Join Our WhatsApp Group

DAJIN KWARANGWAL Complete Hausa Novel Document by DAJIN KWARANGWAL


DAJIN KWARANGWAL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 5687



DAJIN KWARANGWAL

Reading Time: 0 Hours

Added On: 02, Jan 2024

Author: Zaynerb Muhammad kabeer ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09066386347

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 33.59 kb

File Type: txt

Views: 945+

Download: 215+

Last download: 4 days ago

Description/Story: 🌳☠️☠️ *DAJIN ƘWARANGWAL*🌳☠️☠️

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

🌳☠️☠️ *DAJIN ƘWARANGWAL*🌳☠️☠️

*(FREE BOOK)*



*LABARI DA RUBUTAWA*

*ZAYNERB MUHAMMAD KABIR*
*(MUM FU'AD)*


*MARUBUCIYAR LITTAFIN*👇
*🌺🌺 MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺
💐💐 *A SANADIN KUSKURE NA*💐💐
🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️ *HATSABIBIYAR MACE*🧛🏿‍♀️🧛🏿‍♀️
🌪️🌪️ *GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*AND NOW*👇

🌳☠️☠️ *DAJIN ƘWARANGWAL*🌳☠️☠️

*_"Banyarda a canzamun labari ta ko wacce irin siga ba batare da izini na ba_*

_Labarin *DAJIN ƘWARANGWAL* Labari ne dai zai ilmantar ya faɗakar, sannan haɗe da ban tsoro da tarin Al'ajabi a cikinsa , sannan zai nishaɗantar, daku masu karatu......._

_Labarin *DAJIN ƘWARANGWAL* kwarangwal ƙirƙirarren labari ne , banyi shi dan cin zarafin kowa ba suna hali yanayi yayi kamaceceniya to a rashi, labari ne da zai faɗakar da mutane hade da ban tsoro a cikin shi .. ....._

_Labari ne da yazo muku da wata siga daban , na ban tsoro ,shin!! Kuna son kuji wacce wainar ake toyawa a ciki ? Ku dai kasance da ni , dan jin yanda labarin zai kasance ......._

_Kudai fatan zaku dinga suburbudo mun ruwan comments haɗe da dogon sharhi da kuma tayani sharing , , dan Hakan shi zai karamin ƙarfin gwaiwar yi muku typing....._

*SADAUKARWA*
_Sadaukarwa gareki masoyiyah zahrah Abdul (mommyn Ahlan ) garkuwar macizai , marubuciyar Azima da Aziza ....._
_Da kuma ƴan uwana abun kaunata Allah ya bar mutare har karshen Rayuwar ,ya karama haɗin kai da kwanciyar hankali_

*GODIYA*
_Godiya ta musamman ga Zahrah Abdul mommyn_ _Ahlan wato (garkuwar macizai)_
_Allah saka da Alkhairi Allah kuma ya bar kauna ya ƙara basira bazan gajiya da miki fatan Alkhairi ba........_

*_Kamar yanda zanfara lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya ,Allah kuma ya bani ikon rubuta abun da yake daidai , akasin haka kuma Allah ya yafe mun ....._*

_Banyi Alƙawarin muku typing kullum ba ,amma inshallahu zanyi ƙoƙari nayi muku update akai_akai , Kudai ku ta bina da ruwan comments ina muku typing......_

_*ASHA KARATU LAFIYA*_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PAGE 1 & 2*

Sanye take cikin doguwar riga , wacce aka tsara mata ɗinki , da ganinta zakasan cewa ɗinkin Amare ne , wato ɗinkin fitted gown , rigar fara ce tas,sai dai alamu sun nuna dattin rigar yasa ta koma kalar ruwan madara wato milk colour.......

Fuskar tayi jajawur Alamar kuka da taci mai yawan gaske , hannayenta ta ɗaura saman kanta inda ta fara faɗin ", waiyyo Allah!!waiyyo Allah!! Allah na roƙe ka Allah ka kawomin ɗauki , Allah ka fitar dani daga cikin ƙungurmin *DAJI* nan , Allah ka taimake ni tafaɗa tana fashewa da wani matsananci kuka da ya baiyyana dashashiyar Muryar ta da ta dashe tsabar matsanancin kuka da taci .......

Gudu tafarayi ko Allah zai sa taga hanya sai dai duk inda ta ɓullo babu alamar hanya ko inda zai ɓulle da ita a gurin , kasancewar dajin yana da Matuƙar duhun gaske , bishiyoyi da kudiddifaine ko ta ina a dajin , hakan yasan ta laluba ta zauna a ƙasan wata bishiya, jin Alamar jini da taji yana fita a tafin kafarta,hannu tasa takai dai_ dai gurin da take jin matsanancin zafi , jin Alamar jini yasa ta sake wani ihu gamida runtse idanuwanta....

Duk da cewar duhun dajin bai bari taga jinin da idonta ba ,amma hakan bai hanata gane cewar jini ne sossai a ƙafarta ba, ciwo taji batare da ta sani ba ......

Da ƙarfi ta yago net din kasan adon rigarta ta kulle kafar da shi tana runtse idonta tsabar zafin da takeji .......

Nan cikinta yafara ƙugi Alamar yunwa , maƙogaranta kuwa ya daɗe da bushewa Sabida tsananin ƙishin ruwan da takeji ,nan take yawun bakinta da take ɗan tarawa ta haɗiya ya kafe kaf , jingina kanta tayi jikin bishiyar tana juyi tana roƙon Allah cikin ran ta kan cewa ya ɗauki rayuwarta ko zata samu sassaucin wannan azabar da take ciki .......

