Join Our WhatsApp Group

GUDU DA WAIWAYE Complete Hausa Novel Document by GUDU DA WAIWAYE


GUDU DA WAIWAYE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 27414



GUDU DA WAIWAYE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 24, Sep 2023

Author: Bilyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 07067124863, 09032345899

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 160.79 kb

File Type: txt

Views: 2412+

Download: 805+

Last download: 19 hours ago

Description/Story: *_Typing📲_*




*_🏃🏻‍♂️GUDU DA WAIWAYE.....!!_*
_(Shi ya kawo mugun zato)_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*





*(1)*


MALAM Rabi'u Shema, cikakken bakatsine jinin rumawan asali da ALLAH ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini.
Ya fitone da ga yankin karamar hukumar Dutsamma dake jihar katsina, a wani ƙauye da ake kira Shema, danginsa uwa da uba duk sun fitone daga wannan yanki.
Sanadin ƙaddarar neman na kaine ta dalilin kasuwanci ya tsinci kansa a garin kano, shi kaɗai ya fara zuwa kafin daga baya ya kawo matarsa mai suna iya ladi.
Ƴaƴansu huɗu a duniya, maza uku mace ɗaya.

A yanzu haka da shekaru suka shuɗa gidan Malam Rabi'u ya zama family house mai ɓangarori huɗu.
Ginine irin na mutanen da, shiyyasa ya kasance gida babba da har ƴaƴansa Uku duk suka sami gurbin zama da iyalansu a cikinsa.
A yanzu haka dai ALLAH ya azurtashi da jikoki daga tsatson waɗannan ƴaƴa huɗu da zasu iya kaiwa kusan ashirin da huɗu, harda ƴaƴan ƴarsa mace Marwa dake aure acan garin Dutsamma kuma guda biyu.

