikin daji zabbabu yana mai yiwa huzainu jagora har suka dauki hanyar da zata sada su kasar gayyar inda a yanzu zabbabu yake sarauta
.
. *** .
Dawwara yana tafe kan wani ingarman doki yana mai tsananin tsala gudu kamar zai tashi sama , baya saurarawa komai a wannan muhimmiyar tafiya tasa,
.
Tun bayan da boka gayyar yaga ma shiryasa ya ba shi wata alkyabba ta tsafi yasa sannan SHurarih Usman inkiya Shuraih 99% ya bashi wasu guraye ya daura su a dantsensa, sannan ya kama tafiya baji babu gani wanda ayanzu ya shafe kwanaki arba'in yana tafiya batare daya hadu da wani mugun abu ba kan hanyarsa
.
Dawwara ya...


Read / Download RANA DA WATA Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album