Join Our WhatsApp Group

FALAK Book 1 Complete Hausa Novel Document by FALAK Book 1


FALAK Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 49379



FALAK Book 1

Reading Time: 4 Hours

Added On: 09, Aug 2023

Author: Zainab Habib Mom Islam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : E O W

Author Phone : 08141799224

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 274.38 kb

File Type: txt

Views: 900+

Download: 412+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: *FALAK🍒*
_Gajeren labari_

Zainab Habib (Mom Islam

E.O.W

_Bismillahir rahmanir rahim_

morning 11:30am Thursday 29/12/2022


Page 1-2


Iska ce ke kad'awa a hankali, garin yad'auki sanyi sosai, yawancin mutane suna sanye da rigar sanyi.
Tafiya take tana yarfe hannu kamar karamar yarinya,
"Falak"
Taji an kira sunanta cikin kausasashiyar murya, da sauri ta waiga ga mamakinta sai taga babu kowa, juyowar da zatayi taga wasu mutane guda uku ko wanne ya yane fuskarsa da bak'in k'yalle, a tsorace tace "suwaye ku mekukazo yi nan?"
'Daya daga cikinsu ya d'agata cak yasata a mota suka shiga dukkansu suka yiwa motar key, sosai take ihu tana had'asu da Allah babu wanda ya saurareta, wanda aka kira da Oga ya mika saletif aka manne mata baki, tare da wani baƙin k'yalle shi kuma aka rufe mata ido.

•Da sauri  ta sauko daga kan gadon da take kwance tana share zufar dake sintiri a fuskarta, jiki a mace ta nufi k'ofar da zata sadata da d'akin sauran yan matan, tana buɗe k'ofar ta hangosu a kwance sunanta sharar bacci, cikin d'aga murya tace "Munira  Hibba Saudart ku tashi nayi wani mummunan mafarki"
Suna jinta sukayi mata banza, dole ta k'yalesu ta nemi guri a gefen gado ta zauna, sbda bacci ya kauracewa idanuwanta,
A hankali taji ana cewa "ga dakunansu nan ku shiga"
Falak ta waro ido kafin ta shiga tashinsu a hankali, abin mamaki suka jingina wata sanda a jikin Falak suka fice da ita kaf gidan babu wanda ya motsa, sai da aka fice da ita daga gidan.
Cikin tashin hankali Ummu ta bod'e k'ofar d'akinsu Munira, sbda jikinta na bata babu lafiya, kallon agogo tayi taga k'arfe 1:20pm tace "yakamata ku rage wannan barcin ranan da kuka sanarwar kanku, Hibba tayi juyi tana mutsuke ido kafin tace "Ummu ai Falak ma yazo tana ta damun mu bansan lokacin data fice ba"
Ummu tace "na d'auka ko tashiga wanka ne dan naga babu kowa a d'akinta"
Saudart ta diro da sauri ta bud'e k'ofar toilet, wayam tagani babu kowa, cikin tashin hankali dukkansu suka fito sunata Zagaye kowane sashe na gidan Ammae babu ita Babu alamar ta, Ummu tasa hijab taje gurin Mai gadi ta tambayeshi, yace "tun safe yake zaune anan baiga kowa ba.....

Inaso inga inda zaku amshi littafin, inhar naga anyi shar'i da comments read more da yawa zan dingayi duk da labarin bame tsayi bane 08141799224
*FALAK🍒*


Zainab Habib(Mom Islam



Free

E.O.W


Page 3-4

Cikin tashin hankalin Ummu tayi bedroom d'inta domin ta d'auki waya ta kira  Abba, kafin takai ga d'aukar wayar taji wayar na ringing, da sauri ta d'auki wayar tare da karawa a kunnenta,
"Sunana Oga zakiyi mamaki idan nace miki yarinyar da kukafiso kukafi k'auna tana gurina, nasani duk duniya keda mijinki kunfi sonta saboda ɓoyayyen sirrin dake tattare da ita"
Ummu ta fashe da matsanancin kuka kafin tace "dan Allah ku ƙyalemin yarinya na roƙeku dan girman Allah ko me kukeso zava baku"
Ta faɗa tana share hawaye dake kwaranyo mata.
"Karki damu ba wasu kuɗaɗe masu yawa muke buƙata ba, just 10 million nera zaku bamu sai mu sake muku tauraruwarku, nasani kun mallaki abinda yafi haka"

