Join Our WhatsApp Group

HATSABIBIYA JIDDA Complete Hausa Novel Document by HATSABIBIYA JIDDA


HATSABIBIYA JIDDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22247



HATSABIBIYA JIDDA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, Dec 2023

Author: Jidderh ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08130619354

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 132.23 kb

File Type: txt

Views: 1005+

Download: 415+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: Hatsabibiya Jeederh na Jeederh Beauty




*HATSABIBIYA JIDDERH*👯🏼‍♀️

*na jidderh*


*freee book ne littafina sai de rashin comment yasa ya koma na kudi*🤸🏻‍♂️

*kai dagajin sunan kasan jidderh ta tsula tsiyarta ciki*💃

*ga duk mai bukata sai tamin mgn ta wanan nomber*08130619354*

*inkinsan bazakiyi comment ba kar kimin mgn domin zancireki*💁‍♀️

😘😘😘😘🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

*sai munhadu cikin hatsabibiya jidderh*

©🎆

*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...

🅿️1️⃣

...."Allah ya tsinewa duk wache ta dibarmin ruwa."
Bata rufe bakinta ba wata mata naji ta chafe zanchen ta hanyar cewa yatsinewa uwarki, shegiya mara hankali."

Kutt, cewar yarinyar da bata wuce shekara goma sha hudu ba .

"Uwa ta fa kikace, yamah sunanki? Saude koh, to wlh yau kintabo bala'i da kudinki, kar kiga wai kina matar baba na na kyakeki wlh sai kinyi dakinsani zagina da kikayi."
ta fadi tana murguna baki.

"Eheee, nice ma Saude lalle Hauwa kin haifu acikin Sahura tabbas ke jininta ce.

"Au da baki yarda ba kenan? zamu gamu ne wlh sai narama fin zagin da kikamin."

daga haka ta fice agidan batare da tajuya taga Saude ba.

Futar ta babu jimawa ta karasa gun Garba mai shago wanda yake kusa da gidansu

Garba mutum ne masifanfe, wanda shi ka' idarsa baya karbar bashi da rana sai dare mujinki yadawo tukum zeje da kansa yayi sallama ba kuma ze tafi ba sai anbashi kudinsa .

Yasha kashe auran mata da yawa dalilin haka sautari yaje to kuwa sai aure ya mutu atake.

Sallama ta masa tace "Garba mai shago barka da rana, ya kasuwa?"

yace "Hauwa kulu jidderh mai ladabin kare, daga ina haka ?"

Dariya jidderh tayi tace "Inna Saude ce tace kaban madarar ruwa guda biyu da kuma manyan bisket guda uku da leman kwalba guda biyu.

Garba yaji ciniki yace "amma de jidderh bak'i kukayi koh?"

Dariya Jidderh tayi tace "Eh, k'annan malama sukazo daga gashewa .

Yace "Allah sarki, nan Garba ya had'a duk abunda ta lissafa ya bata sukayi sallama ta juya abunta.

Ba gida ta nufa ba, wani gu naga tabi a'lamun layin babu kowa cike tafiya tayi mara tsayi sosai sai kuma tazauna kan dakali ta bude kayan nna taci ta koshi tabar sauran, tasan yau yadda sukayi da Saude bazata bata abuncin ba dan haka tayi maganinta.

Tana zaune agun wata bakar mota tazo da tsaya gefanta

Bata ma kula ba, domin tayi nisa cikin tunanin abunda kuma zata shiryawa saude dan bata huce ba, taya zata dauki ruwan da zatayi wanka ta d'ibar mata, dan ta aiketa markade kafin ta dawo ta d'iba sabida renin wayo.

Wani gaye ne naga ya futo cikin motar amma fa ya hadu iyakar haduwa babu karya cikin haduwarsa cikin sauri
ya karasa gunta yayi ya mata Sallama

Juyawa tayi amma bata amsa ba.

yace "bewar Allah dan Allah Gidan Mlm Kabiru mai kyara nake tambaya?

Jidderh tace "Mlm wah ma kace?"

