Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

DEEN Complete Hausa Novel Document by DEEN


DEEN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 333984



DEEN

Reading Time: 27 Hours

Added On: 27, Aug 2023

Author: Aisha Ashanty ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.94 mb

File Type: txt

Views: 3438+

Download: 4220+

Last download: 2 days ago

Description/Story: *DEEN*


(The heartbreak💔)

An amazing love story💘



Story written by Ashaanty love💖

Marubuciyar
_AUREN KWANGILA_



_Am back again! Alhamdullilah!🧚🏻‍♀️_




*001*




_"So let me know, if you no wan do again, I no go disturb you, I no go hold you!... Let me know uwo uwo if you no wan do again, I no go disturb you, I no go hold you... But no call me back oo, no call me backkk! When you see sey I dey with another person, baby no call me back oo, no call me baaaack when you see sey I dey with another gele..."_

Kpaaam! Kpaaam!! Kpaaam!!! Aka sake bubbuga kofar toilet din kamar za'a 6allata

Inaa? Batama San anayi ba saima qara volume din muryarta datayi tana bin waqar dake tashi a earphones din kunnenta
_"Even if you call e no go connect, cos I no go dey, I no go dey make you forget, come another day..."_ tafada tana lallauye jikinta kamar wata macijiya tana shashafa jikinta dake lullu6e da kumfa cikin wani irin salo

Qara bubbugo kofar akayi da wani mahaukacin qarfi wanda saida taji qarar dukda earphones din kanta

Saurin waigawa tayi ta kalli kofar tana zame earphones din kanta a lokaci daya

"Wai don ubanki bazaki fitoba!!" Aka fada daga waje ana qara bubbugo qofar

Wara manyan idanuwanta tayi kamar zasu fado daga raminsu sannan tashiga dauraye jikinta cikin rawar jiki

*"ZAINAB!"* aka sake kwala kira daga waje, daga ji kasan mammalakin muryar amatuqar fusace yake

"Na... Na'am mummy, wlh yanzu zan...fito" tafada cikin rawar murya tana jawo towel dake rataye a hanger ta daura ba don ta ida dauraye jikinta ba ta sauko daga bathtub din ta nufi kofar cikin 6arin jiki

Kallon kofar take a tsorace tama kasa kai hannu ta bude saboda tsoro

"Wai bazaki fitoba?!" Aka sake fadi cikin tsawa wanda har saida ta zabura

Hannu na rawa ta zare sakatar kofar tana yin saitin gudu

Banko kofar tayi da karfi itama tayo waje aguje tana callara ihu cikin zazzaqar muryarta

Mummy datayi baya baya saboda bangajeta da Zainab tayi tayi saurin dafa wani qarfe dake gefe wanda ba don shi ba da tuni tajita qasa

Zainab kau tana fitowa, waje tayi ido rufe tana sake fasa qara tana kiran sunan Daddy

Bata damu da abinda ke jikinta ba ta sauka qasa da gudu hannu dafe da guntun towel din jikinta ta ratsa yan aikin dake falo suna karakaina

Duk dakatawa da abinda suke sukayi suka juyo atsorace suka bi *MADAM* da kallo cike da alhinin meya biyota

Basu qarasa tunanin zucinsu ba suka samu amsa don *HAJIYA* ce sukaga itama tayo qasa cikin gudu gudu sauri sauri, cable din chaza a hannunta tana kwala kiran Zainab ganin haka zata fita waje

Saurin sunsukuya kai sukayi hartazo ta ratsasu itama tafice sannan suka dago suna girgiza kai na takaicin halin *ZAINAB*

Zainab kau haka ta ratsa ma'aikata dake harabar gidan cikin gudunta wanda hakan yasa duk cinyoyinta suka fito waje, ma'aikatan sai binta da kallo suke amma ita ko ajikinta, itadai burinta ta cinma part din daddy kafin mummy ta kamata don tana jinta abayanta

Ganin mummy ta fito yasa dukkan ma'aikatan dasuka bi Zainab da kallo saurin kame Kansu suna gaidata cikin girmamawa

Babu wanda ta ko kalla sai nufar part din daddy datayi kamar zata tashi sama


Zaune yake yayi balancing a kan wata lumtsetsiyar kujera yayi bake bake yana kallon abinda managern shi ke nuna mashi a laptop

"Daddy! Wayyo Allah nashiga uku!" Suka tsinkayi muryar Zainab hakan yasa duk suka dago alokaci daya suna kallon kofar shigowa

Banko kofar akayi, sai gata ta dirko kamar wacce aka tillo

Kafin kiftawar ido harta qaraso gaban Daddy ta danneshi tana qara cikwikwiyeshi

Iya rudewa Daddy ya rude don sosai take kurma ihu gashi taqi bari ma yatashi zaune bare ya tambayi abinda ke faruwa, tawani qanqameshi tana ihu kamar wacce ake yankawa


Manager kau tsaye yayi agefe yana Kare mata kallo qasa qasa yana lasar le6e ganin yadda duk rabin fresh boobs dinta ke waje ga santala santalan jajjayen cinyoyi mallam

Shigowar mummy yasashi saurin shiga taitayinshi yayi qasa da kai

Ganin shigowar mummy yaqara volume din ihun Zainab tana qara maqalqaleshi cikin 6arin jiki

Sai a sannan shima Daddy yasan meke faruwa hakan yasashi dagowa ya zubamata idanu cikin fushi

Kallon da mummy tayiwa manager yasashi saurin daukar laptop din gaban Daddy ya rufe ya kwashe tarkacenshi yayi musu bankwana cikin girmamawa yayi waje

Fitarshi keda wuya mummy tayo kansu Daddy gadan gadan wanda hakan yasa Zainab sakin wata mahaukaciyar qara ta cusa kanta a qirjin Daddy jikinta na rawa

Ganin hakan yasa Daddy maidata bayanshi yayimata tsakani da mummy yana kallon mummy cikin huci

Mummy kau mazuranshi da siracinshi be hanata qoqarin jawo Zainab dake la6e a bayanshi ba

Qara kareta yayi yana riqo hannun mummy yafara magana cikin 6acin rai
"Wai Maimuna meke damun kwalwarki ne?!"

