Join Our WhatsApp Group

MAGAJIN WILBAFOS BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by MAGAJIN WILBAFOS BOOK 1


MAGAJIN WILBAFOS BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 153993MAGAJIN WILBAFOS BOOK 1

Reading Time: 12 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 841.1 kb

File Type: txt

Views: 407+

Download: 887+

Last download: 2 days ago

Description/Story: MAGAJIN WILBAFOS
Fita na daya 1-50
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
GABATARWA
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.

Kimanin ƙarfe sha biyu na rana, akan wani tsauni dake
kan doron ƙasa ta biyu, waɗansu mutane guda uku, ke ta
tafka gudu a tsakankanin wasu bishiyun giginya acikin
wani daji mai yawan duhuwa.
Biyu daga cikinsu sanye suke da jan sulke, sannan kuma
haye suke kan ingarman dawakai fasalin danda, ɗaya
kuma wanda shi ne na tsakiyarsu yana sanye da sulke
ruwan ƙasa akan ingarma fasalin dandan-akwal.

Kana ganinsu kasan akwai gajiya da raunika a tattare
dasu, amma kuma a lokaci guda haɗe da wannan gajiya
akwai dagiya da kafiya irin ta mutanen farko, wadda tasa
ko kaɗan wannan gajiyawa bata sa sun rage azabar
gudun da suke ba.
Can bayan wasu ƴan daƙiƙu, na ɓangaren daman ya
buɗe bakinsa wanda kana gani zaka tabbatarwa kanka
cewa ruwa ya daɗe bai shiga ciki ba, saboda tsananin
bushewar da yayi, ya ce, "shugaba, suna gab da
cimmana, mai ya kamata muyi?"
Yana faɗar wannan magana yana juya kansa bayansu,
kamar wanda yake karanta wani abu a bayan nasu, duk
da kuwa babu abinda ake gani a bayan nasu sai zallar
duhu. Wanda idan ka kula sosai zaka ga abin mamaki ne,
saboda duk da ranar dake tsakiyar sama, bata iya haskaka
wajen. Hasalima kamar ƙara masa duhu take.
Duk da kasancewar dukkanin fuskokin waɗannan
sadaukai uku a rufe suke, amma dai-dai wajen idonsu a
buɗe yake kana iya ganin idonsu tar-tar, ta cikin wata ƴar
tsaga da akai domin gani.
Mutun biyun dake gefe idanunsu a buɗe suke, sai kuma
na tsakiyar tasu, wanda duk da azabar gudun da suke
amma idonsa duk biyun a rufe suke!
Acikin idanun na ɓangaren damar akwai wani abun
mamaki, wanda ba wani abu bane, illa cewa babu baƙin
ido kwata-kwata acikin idon, sannan kuma a dai-dai
wajensa an maye gurbinsa da alamun hoton takobi
launin baƙi.
Ko kuma zaka iya cewa tunda ita ma takobin launin baƙa
ce, baƙin cikin idon nasa ne ya juye izuwa zanen wannan
takobi.
To koma dai meye acikin tsakiyar idonsa maimakon
baƙin ido, babu komai sai baƙar takobi.
Na tsakiyar tasu wanda shi wannan na ɓangaren dama ya
kira da shugaba, idonsa a rufe yake saboda haka babu
damar ganin menene aciki.
Amma na gefen hagun idanunsa a buɗe suke, kuma zaka
iya cewa sunfi kama dana mutane, idan aka kwatanta
dana ɓangaren daman, duk da kuwa cewa suma idan ka
kula zaka ga akwai wani haske da suke fitarwa a duk
sanda ya ratsa ta cikin duhu, kamar yadda na mage suke
yi da dadaddare.
Wannan jarumi na tsakiya shiru kawai yai baice komai
ba, har tsahon kusan daƙiƙa talatin, bayanda daga bisani
yayi magana cikin wata murya mai cike da wata Izza irin
ta sarakunan farko, "na yanke shawara!
"Wannan Izzar zanyi amfani da ita!
"Ina da buƙatar tsahon lokaci kimanin zuwa sanda rana
zata faɗi kafin na gama!
"Yanzu tambayar ita ce.. zaku iya kare kogon can daga
Ururu shida, har zuwa wannan lokaci?" Yana mai nuna
wani kogon dutse da bashi da nisa daga inda suke,

