Join Our WhatsApp Group

MASHIN SIHIRI 1 and 2 Complete Hausa Novel Document by MASHIN SIHIRI 1 and 2


MASHIN SIHIRI 1  and 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17384



MASHIN SIHIRI 1 and 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Abbas ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 99.39 kb

File Type: txt

Views: 849+

Download: 259+

Last download: 5 days ago

Description/Story: MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 1
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
babban kogon dutse ne mai cike da kayan tsafi iri iri daban da wanda ido bai taba gani.
acikin kogon dutsen an aje wani gunki jingine ajikin bangon kogon.
agaban ana kiran wannan gunki da suna sarkus.
agaban gunkin kuwa wani boka ne durkushe awurin idanun sa arufe.
ga dukkan alamu karance karance yake irin nasu na matsafa.
ga wani kosko akusa dashi hayaki yana tashi .
daga can kuma sai ya bude idanun sa yana waige waige yana duban aljani daya bari acikin kogon.
amma baya nan.
zumbur ya tashi daga in da yake zaune ya shiga yawo akogon ya na neman sa amma shiru kamar maye yaci shirwa.
da ya gaji da neman sa ne ya fara kwala masa kira! kana ina ne aljani mardis!
kana ina!
duk da haka shiru.
hakan yasa ya zauna yai shiru.
kwatsam ba zato ba tsammani sai ya ji an bushe da wata irin dariya. dariya data cika kogon gaba daya da amsa kuwwa!
amma bai ga wanda yake wannan dariya ba..
can kuma sai yaji an yi tsit da barin yin dariyar.
da wata irin babbar murya ake magana.
cikin fushi ake maganar ana fadin.
yakai boka hurujul mahas ina so kasani lokacin rabuwar ka da wannan aljani yayi.
ni ne nan na dauke shi.
sunana aljani jaras ibn safazi.
ba wani bane ya turo ni na dauko shi face.
mai gidana aljani bazagas na dajin jahur.
aljani bazagas ya sani na sato wannan aljani naka ne ba don komai ba sai domin yana so yayi masa wani aiki daban. wanda ni kaina ban san shi ba.
ina so kasani wannan rabuwa da kayi da aljanin ka.
ka rabu dashi kenan basa ka same shi ba.
saboda wurin shugaban aljanun duniya za a kaishi.
kai kan kasan duk wanda ya je wurin aljani bazagas da wuya ya dawo.
da ma ni nazo ne domin na aiwatar da aikin aljani bagazas kuma na aiwatar.
abin da ya rage mini yanzu shi ne na kaiwa aljani bagazas wannan aljani naka domin ya cimma bukatar sa akan sa?
boka hurujul mahas ya daga murya yace.
shin ko zan iya ganin wannan aljani nawa mai yimin hidima shekaru da shekaru.
ka bayyanar min dashi zamuyi maganar.
ka sani cewa idan har ka raba ni da wannan aljani nawa.
ka cuce ni. saboda mun shaku dashi mun zauna dashi shekaru masu yawa?
aljani ya kara bushewa da dariya sannan ya yi tsit yace.
ai yanzu bakin alkalami ya riga ya bushe baza ka kalli wannan aljani naka ba yanzu saboda ya riga ya shigo hannuna.
yanzu haka na rufe bakin bazai iya yin magana ba. har sai na kai sa in da ake bukatar sa.
boka hujurul mahas ya daka wa wannan aljani tsawa tare da fadin.
kai wannan aljani ina mai gargadin ka ka maido da wannan aljani idan kuma ba haka zaka shiga babbar matsala.
kai ba kai bama har wanda ya turo ka.
zan tanadi mara kyau agareku matukar ba kayi gaggawar bayyanar da aljanin nan ba.
hanya daya ce zaku bi ku tsira daga mummunan tanadin zanyi muku. shi ne kawai ka maido da wannan aljani.
koda boka hujurul mahas yaji haka sai ya kara busheya da mahaukaciyar dariya
kamar ba zai daina ba sannan ya tsuke bakin sa ya dakawa boka hujuru mahas tsawa yace.
kai bil'adama ka iya bakin ka kasan da wa kake magana.
fadan irin wannan maganar ga aljani bagazas ba karamin tashin hankali ba ne agareka.
rashin sanin ko wanene shi shiya sa kake fadan irin wannan maganar.
matukar kana so kana ka tsira da rayuwar to ka janye maganar raba ka da wannan aljani naka.
ina son kasan wani abu daya.
idan kana jin gobara daga kogi to shine aljani bazagas!
idan kana jin guguwar annoba to shi ne aljani bazagas.
acikin munanan hadarurruka to aljani bazagas ya wuce yanda kake tunani sanin ko wanene masifa ce.
zan tafi na barka.
kuma inaso ka kiyaye abinda na fada maka.
yana gama fadin haka
sai bar cikin kogon.
yabar boka hujurul mahas ya na kai kawo acikin kogon.
nan take boka hujurul mahas yaje wurin tarkacen kayan tsafin sa ya shiga bincike ta yadda zai gano hanyar da zai bi ya kwato wannan aljani amma babu bai gani.
sai daga baya da ya tsananta binceke ya gano hanya daya ce wadda zai bi don ya kwato wannan aljani nashi.
wannan hanyar kuwa itace.
dole sai ya nemo wani mashi na sihiri. wanda ahalin yanzu bokaye da aljanu da sauran sarakuna suke so su mallaki wannan mashi.
to yanzu ya za ayi ya samo wannan mashi wanda zai iya yakar aljani bazagas kuma ya mulki duniya gaba dayanta.
nan fa ya kama tunani shi kadai.
daga karshe ya yanke shawara dole sai ya fita daga cikin wannan kogo yashi ga duniya ya kara ilimin tsafi ta yadda zai mallaki wannan mashin sihiri?
yana gama aiyana haka ya fara tattara kayan tsafin sa. ya daura gurayen tsafin sa ajinkin sa.
ya fara karanta wasu dalamisan tsafi. nan take ya bace bat daga cikin kogon tamkar bai taba wanzuwa ba.

