Join Our WhatsApp Group

BUSA A MUTU Book 2 Complete Hausa Novel Document by BUSA A MUTU Book 2


BUSA A MUTU Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14810



BUSA A MUTU Book 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Nov 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 78.29 kb

File Type: txt

Views: 889+

Download: 380+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: ßµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Biyu (2)
Part A

Na Abdulaziz Sani M /Gini

Marubucin Yaci Gaba Da Cewa

SA'ADDA boka Rufyan ya zo
jawabinsa sai hankalin yarima Muraisu ya
dugunzuma har kwalla ta zo masa, ya dubi boka
Rufyan cikin tsananin takaici ya ce, "Yanzu ke nan
kana nufin cewa nima mutuwa zan yi nan ba da
dadewa ba kuma idan ban auri gimbiya Husnaila
ba shi ke nan babu mai kawar da su azzalumaí
Huraisu?".
Koda jin wannan tambaya sai boka Rufyan
yai shiu ya kasa cewa komai, kawai sai ya mike
tsaye ya koma can gefe daya ya zauna yana mai
sunkui da kansa kas. Cikin fushi yarima Muraisu
ya mike zumbur yaje gabansa ya tsaya ya dubeshi a
fusace ya ce, "Saboda me ka ki baní amsar
tambayata?"
Boka Rufyan ya dago kai ya dubi yarima ba
tare da shakka ko tsoro ba ya ce, "Ai ba kowacce
tambaya ce ke da amsa ba. Ina so ka sani cewa
zamanmnu anan bashi da wani amfani, domin zaman
Jaki da kaya ne. Idan kana ganin za ka bi wadannan
matakai na samun matar da za ka aura ka tashú mu.
bi sawunsu gimbiya Husnaila.
Dik da cewą tsakaninmu da su akwai tazarata
a kalla tafiyar kwana arba'in, zan iya đaurc mana
kasa mu riskesu a cikin kwana shida da yini daya,
domin ka yakesu ka rabasu da Husnaila idan ka yi
nasara sai mu rakaka izuwa bakin dajin Kirzufa mu
-tsaya daga wajensa kai da Husnaila ku shiga
cikinsa, ba za ku fito ba sai bayan kwana ukun.
Sannan mu rankaya mu tafi izuwa can birnin Lairuf
domin a yi shagalin bikinku",
Lokacin da boka Rufyan ya zo nán
jawabinsa sai jikin yarima Muraisu ya yi sanyi, ya
koma can gefe ya zauna kuma ya yi tagumi inda ya
fada cikin kogin tunani.
Ba wani abu yake tunawa ba face gagarumin
aikin da ke gabansa wanda ya i karfin tunaninsa.
Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, ta ya ya zai
iya tarwatsa wadannan dakaru guda dubu dari uku
shi kadai alhalin KAIFI DA TSINI baya tasiri a
jikinsu? Kuma idan za a kwana uku ana yaki da su
ba z4 su gaji ba? Abu na biyu, ta ya ya zai iya shiga
dajin Kirzufa ya har ya yi kwana uku a cikinsa
alhalin mahaifinsa ma da kyar ya iya yin sa'o'i a
cikinsa?"
Koda Muraisu ya zo nan a tunaninsa sai ransa
. ya baci ya ga cewa boka Rufyan ya raina masa
hankali, domin bai ga dalilin da zai sa ya umarceshi