sannan kuma a lokaci guda yana kallon wanda yai masa
tambayar.
"Zamuyi iya ƙoƙarin mu shugaba!" Ita ce kawai amsar da
suka bashi a tare.
Ba jimawa suka ƙaraso wajen wannan kogo daya nuna,
inda ba tare da ɓata lokaci ya shige ciki kai tsaye, su kuma
waɗannan mutun biyu dake gefensa suka tsaya abakin
wannan kogo.
Kallo ɗaya tak zakaiwa yanayin tsaiwar da sukai, kasan
cewa babu wanda a cikinsu yake da niyyar ɗaga ƙafa
daga bakin wannan kogo indai yana da ragowar
numfashi.
Ba daɗewa waɗansu mutane su ma su uku, suka bayyana
a bakin wannan kogo kamar an cillosu daga sama.
Kana jin irin iskar dake tashi daga jikinsu kasan akwai
sarauta acikinta, sarauta da Izza irin na sarakunan farko.
Kallon farko zakai tunanin malamai ne sanye da baƙaƙen
kaya, amma idan ka lura sosai zaka gane cewa kayan jikin
nasu bawai baƙaƙe bane, amma akwai wani abu a jikin
fuskarsu wanda ke zuƙe haske dukkanin abinda ya
kusance shi, kamar yadda suna bayyana a wajen, gaba
ɗaya ko'ina ya fara yin duhu, duk da kuwa rana tana
tsaka.
Idan ka matsa kusa dasu zaka fuskanci cewa lallai da
gaske akwai wannan abu a jikin fuskarsu wanda ke zuƙe
haske kowanne iri ne, ba wani abu bane illa idanunsu,
wanda suka kasance baƙi-ƙirin, babu alamar fari ko
kaɗan acikinsu.
Ajikin fuskar kowannen su akwai irin waɗannan baƙaƙen
idanu guda biyu, wanda idan ka haɗa zaka ga akwai guda
shida kenan a tare dasu.
Kallon ɗaya kacal zakai koda kuwa daga nesa ne, ka gane
cewa waɗannan idanu na musamman ne; gaba ɗaya farin
cikin idon ya juye ya koma baƙi wuluk, tayadda idan ka
kalli idon ba abinda zaka gani sai baƙi. Irin baƙinnan mai
sawa kaji kamar za'a zuƙe ka ciki idan ka kalla, saboda
tsananin duhu.
Duk da cewa dukkanin cikin idon baƙi ne, amma idan ka
lura sosai zaka fuskanci cewa tsakiyar idon yafi ko'ina
baƙi, hasalima banbancin baƙin dake tsakanin biyun
kamar banbancin sama da ƙasa ne.
Saboda wannan tsakiyar idanu har baƙar kala suke
amayarwa idan ka lura sosai.
Saboda haka nema abu ne mai sauƙi mutun yai kuskuren
cewa cewa tsakiyar idon ne kaɗai baƙi.
Wannan irin idon shi akewa laƙabi da URÚRÚ!!
Babu ko magana ɗaya data faru a tsakanin ɓangare biyun
banda kallon gaba kawai sama da daƙiƙa sittin.
Kafin daga bisani na tsakiyar ma'abota wannan baƙaƙen
idanu da akewa laƙabi da Ururun ya dubi na ɓarin
damansa, wanda kana ganinsa zaka ga alamun ƙarancin
shekaru a jikinsa, ya ce, "Uznu, ka lura sosai, zaka koyi