*** acan dajin aljani bazagas kuwa***
daji ne wanda ido bai taba ganin sa.
aciki dajin ne gidan aljani bazagas yake . amma idan kashi go baza ka taba sanin akwai gida adajin ba saboda akarkashin kasa gidan yake.
aljani bazagas yana cikin fadar sa ya na kaikawo.
yana jiran isowar wannan aljani daya tura ya sato masa aljani mardis.
yana cikin kai kawon ne kwatsam sai ga wannan aljani da ya aika ya bayyana dauke da aljani mardis akafadar sa........
in karasa muku ne.
sai na ji ku

By ABBAS
With Shuraih 99%
ρðšтєđ вч
Shuraih Usman
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 2
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~


aljani bagazas ya juyo.
ko da yayi arba da aljani jafas sai tare da aljani marsdis rungume akafadarsa sai ya bushe dariya kamar bazai daina ba sannan hade fuska yace.
yakai aljani jafas ina so ka kai wannan aljani dakin tsafi na ka aje shi kafin ya farfado ina so juwar masa da kwakwalwa da yadda zai manta da komai hatta wanda yake hidima awurin sa wato boka hurujul mahas.
ya zamana cewa ya dawo yana min kallon boka hujurul mahas?
nan take aljani jafas ya cika umarni yakai aljani mardis dakin sihiri..
shi kuwa aljani bagazas ya kyalkyale da dariya sannan ya bace.
sai gashi ya bayyana acikin dakin sihirin nasa
ko da yaga aljani jafas akwance shame shame akasa sai ya kara bushe dariya sannan ya murtuke fuska ya dauko wani koskon sa na tsafi ya kunna wutar tsafi.hayaki na tashi.
sannan ya shiga kewaye aljani mardis idanunsa arufe yana karanta dalamisan tsafi.
sai da ya gama sannan aje koskon gefe guda ya zubawa aljani mardis ido ya kallon sa.
adai dai lokacin ne aljani mardis ya farfado ko da ya tsinci kansa awannan dakin wanda bai saba ganin sa ba sai ya kama waiga waige.
yana kallon cikin dakin .
sannan ya dubi aljani bagazas wanda yake masa kallon boka hujurul mahas yace.
ya shugaba na ya akayi muka zo nan wurin ko dai mun kaurane daga wancan kogon dutsen. ni nasan na kwanta barci.
ko da aljani bagazas lura da cewa sihirin ya fara tasiri akansa.
sai ya bushe da dariya yayi tayi kamar bazai daina ba.
daga can sai ya murtuke fuska ya juyawa aljani mardis baya yace.
akwai abinda zaka shi yasa muka dawo nan.
kuma rashin cimma wannan buri dana sa agabana babbar matsala ce. kuma nayi bincike na gano kai ne za ka iya yimin wannan aiki. saboda kaifin tunaninka da basirarka da kwazon ka.
ina so kaje birnin zamar.
wato birnin sarki maharu.
ko da jin haka sai aljani bagazas ya tashi zumbur daga zaune da yake. ba komai ne yasa ya tashi ba face sanin sarki maharu.
ba shi da mutunci ga zalunci.
kai hatta birnin baya bari baki su shigo.
don haka ne ya saka dakaru ko ta ina a birinin shi mutun da aljan suna gadi saboda tabbatar da tsaro.
kai saboda mummunan tsaron da sarki maharu ya bayar.
har waje wajen birnin dakaru ne abaje ko ta ina su na kai kawo don ba da tsaro.
sarkin maharu yana da kyakkyawar 'ya ta gaban kwatance.
wanda idan ka kalle ta sai ka rantse cewa babu wata mace da ta kaita kyau duk fadin duniya.
saboda hakane sarki maharu yake bata kyakkyawar kulawa.ko ku da baya so ya sauka ajikinta.
