Join Our WhatsApp Group

ALKAWARIN JINI Complete Hausa Novel Document by ALKAWARIN JINI


ALKAWARIN JINI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 209765



ALKAWARIN JINI

Reading Time: 17 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Hauwa Muh'd Usman Real Smasher ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.12 mb

File Type: txt

Views: 588+

Download: 878+

Last download: 7 hours ago

Description/Story:  💠💠💠💠💠

*AL~K'AWARIN JINI💥*
_(Blood Pledged)._

*STORY,WRITTEN & EDITING BY:*
_HAWWA M.U (SMASHER)._
*COMPILATION BY:*
_HAWWA M.U (SMASHER)._

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*

         *AL~K'AWARIN JINI..* 💥
             _(Blood pledged)_

                       
                          
*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
   *~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
   _This book altogether was sacrifice to my lil sisters *HAFSAT MUHAMMAD USMAN (REAL HAFSY) & ZAINAB MUHAMMAD USMAN (MAMAH ZEE).*_

   _BESTOWED TO:My Sis *HABIBA IDREES (HUBBEEY).*_
••••••••••••••••
      *_It's all about:-#Bloodier,#promise,#separation,#loneliness,#coincidences,#romance,#adoring,#injustice,#blamed,#destinythread,#decisive,#torture._*

    *~My hands are purified on everything i write,i ask Almighty God agains to give me the ability to continue to go without having any problem,,,with hope to continue on this path.~*

  *~WARNING:-I didn't allow some/others to change/sell any part of the story,which he had sold,i left it with Almighty God,because i didn't have this intention,,,hopefully it will be kept.~*

   *Am really sorry.! Especially for those pepz da nake ma sending novel ta PC,a gaskiya a yanzun sai hak'uri dan kuwa al'amura sun sake k'aruwa a kaina babu lokacin da za ace na dunga bin ku d'aya da d'aya ina tura muku,and dan Allah wanda duk yake da shirin bin novel d'innan zanyi posting a group,masu so kuma da masu tambaya idan anyi nisa kuyi hak'uri babu lokacin da zan yi typing sannan na yi aikin tura muku a PC,,kuyi sharing nasa zuwa ga masu buk'ata please,,,na gode.*

*MARUBUCIYAR...*
_1-K'ADDARA KOH SAKACI.?_
_2-K'AZAFIN KISAN KAI._
_3-RAYUWAR WANI._
_4-Y'AR GARUWA._
_5-BAMBANCIN AL'ADU._
_6-INA MAFITA.?_
_7-ZAB'IN WA ZANBI.?_
_8-WANI AL'AMARIN 1&2._

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*1*
_#Destinythread_

*TUSHEN LABARIN.*
       Yanayi da kuma tsarin gidajen dake arean kana kallo zaka tabbatar da ba'a cikin k'waryar gari ko nace birni kake ba,,RUGA ce irin ta Fulani mazauna yankuna daban² a cikin garuruwa,haka nan ita wannan ruga ta kasance ne a d'aya daga cikin k'auyukan *KANO*,a wani yanki  da ake kira *KAUSANI* dake a cikin k'aramar hukumar *WUDIL* a yankin  jihar *KANO* ta b'angaren northeast,ita dai wannan ruga a tun farkon kafuwarta ta kasance ana yi mata lak'abi ne da rugar *MALAM SHEHU MAI DARASU* ma'ana dai mutumin dake da yawaitar almajirai ko d'alibai ko kuma muce wanda ke bada karatu a tak'aice,,kusan zamu iya cewa wannan dattijo wanda tun a shekaru da dama da suka gabata Allah yayi masa rasuwa,sannan ya kasance shi ne shugaba ga wad'annan al'ummah,sai dai a yanzun haka daya kasance baya raye sai y'ay'ansa daya rasu ya bari wanda har wannan lokacin suke cikin wannan yankin,amma kuma batun karantarwa tun bayan da Allah ya karb'i rayuwarsa sai AL'AMARIN ya tsaya saboda rashin wanda zai iya maida hankali ya gaje shi ta bangaren ci gaba da abunda *MALAM* d'in ya rasu akansa wato koyarwa a tafarkin addinin Islam,kasancewar shi ne mutum na farko daya fara zama a yankin ko muce shi ne asali da tushe na kafuwar wannan al'ummah dake rayuwa a wannan yankin,wannan dalilin yasa sai ya kasance shugaba ga wad'annan fulani dama wasu cikin k'abilunmu na Nigeria mazauna wannan d'an yankin sannan sai ya kasance anci gaba da kiran wannan yanki da sunan sa,duk da yankin garin ba wani girma ne da shi ba haka ko ta b'angaren tsarin gidajen dake gurin kad'ai da suka kasance cikin wani tsari mai birgewa,sannan a k'iyasin adadi na mazauna ko nace gidajen da ke wannan ruga duka baza su haura gidaje hamsin ba,idan kuwa har ace zasu haura haka to y'an tsirari ne zasu zama sun k'aru akan adadin farko.