abubuwa da dama, kasan bazan dauwama a gefenka ba
ko!"
Sannan ya juyar da kansa ya dubi waɗannan mutun biyu
dake tsaye a bakin wannan kogo zare da takubban jan
ƙarfe, cikin izgili ya ce, "shekara goma kenan kuna gudu,
sai yau kuka ga dama kuka tsaya!! Hah!
"Bana buƙatar naji dalilin tsayawarku, dan bashi da wani
muhimmanci, abu ɗaya dana sani shi ne da tsayawarku
anan, da kasancewar cewa lallai yau zaku ziyarci lahira,
kaf abubuwa ne wanda haka sarki Dumaƙisu
Kuyurussa'ayi ya ambata zasu faru!"
Wannan ita ce magana ta ƙarshe data faru tsakanin
waɗannan ɓangaro ri guda biyu, kafin daga bisani
azababben faɗa ya kaure a tsakaninsu. wannan faɗa ya
shafe dogon lokaci yana afkuwa, kuma babun wanda
yasan adadin tsahon wannan lokaci sai waɗanda ke
wajen!
Wannan abu ya faru ne a shekara ta 1469 bayan Amri!
Saboda tsananin azabar wannan faɗa daya afku a wannan
shekara har bayan shekara ɗari biyar baya, babu wata
halitta data ƙara iya rayuwa a wannan dajin, wanda ada
ke daga cikin dazuka mafiya girma a dukkan ƙasa ta biyu.
Babu ko kiyashi daya rage bayan wannan faɗa wanda zai
iya bada labarin yadda faɗan ya kasance, sai mutun ɗaya,
wannan ma'aboci Ururu da aka kira da suna Uznu.
Kuma shima bayanda aka gama faɗan, ya isa doron ƙasa
ta farko domin ya kaiwa sarki Dumaƙisu Kuyurussa'ayi
bayanin abinda ya faru, baice komai ba, banda cewa sun
isar da aikin da aka basu.
Sai dai kuma daga baya, bayan ya dawo hayyacinsa ya
bayyanawa sarki Dul'Ururu, shugaba bisa doron ƙasa ta
biyu cewa wannan mutun daya shiga cikin kogon nan
kafin a fara fafatawar ya bar wata takobi bayan
mutuwarsa, wadda keda ban mamaki!
Ya bayyana cewa a ɓangarenta guda akwai rubutu wanda
bai iya karantawa.
Kuma koda sarki Dul'Ururu ya tambayi ko mai yasa bai
ɗakkota ba, sai ya bayyana masa cewa yayi ƙoƙarin
hakan, amma yana kusantar ta, ta juye izuwa wani ɗan
ƙaramin littafi wanda baifi girman hannu ba, kuma ta
ɓace ɓat.
Ya neme ta tsahon kwanaki, badan komai ba sai dan kallo
ɗaya yai mata yaji ta shiga ransa, amma babu yadda ya
iya haka ya haƙura ya tafi!
Ya dai bayyana cewa tunda wannan al'amari ya faru,
Uznu ya shiga halwa ta neman Izza, tsahon shekaru masu
yawa har saida aka manta dashi!
Shekara bayan shekara, sama da shekaru ɗari biyar da
sha ɗaya sun wuce, da dama daga cikin mutane da suka
rayu a wancan zamani sun daɗe da mutuwa, kai hatta
jikokinsu basa nan.
Wannan mutun da ake kira da Uznu'Ururu ya ƙara

bayyana, inda ya jagoranci yaƙi zuwa doron ƙasa ta
bakwai akan wasu masu adawa da salon mulki na
shugaba Dumaƙisu Kuyurussa'ayi, shugaba bisa doron
ƙasa ta farko.
Yaƙin da ya ɗauki watanni ana fafata shi, kafin daga bisani
nasara ta faɗa ɓangaren Ururu!
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 1: Armad djin ko Armad Wilbafos
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Yaƙin daya afku a wannan shekara tsakanin Uznu'Ururu
da kuma jama'un doron ƙasa ta bakwai, ya haɗa harda
sauran ƙasashe da dama.
Wasu suna goyon bayan Ururu, wasu kuma al'ummar
ƙasa ta bakwai.
A ɗaya daga cikin ƙauyukan dake ƙasa ta uku shashin
arewa, wadda akewa laƙabi da Kanyú, da dama daga
jama'ar wannan gari sun ziyarci wannan yaƙi daya
wakana, kuma akai sa'a da dama sun dawo gida bayan
kammala yaƙin.
To amma duk da haka duk fuskar wanda ka kalla acikin
wannan gari zaka babu annuri kwata-kwata a tattare da
ita, duk da cewa da dama daga cikin su iyalunsu sun
dawo!
Ba wani abu bane ba kuwa ya janwo hakan ba, ill abinda
ya faru da wannan jarumai bayan dawowar su daga
wannan yaƙi.
Wannan kuwa ba wani abu bane illa cewa, kwanaki kaɗan
waɗannan mutane da su ka dawo suka fara mutuwa, ba
tare da wani cikakken dalili ba, hasalima da dama babu
wani ciwo na zahiri a jikinsu.
Kafin kace meye wannan sama rabin waɗanda suka dawo
sun isa lahira!
Hakan yasa tun da aka fara sallar jana'iza da binne
gawarwaki bayan isha ba'a dainaba sai zuwa kusan
ketowar alfijir.
Ana cikin wannan hali wani Mai shela acikin wannan gari,
haye kan wani doki samfurin Kilí ya fara zagayawa
kwararo-kwararo yana cewa,''saƙo daga sarki!
"Sarki ya aiko ni, ya ce a gaya muku, ku daina taɓa jikin
waɗanda suka dawo daga yaƙi da fatarku, domin akwai
matuƙar yiwuwar cewa duk abinda yake kashesu za'a iya
ɗaukansa ta hanyar taɓi.''
A wannan gari, acikin waɗannan fuskoki masu cike da
juyayi da baƙin cikin rabuwa da masoyansu akwai wani
yaro wankan tarwaɗa dogo mai cike da kamala, yana
ɗaure da jan ƙyalle a saman kansa wanda ya zagayo ta
gaban goshinsa.
Duk da fuskarsa na nuna yarinta amma kallo ɗaya zakai
masa, ka gano cewa a tattare dashi akwai kwarjini.
Ɗauke yake da wata mace, wadda yake riƙe da ita cikin
yanayi na tsananin kula da kaffa kaffa.
Tafe yake yana sassarfa cikin keta mutane, idanunsa a
sama yana hange-hange tamkar wanda ke neman wani
abu daya rasa wanda kuma in bai samu ba rayuwar sa

