Join Our WhatsApp Group

BAKAR GUGUWA book 1 Complete Hausa Novel Document by BAKAR GUGUWA book 1


BAKAR GUGUWA book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14140



BAKAR GUGUWA book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Shehu Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 76.7 kb

File Type: txt

Views: 751+

Download: 211+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__



BAKAR GUGUWA
littafi na daya 1
Na Marubuci Shehu Usman Muhd
Typing by Shuraih Usman
Part A
posted by Shuraih 99%
.
Zuhairu yana tafe akan ingarman dokinsa cikin sassarfa da hanzari, ya nufn bakin wani makeken lambu ma'abocin ni'ima ta 'ya'yan it'atuwa furanni da koramu masu gudanarwa a cikinsa.

Zuhairu jarumi ne na gasken gaske wanda jarumta da bajintarsa ta shahara a dukka nin fadin alkaryun dake kusa da brinin su, yana da karfin zuciya da rashin tsoro na ban mamaki. Shi kadai yakan fasa rundunar mahara da masu tare hanya suyi fatake masu tafiya a daji fashi.

Al'addar Zuhairu ce yakan ziyarci bakin wannan lambu ako wane yammaci dan yaga wata 'yar sarki da ke zuwa lambun tare da kuyangunta ako wace rana.

Tun daga ranar da ya fara ganinta cikin wasu ranaku da yake yawo a wannan waje, ya ji zuciyarsa takamu da tsananin begenta, irin wanda bazai musaltu ba, sai dai baisan makomar rayuwarsa ba. bisa ga kaunar da yake yiwa wannan 'yar sarki, kasancewarta mai girma da daraja daraja cikin man'yan 'ya'yan sarakunan duniya. °

Ya yi sani da cewa 'ya'yan sarakuna a wannan lokaci' basa auran wanda ba dan sarki kamar su ba. Ko kuma attajiri wanda dukiyarsa ta shahara. Shi kuma gashi ba d‘an sarki ba, dan haka ya kauda kai gabarin tunkararta ya bayyana mata abinda yake zuciyarsa, na daga begenta saboda girman matsayinta da ya wuce nasa. Sai dai yakan ziyarci bakin wannan lambu da take zuwa akowanne yammaci dan ya ganta.

Da isarsa bakin wannan lambun ya sauka daga kan dokinsa ya kaishi gefe ya daure. sannan ya koma gindin wata itaciya dake fuskantar kofar lambun ya zauna ya

dauko wata Sarewa ta azurfa da ya gada a wajen
mahaifinsa ya Soma busawa cikin nishadi yana mai
sauraran isowar wannan 'yar sarki dan ya ganta.
Zuhairu yana zaune a wannan waje har rana ta kusa
faduwa wannan yar sarki bata zoba, ransa ya baci
saboda kewar rashin ganinta ya yi shiru yana tunani da
sake-sake a ransa.
Yana cikin wannan hali kamar daga sama sai yaji
anyi masa magana dawata irin zazzakar murya mai
sanyi daga ababan sauraro. Muryar tace dashi.
"Da kazama mai yiwa zuciyarka adalci da babu
shakka da ka rabu da begen wadda bata san kana
begenta ba. Da ka rabu da tunanin wadda bata san kana
tunaninta ba, da ka sauya lamarinka daga kuncin kaunar
wadda baza ta soka ba, saboda girman matsayinta da ya
wuce naka."
Zuhairu ya dago kansa cikin sauri ya dubi inda ya ji
muryar da ta yi masa magana amma baiga kowa ba, ya
duba kowane bangare na daga inda yake baiga mai
maganar ba.
Muryar ta sake cewa da shi "kada ka damu ko kaji
tsoro mai kaunarka ce take yin magana da ka, ko kana
inkarin abinda na ambata na bayyana gare ka dan
tabbatarwa."
Zuhairu ya dubi inda ya kejin muryar ya ce "ldan kin
kasance tare da alhairi ki bayyana gare ni don nasan wacece ke da kuma dalilin zuwanki gareni har ki kayi sani da halin da nake ciki da fadar Magana mafi munin ambato, 1dan kuma bakya tare da alhairi to kuwa ina mai neman tsari dake tare da rokon kinisanta dani ko waccce ke
Zuhairu ya ji anyi dariya cikin tattausar murya.
sannan muryar ta ce dashi "Zan kasance alhairi gareka tunda ina tare da dumbin kaunarka a zuciyata, dan haka zan bayyana gareka nasanar dakai koni wacece da kuma abinda ya kawoni gare ka kamar yadda ka ce."
.
Ana gama fadar maganar sai yaga wani farin haske ya bayyana a gabansa daga cikinn farin hasken sai ga wata mace ta bayyana kyakkyawar budurwa tana sanye da fararan tufafi hannunta rike da wani dan karamin
gora abin zagayewa da gura ye da kambuna irin na aikin sihiri.