Yaji zafin tambayar amma ganin yabar mara lafiya cikin mota yasa shi cewa "dan girman Allah kisan Gidan Mlm Kabiru mai kyara? Ance kowa yasanshi cikin garin, munzo da mara lafiya ne yana cikin mota pls."

Zunbur ta mike tace "muje nagani ko kalya kake .

Mamaki sosai yayi amma ganin ze bata lokaci yace "Ok muje ."

Har bakin mota yakaita tace "bude nagani toh".

Tsaki yayi wanda yayi dede da budewar motar

Tace "kace beda lafiya amma kuma har yasan tsaki? dan remin wayo kawai."

Na cikin motar ne Yace "dallah Salis shiga mota mutafi ya kuma tsaki akaro na biyu."

Juyawa tayi tace "shikenan naga mai zafin kaine, amma yaci darajarka kuzo muje nakaiku, amma mota bata shiga cikin lungun saide mutafi da kafa."

Salis yace "Ok,

Allah yasa babu nisa."

k'arasawa ya kuma yi jikin motar yace "Oga futo mutafi zata kaimu."

"Dallah Malam kazo kaja mota mutafi, kana ganin yarinyar nan kasan mara hankalice, amma ka zauna kabiye ta sai shirme kuke kai da e'ta."

Salis ne yayi murmushi yace "kayi hakuri Oga futo kawai mutafi.

Yafi minti goma yana na zarin tafiya da mahaukaciyar yariya, Salis ne ya katse masa tunani ta hanyar cewa "haba Oga kafuto man.

Futowa yayi yana karewa unguwar kallo banda dole maize zo yinan, kauyen garibanda bola babu komai , tsaki ya kumayi yayin daya gama futowa cikin motar.

Duk abunda sukeyi Jidderh na kallonsu amma batace komai ba .

Gaba tayi suna binta A baya Salis ne yace "Oga mutafi ahankula sbd kafar taka."

Tsaki yayi yace "mutafi kawai ."

sunyi tafiya takai ta minti talatin tin Salisu yana tambayarta gidan da nisa ne haka, har yayi shiru domin shima ya gaji balle Oga da har e'donsa yayi jah sabida Azaba.

Jidderh kuwa hankali kwace take tafiya ko ina ma bi take dasu babu ruwanta dan bukatarta su jikata kowa yaji A ajikinsa.

Oga ne ya fadi sabida wani zugi da kafarsa takeyi dan Azaba cikin azama Salis yajuya yace "Yah sallam, oga lafiya?

Babu bakin mgn sai kafar yake nunawa Salis cikin furgice yace "Bewar Allah har yanzu bamuzo ba ne?"

Juyawa tayi ta kwashe da dariya tace "Inama zan kaiku? na manta ne ."

Salis ji yayi kamar yaka sheta yahuta, ta manta inda zata rakasu lalle ya yarda mahaukaciya ce."

Oga yace "Salis ka yarda mahaukaciya ce ko? wlh na warke yar nan ko waye Ubanta sai na daureta." yakarshe cikin zafin nama.

Jidderh tace "Oho de, burina shine kasha wuya, kuma kasha dan haka sai anjima.

daga haka ta juya tana dariyar mugunta 😃

Tinda oga yake beta ba shiga bacin rai ba kamar na yau ba, amma yayi alkawarin daure yarinyar ko ze rasa komai nasa .

Wani mai kafu baburne yazo hucewa ganinsu kan hanya yasa shi tsayawa

Yace "bayin Allah lafiya kuke tsaye cikin rana?"

Salis ne yayi karfin hali Yace "yawwa bawan Allah gidan Mlm Kabiru mai kyara muke nema?

Mai kafu babur yace "Ayya kuhau na kaiku ai babu nisa.

Salis ne ya dobi Oga yasan zeyi wuya yahau nape ta daukar kaya

yace "Oga tashi mu hau sai nadawo nadau motar."

Oga da kafarsa yakeji tabkar zata cire shiru yayi bece komai ba,

Salis yace "bawan Allah yi hakuri mu kamasa mu daurasa, baze Iya tafiya ba.