zata iya tagayyara.
Duba ɗaya tak inkai masa ka san cewa yana cikin
damuwa, daga gani wannan mara lafiya dake bayansa
wata ce ta kusa dashi.
Tuni duhu ya fara yi sanda ya isa wata ƴar runfa dake
kudu maso gabashin ƙauyen, inda ya tadda wani ɗan
tsoho aciki.
Ya ɗan duƙa kaɗan yai sallama, sannan a wata murya mai
cike da kwarjini ya fara bayani da sauri-sauri, ''Barka da
yamma baba mai magani.
"Baba ta na kawo, ina fatan ko zaka iya taimakon ta.
"Kaga ko rauni ɗaya babu a jikinta, tana numfashi, kuma
bugawar zuciyarta dai-dai yake amma bisa mamaki taƙi
farkawa ta buɗe ido.
"Na zagaye dukkanin wajen wani mai magani a wannan
ƙauye amma babu wanda ya iya yi mata wani abu.
"Yanzu kaine na ƙarshe daka rage, dan ALLAH ka taimake
ni, ita kaɗai ce ta rage min.''
Nan da nan wannan ɗan tsoho mai yawan farin gashi a
fuska da kai, ya ɗauko ƴar fitila aci bal bal ya kunna
saboda duhun da gari fari yi, sannan ya ɗan duƙa ya fito
waje ta cikin ƴar ƙofar shagon inda ya nufi wannan
saurayi.
Yana zuwa baiyi wata-wata ba, ya dubi matar wadda ke
bayan saurayin ya miƙa hannu ya buɗe idanunta.
Nan take a fili jikinsa ya mutu, saboda da kyar ya iya ɗago
kai ya dubi saurayin cikin yanayin tausayi gami da cewa,
''ɗan saurayi ya sunanka."
Saurayin ya amsa cikin ladabi, ''Suna na Armad Djinn."
Tsohon yaci gaba da cewa, ''Armad haƙiƙa yau na duba
marasa lafiya da dama, kuma mafi yawa duk ragowar
wannan mummunan yaƙi ne.
"To amma kusan da yawan waɗanda na gani haka suke.
"Ba ciwo ba rauni, ba buguwa, amma basu san inda
hankalinsu yake ba!"
Yana cikin magana Ya ɗanyi shiru kamar yana tunani,
kafin daga bisani ya isa ga wannan mata ya duƙa, ya ƙara
buɗe idonta, sannan kuma bakin ta.
Ya ɗakko wata ƴar fitila ya haska kunnenta. Sannan yai
wani dogon numfashi gami da duban Armad, ya ce,
''Armad kake ko?" Wannan saurayi ya kyaɗa kai.
Tsohon yaci gaba da cewa, "Gaskiya kayi haƙuri Armad,
babu abinda zan iya, irin wannan cuta a littafi kaɗai na
taɓa ganinta.
"Abinda kawai nasani shi ne tana da alaƙa da Ururu.
"Kuma dai a iya sani na, mutun ɗaya na sani da zai iya yin
wani abu akai a duk faɗin doron wannan ƙasa ta uku!"
Yana faɗar haka ya nemi waje ya zauna kusa da Armad,
sannan yaci gaba da cewa, "to amma wannan mutum
dana sani bani da cikakkiyar masaniya ko zai iya ko bazai
iya ba, sannan ko zai iya sai yaga dama, kuma baya taɓa
taimako a banza.

