Join Our WhatsApp Group

GIDAN MATI Complete Hausa Novel Document by GIDAN MATI


GIDAN MATI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13030



GIDAN MATI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Bongel Fulani ,Rufaida Omar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 69.2 kb

File Type: txt

Views: 850+

Download: 167+

Last download: 8 days ago

Description/Story: GIDAN MATI
©BINGEL MITA & RUFAIDA OMAR
Hausaebooks
Shuraih Usman
http://shuraih.waphall.com


Buguzum-buguzum ta sanyo kai cikin gidan
tana wak'a.
"Ahayye iye nana..."
D'if ta dakata gami da sakin baki adalilin
abinda ta hango a tsakar gidannasu.
Maigidansu Mati a k'ofar d'akin kishiyarta
Abulle zaune su na hira da dariya. Ganinta
ya sanya Mati yin tsuru da idanu yayin da
ita kuwa Abulle ta washe baki, cike da
dabara ta fiddo takardar naman da ta 6oye
a bayanta ta warware ta d'auki tsoka d'ayan
da ya rage ta jefa a baki ta na tauna gami
da fad'in.
"Maigida kana burgeni, kana kawomin irin
wanda na ke so."
Mati ya watsamata kallon muguwar mace,
shaf a tunaninsa dagaske ta yarr da takardar
tsiren, ashe makirar abinda ta shiryamasa
kenan. Ya numfasa gami da share zufa ya na
duban Nene batare da ya ce uffan ba.
Nene wacce zuciyarta ta gama kaiwa bango
ta fisge mayafin kanta ta had'iye miyan da
ya taru a bakinta tsabar na ranta ya biya ta
ci d'amara ta hau tafa hannu.
"Allah na godemaKa da ka nunamin abinda
ke faruwa a bayan idona! Ashe daman cuta
ta ake yi ana dawowa idan bana nan? To yau
dubunku ta cika Mati, yau sai an bambance
tsakanin aya da tsak'uwa!"
Jin haka ya sanya Mati mik'ewa ya hau
fad'an k'arfin hali da borin kunya.
"Ke ya isa! Yimin shiru dak'ik'iya kawai! Kin
shigo gida ba sallama ba komai sai wak'en
banza sannan ba ki tsaya kin ji dalilin
dawowata ba yanzu kishi zai kaiki ya baro
ki!"
Kafin Nene ta samu bakin magana, Abulle
ta saki wata dariya irin ta wadanda duniya
ta yiwa dadi.
"Kai namiji, namiji akace buhun k'aya.
Sannunka munafuki, inace mun fi awanni
biyu tare? Duk dai abinda za'ayi sai dai a yi
don ba na tsoron kowace mai yanayin
kul6a, miji ne mun yi aurenmu na soyayya
muna zaune lafiya yana kawomin kayan
mak'ulashe koda kuwa ba kwana na ba, sai a
mutu!"
Da jin haka Nene ta zabura ta yi kanta ta na
faman surfa ruwan ashariya.
"Yau sai na nakasa ki tsohuwar bazawara
mai bin maza, saidai wannan tsohon gurgun
ya k'ara haifar wata."
Ai sai su ka shiga kokawa, Nene ta daddage
ta ba ta kyakkyawan cizo a mamanta wanda
ya ke fata ce kawai. Wani ihu Abulle ta saki
gami da fad'in.
"Kan uban can!" Ta cafki jan gashin kan
Nene mai kama da gemun ɗan Bunsuru ta
hau ja da k'arfi, ta kuwa shiga ihu har
zaninta na fad'uwa sai ga ta zirr babu ko
d'an bante. Mati ya tafi da gudu ya d'auki
zanin ya na kokarin suturceta ganin
magulmatan makwaftansu wato Gidan Delu
da Gidan Shafa har sun soma lek'e ta
Katanga.
"Menene haka? Ke Abulle don iyayenki
sakarta!"
Wani turi da Abulle ta yiwa Nene sai kuwa
