Join Our WhatsApp Group

KARSHEN ZALUNCI Book 3 Complete Hausa Novel Document by KARSHEN ZALUNCI Book 3


KARSHEN ZALUNCI Book 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13675



KARSHEN ZALUNCI Book 3

Reading Time: 1 Hours

Added On: 12, Jan 2024

Author: Mansur Usman Sufi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137237071

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 73.51 kb

File Type: txt

Views: 592+

Download: 143+

Last download: 3 days ago

Description/Story: ƘARSHEN ZALUNCI book 3
BABI NA FARKO
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071

Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu masifaffun kibbau sun soke badakaren a idanuwanshi ya kurma wawan ihu ya zube ƙasa yana shure-shure take jikinshi ya sandare ya sheƙa barzahu.
Cikin hanzari mutane suka waiga bayansu domin su ga wane ne ya harbo kibbau ɗin.


Ai kuwa koda suka yi tozali da ko mene ne sai suka yi turus! Bakomai suka gani ya ba su mamaki ba face wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa.
Budurwar takasance mai matsakaicin kaurin jiki ba doguwa ba ce ba gajera ba. Tana da dara-daran idanuwa farare ƙal! Masu haske tamkar tacecciyar madarar shanu, hancinta dogo mai lankwasa a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta dogo mai kyawu tamkar na barewa, ƙirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam basu ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda saboda kyawun su, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya yi tudu ainun ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi masu ɗaukar hankali, babban abin da ya ƙara tona asirin kyawunta shine dogon gashin kanta baƙi siɗik mai ƙyalli ya zuba har izuwa kan kwankwasonta.


Wohoho! Haƙiƙa wannan budurwa ta cika maƙura a kyawu, domin babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi arba da ita face ya kamu da matuƙar ƙaunar ta. Tana sanye cikin ƙayatattun tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayan ta tana rataye da wani kwari, hannunta riƙe da baka, kuma tana zaune ne akan wata ƙatuwar zakanya.
Wata ba ce wannan kyakkyawar budurwa ba face jaruma Sulairat yar Marigayi sarki urwat tare da zakanya Juraima.


Sa’adda sarauniya Abidat tayi arba da ita sai ta miƙe tsaye zumbur daga kan karagarta fuskantarta a murtuke babu annuri tamkar an aiko mata da WASIƘAR MUTUWA, Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su, cikin tsantsar ƙiyayyar juna, inda a ɓangaren guda kuma Sulairat ke satar kallon masoyinta bawa HIMLAS. Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali.
Daga can Abidat ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, a lokaci guda kuma ta turɓune fuska tamkar ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce “lale marhaban da zuwan manyan abokanan gabata, haƙiƙa wannan rana ce mai ɗumbin tarihi a gare ni, domin gashi dukkanin abokan hamayya sun taru a waje guda.


Na rantse da ƙabarin kakana sarki Zaujatul-ashiƙ ba zan ƙyale ɗayan su a raye ba”.
Koda gama faɗin hakan ta zare wata sharɓeɓiyar takobin a gadon bayanta ta dako tsalle a sama tamkar an harbo ta daga cikin baka, ta durfafi inda Sulairat take.


