Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

TARKO Complete Hausa Novel Document by TARKO


TARKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 166740



TARKO

Reading Time: 13 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Zainab Idris Makawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 876.16 kb

File Type: txt

Views: 2328+

Download: 4391+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: 🕸🕸TARKO🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


Da sunan Allah mai,rahama mai jin kyai, duk kan godiya da yabo ya tabbata a gare shi, wanda ya yi mu ya wadata mu da ni,imomin sa,
Wanda ya shari,anta yin addu,a zuwa gare sa, ,kuma yai muna ni,ima da baiwan shi, akan mu roke shi duk bukatocin mu,,
Ubangijin,mu wanda ya ce idan su ka tambaya a gamay da ni,
To ka basu labarin cewa ni din makusancin ne a gare su,
Ina karba adduan mai addu,ar mai, addu,a idan ya roke ni,
Ya Allah tsira da amincin ka su tabbata ga fiyayyen talikai,
Annabi rahama Muhammad S A W, da halaiyen sa da sahabban sa da ma duk wani musulmi wanda yabi tafarkin gaskiya har izuwa ranan Alkiyama,,,,,,,
Ya Allah ina rokon ka da da gode maka da ka bani wanan daman na rubuta wanan dan gajeren labari,
Ya Allah yadda ka nufeni da farawa lafiya Allah ka bani ikon kammalashi lafiya,
Ya Allah dani da na rubuta da wanda duk kabawa ikon karantawa, Allah ka yafe muna kurakuren mu,
Allah ka sada mu da rahamomin ka da ni,imomin ka ,
Ya Allah kasa Aljannan fiddausi tazamo makomar mu,,,,,,,,,

BARKAN MU DA SALLAH YAN UWA,,,,,,

A hankali ya sa hannun shi saman kan shi ya cire farin rawanin dake saye a kan shi,
Farin rawanin da a kasar hausawa sai wani mai, sarauta ko malami ko wani babban mutum ke sawa kan su shi,
Gefen guda daga inda yake zaune saman shimfidar dake a cikin rufan da ke kofar gidan shi,
Rumfar wanda ya a kayi manne da ginar zauren gidan, a ta gefe guda,
Sai shimfidar da akayi wa wani gadon kara dake a cikin rufar,
Shimfidar ya sha kayan laushi irin daddumar nan na da ja,jayen kala,
Daga gefe guda littatafan addini ne kala kala tare a guri guda,
Sai kuma wasu allunan katako, dake tare a guri guda,
Wanan abubuwan zai nuna wa mutum cewa runfar na wani malamin irin kasar hausa ne,
A hankali dan tsohon ya dan jawo jikin shi daga saman shimfidar da yake a zaune,
Gurin da wata butar silver mai ruwan gold yake a je da ruwa ya nufa, a hankali ya fara gabatar da alwala a tsanake, kamar yadda addini ya umur ta,
Bayan ya gama alwal ne ya kara gunda ruwa ga baki yayin da yake mikewa tsaye ya zubar a saman bangon shiga cikin gidan shi
A hankali ya ke dan takawa zuwa kofar fita cikin rumfar tashi,
Jama,a ne a,waje da alamar shi suke jira, daman yafito gaba dayan su , suka mike tsaye,
Bata lokaci aka fara gabatar da sallah azahar na ranan,
Bayan idar da sallah tsohon yadan kai wani lokaci a gurin zaune yana tasbihi,
Duk wanan jimawan da yayi a zaune bai hana mutane zanan jiran fitowar shi ba,
Ya fito fuskan shi dauke da annuri mai kama da murmushi a koda yaushe,
Yara ne daga gefe guda suna ta taruwa da alama karatu zasu yi a gurin,
Saboda irin yadda suke ta tururuwan fitowa daga cikin gidan,
Hakan ya nuna cewa gidan na malam Manya, babba gida ne mai tarin jama,a acikin sa,,

Tarin wanke wanke ne a gefe guda kuda na bin su,
Daidai lokacin da wata mata yar kimanin shekaru, hamsin da tafi daga dakin ta, tana kokarin gyara daurin zanin ta,
Gani kwanonin da ba,a wanke ba har izuwa yanzu yasa matar sake wani irin wawan tsuki, a lokaci guda ,,,
Takalman silifas din ta dake a kofan dakin ta take kokari zurawa kafan ta sai faman mita takeyi, tana cewa ace izuwa yanzu ba,a wanke kwanonin da akaci abinci a cikin sa ba,,,
Amma yau idan na kama wanan Yarinyan sai rayuwar ta ya baci,