Haka suka kama Oga suka sashi cikin ta b'are kamar kayan wanki

Shima Salis be tab'a hawa ba balle Oga koh taxi be hawa, amma yau gashi dalilin mahaukaciyar yarinyar nan sun hau .

Cikin minti biyar ya kawosu gidan hakan kuwa yayi dede da zuwan Mlm Kabiru daga kasuwa

Cikin sauri ya karaso garesu ya kama Oga suka shiga dashi cikin gidan d'akinsa ya nufa dashi suka zaunar dashi kan sallaya da ke shinfide cikin d'akin .

yace "Sannu bawan Allah. cewar Mlm Kabiru

Oga de bece komai ba.

Salisu ne yace "Sannu Baba."
bayan sun gaisa ne Salis yake masa bayanin daga Abuja muke, Baba ni suna na salis wannan kuma Kamal mai gida na ne, sunyi hatsari ne ya karye aka masa daurin asibiti yanzu kuma take masa zafi.

"Ayya Sannu Kamal, bari nadoba naga kafar .

dobawa ya farayi cikin hikima Yace "lah daurin ne beba, sai ansake."

cikin tausayi Salis yace ynzu baba wani dauri za'a kuma masa kenan?"

Mlm Kabiru yace "Insha Allahu yanzu zamu daurashi, kayi hakuri babu komai Insha Allahu

SaLis de zuciyarsa ta masa babu dadi sosai amma babu yadda zeyi tinda hakan shine mafuta garesu.

cikin minti talatin Mlm Kabiru ya d'aurasa ya kuma tausaya masa sosai ganin yadda kafar tayi tsami.

Da gudu ta shigo gidan tana makawa Babanta kira Baba~ Baba jin muryar jidderh yasa shi cewa gani fa shigo ina d'akin fatan de ba magana kika dauko ba .

d'akin ta nufa ta shiga ko Sallama babu ganin wanda ke cikin d'akin yasa ni mamaki 🤔 daman Malm Kabiru mahaifin Jidderh ne?


kallon ~kallo sukayi wa juna tsakanin Salis, da kuma Kamal, ga kuma jidderh.

MUHAD'U SHAFIN GABA 😘😘

*jidderh ce*🥰🥰🥰🥰🥰🥰

*HATSABIBIYA JIDDERH*👯🏼‍♀️

*na jidderh*

©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...

🅿️2️⃣

.........Cikin karfin hali Jidderh tace "lah Baba daman wanan Gunka zukazo? nagansu bakin hanya A zaune."

Mlm Kabiru ne yayi murmushin karfin hali, yasan wannna kallo da walakin abunda yafaru tsakaninsu .

Yace "nan sukazo, ke daga ina kike yanxun?"

Jidderh tace "Inna Saude ce tace nakai mata markade,
to naje nakai yanzu na koma daukowa na tarar Akuya sun cinye garin gaba d'aya bokatin ma sun fasa."😳

Mamaki ne yakama Kalma tabbas maganar sa gaskiya ce, yarinyar bata da hankali.

Salis kuwa dariya abun ya basa ganin budurwa kamar wannan amma babu hankali atare da e'ta .
Mlm Kabiru ya numfasa, Yace "tashi kije ina tare da bak'i zan shigo gidan .

Tashi tayi har taje bak'in kofa sai kuma ta juye ta wa Kamal gwalo tukum ta futa.

Takaici ya kamasa yayi da Salis banda dariya babu abunda yake.
Mlm kabiru yace "kuyi hakuri haka take, nasan ba haka kawai kuka rabu ba, domin kuwa had'uwa da jidderh kaddara ne , dan shari ma ya isa kaguje ta, In kuwa ta jima da ku to akwai muguntar da zata muku sannan ku rabu."

Salis ne ya numfasa, yace "lalle kuwa naga A'lama.

Kamal kuwa da zuciyarsa ke masa zafi be ce kala ba.

Mlm Kabiru ya dauko magani yashafa masa Yace "Insha Allahu nan da kwani k'adan zata warke, zaku zauna a'nan har sa na since daurin zaku tafi ."

Kamal A zabure yace "A nan zamu zauna, gida daya da wannan yarinyar?"