Suna saman suka kaiwa juna sara a kafaɗa.
Cikin matuƙar zafin nama suka sanya takubbansu suka kare harin tartsatsi wuta ya tashi gami da ƙara, sannan suka sauka ƙasa bisa diga-digansu take suka ruguntsume da azababban yaƙi, ita kuwa zakanya Juraima sai ta afkawa dakarun fadar da ciwo da yakushi.
Jaruman biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Wohoho! Haƙiƙa idan gwani da gwani suka haɗu a filin fama dole artabu ya zamto abin sha’awa da tashin hankali.
Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce ranar bikin BABBAR GIWA babu wanda ke fitowa ya taka rawa face JARUMAN DUNIYA.
Komai hassadar mutum idan yaga yadda jaruman ke yin artabun cikin gwaninta dole ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA.
A ɓangaren zakanya Juraima kuwa duk inda ta sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu waɗansu magashiyan.
Nan fa fadar ta kaure da guje-guje da ifice-ificen jama’a kowa ya shiga gudun ceton rai.
Sannu-sannu sai ga shi GWARAZAN MAYAKAN sun shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna bawa hammata iska, suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance tamkar ifritai.
Al’amarin da ya yi matuƙar ɗaure wa jama’a kai kenan kuma ya ba su mamaki suka ce a cikin ransu “haƙiƙa yau sarauniya Abidat ta ɗebo ruwan dafa kanta, kuma ta ɗebo ruwan dafa kanta, domin a iya tarihi ba su taɓa ganin jarumin da ya yi GABA DA GABA da sarauniya Abidat na tsawon wannan lokaci ba ba tare da ta kawar da shi ba, wannan fa shi ake cewa ɗan hakin da ka raina shi ke tsoka ne maka idanu.
A ɓangare guda kuma a ran su suna cewa yau abidat ta sayi ajalinta da kuɗin ta. Kuma mucijin da ta kashe bata sare kanshi ba. Ma’ana ta kashe Sarki urwat ga ‘yarshi ta zame mata ciwon idanu.
Duk sa’adda ɗayansu ya kaiwa abokin gwaminshi hari idan ya zille sai kaga duk abin da takobin ta sauka a kai sai ya yi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne, nan fa manyan giwayen suka hargitsa fadar baki ɗaya, kuma suka tashi duk halittar dake ciki, a ɓangaren zakanya Juraima kuwa ta zame wa dakarun sarauniya Abidat ANNOBA ƊARI kuma ƙadangaren bakin tulu sun rasa yadda za su yi da ita, duk inda ta sanya gaba sai dai kaga zaratan mazaje na zubewa ƙasa matattu, waɗansu cikin mawuyacin hali.
Nan fa fadar ta kaure da ihun mazaje gami da ƙarar karafniyar ƙarafa.
Ana cikin wannan hali ne jaruma Sulairat ta fahimci cewa idan aka ci gaba da wannan artabu a haka gine-ginen dake rushewa za su iya raunata bawa HIMLAS da baiwa SUNAILA.
Koda gama tunanin hakan sai ta dako tsalle daga inda take ta dira a daf da inda bawa HIMLAS da baiwa SUNAILA suke cikin zafin nama ta sanya takobi ta sare sasarin dake jikinsu, sannan ta sake dako tsalle ta dira akan zakanya Juraima, kawai sai juraima ta dako sufa izuwa inda su Himlas suke suka haye gadon bayanta sannan ta durfafi ƙofar fita daga fadar.
Amma sai sarauniya Abidat ta dako tsalle sama ta sha gaban su ta kaiwa SUNAILA sari da takobin ta, cikin zafin nama ta sanya takobi ta kare saran sannan ya mayar da martani, duk da ƙoƙarin da abidat ta yi na kare harin sai da takobin sunaila ta tsarga kumatunta kaɗan jini ya yi tsartuwa.


Kafin Abidat tayi wani yunƙuri, Cikin wani irin baƙin zafin nama Juraima ta daka wawan tsalle ta tsallake Abidat da dakarunta dira a ƙofar fadar ta falfalwa da azababban gudu cikin matuƙar takaici da baƙin ciki dakarun sarauniya suka rufa masu baya, amma kaico! Koda suka fita sai suka tarar wayam babu kowa, cikin matuƙar takaici suka suka ja suka tsaya, abin da ba su sani na shine jaruma sunaila ta sanya wannan sarƙar sihiri, bisa wannan dalilin ya sanya idanuwansu basu iya ganin su.
Koda labarin ɓacewar su bawa HIMLAS ya zo wa sarauniya Abidat sai kawai ta ɗauko madubin tsafinta a cikin aljihunta ta shafe shi da hannunta na hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, domin ta gudanar da bincike akan su, amma sai madubin ya yi bindiga ya tarwatse.
Cikin matuƙar takaici ta ƙarƙare kurma wawan ihu da karaɗe fadar baki ɗaya kuma ya amsa kuwwa izuwa gidan sarauta.
Tsawon daƙiƙa talatin tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta tsuke bakinta sannan ta durfafi ƙofar da zata fitar da ita daga fada ta kai ta izuwa gidan sarauta, fuskarta a murtuke babu annuri tamkar an watsa mata garwashin wuta a kai, cikin hanzari dakaru suka rufa mata baya.