ta jefata jikin Mati su ka yi kyakkyawan
zubewa a k'asa abinka da siririn mutum. Da
sauri Nene ta mik'e ta suturta jikinta ta na
huci.
"Shegiya mai kalar mayu zan yi maganinki a
gidannan, za ki san kin shigo gidan Nene."
Wani banzan harara Abulle ta watsamata
sa'ilin da ta ke gyara zaman rigarta.
"Yanzu aka fara tashin hankula a gidannan
muddin ba za ki fita a harkata ba. Mace ba
ta ajiye komai ba sai ta ci ta yasar da k'aton
kashi a masai! Gwara ni, tunda ko ba komai
na yi 6ari an ga shaida!"
Nene ba ta jira komai ba ta nufi wajen
girkinsu ta rarumo ta6arya ta taho a guje,
ai Abulle na ganin haka ta fad'a d'akinta, ga
shi ta kasa d'aga labulen kaban k'ofar d'akin
hakanan kawai ta turo kyauren.
Nene ta tsaya ta na huci ganin Mati ya sha
gabanta.
"Shegiya kai, ashe ke 'yar iskar k'arya ce, yo
ki tsaya mana idan ban nakastaki ba anan."
"Haba Nene, ya isa hakanan, muje daga ciki
ki ji."
Fad'in Mati hankali a tashe don shi har ya
rasa ma yanda zaiyi ga makwafta 'yan gulma
na kallo.
"Haba ke kuwa Nene, ki yi hakuri mana."
Fad'in Delu kenan cike sa tsegumi.
Wani banzan kallo Nene ta watsamata, sai
lokacin ta lura da tarin magulmatan
makwaftansu da ke lek'e.
"Kai! Allah Ya tsaremu da munafukai,
mutane ba su ajiye komai ba banda
munafunci da gulma, dadin abin dai mijina
bai ta6a jibgata ba kuma bai ta6a haikewa
wata ba."
Delu wacce tasan ita miji ke jibga ta ja tsaki
ta ce.
"Oho dai! Duk acikin so ne." Daganan ta bar
lek'en tare da yanmatan yaranta uku. Ita
Shafa salin alin ta sauka ba ta ce uffan ba,
to ina bakin magana tunda tasan da gaske
mijinta kwarto ne na a kwantanta.
Dakyar dai Mati ya kashe rigimar tare da
alk'awarin zai kawomata na ta k'unshin
tsiren. Abinka da kwad'ayyiya kamar
Asma'u a gari, ba musu ta hak'ura.
*** *** ***
Abulle ta ta6e baki.
Mati bai ko kula ba ya ci gaba da
maganarsa.
"Sanin kanki ne dai Inna ba ta damu da
zuwa k'auyen nan ba tunda Baban su Ladiyo
ya d'and'ana mata zaman birni, yanzu kuma
musamman don ni za ta zo ayi zumunci.
Don Allah Abulle, ke ce k'arama, ke ce
kuma ba ta sani ba, ki taimaka ku zauna
lafiya har ta tafi. Sannan inda hali inason ayi
wani abu."
"Menene shi?"
Ta fad'i da sauri.
Ya yi shiru sai kuma ya numfasa ya sassauta
murya.
"K'aryar ciki."
Gaba daya ta zaro idanu ta na dubansa. Ta
murza bajajjajen hancinta.
"Yi min gwari-gwari dai."
Ya hau bayani.
"Inna ta sanarmin cewa muddin ta tarar
kema ba ki da ciki to lallai za'a samu
matsala don kuwa sai na sake ki na yi wani
auren. Ni kuma kinsan dai ina sonki ina son
zama da ke, don.."
"Tsaya tsaya Mati, shi ke nan wannan abu
mai sauk'i ne zan yi, sai dai menene ribar?
Wace kyautar bajintar za ka samu bayan
hakan don nasan halinka, ba ka aikin
banza."
Ya yi 'yar dariya ya shafi sumarsa.
"Kai kai Abu tawa ta kaina, kina da saurin
fahimta kam. To bari ki ji, akwai wata
tafkekiyar gona ta Inna da kuma gida da ta
ke bayar da haya ana biyanta balas duk
karshen wata, ba yanda ban yi ba akan ta