aljani mardis ya dubi aljani mardis yace . birnin zamar fa kace naje.
ba ka da labarin sarki maharu ne irin zaluncin sa da irin mummunan matakan tsaron da ya aje agidansa na dakarun mutane da aljanu.
aljani bagazas ya yi magana ba tare da ya juyo ba yace.
na sani kuma kai kadai ne za ka iya yin wannan aiki amatsayin ka na sadaukin aljani.
ina so ne kaje birnin zamar.
akwai wani mashi na sihiri awurin sarki maharu shi nake so ka sato min ka kawo min shi nan wurina.
akwai wani dalili daya sa ni bazan je da kaina ba.
na samo labarin cewa wannan mashi yana hannu sarki maharu.
kuma duk wannan ya mallaki wannan mashi idan har yayi wata daya ahannun sa to shi zai mallaki duniya gabadayanta.
mutane duniya su dawo gareshi ya zama dole kafin sarki maharu ya cika wata daya da wannan mashi to mu tabbatar mun rabashi dashi.
ka sani cewa ba mu kadai ba ne muke da muradin wannan mashi akwai sarakuna da manyan bokaye wanda suma burin su suga sun mallaki wannan mashi.
matukar idan bamu mallaki wannan mashi da wuri ba to fa akwai babban ruguntsumi agaba saboda sarki maharu ya kammala abinda zaiyi da wannan mashi har wata daya ya cika to mun shi babbar 'ukuba ya zama dole ka aiwatar da abinda na saka ka da wuri wuri amatsayi na na wanda yake saka hidima.
ina so ka sani baka da sauran wani hutu kawai sauri ka fara shirin tafiya birinin zamar domin raba sarki maharu da wannan mashi na sihiri............
kuyi comment da wuri.
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 3
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
aljani mardis ya sunkuyar da kansa na dan karamin lokaci yayi tunani kafin ya dago da kansa ya dubi aljani bagazas yace.
naji ya shugabana zan tafi saboda abinda ka fada na cewa zamu shiga mummunan hadari idan har bamu raba sarki maharu da wannan mashin sihiri ba.
to yanzu kana ganin mu idan muka samu wannan mashi ta yaya zamu rike shi har wata daya. ba tare da wasu sun kawo mana farmaki ba. kasan cewa dole yanzu matsafa su dukufa wajen neman wannan mashi.
domin su mallake shi.
ina ganin kamar wasu ma suna kan haryar zuwa wurin sarki maharu su rabashi da wannan mashi. duk da nasan baza su iya ba.
.
aljani bagazas yace.
ai shi ne nace kayi gaggawar tafiya saboda gagarumar matsalar da take tasowa nan gaba.
ina so muyi muga mun samo wannan mashi mun cimma bukatar mu akansa.
duk abinda zai faru abirnin zamar zan dinga kallonka ta madubin tsafi na.
idan naga abin zai fi karfinka zanzo na kawo maka dauki.
amma ina so kai ka fara zuwa.
aljani mardis yace ina so ka hada ni da dakaru wadanda za sumin rakiya.
izuwa birnin zamar.
aljani bagazas ya bushe da dariya yace wannan ba matsala bace.
ka fita waje zaka wadanda dakaru na jinsun ku na aljanu sai ku tafi tare dama tuni na tanadar maka su.
ko da jin haka sai aljani mardis ya fita waje sai gashi yayi arba da wadannan dakaru na jinsin sa.
nan take aljani mardis ya bude fuka fukan sa ya tashi sama suma sauran dakarun suka tashi sama su bishi abaya.
su dukan su suka luluka acikin gajimare suna zabga gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya.