    Around 6:30am matashiyar y'ar budurwar da duka a shekaru bazata wuce shekaru goma sha hud'u ba,ta fito daga cikin wani gida wanda yake d'aya ne daga cikin gidajen da ke a castles na rugar wanda dukansa yake encircle with kinda traditional wall,a mafi yawan lokuta idan har mutum yaga irin wannan wall ko tsarin ginin gida makamancin wannan tofa tabbas zai kasance ne ga jama'a mazauna k'auyuka wanda su kanyi shi da karare,,she's black in skin colour buh not dark in nature,she's kinda American blacks,fatar jikinta mai kyau tana fidda wani irin sparkling mai d'aukan ido cike da burgewa kai baka ce zata kasance a irin wannan gidajen ba,sam baza'a a sata a jerin masu tsayi ba,haka ma baza'a ce mata gajera ba,dai² misali tana da d'an tsayin ta cif wanda ya sake k'awata gangar jikinta da Allah (S.W.T) ya hallice ta da shi,duk da tana sanye ne da hijab wanda tsayin sa duka yake saman knees d'inta,buh hakan baya hanawa idan har tayi taku d'aya next to go forward jikinta yayi wani irin girgizawa kamar tana sane ne take yin hakan,tana da round face mai d'auke da manyan idanu nd smaller mouth,haka nan da dogon hancinta,kyau dai² wanda duk wani bawa zaiyi fatan ya kasance yana da shi a tare da wannan baiwar Allah akwai shi sai muce "masha Allah da yadda duk ubangiji ya haliccemu sannan mu kasance masu yi masa godiya a kowane lokaci",sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar wata jinin sarauta nd deep kuma not minding cewa wani abu zai iya faruwa a time d'in kasancewar sanyin safiya da hanya yake shiru babu alamun mutane sun fara fitowa zuwa gonaki,a haka take ci gaba da tafiyarta cikin nutsuwa har ta k'araso bakin rafi.

