Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

NAZLAH Complete Hausa Novel Document by NAZLAH


NAZLAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 29808



NAZLAH

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Nov 2023

Author: Salmaji Yar Lelen Royal Star ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 07033371851

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 167.25 kb

File Type: txt

Views: 790+

Download: 532+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: [11/27, 7:15 PM] Masoyiya💖💖💖💖: ☘️☘️NAZLAH☘️☘️



*DAGA ALƘALAMIN*


SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️






*WANNAN LITTAFIN TUN DAGA FARKINSA HAR KARSHENSHI SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF) WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI , ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA KARA RUFA MIKI ASIRI DUNIYA DA LAHEERA..........*




*WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE #200 NE KUƊINSA KI DAURE HAJIYA KI BIYA NAKI, DOMIN SHAN KARATUNKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI......*




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*( DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI, YAH RAB YARDA NA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA KASA NA KARESHI LAFIYA, ALFARMAR ANNABI DA AL-QUR'ANI)




3-4.





"""""""""""""""""Ba sai kin kara fada min komai ba, ai dama bakyason laifinsa duk ranar da baƙin cikinsa ko muguntarsa suka kasheki zaki gane mugun halayarsa",,ta fada tana taimaka mata, shi kuwa jin hayaniya ta kara yawa a kansa yasa yace "Wai ha haka ne, ke meyasa jaka ce, duk yarda na fada miko magana bakyaji, ko kullum kinfi son nayi ta dukanki sai kace jaka, kina cikin wannan halin ma ba zaki tausayawa kanki ba Mutswwww" ya ƙarasa fada yana jaan tsaki.........






Haushi kamar zai kashe Iya,, cikin fusata tace "Uwar kace Jaka, kai dama ashe har yanzu halinka bai chanja ba, ina ga bayan shaye-shayen da kakeyi har da ciwon hauka ya kamaka", ta fada tana ɗankara mishi dakuwa...........





sosa kanshi ya yi, tare da cewa, "Au wai da Iya ce", banza tayi dashi, ganin ya yi zaune yasa tace "Malam ka bamu guri dan Allah", sumi-sumi ya wuce daga ɗakin yana wani haɗa hanya, yanayin tafiyarsi kawai zaka kalla kasan shi din Dan shaye-shaye ne ma bugawa a jarida................





mayar da hankali Iya tayi akan Maryama da take ta uban nishi, ruwan rubutun da tazo dashi ta fasa ledar tare da sanya mata a baki, sha ta fara yi cikin fita hayyaci, bayan ta gama sha , ta shafe mata tun daga saman cikinta har ƙasan mararta da ruwab rubutun, cikin ƙanƙanin lokaci Naƙuda ta tahau gadan-,gadan cikin mintuna da bazasu wuce 20 ba Allah ya sauketa lafiya, tana haihuwa ta matsa daga kusa da Yarinyar da take tsanyara kuka ta kwanta tana sauke numfashi, wani bacci mai mugun nauyi ne ya yi Awan gaba da ita.............






Gyara Yarinyar da take tsala kuka Iya tayi tare da ajiyeta gefe, kayan jinin ta fita dasu, sai da ta daura ruwan zafi akan katon murhun da yake tsakar gidan kafin ta ci gaba da wanke kayan da aka ɓata, lokacin da ta gama wankewa ruwan zafin ya yi zafi sosai, ɗiba tayi tare da shiga dashi ciki, kyakyawar jaririyar da take kwance idanunta kyarrr tana kallon sama ta dauka, tare da yin bissimillah ta fara dan shafo ruwa da hannunta ta goga mata, wani jalar kuka mai firgitarwa ta tsanyara, wanda yasa ita kanta Iyar sai da taji tsoro.............




ganin babu abin da ya sameta, yasa taci gaba da mata wankan, tana dan murmushi, gani Yaringar Sak Uwata ta biyo komai, sai dai har tafi Uwarta fari, dan ita wannan fara ce mai sirkin jaa-jaa kalar dai fatar turawa.............




bayan ta gama mata komai, ta Ajiyeta domin zuwa ta dauko wani kwalli da ta daka domin ringawa Jaririyar Amfani dashi, tana ajiyeta ta sanya kuka, ficewa tayi da sauri domin zuwa ɗakkowa, tana fita Lawan na shigowa, direct dakin ya nufa, in da yake jin kukan Yarinyar yake kallo sai dai bai ga Yarinyar ba, hakan yasa ya yi kan Maryama da take kwance tana baccin wahala, ƙafarshi yasa ya fara shurin hannunta tare da cewa "Ke! ke!! ke!!! ke ki tashi ki dauke wannan Aljanar Yar taki ", ya fada yana zama, dakyar ta mike ta nufi inda takejin kukan yarinyar ..............