Duka ƴaƴan malam Rabi'u ALLAH baisa sunyi karatun boko ba har suka kai minzalin hankali, amma sunada ilimin addini gwargwadon iko.
Babban ciki mai suna Hamza shine ya fara auren matarsa ta farko Ruƙayya, wadda ya koma gida ya auro ɗiyar zumu, wato ɗiyar gwaggonsa ƙanwar mahaifinsa.
Ruƙayya ta tare a kano tare da mijinta Hamza annan cikin gidansu, ya gina ɗakuna biyune da bayi ya katange wajen, Ruƙayya tana samun soyayyarsa data iyayensa mai tsafta harma da ƙannensa.
Sai da Ruƙayya ta shekara uku a gidan sannan ta samu ciki, bayan ya kai haihuwa ta haife ɗiyarta mace wadda taci suna maryam.
Haihuwar Maryam da watanni biyu Muktar yazo da batun sake aure.
Hankalin Ruƙayya ya tashi ƙololuwa, hakama iyayensa suka nuna sam basu yardaba.
Yashiga damuwa sosai, saboda yanason Suwaiba, kuma harma sunyi alƙawarin aure, da farko yaso ya haƙuran amma sai ya kasa, yaje can gida Shema ya sanar ma mahaifin Ruƙayya halin da ake ciki.
Mahaifin Ruƙayya yazo kano, inda ya wanke Ruƙayya da faɗa tas, sannan ya koma nasiha a gareta, hakama iyayen Hamza ya samesu ya nuna musu suyi haƙuri su barsa tunda yanaso, da yaje gefe yana aikata abun banza gara ya auro yarinyar zaifi kwanciyar hankali.
Badan su iya ladi sun soba suka amince akai auren Suwaiba da Hamza.
Suwaiba dai asalin iyayenta ƴan dawanau ne, amma yanzu suna nan zaune a cikin garin kano, bata da damuwa sam, dan tunda ta tare gidan Hamza batajin daɗin kowa sai shi, iyayensa da ƴan uwansa basa sonta, ƙiri-ƙiri suke nuna mata fifiko akan Ruƙayya.
Danne zuciyarta tayi tamkar bata gani, takuma kwantar da hankalinta tana musu biyayya su duka, wannan halayyar tatace ta saka suka fara sassauta mata, har itama Ruƙayyar kanta.
Koda yaushe zakiga Maryam maƙale da Suwaiba, dan tanada son yaran tsiya, tun Ruƙayya na ƙwacewa bisa zugar matar Yusha'u harta hakura ganin Suwaiba bata taɓa cutar da Maryam ɗinba, lokacin ma da Ruƙayya zata yaye maryam sai Suwaiba ta amsheta ta yayeta, tundaga wannan lokacin kuma zaman Maryam ya koma hannun Suwaiba.
Kawaicin ɗan fari yasa Rukayya ta ƙyale mata.
Cikin hikimar ALLAH kuma sai Suwaiba da Ruƙayya suka fara laulayin ciki a tare, Rukayya na biyu, Suwaiba na farko, tare sukaita laulayinsu har ALLAH ya saukesu lafiya, sai dai Ruƙayyace ta fara haihuwar ɗiyarta mace, taci sunan Rahama, bayan kamar sati biyu dayin suna sai itama Suwaiba ta haihu, amma ita namijine.
Itama ranar suna yaronta yaci suna AHMAD, Suwaiba mutum ce mai azabar kawaici, sai yazam har akan Ahmad halayyarta na nan, dan sam yitake kamar ba ɗantaba, dukda kuwa tana ƙaunarsa sosai, wani lokacin tana zaune zaita kuka amma tai biris dashi, har sai Ruƙayya ta shigo ta ɗaukesa tana mata faɗa, ko bashi nono sai Ruƙayyan ta tsaya a kanta wani lokacin.
Wannan kawaicin da takeyi mai tsanani a kansa yasaka Ruƙayya maida hankalin kula dashi da Rahama, sai suka taso tamkar wasu tagwaye, idan ka ganshi hannun Suwaiba to nono zaisha.
Maryam kam ta zama ƴar ɗakin Suwaiba, itace tamkar uwarta, itama Ruƙayya tana kawaici akanta, dan bata faɗar koda sunanta kamar yanda itama Suwaiba bata faɗar sunan Ahmad.
Ahaka yaran suka fara wayo har zuwa yaye, sai zaman Ahmad ya koma wajen Ruƙayya gaba ɗaya, kamar yanda Maryam take hannun Suwaiba.
A wannan karon sai Ruƙayya ta fara samun ciki kafin Suwaiba, sai da cikinta yakai kusan wata bakwai sannan Suwaiba itama ta fara laulayi, a wannan haihuwarma dai Ruƙayya mace ta haifa, wadda taci suna Sakina.
Su Ahmad sunyi murna sosai an haifa musu ƙanwa, sai nan nan suke da ita dukdama bawani wayone dasuba lokacin.
Bayan haihuwar Sakina da kusan wata taƙwas itama Suwaiba ta haife ƴarta mace, itama taci suna Raheenat.
Ƴaƴa zun fara cika gidan malam Muktar, dan haka sunayen iyayensu ya fara ɓuya, Ruƙayya ta koma Ayyah, Suwaiba kuma Gwaggo.
Tun daga kan Sakina Ayyah (Ruƙayya) bata sake haihuwaba, sai Gwaggo (Suwaiba) ce ta cigaba da haihuwa, tayi Mudanseer, Abubakar, Fa'iza, Sadiya, sai auta Zainab.
Daganan ne haihuwar ta tsaya itama, yaransu sun taso kansu a haɗe, inba sanar maka akaiba baka taɓa sanin ƴaƴan wance da wance, tare suka haɗu wajen gina ƴaƴansu a tarbiyya, sun gina gidansu bisa ƙyaƙykyawan tsari mai birgewa duk da sheɗancin kishin sauri da suke fuskanta lokuta da dama.