Al’amarin su jaruma Sulairat kuwa sa’adda ta ceci rayuwar su bawa HIMLAS suka cigaba da gudu a bisa kan zakanya Juraima sai suka shafe tsawon sa’a ɗaya suna tafiya, sannan suka iso dajin Baitul-Shazwas, tun daga nesa Suhaimat ta hango su koda ta ga su uku a maimakon ‘yarta kaɗai sai ta cika da matuƙar mamaki, sannu a hankali suka iso gare ta bakin Kogon dutsensu.
Bawa Himlas ne ya fara sakkowa daga kan zakanya Juraima sannan Sunaila, Sulairat ce a ƙarshe.
Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta tare su tana mai yi masu lale marhaban, fuskarta cike da annuri tamkar ta haɗu da ‘yan uwanta na jini.
Kai tsaye ta jagorance su har izuwa cikin kogon dutse ta zaunar da su, sannan ta kawo masu abin kalaci da ruwan sha.
Da yake Sunaila da hilwas suna cikin matuƙar galabaita da yunwa nan fa suka shiga cin abincin hannu baka hannu kwarya, ita kuwa Sulairat sai ta dinga satar kallon Hilwas a fakaice.
Bayan sun kammala ne sun samu nutsuwa nan take Sulairat ta kwashe labarin abin da ya faru da ita a daren jiya ta yi mafarki bawa Himlas da Sunaila na cikin mawuyacin hali bisa wannan dalili ya sanya ta ziyarci birnin sin domin ceton rayuwar su.
Kuma ta bata Labarin irin gwagwarmayar da ta sha kafin ta ceto rayuwar su bawa Himlas tun daga farko har ƙarshe.
Sa’adda Suhaimat taji wannan batu daga bakin ‘yarta Sulairat sai ta cika da matuƙar tausayin su Sunaila, kuma hankalinta ya dugunzuma ainun.
Abu na farko da ya dugunzuma hankalinta shine haƙiƙa ceto rayuwar su bawa Himlas tamkar siyan ajalinsu ne da kuɗin su domin zai kasance dare da rana sarauniya Abidat na farautar rayuwar su. Sannan a halin yanzu shin Sulairat ta samu gagarumin ƙarfin da za ta iya GABA DA GABA da sarauniya Abidat har ta FANSAR RAYUKAN jama’ar birninsu da mahaifinta.
Kawai ta ɗago da kanta ta dubi Sunaila da Hilwas ta ce “haƙiƙa labarin ku akwai taɓa zuciya, kuma ni da ‘yata Sulairat zamu zauna tare daku cikin amana, har kawo lokacin da zamu ɗauki fansa akan AZZALUMA sarauniya Abidat.
Amma wani hanzari ba gudu ba, dole ne a kodayaushe mu kasance cikin shiri domin a kowane lokaci Abidat da dakarunta za su iya kawo mana FARMAKIN BAZATO”
Koda jin wannan batu daga Suhaimat sai Hilwas da Sunaila suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Hilwas ya buɗi baki ya yi gyaran murya sannan ya fara magana a karo na farko ya ce “haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki yadda kuka ƙarɓe mu kuma kuma bamu mafaka tare da ceton rayuwar mu, bamu da wani abu da zamu iya biyan ku. Ina mai yi maku alkawari ni da ummina cewa ba za mu ci amanar ku ba.
Sannan game da batun sarin bazato da Abidat zata iya kawo mana ina da wasu shawarwari da idan muka bi su za su cimma nasara.
Da farko a yau zamu kafa dukkan tarkuna a sama bishiyu da duk wata hanya ta shigowa wannan daji,

Sannan zamu kasu gida huɗu kusa da juna ta yadda zamu dinga samun bayanan juna,
Sannan dole ne mu yi amfani da makamai biyu Kwari da baka da wani daban domin kai hari ta nesa kafin yin karon batta da abokan gaba.”
Sa’adda bawa HIMLAS yazo dai-dai nan a zancen shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, domin ya kawo shawara mai kyau.