Salis ne ya tarin zanche Yace Babu komai Baba zamu kira gida musanar musu Insha Allahu zamu zauna kamar yadda kace."

Mlm Kabiru yace "babu komai yaro bari nashiga cikin gidan.

"Toh, shine abunda Salis ya furta yayi da kamal yaji kamar ya kashe Salis dan haushi.


"Saude!! ~Saude!! kina Ina wai? naje nadauko miki garin akuya ta cinye, harma ta fasa bokatin.
cewar Jidderh

Saude ta futo hankili tashe tace "ta cinye garinfa kikace?

Toh wlh ko Uwarki zaki siyar sai kinbiya kudin garin nan."

Bata rufe bak'inta ba akayi sallama cikin gidan,

Saude lafiya kuwa naji hayaniyarki har gida na?"

cewar wata makobciyar Saude da tsautsayi yashigo da e'ta .

Barni Salma, wlh wannan shegiyar yarinyar ce na bata gari nik'a ta dawo wai akuya ta cinye."

Salma Tace "na gaya miki kice Mlm Kabiru ya dauketa yakaita gaban Uwarta baki yarda ba, toh wlh inde Jidderh ce sai ta kasheki da raiki ."

To wai ke Mlm Kabiru tin yaushe nake gaya masa, yarinyarce mayya mai jinin mayu taki tafiya. manta Sahura kikayi irin nacin dake cikin Sahura to shi tabiyu shegiya mayya." cewar Saude

Salma Tace mayya kuwa ta gaske, ki kamata kimata dokan kudinki ko kuma ki karya ta ta zauna gu d'aya tinda bata da amfani .

Duk abunda suke fadi Jidderh na tsaye tana jinsu bata ce komai ba.

futa tayi daga gidan ba tare da tace komai ba

tafiya kadan tayi taje gidan sirikan Salma daman tsakaninsu babu wani jituwa dan basa san Salma kawai tana zaune ne dan dole, dan ko magana bata had'asu da dangin mujinta .

Sallama tayi tace "Mama Tabawa kina nan ashe?
Mama Tabawa tace "Jidderh ina zani?

Tace Mama Tabawa wani magana nazo muyi amma dan Allah karki ga yawa Kawo mujin Salma dan ba zeji dadi ba."

Mama Tabawa kuwa nutsuwa tayi dan jin bayanin Jidderh tace "Ina jinki Jidderh lafiya ?

Tace "yanzu na gansu da Saude sun tafi gun boka wai kawu banza ne kee kuma bakya santa zasu rufe miki baki wai ya bada dubu dari zatayi jari in tayi kudi takaisa koto ya saketa ta aure saurayi, wai daman tana da wanda zata aure kullum sai sunyi waya dashi Kawu be sani ba." takarshe cikin hawaye

Mama Tabawa tace "Tabb, d'injam nasan daman za'ayi haka, to wlh bata isa ba, tinda da futa ta futa kenan muje nasawa gidan mukuli saide tazauna gidan Saude Kabiru ya aure ta.

Shijab ta dauko suka futo da Jidderh ko gidan bata rufe ba, suka nufi gidan Salma har lokacin kuwa Salma bata futo daga gun Saude ba.

Mama Tabawa rufe gidan tayi da mukuli saboda mujin Salma baya gari yatafi rani be dawo ba.

Tace "Jidderh muje gidan naku na bata takardarta, in Kabiru yana gida sai ya aureta.

Jidderh Tace "Mama Tabawa ai za suce nice nagaya miki, bari na jiraki kawai kije ki futo .

Mama Tabawa tace "hakane kuma, bari naje toh, ke de Allah yamiki albarka da kika tona musu asiri .

Cikin gidan ta fad'a tace
"Salma munafuka tsanannu, to asirinku ya tonu wato ni zakukai gun boka? to bari kiji na rigaki nace allah baki isa kimin komai ba wlh.
gida kuma kin barsa kenan har abada, sai de Kabiru ya aure ki ku zauna da Saude .

...


Read / Download HATSABIBIYA JIDDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On HATSABIBIYA JIDDA
avatar
aisha-suleiman-jajere

4 months ago

Reply

I like it

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album