Oga ya fad'a ya tuntsire da dariya, ya cire sim card d'in dayayi kira dashi ya karyashi.
Juyowa yayi ya kalli Falak kafin yace "idan iyayenki suna sonki zasu bamu abinda muka buk'ata idan kuma basa sonki zamu zauna tare dake"
Idanunta da suka gaji da tsiyayar da hawaye ta d'ago kanta tana dubansa, duk inda kakai da gane kamannin mutum to shi wannan ya gama rufe fuskarsa, iya bakinsa da ido kawai ake iya gani, ya matso zai ta6a Falak, da sauri ya matsa tare da kallon idanunta da suka sauya daga kamanninta suka juye kamar na mage (cat),

"Ke wacece wane sirri ne a tattare dake, meyasa mahaifinki duk tafiyar da zeyi sai yaje dake k'asar waje, bayan ga y'an uwanku nan a gida harda yayarki"
Yaje a hankali ya cire mata salatip d'in dake manne a bakinta, kafin yace "ina jiran amsarki"
Magana take amma sam baya ma jinta, sbda tsananin kyawun hallitta da Allah yayi mata, farace tass gashin kanta Shiba jaba kuma Shiba bak'i ba, asalin k'wayar idonta baki ne gashin saman idonta Zara zara sai gashin girarta data kwanta tayi luf, bakinta ya kasance d'an karami Mai d'auke da pink color kamar ansa masa jambaki.
"Mugu"
Kalmar daya tsinkayo kenan, ashe harta gama tofe masa fuska da miyau yana zaune yana kallonta, ya shafe fuskarsa kafin yakai hannu zai mareta, hannunsa bai kai ga jikinta ba wani miciji yazo ya nannad'e masa jiki har hannunsa da k'afa, tafara magana da muryarta mai d'aukar hankali tace "meyasa kakeson cutar da rayuwata , meyasa kukeso sai kunga bayan Abbana mai yasa kuke bibiyarsa ko akwai abinda yayi muku ne?"
Oga dake d'aure snake ya cukuikuyeshi yace "please ki ce ya sakeni yanzu zaki koma gida"
Falak tayi murmishi kafin tace "bance maka inason komawa gida ba, ban kuma ce maka banason komawa gida ba, abinda nakeson ji shine me Abbana yayi muku?"
Bai sanar da ita abinda ta buk'ata ba, sai ma k'walawa abokan aikinsa Kira da yayi, da gudu suka shigo, a tsorace suka kalleshi kana sukace "oga meye naga kamar snake ne ya nannad'e ka?"
A hassale yace "ubanku ne ya nannad'e ni oya ku kunceni tun kafin inzo gareku"
'Dayan mai suna man ya taho da k'arfinsa har wani huci yake, yaje da sauri zai tunkari Ogan nasu, macijin ya d'ago kansa yana kallonsu, suka arce da uban gudu,
"Dan Allah nasan duk wannan abun bai wuce keba please nakuma rokonki akan ki k'yaleni bazan sake bibiyar rayuwarki ba"
Falak ta lank'wasa hannunta yayi k'ara, abin mamaki sai micijinan ya 6ace, tace "fad'amin"
"Daman haka kawai ne, zanyi aure bani da kud'i shine nabi ta wannan hanyar Ina. ganin zan samu abinda nakeso"
Falak ta girgiza kai kafin tace "wannan ba hanya mai 6ullewa bace, kana tunanin da kud'in sata zakayi aure?"
"Kiyi hak'uri sai da nayi hakan na gano nayi kuskure"
Kallonsa take kallo na tsanaki kafin tace "sau tari akanyi kidnapping mutane akan dalilin da sam bashi da K'arfi wannan ba hujja bace, son zuciya ne, dani zakayi auran kenan for what?"
Ta fad'a tana kuka,
"Kunfi son ku dinga tayarwa da Abbana hankali, duk lokacin daya bar Nigeria sai an yi kidnapping d'in bansan me na tarewa mutane ba"
Oga yace "Dan Allah ki taimakeni karki sanar cewa nine na saceki wlhi kasheni za'ayi"