A gabar tekun Baharul-Aswad dake yamma maso kudancin duniya an yi wata babbar ƙasa da ake kira da suna Madinatul-haiwan.
Kasar Madinatul-haiwan ta bunƙasa a noma kiwo da ƙarfin tattalin arziki, daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan mayaƙa masu juriya a filin daga.
Sarkin dake mulkin birnin yakasance GWARZON MAYAƘI mai tarwatsa dandazon mayaƙa a filin fama, mashahurin attajiri ne kuma gawurtaccen matsafi na kiran shi da Nadiyar ibn shaiban.
Sarki Nadiyar ya shara a kaf nahiyar a jerin sarakunan dake makwabtaka da shi bisa ƙasaitar sa ne ya sanya sarakunan dake shakkar shi, domin ya zame masu ciwon idanu” kuma ƙadangaren bakin tulu”.
Sarki Nadiyar yana da matan aure guda bakwai. Gaba ɗaya matan sun kasance ‘ya’yan ‘ysn majalisar sarki bakwai, baki ɗaya ‘yan majalissar sun kasance wakilan ƙabilu bakwai mafiya yawa a ƙasar.
Domin haka kowacce ƙabilar tana matuƙar kwaɗayin ace jinin ƙabilarsu ta samu juna biyu ga sarki Nadiyar, sai dai duk cikin su babu wacce ta taɓa samun rabo, sarki ya gudanar da bincike sai shirun masaƙi domin ya gano mene ne ya sanya ya kasa samun magani amma sai halarar tsafin shi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa samun haihuwa ba face ya mallaki abubuwa guda biyu masu matuƙar wahalar gaske waɗanda neman su dai-dai yake da neman jaki mai ƙaho.
Abu na farko shine wata takobi mai abubuwan al’ajabi, mallakin sarkin bokaye.
Na biyu shine wata zakanya mai abubuwan al’ajabi dake ake kira da suna Juraima.
Waccan takobi zai yi amfani da ita wajen kashe wata mucijiya dake zaune a kogon Garul-musib, wacce da ake yiwa laƙabi da kuburul-shamshan wato uwar mucijan duniya, bayan ya kashe mucijiyar zai samu damar shiga wata ƙorama har ya ɗebo ruwanta ya kawo ɗaya daga cikin matanshi ta sha ruwan sannan zai samu magaji.
Binciken bokaye da masu hasashe ya tabbatar da cewa a halin yanzu a duk jinsin miyagun halittu babu mai ƙarfin damtse da sihirin tsafi tamkar mucijiya kuburul-shamshan.
Waccan zakanya kuwa zai yi amfani da ita a matsayin abin hawa, lokacin ita kaɗai dabbar da za ta iya jure wahalhalu har ya cimma nasarar isa kogon Garul-musib.
Sa’adda sarki Nadiyar yaga wannan al’amari sai hankalinshi ya dugunzuma ainun kuma ya cika da matuƙar farin ciki.
Abin da ya sanya shi farin ciki shine ya gano hanyar da zai samu haihuwa.
Abin da ya dugunzuma hankalinshi kuwa shine halarar tsafin shi ta kasa bayyana mashi cewa a ina ne zai mallaki takobin haɗe da zakanya.
Wata rana sarki Nadiyar na zaune a turakarshi bisa kujera, sanye da riga ‘yar shara da gejeran wando irin na hamshaƙan sarakai, ya ɓaje alƙalumman sihirin shi yana gudanar da bincike domin ganin irin wainar da ake toyawa a duniya, yana cikin wannan hali ne kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki.
Bakomai ne ya sanya sarki Nadiyar wannan dariyar farin ciki ba sai domin wani al’amari da ya gani a cikin halarar tsafin shi, wannan abu ba komai ba ne face a halin yanzu yana da halin da iya mallakar takobi tare da zakanya Juraima, kasancewar jaruma Sulairat dake da mallakin su ta bayyana kuma tana shirin kwabza yaƙi da wata ƙasaitacciyar sarauniya dake mulkin birnin sin.
Sai dai wani tunani da ya faɗo mashi shine ta ta ya ya zai mallaki abubuwan biyu, shin zai haɗa kai ne da sarauniya Abidat ko kuwa shi kaɗai zai farki dajin Baitul-Shazwas.
Haka dai ya cigaba da binciken a inda ya gano cewa akwai ɓoyayyen jarumi da zai kawo mashi cikas wajen cika wannan buri na shi, sai halarar tsafi bata bayyana mashi a ina jarumin yake ba.
Tun daga wannan rana sarki Nadiyar ya fara shirye-shiryen tafiya izuwa dajin Baitul-Shazwas domin farautar zakanya Juraima da takobin sarkin bokaye.

Ranar da tafiya dajin Baitul-Shazwas tazo tun da duku-dukun safiya sarki Nadiyar ya kammala shiri tsaf kuma yayi bankwana da dukkan iyalinshi gami da al’ummarshi ya kama abin hawa tare tawagar rakiya dakaru dubu biyar suka ɗauki hanyar da zata kai su izuwa birnin Sin.
Wannan shi ne abin da ya wakana ga sarki Nadiyar na kasar Madinatul-haiwan.

Mu haɗu a babi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen littafi
MANSUR USMAN SUFIHausa adventure novels
KARSHEN ZALUNCI book 3
Babi na biyu
Rubuta labari
Mansur Usman Sufi
08137237071
Littattafan Marubucin:-

Tafarkin tsira
Jaruman Duniya
Kogon Annoba
Sarautar mutuwa
Kangin bauta
Karshen...


Read / Download KARSHEN ZALUNCI Book 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album