Ta dubeshi tayi murmushi tare da juya fararan
idanunta dan jan hankali. Zuhairu ya kare mata kallo sannan ya ce da ita "Wacece ke kuma meya kawoki gareni cikin wannan
yanayi na aikin sihiri, ki sani cewa babu aminci tsakaniin Musulmi da duk wasu mushiriki ma'abota tsafi da sihiri, matukar basu tuba sunbi Allah ba." Kyakkyawar budurwan nan tayi dariya sannan ta ce da shi "Da dai kayi sani da irin martaba da daraja da
take tattare da alkaluman sihiri, da kuwa kayi biyayya ga ma'abota mallakarsu dan kazamo daga cikinsu. Shine
abin tunkaho da alfaharin mu dan a yanzu duniyar
ma'abota sani na alkaluman sihiri ne keda tasiri akan
komai."
Ta sake yi masa murmushi irin na jan hankali sannan
ta ci gaba da cewa "Suna na BUNIYATUL HAJARI BIN KAUWAS mahaifina shine shugaban bokaye da
ma'abota aikin sihiri dake yammacin bimin SINAR. Ya
rasu cikin wannan shekarar yana tsakiyar tafiya ba tare
da wata rashin lafiya ko cuta ba, bayan rasuwar sane
muka gaji sirrin tsafi da sihirinsa ni da yayana da ya rasu
ya barmu a duniya, na gaji kashi daya cikin dari na
alkaluman sihiri. Mahaifina yayana kuma ya gaji kashi
casa'in da tara daga ciki.
Dalilin zuwa na gareka kuwa shine na kasance mai
bibiyar rayuwarka tun daga lokacin da na fara ganinka
zaune a wannan waje kana busa sarewa, tun daga
busar sarewar da kake yi mai sanyaya zuciya har
wannan rana nakan ziyarci wannan waje dan na saurari
zuciyata ta kamu da tsananin begenka. Sai dai bantaba
bayyana gareka ka ganniba sai a yau, kuma na lura cewa
zuciyarka ta kamu da kaunar wata 'yarsarki da take
zuwa wannan lambu, dan haka na baiyyana gareka dan
na raba tunaninka da begen wadda bata san kana
begenta ba."
Zuhairu ya fusata dajin wannan magana ya ce da ita
"Da kinsan yadda nake tsananin gaba da kiyayyar
mushirikai ma'abota tsafi da sihiri da ko kusa baki
tunkari inda nake da bukatar na kaunace ki ba, kiyi
alkawarin zaki musulunta dan samun cabo da kaucewa
bata na aikin sihiri da kike aikatawa, ko kuma ki nisanta
da inda nake. Idan ba haka ba kuwa na rantse da wanda
raina yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni
da azabar kaifin takobina."
Buniyatu tayi dariya sannan ta ce da shi "Babu
kiyayya ko gaba a tsakanina da kai masoyina, idan da
ina gaba da kai zai zama mafi sauki gareni na halakaka
ta hanyar karfin tsafi da sihirina." Ta daga kurtun sihirn
da yake hannunta ta girgiza shi ta soma wasu irin surutai
da sambatu irinna aikin sihiri nan take wuta takama daga
kowace kusurwa hudu dake zagaye da Zuhairu. Sannan
wutar ta taso kansa gadan-gadan zata konashi ya halaka
Zuhairu yayi niyyar Kaucewa amma yaji ya kasa
koda motsi daga inda yake kamar wanda kasa tarikeshi
Wutar ta taso masa haikan zata koneshi ya halaka sai da
ta kusa zuwa inda yake ya soma jin zafin da hucinta,
sannan sai yaga wutar ta mutu ta kuma bace ya dena
ganinta.
Buniyatu ta sake bushewa da dariya sannan ta ce da
shi "Wannan kadan kenan daga tasirin tsafi da sihirin
da na gada a wajen mahaifina wanda zan iya halakaka
dashi idan naso. Sai dai bani da nufin cutar da kai bare
aje ga batun halakaka, saboda kaunar da nake yi maka.
Kai dai kayi azama ga zurfafa tunani dan amincewa da
kaunar mai kaunarka, zai zama mafi kyautuwa gareka
ka
ka amince da bukatata muyi aure. Wannan shine
kudirina akanka kayi tunani akan maganar. Na barka
lafiya."
Tana gama ladar maganar sai yaga ta bace daga wajen
ya dena ganinta. Sannan yaji shuru bata sake yin magana
ba bare motsinta. Dan haka ya tabbatar da cewa ta tafi
tabar wajan, da ganan ya tashi ya kama dokinsa ya hau