yin abinda shi kansa ya san cěwa ba zai yiwu ba.
A fusace ya sake mikewa tsaye ya nufi kan boka
Rufyan gadan-gadan, kawai sai boka Rufyan ya
mike ya tareshi ya ce, "Idan ka so ka zare
takobinka ka kasheni yanzu take, amma ka sani
cewa zabi daya ne garcka cikin biyu. Walau ka
koma gida ka zuana ka įira ranar da makiya za su
Z0 Su cimu da yaki, kana ji kana gani, ko kuma ka
nemi matar aurenka wacce za ta haifa maka dan da
Zai kwatar mana 'yanci anan gaba. Ko ka ki ko ka
so baka isa ka sauya kaddara ba.
Babu makawa sai an ci mu da yaki kuma ba
lallai bane ni ko wadannan abokan tafiya namu
dayanmu ya yi nisan kwanan da zai ga ranar da za
a karbar mana 'yancin mu ba."
Koda jin wannan furuci sai jikin yarima
Muraisu ya yi sanyi a karo na biyu, ya koma inda
yake ya zauna yai shiru bai ce komai ba, ya shuga
sabon tunani. Nan take yaji duniyar gaba đaya tayi
masa zali, musamman da ya tuna cewa shi fa yanzu
bashi da uwa kuma a ko yaushe ma zai iya rasa
mahaifinsa.
"To wai shin na akan Wane dalili zai damu da
duniya tunda bashi da saran masoyi?"
Wata zuciyar kuma ta ce da shı, "To mene ne
am fanin kaina ka gushe kamar yadda iyayenka za
Su gushe ba. tare ta ka bar. zun ar da za a gania
Tinka tunawa da kai ba?"
Koda ya zo nan a tunaninsa sai hawaye ya
zubo masa. Yana dago kai ya ga kuyanga Sabirat
tsaye a gabansa. Sabirat ta zauna kusa da yarima
Muraisu ta dubeshi a nutse, sannan ta ce, ""Ya kai
jarumin kwarai, ka yi sani cewa namijin baya kuka,
kuma bai san tsoro ba. Shi ne wanda baya shakkar
shiga ckin kowanne irin bala'i kuma shi nc wanda
bai dauki RAI a bakin komai ba, muddin bukata za
ta biya."
Koda yarima Muraisu yaji wannan batu sai
dukkanin tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa kawai
sai ya dubi Sabirat ya yi murmushi ya ce,
"Madallah da kuyanga ta gari wacce ke yiwa
ubangidanta tuni bisa abinda ya kamaceshi."
Gama fadin hakan ke da wuya sai Muraisu ya
mike tsaye ya dubi Boka Rufyan da Badakare
Kirzal ya ce, "Ma za ku samu akan hanya wacce za
ta kaini inda zan riski gimbiya Husnaila da
jama'arta a cikin kankanin lokaci"
Kafin Muraisu ya gana rufe bakinsa tuni
Kurzan da Rufyan sun mike zumbur sun kama
dawakansu sun haye. Saoirat da Muraisu ma suka
yi sauri suka hau nasa dawakan. Kurzal ne ya wuce
. kan gaba, Boka Kufyan na-biye da shi sannan su
yarima.
Dukkaninsu suka sukwani dawakansu da
gudun tsiya suka nausa cikin daji.
Nan fa Yarima, Kurzal da Sabirat suka rinka
ganin abin al'ajabi, domin cikin dakiku kadan suka
rinka shafe tafiyar sa'o'i. Nan da nan suka ga sun zO
wani wuri maj irin yanayi dabam da sauran
dazuzzukan da suka wuce.
Shi dai wannan wuri da suka zo ya kasance