Sai ƙanin Hamza mai suna Yusha'u, shima dai matarsa ɗaya da ƴaƴa biyu, shima a cikin gidan ya gina nashi ɗakin matarsa ke zaune, shima sai ya ja katanga iya sashensa kamar yanda Hamza yayi, ya auri matarsa mai suna Ɗausiyya (Gaje) kusan tare da auren yayansa hamza na biyu, hakanne ya saka Gaje ɗaukar kishin duniya ta aza akan Suwaiba tamkar mijinsh ɗaya, dan komai na auren Suwaiba yafi nata.
Taso saka ruɗani a zaman Suwaiba da Ruƙayya, su haɗe kai su ware Suwaiba a gidan, amma sai UBANGIJI ya hana hakan, babu irin munafircin da batai musu, sai yazam ko saɓanin ya shigo tsakaninsu baya wani daɗewa suke fahimtar juna.
Lokacin da riƙon Maryam ya dawo hannun Suwaiba ba ƙaramin baƙin ciki Gaje ta shigaba, taita zuga Ruƙayya akan ta amshe Maryam, amma sai ALLAH bai ƙaddara hakanba.
Abinda kuma yazo ya sake haɗa ƙiyayyarsu Haihuwar namiji da Suwaiba tayi, wato Ahmad, dan kusan tare itama Gaje ta haihu dasu, sai dai itama mace ta samu kamar Ruƙayya, wadda taci suna Binta.
Nanma Gaje ta so ta cusama Ruƙayya ƙiyayyar Ahmad sai hakan bai faruba, dan kuwa Ahmad ma sai ya dawo hannun Ruƙayyan gaba ɗaya.
Tunda Gaje ta fuskanci bazatai galabar ɓata zaman Ruƙayya da Suwaiba ba sai ta koma kishi dasu gaba ɗaya, kullum burinta ta yaya zata ƙuntata musu kota haɗasu faɗa.
Sukam watsar da lamarinta sukayi tankar basusan da zamanta a gidanba.
Ahaka zaman nasu yaci gaba da tafiya har Ilyasu ɗa na uku wajen su malam Rabi'u yayo nasa auren shima.

Ilyasu ya auro matarsa mai suna Sailuba, tunda Sailuba ta tare a gidan sai Gaje ta shiga jan ra'ayinta da cusa mata tsanar su Ruƙayya (Ayyah) a zuciya, a hankali itama abun ya fara tasiri a ranta, sun ware kansu su biyu, bakajin cikinsu sam a gidan, sannu a hankali sai suka fara jan ra'ayin mazansu ma.
Daga nan ne fa zumincin iyalan malam Rabi'u yaso fara tangal-tangal.
Hankalinsa ya tashi lokacin da ya fahimci daga inda matsalar ke neman fitowa, dan haka ya tara ƴaƴansa duka huɗu har Marwanatu autarsu da itama tai aure acan dutsamma.
Ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba wajen banbamesu da masifa akan sheɗancin matansu dake nan lalata zumincinsu.
Jikinsu kuma duk sai yayi sanyi, dan tabbas sun fahimci kuskurensu sosai, haƙuri sukaita bama iyayen nasu.
Iya Ladi tace ita sam bazata haƙura ba sai Yusha'u da Ilyasu sun ƙara aure, danta fahimci matsalar daga wajen matansu take.
A take Ilyasu ya amince zai ƙara auren, amma Yusha'u sai ya bada haƙuri akan shifa baida ra'ayin sake mata bayan matarsa Gaje.
Iya Ladi tace aikuwa bai isaba, ƙara aure ya zamar masa tilas, tadai bashi lokaci yaje ya nema wadda taimar daga lokacin har tsawon shekara uku.

Kwanaki kaɗan dayin wannan Zama, zancen ƙara auren Ilyasu ya taso, zai auri wata yarinya anan ƙasan layinsu mai suna Zubaida.
Bayan Ilyasu ya ƙara aure a nanma sai Gaje taita tunzura Sailuba, sam zaman lafiya yaƙi tsakanin matan Ilyasu saboda munafurcin Gaje.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya a wannan family, a cikin gida ɗaya har kawo yanzu da duk sun mallaki hankulansu, ƴaƴansu duk sunyi girma, yayinda tsufa ya kama Malam Rabi'u sosai, hakama iya ladi, dukda dai ita Alhmdllh jikinta da ƙwari tunda komai tana iyayima kanta.

Hamza talakane mai ƙoƙarin neman na yau da gobe, yanada wadatar zuci da bai amince ya zauna roƙoba, duk wahalar sana'a yana ƙokarin ganin yayi ya samawa iyalansa abinci, da abinda zai kula da iliminsu, dan ya tashi zuciyarsa nason ƴaƴansa suyi karatun boko, amma ga sauran ƴan uwansa sam ba haka baneba, sun tsani ilimin boko, a ganinsu watsa tarbiyyar yarane kawai, inda yana da kyau da iyayensu suma sun sakasu ai..
Hamza yasha zaunar dasu ya fahimtar dasu banbancin zamanin yanzu da nasu daya shuɗe, sai dai sam sunƙi fahimtarsa, hakanne ya sakashi ƙyalesu kawai.
Shi ƴaƴansa Suna zuwa makarantar boko ta gwamnati tamkar sauran yara, sannan da yamma suje islamiyya, da dare suje allo.