ya nufi hanyar komawa gida.
Da isar Zuhairu gida ya daure dokinsa ya tafi wajan
kakansa MARWAN BIN HADIS wanda shi kadaine ya
rage masa a duniya. lyayansa sun rasu tun yana karami,
a hannun kakan nasa ya taso. Ya zauna kusa da shi ya
gaisheshi sannan ya kwashe labarin abinda ya faru
gareshi tsakaninsa da wannan shu'umar mace da suka
hadu da ita a fitarsa ta wannan yammaci, ya sanar da
shi.
Dattijo Marwan ya cika da mamakin wannan labari
sannan ya ce da Zuhairu "Babu shakka duniya ta kara
kazanta da shu'uman mutane mushirikai ma'abota tsafi
da sihiri a doron kasa."
Ya tashi daga inda yakezaune ya nufi wata akwatin
bakin Karfe dake karshan dakin ya bude, ya bincika
kasan akwatin ya dauko wani zobe na azurfa ya dawo ya
bawa Zuhairu sannan ya ce da shi "Ka sanya wannan
Zoben a dan yatsanka cikin yardar Allah zai zama kariya
gareka daga sharrin ma'abota tsafi da sihiri, babu wani
aikin sihiri da zaiyi tasiri akanka kuma komai rintsi kada
ka sake ka cireshi daga hannunka, a duk sanda wani
matsafi ya tunkareka ko mai aikin sihiri zakaji zoben
yayi mosti a hannunka koda kuwa baka ganinsa, haka
kuma idan kaji dokinka yayi haniniya to ka lura akwai
Wani abin cutarwa kusa da kai, dan shi yana ganin
abinda kai baka gani, kuma kada kasake kashiga inda
dokinka yayi gardamar shiga, haka kuma kada kaji
tsoron duk abinda dokinka baiji tsoron ganinsa ba. Kada
kamanta yawan addu'a aduk inda kake dan neman tsari
da kariya daga wajan Ubangiji, ka kiyaye da abinda na
sanar da kai."
Zuhairu ya karbi zobe ya saka a hannunsa sannan
ya yiwa kakansa dattijo Marwan godiya ya tashi ya fita
Washe gari da yamma Zuhairu ya sake yin shiri ya
kama dokinsa ya hau, ya nufi hanyar wannan lambu da
Gimbiya Hasima take zuwa akowane yammaci dan ya
ganta.
Ya ci gaba da tafiya cikin sassarfa da hanzari har ya
Soma hango bakin lambun da Gimbiya hasima take
zuwa. Kafin ya karasa bakin lambun sai ya hangi wasu
barada su kimanin arba'in sanye da kayan fada da
makamai, sun zagaye wasu yammata sun kamasu sun
dora akan dawakansu zasu tafi da su, yammatan suna
kuka da kururuwar neman taimako amma babu wani
wanda zai iya taimaka musu a wajen.
Zuhairu ya saki linzamin dokinsa ya kara azama dan
ya isa garesu yaga abinda yake faruwa da isarsa wajan
sai yaga gimbiya Hasima ce tare da kuyangunta baradan
nan suka kama zasu tafi da su.
Zuhairu ya fusata da ganin wannan aikin zalinci ya
dakawa baradan tsawa ya ce da su "Kai fajirai
kaskantattu ma'abota zalunci da rashin imani, me kuke
nufin aikatawa ga wadannan bayin Allah da ku ka
"Kai
kama."
Baradan nan suka juyo suka dubi Zuhairu, da suka
ga shi kadaine tsaye akan dokinsa sai suka bushe da
dariya irinta mugunta da zalunci, sannan daya daga
cikinsu ya bashi amsa da cewa " Babu shakka ajaline ya
Kusanto da kai wannan waje, har kake tambayar abinda muke nufin aikatawa ga wadannan yammata, bari mu
sanar da kai dan ya zama guzirinka na tafiya barzahu,
zamu tafi da su ya zuwa ga shuwagabannin mu dan,su
zama bayinmu
bukatarmu dasu duk sanda mu kaga dama idan mungaji
dasu ko kuma ansamu kata daga cikinsu tasamu ciki, sai
mu sare kanta dan shayar da jininta ga ababan bautarmu,
wannan shine makomarsu da abinda zamu aikata garesu
masu yi mana hidima da biyan
Idan mun tafi dasu."
Zuhairu ya fusata dajin wannan magana ya ce da su
"Kaicon rayuwarku da abinla kuke aikatawa
mafi
munin makoma na zalunci da rashin Imani. Kuma idan
wannan shine kudirinku a rayuwa to kuwa zan halakaku da shafe ruhinku daga doron kasa dan kawar da wannan
zalunci."...