Ya fad'a yana kuka shima harda majina.
"Sau nawa kana kidnapping mutane?"
"Sau d'aya a kanki"
ya ciro wayarsa ya nuna mata save the date na auransu, tare da hotunan da sukayi da matar da zai aura, harda hoton da sukayi dukkansu harda mahaifiyarsa.
Yace "bari a kawo mota a kaiki gida"
Falak tace "no zan tafi da k'afata" ka bani account number d'inka, karka sake waiwayata ko godiya bana buk'atar ka Kira kayimin ka godewa Allah, inhar kayi tunanin sake cutar da wani zuwa gaba, to zaka iya rasa ranka"
Falak ta fad'a tana nunashi da yatsanta.
Bayan ya mik'a mata kati mai d'auke da number ta fice a hankali tana zuwa  bakin k'ofa ta k'ara  da gudu.
Tayi tafiya mai nisa kafin takai bakin titi, ganin shigar dake jikinta ne ya mugun kunyatata, gajeren wando ne na jeans iya guwaiwa sai riga mai siririn hannu ta rufe mata cibiyarta bata k'arasa har mararta ba, cikin sa'a wata mota tayi parking a gefen hanya,
Magidanci ne Wanda a k'allah zeyi shekaru 72yrs bakinsa yana sanye da hak'orin Makkah, ya rage tsayin gilashin motar kafin yace "tafiya ne Hajiya?"
Jikinta na kyarma tace "dan Allah ka ragemin hanya ko a y'an tifa ka ajiyeni zan k'arasa"
"Muje har gida zan kaiki"
Falak tace "a'a kaidai kawai ka ajiyeni a inda nace maka, sai ka bani aron waya"
Cikin son jin abinda ya faru da ita yace "shin meye matsalarki?"
Bata bashi amsa ba ta rufe k'ofar,
Ya mik'a mata wayar kana yace "a sim one zakiyi Kiran"
"Ok" tace masa ta fara jero number da zata Kira,
Cikin sa'a Kiran ya shiga akayi sallama daga can 6angaren tace "Hamma Aliyu kazo y'an tifa a gurin masu siyar da kayan miya ka d'aukeni"
Daga can Hamma Aliyu yace "Wai meke faruwa ne yanzu nake gani a T.v, batace masa komai ba tace "gani please kazo"
Tana gama waya ta goge number tare da share zufar data karyo mata.
Sunyi tafiya mai nisa kafin sukazo inda ze sauketa, tana sauka Hamma Aliyu na isowa, tayi wa Mai mota godiya ta shiga motar yayan nata suka wuce.
Hamma Aliyu ya kalleta kafin yace "k'anwata meke faruwa naga mood d'inki ya sauya ko ankuma ne?"
Falak tace "Hamma wlhi wannan mutumin ma ragemin hanya yayi idan dady ya sake dawowa sake dawowa zan bishi bazan sake zama ana neman hallakani ba gaira babu dalili ta fashe da kuka tare da tura y'an yatsunta cikin sumar kanta tana cigaba da cewa "bansan mena tarewa mutane ba bansan menake dashi wanda yasa suke neman rayuwata ba"
Hamma Aliyu yayi murmishi ya shafi kwantaccen sajen fuskarshi kafin yace "Falak kin kasance y'ar baiwa, duk da duniya tanada fad'in da babu wani mahaluk'in da zai iya lissafa adadin mutanen cikinta, kinada baiwar da kowanne namiji zai so had'a zuri'a dake, kinada kyau mai rikita maza harda mata, kinada kwarjini, sannan kinada wani sirri wanda babu wanda ya sanshi komu ma mundaiji ana cewa kinadashi amma har yanzu bamu gano komai ba"
Falak ta ta6o hannun Hamma tana share hawayen da suka zame mata jinin jiki koda wane lokaci tace "duk naji amman inaso in dinga rayuwa kamar ku, kamar inda kuke zuwa ko Ina a kuma lokacin da kukaga dama, shin nima zan zamo kamar ku?"