daji ne mai yawan lumshi tamkar rana ba ta taba
baiyana ba a cikinsa. Bishiyoyin da ke cikinsa
kuwa duk dogaye ne masu fala-falan ganyaye, haka
kuma akwai duwatsu manya-manya in-in masu
tsawo da fadi.
Koda 1SOwar Su yarıma wannan wuri sai
Kurzal yai sauri ya sauko daga kan dokinsa ya kifa
kunnensa akan kasa yai nazari, sannan ya mike
tsayc, ya dubi yarima ya ce, 'Ya shugabana nan
gaba kadan tafiyar 'yan dakiku akwai mutanc sama
da guda dari biyu a labe cikin duhuwar bishiyoyi".
Koda jin haka sai Boka Rulyan ya yi
murmushi, sannan shuma ya dubi yarima ya ce, "Sai
ka shige ciki ka riskesu ka karbo gimbiya Husnaila
ta kowanne hali. Mu kam amu Jiraka ne nan har
iZUwa tsawon sa'a bakwaj.
Jdan ka fito da nasara sai mu rakaka izuwa
bakin dajin KirZula, acan mas mu jira izuwa
sa'adda za ku kwana uku a cikinsa ku fito, sannan
mu rankaya gaba daya izuwa gida. Idan kuma mu
ka ji shiru ba ka fito ba, mun san ccwa ka hallaka
sai mu juya mu koma gda".
Yarima Muraisu ya gyada kai ya ce, "Haka za
a yi". Kawai sai ya juya zai shiga cikin wannan daji
mai kwarjini, ai kuwa sai ya hada ido da kuyanga
Sabirat. Bisa mamaki sai ya ga hawaye ya zub0 a
idanunta.
Boka Rufyan da Barde Kurzal kuwa, ko
kwalla babu a cikin nasu idanun. Nan take Muraisu
yajı zuciyarsa ta sosu kuma ya cika da mamakin
dalilin da ya sa Sabirat ta zubar masa da hawayc,
alhalin bai kasance komai
face
ubangidanta.
gareta ba
Shin tsananin sabon da tayi da shi ne ya sa ta
Zubar da wannan hawaye ko kuwa so nc irin wanda
ke tsakanin mace da namiji?
Nan fa Muraisu ya kasa baiwa kansa amsa,
kawai sai ya kau da kai ga barin kallonta, ya kunna
kai cikin wannan daji yana mai zare takobinsa.
Karar zare takobin tasa ce ta fargar da
wadannan dakaru guda dari uku masu gadin
gimbiya Husnaila, su ma sai lkowanncnsu ya zare
tasa takobin.
A wannan lokaci gimbiya Husnaiíla tayi
tumbur a cikin wata korama tana wanka, Wasu
kuyanginta guda hudu suń rike manyan mayafai
sun kare inda take don kada wadannan Dakaru su
ga tsiraicinta.
Kwatsam! Ba za to ba tsammani sai gimbiya
Husnaila da kuyanginta suka ji an barke da
azababben yaki banda karar karafa babu sautin da
ke cika dodon kunne, har amsa kuwwa yakea cikin
dajin.
Ko kadan gimbiya Husnaila ba ta tsorata ba,
domin ba ta ma san mene ne tsoro ba a rayuwarta,
amma su kuyanginta sai suka firgice, jikinsu gaba
đaya ya kama kyarma. Nan da nan suka hada gumi
sharkaf. Koda gimbiya Husnaila ta ga halin da
kuyanginta suka shiga sai ta daka musu tsawa ta ce,
"Idan ba za ku iya ci gaba da aikinku ba zan sa
takobi duk na sareku".
Koda jin haka sai dukkanínsu suka nutsu akan
aikinsu. Ita kuwa Husnaila sai ta ci gaba da