****al'amarin boka hujurul mahas kuwa***
tun lokacin daya bace daga kogon dutse bai bayyana ako ina ba sai acikin wani daji in da gidan wani shaharen boka yake .
lokacin da boka hujurul mahas ya shigo wannan daji sai yayi murmushi kawai sai ya fara tafiya acikin dajin.
sai da yayi nisa da tafiya acikin dajin yazo tsakiyar dajin sannan ya fara karanta wasu dalamisan tsafi.
faruwar hakan kenan sai ga wata mararrabar hanya guda uku ta bayayyana.
nan take boka hujurul mahas ya tsaya yana nazarin hanyoyin guda uku ya rasa wacce zai bi acikin su wacce zata kaishi izuwa gidan boka saljan.
ko da ya ga kasa gane hanyar da zai bi sai ya dauko wata sanda ta tsafi ajikin sa.
ya karanta wasu kalmomi irin nasu na matsafa ya tofa ajikin sandar sannan ya sake sandar ta tsaya cak acikin iska kawai sai sandar ta fara tafiya ta taba hanya farko. sannan ta wuce hanya ta biyu.
ko da ta taba hanya ta biyu sai ta tsaya cak. ta kasa gaba ta kasa baya.
ko da boka hujurul mahas yaga haka sai yayi murmushi .
ya tabbatar da cewa wannan itace hanyar.
kawai sai ya dauki wannan sandar tasa ta tsafi ya shiga wannan hanya ta biyu.
maimakon ya tsinci kansa agidan boka saljan sai ya kara yin arba da wasu hanyoyi guda shida agabansa.
nan take ya tsaya yana karewa hanyoyin kallo yana nazarin ko wacce hanya .
amma ya kasa gano hanyar da zai bi.
hakanne yasa ya dauko wannan sandar tasa ta tsafi .
ya karanta dalamisan tsafi kamar dai na farkon hayoyin da ya wuce.
amma ya na sake sandar sai yaga ta fadi kasa.
sihirin sa yaki yayi tasiri.
al'amarin daya dugunzuma hakalin sa kenan.
ya sunkuya ya dauki sandar ya karasa gaban hanyoyin yana kare musu kallo.
yanzu acikin wadannan hanyoyi guda shida wacce zan bi. ya tambayi kansa amma babu amsa.
hakanne ya sa ya dubi hanya ta biyar kawai sai ya shige kai tsaye .
yana shiga kofar ta kulle kanta.
al'amarin daya bashi tsoro kenan.
kawai sai ya cigaba da tafiya yana waige waige.
ya na cikin tafiya sai tsintar kansa yayi acikin kusugumin daji daban .
abin da ya bashi mamaki kenan.
sai yanzu ya tabbatar da cewa yabi wata batacciyar hanya wadda ba itaba.
kawai sai juya da baya da nufin ya fita yabi wata hanya.
kwatsam!!
sai yayi kicibis da wani jibgegen zaki mai tsananin girma da kwarjini wanda sai an hada manyan giwaye guda biyu kafin suka girman shi.
ko da ya yi arba da wannan zaki sai yayi baya da gudu

BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 4
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
ya bar zakin atsaye awurin ya cigaba da gudun.
shi kuwa zakin ya tsaya a inda yake yana kallon boka hujurul.
daga can kuma sai ya bace bat.
sai gashi ya bayyana agaban boka hujurul mahas.
cikin zafin nama boka hujurul mahas ya zare takobin sa alokacin da zakin ya yi tsalle ya kawo masa farmaki.
da azama ya kare harin zakin.
nan take suka cigaba da bakin gumurzu.
ana fara wannan artabu boka hujurul mahas ya lura da cewa wannan zakin yafi karfin sa.
ko da ya fahimci cewa zakin zai iya hallaka shi farat daya.
kawai sai yayi amfani da karfin sihirin sa.
ya tashi sama.
ya cigaba da...


Read / Download MASHIN SIHIRI 1 and 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album