TOFA MUN FARO KENAN

MASU SON LITTAFIN COMPLETE SAI SU DANNA HOTON KASANNAN

https://youtu.be/YSYyhta02NI

BAKAR GUGUWA
littafi na daya 1
Na Marubuci Shehu Usman Muhd
Typing by Shuraih Usman
Part B
post by Shuraih 99%
.
Baradan nan suka sake bushewa da dariya sannan
daya daga cikinsu ya fita gaban Zuhairu ya tsaya yana
sanye da sulke da kayan fada hannunsa rike da bakar
takobi yayi huci ya daga takobin sama cikin karaji ya
taso kan Zuhairu.
ZUhairu ya zarce tasa takobin ya tare shi suka hadu,
ta kubbansu suka yi karciya tartsatsin wuta ya tashi
sama, zuhairu ya sake kai masa sara bardan ya goce
kaifin takobinsa ya tafi ya zuwa wuyan dokinsa nan take
ya sare wuyan dokin suka tafi suka fadi kasa gaba daya.
Bardan nan ya mike a fusace kafin yayi wani
yunkuri Zuhairu ya cimmasa ya sanya takobinsa ya yi
masa saran karan tsaye nan take ya tsarge shi gida biyu
duk da sulken karfe da yake jikinsa, ya zube kasa
matace bai ko shura ba.
Wani daga cikin baradan mai karfin zuciva ya sake
zaburowa.cikin karajin fusata. Zuhairu ya tareshi da
zamiya ta salon iya fada irin na zaratan sadaukai, ya kai
masa wani gawurtaccen sara da karfin karar da ruhi,
bardan nan ya sanya garkuwarsa ya kare, garkuwa ta
kece gida biyu saboda tsananin karfin saran, kafafun
dokin bardan na gaba suka durkushe dokin ya yi
haniniya wadda ta hadu da hucin saran da Zuhairu ya
sake kaiwa bardan ya sameshi a tirken wuya, nan take
ya sare masa kai ya fadi kasa matacce
Da gani haka sai ragowar baradan suka fusata suka
sauke su gimbiya Hasima da kuyanginta daga kan
dawakansu suka zare makamai, suka tasar ma Zuhairu
baki daya cikin karaji da gunjin lusata.

Shima Zuhairu ya karkata garesu ya taho suka hadu
yana mai kai sara a tsakaninsu irinna karar da san sanin
abokan gaba, baradan nan suka zagayeshi ta ko ina suka
yi masa kawanya, amma duk inda Zuhairu ya keta sai
dai kaga yana saransu suna zuba kasa matattu, haske
takobinsa ya koma ja-jawur saboda keta jinin azzaluman
baradan nan. Gaba daya wajan ya yamutse aka shiga
artabu da bakin gumurzu wanda ya kawo salwantar
rayukan barada masu dama.
Da baradan an suka ga haka sai wasu daga cikinsu
suka razana suka...


Read / Download BAKAR GUGUWA book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album