wankanta tamkar a cikin gidanta take.
Cikin tsananin gudu yarima Muraisu ya.ratsa
cikin wadannan Samudawan dakau da nufin ya
wuce ta tsakiyarsu ya isa inda gimbiya Husnala.
take wahka, ámmna sai wadannan Dakaru suka ce
wane shi, nan take suka yanyameshi suka haushi da
sara da suka. Shi kuwa ya wanzu yana mai karcwa
da mai da martani.
Shi kansa sai da ya yi matukar mamaki bisa
ganin inin tsananih zafin naman da ya samu a yanzu
wanda a da can ya tabbatar da cewa bashi da irinsa,
in da ya sami matsala shi ne, tunda Dakarun suka
kewayeshi a waje daya aka ci gaba da gumurzu sai
ya kasa karawa gaba. Domin sun babbake hanya
babu ta inda zai iya wucewa.
Abinda ya fi daga masa hankali shi ne, duk
sa'adda ya sari dakarun ko, kuma ya sokesu da
takobinsa sai ya ji kamar karfe ya kaiwa hari,
domin tartsatsin wuta ne ke tashi gami da hayaki.
Su kuwa duk sa'adda suka sari jikinsa makamin
baya tasiri, amna sai jikinsa ya gaya masa, domin
ji yake kamar an sa shi a cikin turmi ana yi masa
lugude da tabarya.
Hakika Muraisu ya yi mamakid a ya ga karfe
bai ci jikinsa ba, domin shi dai ya san bashi da
wannan sihiri, amma da ya tuna cewa ai ya sami
zafin nama irin wanda bashi da shi a da sai ya gane
cewa lallai akwai sabon al'amari wanda ya zo masa
bako tuntuni.
"Mene ne sabon wannan al'amarin ?" Muraisu
ya tambayi kansa a cikin zuciya, amma sai ya kasa
ftar da amsa.
Lokacin da dakarun suka ci gaba da laflawa
Muraisu makanansu a dukkan jikinsa, sal ya
Zamana cewa ya kasa ci gaba da yaki, har ma ya
yarda takobinsa kuma ya fadi kasa.
Koda ganin haka, sai suka ci gaba da
tattakashi, nan da nan suka yi laga-laga da shi, jini
ya rinka tsartuwa daga cikin bakinsa da hancinsa.
Kafin cikar 'yan dakiku ya baje wanwar a
kasa yana num fashi da kyar ko yatsansa guda ya
kasa mnotsawa. A wannan lokaci ne. shugaban
dakarun ya yi mnusu inkiya suka ja da baya sannan
ya dubesu gaba daya ya ce, "Duk yadda aka yi
wannan jarumin ya fito ne daga kasar Lairus, kuma
ya zo ne domin ya sace gimbiya Husnaila ya tafi da
ita. Tunda dai makami ya ki ya yi tasiri a jikinsa,
ma za ku kamashi da karfin tsiya ku murde masa
Wuya ku jefa gawarsa cikin wancan ramin".
Shugaban dakarun ya yi nuni da hannunsa
izuwa ga wani rami mai zurfin gaske wanda ya kai
kamu dari da tamanin.
Kamar a cikin kunnen yarima Muraisu
shugaban dakarun' ya yi wannan bayani, domin ba
za to ba tsammani, sai suka ga Muraisu ya mike
Zumbur! ya daka tsalle sama ya dira a kan kafadar
daya daga cikinsu,
Cikin bakin zafin nama Muraisu ya kama kan
Badakkaren da ya dira a kafadarsa ya mrde masa
wuya. Take Badakaren ya sulale kasa matacce, ji
ka ke dam! kamar giwa ta fadi.