    Zaune saman had'ad'd'en rocky mountain bicycle yake ta faman shek'a gudu abunsa  bisa saman bridge d'in dake saman ruwan garin na wudil,as usual idan har zai fita morning exercise,kansa yana d'auke da p-cap black colour daya kusan rufe fuskarsa,yayin da a ta gaban daga saman forehead d'insa a jikin cap d'in aka rubuta PUMA da yellow color,yana sanye cikin sport wear black nd yellow colour wanda duka shima yake d'auke da tambarin company puma,haka nan k'afafunsa suna sakaye cikin wani yellow nd black mens casual shoe shima dake d'auke da rubutun puma wanda ak'alla darajar takalmin kad'ai ya kai #33+k,fatarsa tana da haske haka nan fuskarsa daga ta gefe ya kasance nd yana d'auke ne da wani irin mustache dake fidda kyallin dake nuni da lallaifa yana samun kulawa da gyara,sai dai fuskarsa har a wannan lokacin bata kasance a bayyane yadda mutum zai iya zayyana asalin kyaun wannan matashin ba,,dai² yazo k'arshen bridge d'in a hankali ya fara yin k'asa yana gangarawa zuwa k'ark'ashin bridge d'in wanda k'orama tabi ta k'asansa,ak'alla zuwa wannan lokacin idan da ace za'a lissafa tafiyar da yayi daga cikin KUST (Kano state university of science and technology wudil) na tabbata zata iya kaiwa ak'alla ta mintuna 15 koma ta haura hakan zuwa arean Kausani da yake a wannan lokacin,,sai daya tabbatar ya tsaya sosai sannan ya sauka daga saman bike d'in yana zare p-cap dake saman kansa,bayan ya samu guri daga gefe ya ajiye bike d'in sannan ya tsuguna gaban ruwan yana janye hannun jacket d'insa zuwa sama ya fara d'iban ruwan yana wanke fuskansa,yanayin sanyin safiya da yasa ruwan ya kasance mai sanyi sai ya sashi yin sanyayyar ajiyar zuciya,kyakykyawa ne wanda irinsu ne tun a karon farko ake gane cewa su d'in ajin farko ne a komai na tsarin halittarsu ba sai an kuma na biyu ba,lissafa muku shi b'ata baki ne just imaging,,yana nan tsugune bayan ya gama abunda yake ya sake mik'ewa sannan ya nufi inda bike d'insa yake da niyyan barin gurin da niyyan komawa inda ya fito wato ya kama hanyansa na komawa zuwa campus.
     Har ya d'aga k'afarsa zai haye bisan bike d'in k'aran fad'uwar abu da fashewarsa yasa shi dakatawa,cikin nutsuwarsa ya d'aga madaidaitan idanunsa yana waigawa had'e da duba gurin daga nan inda yake tsaye,ko da yaga bai ga komai ba,sai kawai ya tab'e baki had'e da hayewa saman bike d'in ya juya abunsa cike da niyyansa na barin gurin.
   Cikin wani firgitattun ihu dake yawo a ilahin gurin,da kunnuwan duk wani mai ran dake gurin muryan bazai b'oye daga jinsa ba ta shiga amsa kuwwa a gurin
    "Wayyoo Allah! Taimako,, a taimaka min..! Babu kowa a nan ne,,ku rabu dani...Ku kyale ni..Me nayi muku.!?"
    Cikin hanzari ya dire daga saman bike d'in had'e da ci gaba da dube² wanda jin wannan ihun yasa shi tunanin definitely ne something must happen,dole ne akwai wani abu a bayan wannan ihun da yaji buh duk iya hangensa har lokacin bai ga ko da kwaro ya wuce ta wajen ba,haka nan ihun daya ji daga sau d'ayan nan sai yaji anyi shiru,sak'e² zuciyansa ta fara akan ya duba ko kuma yayi saurin barin gurin,,ya d'an shafe mintuna yana nan tsaye,can wajen kimanin mintuna biyu ba tare daya gama yanke hukunci ba,nd still yana waiwayawa asides ko zai ga wani alama da zai masa showing inda AL'AMARIN yake faruwa,,sannu a hankali ya kalli gurin sannan ya ajiye bike d'in ya fara ratsawa ta cikin gonakin dake gurin yana tafiya cikin sanyi da son kama koma mene ne a gurin,buh rashin wadataccen haske da yake har lokacin garin ba wai ya gama wayewa bane ga kuma duhun shuke² shi ne yafi komai bashi takaici,da sauri ya shiga laluba jikinsa ko zai samu abunda zai haska gudun kada ya had'u da wani halittar mai cutarwa amma sai bai samu ba wanda sai ma a lokacin ne ya tuna da ya bar phones d'in nasa a hostel,azama ya sake k'arawa yana ratsa tsakanin shuke²n.