bani gonar ta k'i, to ta tabbatarmin za ta
bani har da k'arin gidan nan ya zama
mallakin jikanta."
Abulle ai sai ta hau tsallen murna da sakin
gud'a.
Mati ya hau rufemata baki a tsorace.
"Ke ki rufamin asiri kada waccan ta ji."
Tunanowa da Nene da ta yi ne yasa ta
saurin sai ta kanta.
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
*GIDAN MATI*
©ƁINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Daga waje kuwa Nene na jin haka sai ta yi
wuf ta fito daga maɓoyarta, can baya take
zagayawa ta hau kan ɗan dutse tana kasa
kunne a ƙaramar tagar ɗakin Abulle. ta na
yi tana leƙa bayanta ko wani zai taho
wucewa kasancewar daga nan ana hangen
waje a dalilin gajartar katangar.
. Ɗakinta ta shige da saurinta, jiki na
rawa ta hau sauke kwallayenta tana faɗin;
"Idan sammako ku kayo, ni asubanci na yi."
Ta fiddo wani maganin gargajiya wanda
tayi mugun tsanar warinsa, sannan ta mai
da kayan ta afka garin kusan rabi a baki. Kan
ka ce mene wannan cikinta ya murɗa ga
yunƙurin amai da ta soma. Ai a guje ta fito
ta isa gaban makwararar ruwa ta hau sheƙa
aman iyakar ƙarfinta tana nishi yanda ta
tabbatar za su tsinkaya...
"Ni fa kamar kakari nake ji." Cewar Mati
yana kallon Abule.
"Kai fa daɗi na da kai har yanzu baka
bambance kukan Jakinka dana Akuyar
Delu."
"To idan ma itan ce kinyi zaune salon tamin
ta'adin da ta saba?"
Ya faɗa yana mai mi'kewa tsaye, itama da
sauri ta mi'ke tana mai rufa masa baya.
Ita ɗin ma ta wajen jin tahowarsu ya
sata zubewa gefen kwatamin tana mai ri'ke
cikinta da faɗin "Wayyo! Mati..."
Da gudansa ya 'kara so wajen yana mai
janyeta gefe.
"Ikon Allah! Nene ashe ke ce. Sannu me
kika ci ne haka?"
"Ba komai tun safe nake jin tashin zuciya da
rashin jin daɗi."
Ta faɗa da ƙyar tana sauke numfashi.
"A'a irin wannan ciwon ai ba na shiru ba
ne Nene, karki manta da haka Sahura ta
mutu da irin shirun nan."
"To Mati ana ta kai wa yake ta larura?
Taimaka min zakai Abule ta dubomin 'Yar
Magaji, ji nake kamar ana daka yaji a
kirjina."
"Huu'umm!" Abule ta faɗa tana tafa hannu.
"Ai wallahi da aiken kishiya gwamma na
jibgi Uwar miji. Kai ni ban ma yarda da
wannan ciwon ba. Saboda Allah Mati baka ji
warin tazargaje ba?"
Ta faɗa tana mai ɗaɗɗaga hanci sama.
"Me kike nufi ne? Kinga Abule ban san
fitina, ya mutum na halin ciwo kina kawo
shashanci. Idan na isa dake to maza ki je ki
dubomin 'Yar Magaji."
. Mintuna kaɗan Abule ta dawo da 'Yar
Magaji biye da ita ta rataya wata tutturna
jaka me kama da ta wazirin Sarkin kutare.
Kallo ɗaya tama Nene maƙaryaciyar
zuciyarta ta kisa mata menene,
dan haka ta kalli Mati da murmushi.
"Malam ai ba wata larura ba ce mai girma,
ƙaruwa ce zaku samu, a taƙaice dai Nene
ciki gare ta har na tsawon wata biyu."
"Kan babban bala'in can! Alkur'an
wannan ƙarya ce."
Abule ta faɗi tana mai buga tsalle gefe,
kafin kuma ta yi ɓarin da Nene ke kwance.
"Ke Nene ki ji tsoron Allah, ina ce ba
shekaranjiyar nan muka gama rikici kan