Zan dakata anan saikuma wani lokacißµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Biyu (2)
Part B

Na Abdulaziz Sani M /Gini

KAICO! Ashe tsuliyar dodo Muraisu ya tabo,
domin suna ganin ya kashe daya daga cikinsu sai
suka yì kukan kura suka afka masa gaba dayansu
aka sake kacamewa da azababben yaki.
Wannan karon dayansu bai samį damar koda
taba jikinsa ba, domin wata iriyar zulliya ya rinka
yi a tsakankaninsu
ya inka kama
hannaycnsu da kafafunsu yana kakkaryawa tamkar
yana karya sillen kara.
Gumbiya Husnaila da ke can cikin korama
tana ta wanka, sai ta fara jiyo ihun Dakarun
tsaronta. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke
Cikin hanzari ta karbi mayafi daga hannun
kuyanginta ta daura iya kirjinta, sannan ta fito daga
cikin koramar. Ko tufafinta ba ta tsaya sawa ba ta
durfai inda ake wannan gumurzu.
Su kuwa wadannan kuyangi na ta sai suka
ruga izuwa cikin daji a dimauce ba tare da sanin
inda suka dosa ba, saboda tsananin razanar da suka
yì domin sun san cewar bala'in da ya sa wadannan
samudawan dakarun ihu ba Karami bane.
Tun daga nesa gaimbiya Husnaila ta hango
dakarunta suna zubewa kasa tamkar ana sassabe a
gona.
Koda ta kara matsawa kusa sai ta ga ashe
wanda yake ragargazar su ma dan mitsitsı ne
akansu, bai fi ta kwatantashi da dan tsako ba a
cikin tsakiyar dubunnan Muzurai.
A iya rayuwar gimbiya Husnaila yau ne ranar
farko da ta ga abinda yai matukar ba ta mamaki,
amma ba wai burgcta ya yi ba.
Koda ta ga yadda Muraisu ke ta kakkarya
dakarunta suna zubewa kasa sai ta sunkuya ta
dauki mashin daya daga cikinsu ta ike ta tsaya
cak! Tana jiran ta ga abinda zai faru.
Kafin cikar rabin sa'a Muraisu ya zubar da
dukkan dakarun a kas suna ta koke-koke da iface-
iface, babu đayansu da ya iya mikewa tsaye.
Koda Muraisu ya ga ya gama da dakarun sai
ya yi arba da kyakkyawa Husnaila a tsaye a
gabansa ike da mashi, fuskarta a murtuke babu
annuri, kuma ga ta a tsayc kyam babu wata alamar
tsoro a tare da ita,
Koda ya ga kyakkyawar surar jikinta da kuma
wani kyakkyaw an gashin kanta sar ya rude ya
dimauce, bai san sa'adda ya nufeta ba gadan-gadan
da nufin ya rungumeta.
Koda ya ragc bai fi saura taku daya su hadu
ba sai ya kai ma ta raruma, ita kuwa ta goce ta soka
masa mashi a gefen kirjinsa.
Bisa mamaki sai ya ji mashin ya nutse a cikin
kirjin nasa, bai san sa'adda ya kwalla ihu ba.
Husnaila ta zare mashi jini yai feshi daga cikin
kirjin Muraisu, ya sake rusa ihu a karo na biyu. Jiri
ya debeshi ya yi luu!! kamar zai fadi kasa, amma
sai yaı ta maza ya tsaya bisa kafafunsa.
Husnaila ta sake saitashi da mashin ta tsaya
cak! A waje daya suka fara kallon-kallo. Daga can
sai ta dubeshi ta kyalkyale da dariya a cikin sautin
murya mai zakin gaske, sannan ta hade rai ta ce,
"Kai wayc, kuma me ka ke nufi da ni? Saboda mne
ka zo ka ragargaza mini dakaruna? Ka san kO ni
wace ce kuwa? Ka amsa mini tambayoyina da
gaskiya ko kuma na hallaka ka yanzzun nan!"
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya bushe
da dariya sannan ya ce, "Ni ne yarima Muraisu dan
Sarki Salmar mai binin Laius, wato babban
makiyi ga dan uwanki Sarki Ishmar.
Ina mai sanar da ke cewa na baro gida ne
domin neman matar da zan'aura, kuna ba wata ba
ce wadda zan aura face ke din nan".
Koda jin haka sai Husnaila ta tuntsure da
dariya, 1lokaci guda kuma ta hade rai ta sunkui da kanta kas tana tunani. Muraisu ya katse ma ta
hanzari ya ce, "Ya ke Husnaila Sarauniyar mata,
me kike tunani ne?"
Husnaila ta dubeshi ta ce, "Mamaki nake bisa
daıyar da na yi yanzu, domin kaine mutum na
farko da ya ta6a ganin dariyata..
Hatta dan uwana kuwa Sarki Ishmar sai dai ya
Ce ya ga murmushina ko hawaye na, amma bai taba
ganin dariyatą ba ko kukana'".
Da jin haka sai Muraisu ya yi mumushi ya ce,
"Al ni mutum ne na musamman a cikin mutane, da
sannu za ki gasgata haka".
Husnaila ta ce, "Ai kuwa na ga alama tunda
ban taba sukar wani abu da makami ba ya rayu sai
kai. Shin za ka iya gaya mini sirrin da ke tattare da
kai?"
Muraisu ya cire wani rawani da ke ikin
damararsa ya daure kirjinsa lamau don tsaida jini,
sannan ya dubi Husnaila a nutse ya ce, '"Ina zaton
dai irin sihirin da ke tare da ke shi ne a tare dani,
domin gashi dakarunki sun kasa cutar da ni da
makamansu, amma ke gashi kin cutar da ni".
Husnaila tayi murmushin mugunta, sannan ta
ce, "Ka yi babban kuskure da kake tunanin za ka
aureňi, domin abu ne wanda ba zai taba yiwuwa ba
Babu wani da namiji da ya isa ya mallakeni, idan
kuma kana ganin za ka iya ka jarraba!"
Muraisu ya gyara tsayuwarsa...


Read / Download BUSA A MUTU Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album