laluɓawa ta farayi har ta samu inda take, raɓata jikinta tayi, tuni tayi tsiit kamar wadda akace wa Mamarta ce ta dauketa, ba'a dau lokaci ba Iya ta dawo da tandun kwallin sanya mata tayi, tare da mikawa Lawan ita tace "kar ɓeta ka riketa zamu shiga wanka", tana daurata kan hannun Lawan ta fasa kara da kuka sosai, kallon Iyar ya yi tare da cewa "Iya kuka take,kuma ni wlh banason kukan Yara", harara ta dalla mishi tare da cewa "Nima ai haka nasha wahalar kukanka dan haka ka ɗana", ta fada tana jaan hannun Maryam , tsakar gidansu dake kwal-kwal a shere suka fito, kama hannunta Iya tayi suka shiga bandakin da yake fes shima yasha shara.............






Wankan Runhu Iya tawa Maryama , ai kuwa kafih su fito har ruwan nono ya sauka sosai, har tana ji yana dan zubar mata, har kuma suka fito daga wankan Yarinyar nata tsala ihu iya karfinta..................






da kanta ta taka ta nufi cikin ɗakin, Tabar Iya waje, tana shiga yace "Ungo wannan Yar mai masifar kuka", jikinta har rawa yake takarɓeta, ɗiwawunta ta fara neman inda zata ɗosana, zama tayi kusa dashi kaɗan dan ba duka tama zauna ba, tsawa ya daka mata tare da cewa "sauka! sauka salon ki zubamin ƙazanta a saman gado, to wallahi har ki yaye na haramta miki hawanshi", da sauri ta zauna ƙasa, Iya ce ta shigo, ɗakin hannunta dauke da kaskon wuta rushi ringis a cikinshi jaajir, akiyewa tayi tare da komawa ta ɗauko faranti, ajiyewa tayi tare da cewa "ke baki da hsnkali ne kike zama ƙasa, daga haihuwarki yau, salon kije ki janyo mana wata matsalar", ta fada tana kallonta, dan murmushi tayi tare da cewa "ba komai a ƙasan fa Iya", shiru Iya tayi dan tasan ba kowa zai hanata hawa gadon ba sai Lawan..........




"to taho Maryama kici Abin ci", matsawa tayi gurin Iyar tayi, bde mata kwanon tuwan dawo da miyar kuka tayi, miyar taji haɗi ga ƙanshin man shanu na tashi sosai,kallon Iya Lawan Ya yi tare da cewa "Iya ni ina nawa ?" sakin baki tayi tana kallonshi, sai kuma tace " ni nace kaje ka buga chacha da kuɗin da zaka ci abin ci dan haka sai ka nema", shiru ya yi yana kallon tuwon da ba ƙaramin bi dashi ya yi ga..........






Haleeem da ya shigo dakin ta jawo jikinta tare sa fara bashi abincin yana ci yana shafa kan baby gal din da yake luluɓe da gashi baki siɗik mai yawa sosai, ganin komai normal yasa Iya mikewa ta tafi gida, tana fita ya diro daga kan gadon, anshe tuwon ya yi, tare da komawa gefe ya ci gaba da ci, ba tare da tunaniin sun koshi ba ko basu koshi ba ...............






ganin gari na walkiya yasa ta mike ta fara shiryawa cikin kodaɗɗun kayanta, wata tsohuwar rigar Haleeem ta dauka ta sanyawa babyn tare da luluɓeta, shimfiɗa ta shiga yi musu a ƙasan sumintin cikin ɗakin, kafin ta gama Haleeem ya yu bacci gyara mishi kwanciya tayi tare da kwanciya itama, tana kwanciya ruwan sama mai karfi ya tsuge, ruwan aka fara mai karfin kamar zai ɗaye rufin kwanukan mutane ya tafi da su..............





luluɓe Haleeem tayi da kyau, tare da daura baby'n akan kirjinta ta luluɓe sosai, kasantuwar kayan jikinta ba wani na kirki bane yasa sanyin da akeyi take busu mata, sanyi ne ya kamata kyarma ta soma yi, gashi ɗakin babu ko abun rufewa balle ta rude, labulen kuwa irin boka-bokan nan ne, ba wani na kirki ba , kyarma jikinta yakeyi, Addu'o'i ta fara...


Read / Download NAZLAH

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album