tsumma na da kika yaga kikai kunzugu da
shi ba?"
"Wayyo Ni Abule! Yau na ga abinda yafi
'karfina, wai cikin ma har kinsan ya yi wata
biyu sai ka ce wacce kika haɗa iri da Mayu.
ke kam 'Yar Magaji anyi tantiriyar
ma'karyaci wallahi. Matar da ake raɗe-
raɗen Aljanu sun sace mata mahaifar ne ke
da ciki?"
"Ke! Ke! Abu kin cika mana kunne da
shegen karaɗi. Ki tsayamana abu abin a
sannu idan ma ƙaryar ce ai 'Yar Magaji za ta
faɗi.
"Wane irin bi-sannu Mati? Ai fa magana ta
riga ta ƙare, Nene dai ciki gare ta, maganar
ganin jini kuma wanann a bayyane yake, ko
Magaji ka tambaya zai idar maka wannan
zance. Lalle ne akwai Matan dake jini da
ciki. "
"Ke kuma Abule da kika haɗa Ni da
Maita ina jin dai tsohonki shi ne Bazawari
na? Dan haka bushiya dai ba zata wa
Kunkuru gorin ƙafa ba , ko zaki mutu dai
Nene ciki gare ta na wata biyu."
"Kai kuma yanzu ya rage naka sai ka dinga
mata abinda take so. Ni kaga tafiya ta."
Muna zuwa...*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
"To ai sai ki kauce daga samanmu tunda
dai shegen baƙin cikinki ya jawo kinji
abinda Tsohonki ke aikatawa a waje."
Mati ya faɗi yana hararar Abule da
tayi tsaye hannu bisa ƙugu tana jinjina
maganar 'Yar Magaji.
"Oho dai, daɗin ta Bazawari aka ce
ba Ɓarawon Jakai ba."
Ta faɗa tana hararar Nene dake yatsine-
yatsine.
.
"Kyale ta kinji Nene uwargidan Mati, muje
na raka ki ɗakI ki kwanta, daga yau ko
tsinke ban yarda kin ɗage a gidan nan ba,
wanda ba zai iya gani ba yayi zuciya mu gani
a ƙasa." Ya faɗa cike da lallami.
Ita ɗinma miƙewa tayi cike da
kwarkwasa har da riƙe rigar Mati. Gab da
zata ɗaga labulen kabar ta ne ta waigo ta
kalli Abule fuskarta ɗauke da murmushin
kaɗan kika gani.
Dogon tsaki itama taja tana hararar ɗakin
bayan shigewarsu. "Wai Kura ce ta samu
damar miƙe ƙafa, ayi dai mu gani, muna
nan za ka zo kana min 'yar murya. Har
yaushe ma akai daren?" Jin shiru ba su
amsata ba sai tashin dariyarsu da take ji ne
ya sata juyawa a fusace zuwa na ta ɗakin.
Kwana biyu gidan shiru daga uhumm
sai hu'umm wai uwargulma tayi cikin shege.
Duk san Abule na ta gane gaskiyar cikin
Nene abun yaƙi yiwuwa. Sai ma barinta da
takaicin arba da ledar Burodi da Tsire da
take yi kullum safiya. Idan ma ta yi dakon
hana ido barci dan a kasa da ita Mati baya
shigowa gidan sai dare ya raba, kafin ta
gama barcinta ya kaɗa na sa Jakan yayi gaba
tsabar rashin gaskiya.
Sauri take ta isa gida, dan ta fara
gwada maganin saka laulayin da Gwaggonta
ta bata ta dinga shansa duk dare, bayan ta
sanar mata da abinda ke faruwa a gidansu.
Ta tsinkayi muryar Delu na kwaɗa mata
kira.
Kamar ba za ta tsaya ba, sai dai taja tunga
ganin Delun harda ɗan gudunta.
"Uhm! Tunda na taho nake Addu'ar
Allah ya sa na ganki, dan kuwa ba za ai
wannnn cin Amanar a gaba na ba."
Gabaɗaya ta mai da hankalinta kanta
"Me ya faru Delu? Na sanki baki maganar
banza."
"Ke dai Allah ya raba mu da Miji mai
ɗabi'ar hankaka. Mati na gani yanzun nan
gun 'Yarbaiwa mai Fara ya sai har ta Naira