"Sannan kuma tunkararsa abu ne mai matuƙar hatsari,
tunda shi mutun ne wanda ba'asanshi akan taimakon
mutane."
Tun kafin wannan tsoho ya gama rufe baki, Armad ya
zabura cikin zafin nama ya miƙe gami da cewa, ''ko ina
ne kuma ko wanene, ka gaya min zan tunkare shi indai
akwai yiwuwar mahaifiyata ta iya samun sauƙi ta
hanyarsa!"
Tsohon yai shiru yana kallon Armad fuska cike da jimami.
Kafin daga bisani ya girgiza kai gami da cewa, "sunansa
sarkin duba Abul Babara!
"Kuma ina kyautata zaton kasan inda zaka sameshi?"
Da jin haka Armad ya miƙe zumbur gami da yin godiya
ga wannan tsoho. Kan kace meye wannan tuni Armad
yayi sallama da wannan mutun ya kuma doshi inda
sarkin duba yake.
Har ya kusa ƙulewa yajiyo muryar wannan tsohon yana
masa magana, "ka kula, ba komai ya gayama zaka
yarda!!"
Armad bai iya bashi amsa ba saboda sauri da yake, sai
kawai ɗago masa hannu da yayi.
Wannan saurayi daya kira kansa da suna Armad Djinn,
yaro ne ɗan kimanin shekaru sha bakwai, ƙafa huɗu a
tsaye.
Wani abu guda shi ne, wannan yaro yana da kyawun
fuska sosai, ta yadda a ganinka dashi na farko, zaka iya
kuskuren cewa wannan yaro ba mutun bane, ɗaya ne
kurum daga cikin manyan ƴaƴan aljanu!
Duk da rigar jikinsa nada ɗan faɗi amma murɗaɗɗɗen
ginin jikinsa saida ya bayyana duk da haka.
Yana sanye da kayan da yafi so wato, farar riga ƴar shara
zuwa ƙugu mara faɗi sosai. sai kuma baƙin wando wanda
bashi da faɗi zuwa idan sahu.
Sannan kuma kamar kullum yana tare da, wani jan ƙyalle
da yake ɗaure kai dashi.
Zuwa wajen Abul babara dan neman magani abu ne
wanda aka daɗe matuƙa da hanashi daga fadar sarkin
Hán-na-ɗaya, wanda shike mulkin ɗaya daga cikin mafiya
girman ɓangarori biyu a doron ƙasa ta uku.
Kusan kowa yasan Abul'Babara a wannan ɓangaren na
ƙasashen ƙasa, musamman saboda irin halayensa, da
kuma yadda sarki Hán wanda akafi sani da Hán-na-ɗaya
yasa aka koreshi daga cikin gari.
Saboda hakan ba abin mamaki bane Armad yasan wajen
da aka kora wannan ɗan duba.
Kai tsaye ya nufi wajen. Babu abinda yake sai sassarfa
cikin kula kada yayi abinda zai cutarda mahaifiyar tasa.
Tuni dare yayi tsakiya Armad yana tafiya, amma har
wannan lokaci Armad yana tafe bai tsaya ba.
Iska tana kaɗawa daɗan ƙarfi, sannan kuma gari ya fara
yin shiru. Amman Armad babu ko alamun tsoro a tattare
dashi kawai burinsa ya ƙara nutsawa zuwa ga bakin gaɓa

wajen da yake sa ran zai tadda AbulBabara.
Kan kace meye wannan, Armad na tafe har yayi awannin
yana abu ɗaya, kuma bai haɗu da wani mahaluƙi ba,
saboda dama ko idan ka cire makokin dake faruwa acikin
garin, wannan wajen ba wajen ziyartar mutane bane.
Can wajen tsakiyar dare, Armad ya fara hangen bangon
Arewa, nan take yasan cewa lallai ya kusa bakin gaɓa.
Koda ya kusa sai yaɗan fara rage tafiya yana dudduba
muhallinsa, dama da hauni ko zaiga alamun wannan ɗan
duba, amma ina babu wani alamu, sai kawai yaci gaba da
tafiya.
Bayan wani lokaci saiya fara hangen wata ƴar bukka daga
ɗan nesa, nan take kuwa ya durfafeta...


Read / Download MAGAJIN WILBAFOS BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album