Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

A MAFARKI NA SANTA BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by A MAFARKI NA SANTA BOOK 1


A MAFARKI NA SANTA BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 83830



A MAFARKI NA SANTA BOOK 1

Reading Time: 6 Hours

Added On: 13, Nov 2024

Author: Pha'eezah Almustapha ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION, ESSENTIAL WRITER'S

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 499.99 kb

File Type: txt

Views: 737+

Download: 971+

Last download: 1 hour ago

Description/Story:

💫A MAFARKI NASANTA 💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah almustapha

Daga alkalamin✍️✍️Fa'eeh Bungudu


BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Wannan shine littafina nafarko Dana fara wallafawa Allah Ina rukonka daka bani damar kamalashi lafiya kamar yanda nafarashi lafiya👏


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

💫P.E.W.A💫

Home of Perfect Writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*

Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*


Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha Murai💔


Yaa Allah ina rokon ka kabani damar rubuta abunda Al umma zasu yi aiki dashi kuma su Amfana, kabani ikon rubuta shi cikin koshin lafiya na kammala shi lafiya👏👏👏

Warning!!!Banyarda wani ko wata su juyamin labarina ba ta kowace siga batare batare da an nemi izini na ba wannan dokace kuma duk wanda yayi ban yafe ba wannan labari kirkira ne bada gaske bane duk wanda yayi dai dai da labarinsa to yayi hakuri akasine. Daga cikin abund littafi na ya kunsa
*Tausayi*
*zumunci* *zazzafar soyayya*
*sarauta* *cin amana* *ta,addanci*


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJINKAI


EPISODE 1️⃣

FREE PAGE1️⃣


Natsatssiyar budurwa ce ke tafiya anatse bata kallon komai face inda take sanya kafafunta, tayi nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Halee! Halee! da jin wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan halee ko ba,a fada mata ba tasan khady ce tsayuwar ta da minti biyu sai ga khady ta iso inda take atsaye.

Isowar khady keda wuya ta furta haba Halee kinsan bakya da issashiyar lafiya ya za,ayi kije Aiken baba ta ta maimakon ki fada mata gaskiyar cewa baki da lafiya nasan zata k'yaleki ni sai intafi kinga ko yanzu gudo wa nayi bayan bayan tashiga bandaki,nasan da kin sanar mata da ni sai intafi koh haka ke da dadi ga uwar rana gashi bakya da lafiya,har taga ma mitar ta kyakkyawar budurwar nan da aka kira da halee bata tanka mata ba.. Daga ni dai yarinyar miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar bataji abunda khady ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass kuma tasan tabbas ko ba,a fada ba khady gudowa tayi tabiyo ta.

Da khady taga alamar ba tsayawa zatayi tabata kudin aikar ba na baaba tsaibe,kuma taga alamar yan miskillancin sun motsa dole haka tabita suka cigaba da tafiya atare har suka iso kantin da zasu yi siyayyar ta kayan miya

Sallama sukayi atare amsa musu sallamar tsohon dake tsaye akan tebir na kayan miyan yayi cikin sakin fuska Dan dama baba tsohon yasan su musamman halee ya saba da ita sosai tunda kusan kullum sai an aike ta yin cefane da sauran aikace aikacen akasuwa.

Washe baki tsohon yayi yana furta a,ah Haleematu sadiya ce kayataccen murmushinta tasaki jin ya ambaci cikakken sunanta Wanda mutun daya ne ke kiranta da wannan Sunan sai kuma mutun daya Wanda bata San ko wanene shi agareta ba Amma tabbas aka ambaci cikakken sunanta tana jin wani iri ajikinta

Muryar baba tsohon ce tadawo da hankalinta agaresa yana furta na nawa za,a bada cikin Dan murmushi ta furta baba tsohon ina wuni lafiya,ita ma halee haka amsa musu yayi duka yana dariyar halee aransa najin ga tambayar da yayi mata ga abunda ta furta masa shiyasa yarinyar tashiga ransa Dan akwai tarbiya gata kamila anatse kara mai maitawa yayi" na nawa za,a bada"cikin Dan yin kasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa ko algaitu gata da sanyi Wanda intana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi na Dari uku da ta furta ne yasanya ni dawo wa daga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta gaisar da tsohon.