Rayuwa ta shuɗa inda malam Hamza (Baba) ya fara aurar da ƴaƴansa, Maryam ita aka fara kaiwa ɗakin miji, sai Rahama da suka tashi sa'anni da Ahmad, daga nan sai Raheenatu.
Shima Yusha'u ya aurar da Binta, wanda bayan bikin da kwanaki kaɗan yace zai kara aure.
Tashin hankali kenan, da ga mama Gaje, wadda tai tsalle ta dire akan bai isaba, ita tafi ƙarfin zama da kishiya wlhy.
Rigima tayi rigima har takai Yusha'u ya saki Gaje da cikinta ɗan wata bakwai.
Wannan shine sanadin barin Gaje gidan, shikuma yayo aurensa.
Daga nanne suka sami zaman lafiya, kowa ya koma mutunta ɗan uwansa a gidan.
Amaryar Yusha'u ta sinkuto masa ɗiya mace bayan shekara ɗaya, wadda taci suna Umm-Rumana.

Ƴaƴan Baba Hamza mata daya aurar Dukansu iyakarsu sakandire aji uku yake musu auren, dan haka Ahmad ne ya fara wuce aji uku na sakandire a gidansu.
Ahmad ƙyaƙyƙyawan yaro mai cikar halittar asalin rumawan katsinawa, komai nasa mahaifinsane, yanada ƙwazo a makaranta ga rashin hayaniya, dan sam da wahala kaji ance ga abokin faɗansa, inhar kaga yayi faɗa to ankaisa maƙurane, dan yanada zafin zuciya idan aka kaishi ƙarshe, sannan idan yay fushi da abu Ayyah ce kawai ke iya lankwasashi cikin sauƙi.
Dan Ahmad ɗan gatan Ayyah ne sosai, duk abinda kaga Ahmad ya nema ya rasa sai dai idan Ayyah bata da ƙarfin siyensa, shima kuma saitayi ƙokarin saya masa makamancinsa, harya fara zama saurayi komai nashi yana ɗakinta, tsakaninsa da mahaifiyarsa kuwa gaisuwace kawai, dan kallonsa ma bata iyayi saboda kunyar ɗan fari.
Ya daɗe baisan ba Ayyah ce ta haifesa ba, da yasani kuman ma bai damuba, abinda kawai ke bashi mamaki kawaicin mahaifiyarsu, dan sam bata sakewa dashi, tun abun bai damunsa harya ɗan fara damunsa, amma daya ƙara hankali sai ya fuskanci ba sonshi bane batayi kawai al'adace irinta hausawa, tunda itama Ayyah ai bata kula yayarsu Maryam, komai sai gwaggo.

Tun Ahmad na sakandire aji ɗaya suka haɗu da Samina, an tashi makaranta sun nufo gida shi da su maryam sai suka iske yara na damben faɗa a wani lungu.
Maryam tayi ƙoƙarin rabasu amma ta gaza, hakan yasa Ahmad ɗaukar ƴar bulala ya tsutstsula musu a ɗuwawu, dole suka rabu kowa na shafa wajen yana kuka.
Yarinya ɗaya a cikinsu sai ta maido faɗan akan Ahmad daya dokesu, tsayawa yay kawai yana kallonta da mamaki, dan alokacin shekarun nata bazasu gaza bakwai ba, inma sun wuce sai dai ƴan wattani.
Kuka take kashirɓan akan saita rama dukan da yay musu, ta kama ƙasan rigarsa ta riƙe tana kai masa duka da ɗan hannunta.
Shi dariyama ta bashi, dan haka ya tsaya yana kallonta yanayi, ganin da gaske take sai Rahama ta kamata ta janye tana dungure mata kai, nanko yarinya takuma daddagewa ta fasa musu kuka harda zagi.
...


Read / Download GUDU DA WAIWAYE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album