"Hauka ke damunta! Nace hauka nake, wlh yau babu mai hanani illata wannan shashashar anan!" Tafada tana qara yunkurin kamo Zainab dake bayan Daddy tana kuka sosai

"Saiki illata ta din! Nace ki illatata! Wai Maimuna kanki daya kau? Kibiyo Yar qaramar yarinya da gudu da wannan lafcecciyar wayar a hannu, nufinki me to? Badai nufinki akanta zaki dora wannan tsinnaniyar wayar ba?" Yafada rai 6ace

"Qaramar yarinya? Did you just called Zainab yarinya? Macen dake cikin shekara ta ashirin da daya? 21 ba 12 ba! Ace batasan daidai da rashin daidai ba? Bata iya ware fari da baqi? Kaikuma bakada aiki sai kareta? Bakada aiki sai lallata yarka da kanka!" Tafada cikin tsananin 6acin rai hawaye na kawomata

"Yanzu me tayi kuma dazaki biyota dagudu kamar wata qaramar yarinya riqe da wannan uwar bulaliyar kamar ta bugun jakki? Anya kinada tausayi? Yanzu da kin samu riqeta da zubamata ita zakiyi ko? Don rashin imani irin naki, wlh ba don agida kika haihu ba kuma kuna kama da jewel da wlh nace ke ba uwarta bace, 'ya guda tilo da Allah yabamu duniya da lahira shine zaki kashemana ita? Inbanda abinki duka nawa take dazaki dinga addabar rayuwarta haka? To wlh baniso, banaso! Karki sake min haka don ban hada diyata da kowaba kuma zan iya yin komai akanta, idan ke baki sonta to ni inason abuna" ya qarashe yana huci sosai

Mummy da tun lokacin daya fara zuba ta kafeshi da idanunta dake digar hawaye ta sa bayan hannunta ta share hawayenta ta saki wayar chazar dake hannunta ta juya tanufi hanyar fita afusace ta fita tana rufo qofar da qarfi

Wata wawiyar Ajiyar zuciya suka sauke mai nauyi bayan sun rakata da kallo

Komawa da baya Zainab tayi tafada kan kujera tana maida numfashi ahankali tareda furzo wata zazzafar iska daga baki

Daddy da duk jikinshi yayi sanyi ganin yanayin da mummy ta fita ya nemi guri kusada Zainab ya zauna ya miqa hannu ya jawota jikinshi

"Baby na, hope dai kina lfy?" Yafada cikin tsantsar kulawa

Fizge jikinta tayi daga riqonshi sannan tafara magana cikeda tsiwa
"Inafa lfy Dad? Ni wlh Allah yasani wannan Matar ba qaramin takurawa rayuwata tayi ba, can you imagine wai dukana zatayi? Yanzu data samu damar kamani fa dukana zatayi, am almost 21 amma ban girmi dukaba a gidanmu, imagine" taqarashe tana girgiza Kai fuska a yatsine

Qara rungumota Daddy yayi cikin sigar rarrashi yace
"Shiiii... Ya Isa haka, nayi maki alqawari zanyiwa tufkar hanci"

Cikeda rashin kunya da tsantsar sangarta tace
"Yaushe? Tun yaushe kake cewa haka amma abu ya gagara? Ni wlh haryanzu ban yarda wannan matar uwata ce ba, matarda kwata kwata bata qaunata? Ta tsani ta ganni cikin walwala da annushuwa, duk hanyar datasan zatabi domin daqile farincikina tasanshi, komai na duniyar nan idan nayi to ba daidai bane, tasamin ido tasamin hanci da baki, kai wlh nagaji, ace agidanku bakada freedom? A matsayina na diyar *Alh. Farouq Dan faranshi* diyarshi daya tilo ace banida freedom? Gasu kucakan friends dina wanda ko kwatan arziqinmu basu dashi suna life dinsu yadda sukaga dama, suna living free live babu takura, saini daddy? Saini the whole *ZAINAB FAROUQ DAN FARANSHI?*" ta qarashe zancen tana sakin kukan ta6ara

Qara rungumeta yayi sosai yanajin kukanta na ta6a Mashi zuciya sosai

"It ok Darling, Dan Allah ki daina kukan nan kar yajamaki wani ciwon, insha Allah zanyiwa tufkar hanci ok?"

"Till when Dad? Nace ka kaini abroad na qarashe karatuna ka qiya, ka biye mata kun Sani a wannan Yar iskar makarantar da duk tarin yan jagaliya ke ciki, kai shikenan duk abinda mummy tace saika biyemata, da farko ka yarda zaka kaini UK karatu amma daga ta janyeka daki tayimaka karatu saika chanza magana, wai Umaru Musa Yar adu'a, wai kamar ni a UMYAU, mtcheew!" Taja tsaki cikeda rashin kunya

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke cikin rashin sanin tacewa saikuma can yace
"Yanzu dai it ok, banason ganinki a 6acin rai wlh, hankalina tashi yake, and batun karatu abroad bawai don mummynki ta nuna batasoba yasa nafasa turaki canba, kawai baxan iya jurar zama na tsawon wasu lokutaba batareda na sanyaki a ido ba, Zainab kema...


Read / Download DEEN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album