Toh baba tsohon ya furta aleda ya saka musu baka ya mika musu sallama sukayi masa sukayi wucewar su, suna tafiya khady na zuba uban surutu alokacin da ita kuma Halee take ta zullumin komawar ta gida Dan tasan gamuwar su da Babah Asabe bamai kyau bace dan tasan sai ta mata fadan dadewar ta duk da dama ta saba,Amma yau da yakasance batajin dadin jikinta tana fama da matsanancin ciwon kai sai take jin shakkun yadda zata iske gidan,tana cikin wannan tunani sai ga hawaye shar😢 a idanunta gwanin tausayi Khady data lura da yanayin da take ciki ne duk da ba bakonta ganinta hakan Dan danan hankalinta yatashi Dan tana mugun son halee kamar jinin jikinta,da tausayinta cikin tausayinta ta furta haba Halee meyafu kuma, dan Allah kitsaida hawayen nan suna Sosa mun rai kuma kinga kan hanya muke kiyi hakuri nasan damuwar da kike ciki bata wuce sanin ko ke wacece bah da damuwar baabah ta 'baaba Asabe' kiyi hakuri in sha Allah komai zai zamo tarihi Halee nah hawayenta ta share mata wayenda ke tsiyaya a I danunta tana girgiza mata kai alamar ta tsayar dasu da kyar ta tsayar da hawayen ta ganin damuwa kwance akan fuskar Yar uwarta!tafiya suka cigaba da yi kowa da abun da yake sakawa aransa,babu Wanda yakara furta uffan har suka iso gidan,

Dan madaidaicin gidane suka tsaya kafin su shiga cikin dar dar musamman Halee gidane dai dai na talaka mai rufin asiri ginin bulo da filista zauren gidan suka tsaya suna shawarar Wanda zai fara shiga domin gudun abunda zasu tarar dakyar dai dukansu sukayi shahadar shiga da sallama abakunan su

Sallamar su ta ta katse ganin Baba Asabe na mitar rashin dawowar Halee akan lokaci da kuma fitar Khady bada saninta ba,

A hankali halee take ta durkusa gurin Yar matashiyar matar da bazata wuce shekara talatin da uku ba a duniya!Baba Asabe kenan wadda Sunan ta yake Lauratu amma mafi yawan mutane suna kiranta da Asabe saboda masifarta da ankira Baba Asabe za,a San itace Dan Sunan ta kaf ya bace.

Cikin sanyin muryarta da yazame mata jiki tace baaba ga kayan miyar kinga na dad'e koh wallahi Baba tsohon ne mun tarar da layi agurin sh...uwar hararar da baba Asabe ke sakar mata ce tasan ya ta yin shiru badan ta shiryawa hakan ba,dama kanta adone yake dan bata son kallon cikin idanun manyanta musamman ma na Baba Asabe ....taci karo da hararar da take sakar mata,bata ida ganin tsawon hararar ba ta kara done kanta kasa cikin tsoron abun da zai biyo baya..

Kiran Sunan Allah take yi a zuciyarta Dan tasan yau tata takare sai ta sha rankwashi akai da gori kala kala da zagin da bata so zuciyarta ce taji tsinke tausayin kanta da kanta yakamata.

Bata ida gama tunaninta ba ta tsinkayi muryar Baba Asabe nama khady fadan binta da takeyi abaya inta aiketa duk da kullum haka suke muddin Baba asabe ta aiki Halee to tabbas in Khady tadawo sai ta bita sundawo tare koda kuwa dawowar su daga makaranta ne aka tura Haleen sai ta yi sand'a ta bita...

Baba asabe ce take furta wallahi Hadiza ki shiga taitayinki Dan ubanki na fahimci bakya game zancen da nake maki ace ke kullin sai kinsaka ni yakar baki ehh~bakinta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download A MAFARKI NA SANTA BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album