    Kokawa sosai suke yi da su,k'artin maza har uku a kanta,amma a hakan sai son k'wace kanta daga gare su take ba tare da girma,yawansu ko k'arfinsu ya tsorata taba,illah mugun nufinsu a kanta da take hangowa,buh ta kasa saboda k'arfin namiji koda guda d'aya nema da mace bazai tab'a zama d'aya ba bare ita da suka had'un mata har su uku,dole ne ta kasa k'wacewa daga irin rik'on da suka mata,,ihu take son sake yi a karo na biyu ko zata samu ubangiji ya aiko mata mai ceton ta amma shima d'in basu bata wannan damar ba dan yadda suka d'aure mata baki da hijab d'inta,hakama sauran jikinta duk sun d'aure ta,,wanda zuwa wannan lokaci tuni har hawaye ya gama jik'a mata fuska kamar yadda take jin tsoron faruwar abunda suke shirin aikata mata haka zuciyarta cike take da fargabar rashin samun mai ceton ta,,dai² wannan lokacin ne d'aya cikin samarin dake kewaye da ita ya kalleta yana yi mata murmushi kafin ya furta
   *"SABINA.!* kenan wato kin d'auki magana ta wasa ko..? Shin kina ganin k'iyayyar da ke da mahaifinki kuke nunawa akan maganar aure na zai hana ni aiwatar da wani k'udurin na daban ne..?? Kina kallon kanki a mai wayo ko..?? Idan kuwa har kunyi wannan tunanin lallai kun jahilci kanku da har kuke tsammanin idan kunk'i amincewa da batun aure zan rabu da ku..Ni ba irin ku bane,kuma ba irin sauran mutane ba,da kuke d'ora yak'inin ku akan *HAK'URI* sam ni ban san shi ba,,kuma ban had'a hanya ta da shi ba,abunda kuka kasa fahimta ta da shi shine,,a duk lokacin dana ga abu na nuna ina so,to ko ta wane hanya saina na tabbatar na mallake shi,,dan haka a yau zan mallake ki,zan maida ke tawa,da duk wani abu da kike tak'ama da shi,,zan cimma burina a kanki,idan yaso kinga babu yadda tsoho zai yi dolensa ne ya bari a d'aura mana aure anjima tunda ya san babu wanda zai yarda ya auri *RAGOWA...!* ko ya kuka ce y'an hannuna..!?"
    Dariya dukansu uku suka shek'e da ita har suna buga k'afa irin ta tura haushi d'innan,ita kuwa Sabina dake yashe a gurin yunk'urin magana ta shiga yi a yayin da wasu hawayen bak'in ciki suke sake tunkud'owa,,dariya still duka suke yi mata,cikin wani irin murya wanda yayi magana ta farko ya kalleta yana rawa da girgizawa tamkar wani d'an iska kafin ya d'age kai da fad'in
  "Wai magana kike son yi ne..?? Naga kina kallona kina girgiza kai..wani abu zaki ce..??"
  Saurin girgiza masa kai tayi tana matse ido
  "Hhhh! Gayu kunji fa wai magana za tayi..! Yo maganar ya wuce tace nayi hak'uri na kyaleta,, Hhh Cikin ku ko akwai wanda zai taimaka mata ne tayi magana..??"
  Dariya suka sake shek'ewa da shi can daga gefensa na dama wanda ke kusa da shi d'in ya ce
   "Haba oga..! Waye zai bata wannan damar,,haka kawai muna ganin gara a gaban mu muje ta wuce mu..ai da zarar mun bud'e mata baki shi kenan asirin mu ya gama tonuwa,,dan haka kawai mu k'addamar mata..Amma fa oga kada ka manta nine a layi,,daga kai sai ni ko ya oga..!?"
   Dariya sosai suka sake fashewa da shi wanda aka kira da oga yace
   "Shege GOJE kace kai duk wannan batun naka hanya kake gyarawa kanka.."

   "Aaa..! Mai gida wa yak'i banza tunda ka lamunce mana yau d'aya dai..??"
 
    "Gaskiya fa sarki ina ganin kamar GOJE yayi gaskiya,garama kawai mu hanzarta tun kafin tsohon nan naku ya biyo sahu..Allah wallahi ka sanshi baya sanya akan wannan kadarar.."
  Duka suka kalleshi suna had'a baki da cewa
   "Shege a haka kamar baka magana amma kaji shi yanzun har cewa yake ayi sauri..!"
  Cewar GOJE kenan da yake dariya k'asa²,amma ga shi ogan nasu kuwa wani sabon had'e rai yayi yana kallonsa had'e da nannad'o wata uwar ashar yana fad'in
  "Kai dan uwarka waye tsohon namu..?? Kana nufin wannan rikitaccen dattijon nata ne ya zama nawa.??"

  "Sorry mai gida,,,ai gani nayi kai da ita duk yumb'unku iri d'aya ne..Shi yasa nace ehh haka..ka gane mana ba wani ehh abu daban bane nake nufi.. Ko yah kace GOJE.!?"
   Shi dai GOJE kallonsa yayi yana murmusawa kafin yace
"Ehh! Kuma fa kaima kace wani abu ILA..Amma dai kasan oga baya son irin wannan wargin..!"
  Kafinma ya kai aya tuni ogan nasu ya datse shi a maganar tasa da cewa
  "Amma dan uwarka kai wane irin kija(jaki) ne.? bance kada ka sake cewa wannan dattijon tsohona ba,alak'atar dake tsakanimu da shi daban,alak'ar dake tsakanina daku daban,dan haka ni bai haife niba,amma idan har ka sake Allah sai na cire maka hak'ori idan ma ban fafe kaba,,,,kawai²..!"
   Da yake duk sun san yaren nan take ILA ya shiga bashi hak'uri dan yasan ogan nasu akwai saurin d'aukan d'umi,bai tsaya sauraren ILA ba ya buga musu tsawa da cewa
  "Dallah kusa kai can ku jira ni..kai kuma ehh daga yau ka kiyaye harshenka,idan ba haka ba Allah zamu dunga samun sab'ani.."
 
   "Ayi masa afuwa mai gida,,zai kiyaye nan gaba.."
  Fad'in GOJE da yake wani bud'awa kamar wanda zai shiga filin dambe,,murmushin da mai gidan nasu yayi ne ya bawa ILA sukuni had'e da tabbacin...


Read / Download ALKAWARIN JINI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album