Hamma ya taka burki a lokacin da suke shiga anguwarsu Falak, Bauchi road, kafin yace "idan nace miki miki eh nayi k'arya babu tabbacin zaki iya rayuwa cikin dubban mutane ba tare da kin sami gagarumar matsala ba, so abinda nakeson ki sani shine ki kwantar da hankalinki ki rage damuwa har Abba ya dawo sai musan abinda zamuyi, ni daga nan zan wuce gida ne"
"Hamma bazaka shigar dani ciki ba"
Ta fad'a cikin marairaice murya,
"Am sorry idan na shiga Saudart zata rik'eni da surutu zuwa k'arshen sati zanzo ki gaida Ummu"
"To kawai tace masa ta bud'e get din gidansu ta shiga"
Ya d'au tsawon lokacin yana kallon k'ofar data shiga, ya girgiza kai tashi d'aya tausayin k'anwar tashi ya kamashi, yaja mota ya tafi.
Mai gadin gidan na ganinta ya durk'usa yace "Hajiyarmu uwar adalci barka da dawowa"
Ma'aikatan gidan sun saba da 6atanta saboda inhar ta dawo Nigeria sai an saceta duk da wannan na hud'u kenan, koda an saceta basayi mata komai ana basu kud'i shikenan ake saketa, ta shigo main parlonsu bakinta d'auke da sallama, Ummu Saudart da Munira Hibba dukkansu suka fito, suka rungumeta suna cewa "sister Falak babu abinda ya sameki ko?"
Falak tayi murmishi sbda Ummu dan tana ganin fuskarta a cikin damuwa kwana zatayi babu bacci, Falak ta rungume Ummu da har yanzu batace komai ba, Falak tace "Ummu Ina lafiya wlhi k'alau na dawo Ummu"
Sai a lokacin kukan da Ummu ke 6oyewa ta fito ta fashe da kuka tana cewa "Falak.. kowa bashi da damuwa sai Falak, mutane suna so su kashemin kene kokuma dukiyar mahaifinku ne ya damesu?"
Ummu tayi maganar tana zubewa a k'asa.
Saudart taje da sauri ta rungume Ummu kafin tace "Ummu kowane bawa da tasa k'addarar mu k'addara itakuma tata k'addarar kenan"
Ummu ta nuna Saudart da hannu tace "Saudart meyasa Falak bazatayi rayuwa kamar y'an uwanta ba?"
Dukkansu sukayi shiru saboda suma kansu abin yana d'aure musu kai.
Kiran sallahr Magrib ne yasa suka watse kowa yaje yayo alwalah, Falak kam sai da tayi Azhar sannan ta yi la'asar tayi magrib, tana idarwa ta d'auki alkur'ani wanda ya zamo mata farilla, sbda duk bayan kowacce sallah sai ta karanta koda aya goma ne kafin tabar kan sallahya.
Tana idarwa ta d'aga kyawawan hannayenta sama tana karanto sunayen Allah tare da rok'on buk'atunta a gurinsa, tana kammala adu'ar ta shafa tare da mik'ewa ta d'auki wayarta taga miss call har 50 bata duba ko waye mai Kiran ba ta cire zumbulelen hijabin datasa ta cire kayan jikinta, ta d'auki towel ta d'aura ta shiga bathroom, saidata tara ruwa Mai yawa, ta shiga ciki tayi lamo tare da lumshe ido, d'ago kanta tayi ta kalli mirror d'in dake manne a jikin bango ta janyo gashin kanta tana wasa dashi, abin mamaki kidnapping d'inta da akayi ta dawo babu alamun damuwa ko gajiya a tare da ita, sai data seke ruwan ya tafi kafin ta tar wani tayi wanka, bayan ta wanke gashinta da had'ad'un mai,  ta fito d'aure da towel fari ta d'aure Blu k'arami a kanta, ta zauna akan stool tare da kallon yawan gashinta, ta busar da gashin tana gamawa ta shafa mai da powder sai lipstick dasata mik'e tana cewa "Ummu.."
Maganar da K'arfi take kamar inda Ummu zata iya jiyota,
Ummu na kitchen itada Saudart tace "ku kammala had'a salad d'in auta na kirana"
Ummu na shigowa Falak ta kwanta a kan kafad'arta kafin tace....!