Cikin gidan babbane mai sassa guda dai,dai har goma sha, biyar, duk sassan gidan na 'ya'yan malam Manya ne, sai mutum uku ne kawai diyan yan uwan shi da ya karantar kuma yai masu aure suna zaune a tare dashi,
Duk diyan malam suna da aure sai mutum guda wanda shine autan malam wanda ake cewa Isah,
Amma Abdullahi ya bace wada suke kiran shi, da shi saboda acewar mahaifiyar shi tun haihuwar shi da tasamu kudin suna ta, sai dabbobi tana kiwo shine suke ta kawo mata kudi,
Mahaifiyar Audi, itace matar malam na karshe wacce daga ita bai kara wani aure ba,,

Dan malam na farko shine baba Buhari, sai na biyu Sha,ibu, sai Musa, sai Gwago, Laira, gwago Lanto, sai Hamza,, Yahaya, duk diyan mace guda ne,
Ismail, shi da Habiba uwar daya amma ta rasu dadewa, tun gurin wani haihuwa,
Asiya, Rabi, da Audi su kuma diyan mama Rukaiyya ce Amaryam malam, ta yanzu,
Wanan babban gidan na malam manya, yana nan a cikin uguwar da ake kira da Shiyan Sarakuna, dake a cikin garin Birnin Kebbi,
Wanan shiyan kowa yasan cewa shiya ce ta haifaffun gari da kuma baki masu asali, ke zama gurin,
Yanzu haka, zaka samu mazauna unguwar duk kowa yasan kowane gasu da yawan ilimin addini tare da na zamani,
A tsakiyar unguwan zaka samu gidan malam Manya, wanda shi da daukacin iyalin shi suke a ciki,,
Babban diyarn Buhari mariya, sai, Abubakar wanda ya ke bi matan sai mata ne har su biyu, su ke bi mashi, sai daga baya mahaifiyar tasu ta samu maza,biyu da mata biyu,,,
Don haka yaranta sune manya a gidan gaba dayan, saboda, a kusan jere tai ta haihuwan ta,
Ba karamin kokari malam Manya keyi ba gurin ganin cewa hankalin iyalin shi, ya zamo guri guda,
Amma duk da haka akwai, baraka a tsakanin matan wanan babban gidan don sun kashi kashi dakashi a tsakanin su,,,,,
Yanzu haka ita matar malam wace a,ke,cewa maman Audi,
Kansu a hade yake da Amaryan malam watau maman Audi,
Wanda hakan ya samu asaline don kusan a lokacin da malam ya auro ta ita mahaifiyar su Audi,,,,
A tare suke hurda da mama Ladi, wace da ma bata kaunar zama da mahaifiyar mijin ta,
Hakan yasa da malam ya auro maman Audi, sai Ladi ta jata a jiki,
Shiko Ismail da kaunar shi wace da mahaifiyar su bata da rai, a gidan sai aka ware su,
Hakan ya sa Shi Ismail yake da kwazo da neman na kan shi,
A can cikin dangin mahaifiyar su gwandu ya auro matar shi,
Wace take zaman hakkuri a gidan tare da yaran ta,
Sai dai sauran matan yan uwan Buhari sam basu yarda, da wulakancin mama Ladi ba sam, saboda suna ganin cewa bata fisu ba,
Ya sa sam ba su yarda da da wanan cin fuskan da,takewa sauran matan gidan,

Sashin mata daban a makarantan sashin maza da ban
Matan suna zaune kusa da kakan su inda suke daukan karatu,
Malam baya yarda yarinya ta girma batare da ta sauke alkur,ani maigirma ba,
Don duk wace zaiwa aure a gidan dole sai ya kasan ce ta sauke littafi mai tsarki,
Don haka komai kankantar yarinya dole tana zama da zaran lokacin karatu yayi don gudun makara saboda bulalan da malam ke dan shada masu a hannun su idan sunzo a lati,,,
Sauri takeyi don gudun makara don tasan cewa malam yanzu ya fito daga cikin massalaci,
Saboda agogon bango dake sagale dakin mahaifiyar ta ya nuna mata cewa, biyu da minti talatin daidai,
A cikin saurin da ta keyi ne suka hade hanya da mama Ladi wace ta zo sa shen nasu don neman Meenat din
Meena wace ganin mama ladi yasa gaban ta faduwa don tasan cewa ko banza sai kunuwar ta yasha murda gurin mama,
Da sauri Meena ta ja baya daidai inda mama ta kai mata bugu ta gwauce,
Gaba ta sata da masifa inda dole ta aje Alon ta zuwa sashen mama ladin,
Sai da ta wanke kwanonin tas sanan ta, dauki allon ta zuwa kofan gida,
Tun fitowar ta hankalin malam Manya, yake a kan yariyar wace, ke ta dan sharan kwalla, da habar hijabin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download TARKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album