Hansin wai Uwargida ke kwaɗayinta, baki
ganta ba fal ledar..."
"Fara fa kika ce? Farar da tunkan muyi aure
yake min alƙawarin cinta?" Ta tari
numfashinta.
"Idan ƙarya nake miki wannan zance tsawar
bana ta sauka gonar Malam Alkur'an."
"A'a me na jan masifa? Zai yi fin haka ko
dan ya nunan shi Namiji ne kwandon zawo,
barni da shi, yau ko zai mutu ba za ta ci
Farar nan ita kaɗai ba. Ke har ke sai kin
ɗanɗana, na gode miki Delu, bari na ƙarasa
gidan.
Da sallamarta gidan ta yi jifa da
kallabin kanta gefe, luma yatsunta ta yi
cikin gashinta ta fara wargaza shi, kan kace
mene wannan ta tada hankalin gashinta ya
yi tsaitsaye tamkar gemun Mahaukaci da ya
shekara ana jifansa. Nene dake gefe ana
ƙoƙarin sai ta kai, sai gani tayi Abule ta
zube tana wani nannaɗewa, doka ihun da
zata yi sai ga shigowar Mati yana mai da
aljihunsa baya. Ganin Nene jiki na ƙyama
ya sashi yin wurin Abule yana salallami.
"Karka ƙaraso! Kana ƙarasowa idan muka
fyauɗe ka sai ka dangana da Gyatumarka"
Yaji murya na gargaɗinsa kamar ta
Kuyangar Kutare.
Turus! Yayi ƙafafuwansa na rawa kafin kuma
ya zube ƙasa yana kallon yarda Abule ke
naɗewa bakinta na dilalar yawu.
"Kiyi haƙuri Abule wallahi bansan kina da
larura ba."
Ya faɗa kamar zai fashe da kuka.
Taja majina.
"Kai! Ka iya bakinka, wanann ba lalura ba ce,
kai ne ka kira mu da kanka da kake taɓa
mana Goɗiya kana sa ta kuka."
Ta faɗa tana zare manyan jajayen
idanuwanta.
"Ƙarya take min bantaɓa sa ta kuka ba,
Nene shaida."
"Munafuki menene wannan a aljihunka na
hagu?"
"Fa..fa ...fara ce."
"To wa ka siyo wa?"
"Abule mana, ita ce Amarya ta da bana iya
motsi sai da ita."
"To bawa waccar ta kawo farar nan
gabanmu, gargaɗin ƙarshe kuma ka kuskura
ka ƙara kawo ko Dusa ce ba ka haɗa da
Goɗiyarmu ba sai mun musanya mata
yaron cikin da take ɗauke dashi da
Kadangare."
"Ban..ban..gane ba..."
"Au! Dan fitsara ma baka San Goɗiyarmu na
da cikin ka ba?"
"Na sani, ku yi hakuri. Ke Nene miƙa musu
Farar mana."
Ya faɗa yana jefa mata kullin ledar dake ta
kyallin mai .
Abule ta kalla idonta kamar zai faɗo dan
tsoro, gani take kamar bakinta ma ya koma
gefe, dan haka ta Yi baya cikin hawaye.
"Ba zan iya ba Mati."
"To kuwa zan fita na barki da su, ki miƙa
musu ko za su tafi."
Ya faɗa da tsawa.
A ɗarare ta miƙa ledar gaban Abule dake
naɗe, a guje ta juya zuwa ɗakin ta ta lafe
bayan kaba tana hangen su.
Ƙatuwar Hamma Abule ta saki, kafin kuma
ta ɓingere gefe maƙale da ledar farar ta.
Akwai alamun Borin ya sauka.
*** **** ***
Muna zuwa
*GIDAN MATI*
©BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Assalamu Alaikum mutan gidan." Fad'in 'yar
doguwar dattijuwar kuma tsamurmura mai
sharɓa-sharɓan tsagu a gefen bakinta, bak'a
ce wuluk kamar d'anta Mati. Mati ne a gaba
d'auke da k'aramar akwatin kayanta, ita
kuwa tana biye da shi a baya.
Abule ta soma fitowa daga d'aki sai Nene
daga band'aki suka...


Read / Download GIDAN MATI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album