Naga comments tabbas yawan comments dinku yawan typing ina k'aunarku masoyan gaskiya, ga masu son in sasu a group dinda nake typing suyi saving numberta sai suyimin magana please mata zallah 08141799224

Mom Islam
*FALAK🍒*

E.O.W

Zainab Habib (Mom Islam

Free

Marubuciyar
Ladidin  ƙauye
Lamarin ƙaddarar aurena
Mk mijin delu
Nancy ƴar ƙarya
Yarinya mai taɓargaza
Diyana
Guntun goro
Nida yarinya
Zaɓinshi ne
Hatsabibiyar yarinya
Macen sirri
Tsautsayin tauna

Page 5-6
Ummu ta k'araso bedroom d'in cike da kulawa tace "my auta gani"
"Ummu inason zuwa anguwa gidansu Amal ya zanyi?"
Ummu tayi shiru kamar wace ruwa ya cinyeta kafin ta kamo hannun Falak tace "yakamata ki dinga kiyaye abinda yake zuwa da dawowa, Falak kinsan rayuwarki na cikin hatsari ko?"
"Yes Ummu sanin hakanne yasa nake neman shawararki"
Ummu taja dogon numfashi kafin tace "just ki hak'ura kawai, fitarki zata iya zamowa barazana ga rayuwarki ko kinaso ki sake tayarmin da hankali ne?"
"Idanun Falak sun sauya launi tana shirin yin kuka tace "meyasa bazanyi rayuwar farinciki ba, meyasa kullum a killace nake way?"
Ummu ta dafa kafad'arta kafin tace "zakiyi Falak komai nada lokaci kinji"
Share hawayen da take k'ok'arin 6oyewa suka zubo tayi kafin ta koma ta kwanta Ummu ta fita.
Tayi juyi yafi abinda yafi, zaman gida ya isheta, kwatsam ta tuno mutumin d'azu, ta janyo wayarta tare da duba wandon data cire ta d'auko number mutumin tayi masa transfer na dubu d'ari biyu, ta koma ta kwanta.
Oga, wanda a zahirin sunansa Ammar, yana zaune tare da mahaifiyarsa yaga alert na kudi, a razane ya mik'e dama ya gama bawa mahaifiyarsa labarin lefin daya aikata, tana tsaka dayi masa nasiha yaga sak'o, ya nuna mata, sai da tayi hawayen farinciki tsabar jin dad'i, tace "shikenan gobe insha Allah biki zai kankama harna fara tunanin abinda za'aci.
Germany•• anguwa Munich
Akwai wani katafaren company wanda ya amsa sunansa, abin mamaki anan shine mamalakin company d'in dady Falak ne, yanada kamfanoni uku, kaf cikinsu wannan shine babba anan yake san'ar siyarda su zinarai gwala gwalai daduk wasu abubuwa da suka shafi hakan, sosai ya k'ware a aikin, amman Falak tafishi sanin makamar aikin sbda shi ta...


Read / Download FALAK Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album