Runtse idonta tayi tayi shiru kamar me nazarin wani abu , tunani tafarayi cikin ranta take faɗan," ina ma ace mafarki ne , ina ma ace wannan mafarki ne ,da ko tabbas in ta tashi bazata koma ba , cike da wannan tunani cikin ranta tafara jin Alamar kamar ana ɗan taɓata ta gefen ƙugunta a hankali , a firgice ta buɗe ido ta fara waige_waige ,jikinta yafara kyarma yana rawa , ganin bataga Alamar kowa ba yasa tafara tunanin ko tsarguwar da tayi ne yasa take ji kamar ana taɓa ta .......

Cikin tsoro dai ta kuma runtse idonta tana matse cikinta tsabar tsananin yunwa da ƙishiruwa......

Cike da mamaki tafara ganin haske kaɗan yafara baiiyyana cikin idonta ,saurin buɗe ido tayi dan ganin da gaske ne ko kuwa gizo ne Kawai .....

Ganin hasken na cigaba da yawa ne yasa ya tabbatar mata da cewar gaske ne ba gizo bane , nan fa jikinta yafara rawa haɗe da kakkarwa tamkar me ciwon farfaɗiya,

Nan take taji ansharara mata marin da sai da ta buɗe jajayen idanuwanta haɗe da sakin fitsarin azaba cikin wandonta , hannunta rike da gefen da aka mata marin , waige_ waige tafarayi bakinta na rawa , ga azabar marin da tasha da ya gigita mata tunani........

Wata irin tsawa ce ta fara baiyyana cikin dajin , duwatsu sukafara zubowa , bishiyoyi suka fara bada wata irin iska mai ƙarfin gaske , guguwa mai karfi ta fara tasowa, tsuntsaye suka fara kuka , bishiyoyi na ƙara jijjiga ,ga wata irin dariya da ta mamaye dukkanin ilahirin dajin, dajin yafara amsawa, nan dai dariya ta ƙara yawa ba ƙaƙƙautawa ......

Duk da rawa da hannuwanta sukayi bai hana ta kai su dai_dai kunnuwanta ba ta toshe su da hannayenta , gudun kar dodon kunne ta su toshe, ganin hannuwanta basu rage mata komai ba yasa tayi saurin kunce tuntun ɗaurin dake kanta ta kai dai_ dai kunnuwanta ta rufe su, duk da hakan bai sa ta daina jin karar dariyan ba ........

A ƙalla anshafe minti goma sha biyar ana dariyar , Kafin daga bisani komai ya tsaya ɗif tamkar anyi ruwa an ɗauke , Itadai tana manne a tsaye a jikin wannan bishiya, tana jiran yanda hali zaiyyi da ita.....

Take wasu *kwarangwal* masu launi daban_daban suka fara baiyyana wasu launin fari , wasu launin toka, wasu jajayen ,wasunsu kuma baƙaƙƙene , wasu koraye, nan take suka baiyyana cikin dajin , Aƙalla sun kai guda ɗari biyu ko fiye da haka , ganinsu suna dunfarota yasa ta tsalla ihu , tafara shirin gudu da niyyar barin gurin , amma ciwon da kafarta take mata yasa ta kasa koda dagawa ma bare ta samu damar guduwa, nan dai taɗan fara jaa da baya.....

Kamar anyi ma kwarangwal ɗin umarni da su tsaya , nan suka tsaya cak batare da sun ƙara ko
motsawa da ko da taku ɗaya ba ......

Wani ihu ne da kuruwa yaƙara gauraya a cikin dajin , nan take wani katon *ƙwarangwal* ɗin ya baiyyana , kanshi nada matuƙar girma sossai fiye da girman jikinshi gaba daya, sai ƴan siraran ƙafafuwan shi na kwarangwal da kuma hannu shi na kwarangwal , saɓanin kanshi da fukarshi da yake yanayi da na mutane , sai dai ba irin halittar mutane bane , fuskar shi baƙa kirince Kamar gawayi , sai kan shi dake cike da wani kazamin gashi da ya cika kan ko ta ina , idan shi jajuwar ne kamar jan gauta sai hancin shi ɗan karami kamar an manna shi a gun , sai dai ƙofofin hancin suna da matuƙar girma , bakin shi kuwa tsayawa fadar irin girmanshi ɓata lokaci ne, domin girman bakin yakusa haɗewa da kunnawanshi , fatar bakinshi jajawur ce ga wani irin ƙaton ƙulu a gefen kumatun shi ,sanye yake cikin wata baƙar doguwar rigar mai hula a jiki, tsayawa faɗin munin halittar kwarangwal ɗin bata lokaci........

Cikin wata ita murya mai rikita tunani da firgita zuciyar mai sauraro , magana yake bakinshi na fitar da wani irin hayaƙi baƙin ƙirin........

Nan take jikinta yafara rawa ganin irin munin halittar dake gabanta tana kallo , musamman ganin gadan_ gadan yana nufota kai tsaye , nan take numfashinta yafara barazanar ɗauke wa , idanuwanta suka fara kakkafewa ,tsabar zalla tsoro da firgici da take ciki ......

Sauran ƙwarangwal ɗin suka biyo bayanshi , sai da ya matso daff gurinta ,nan yayi musu nuni da jajayen idanuwanshi , Wanda su kaɗai suka san abun da hakan ke nufi.......

Cikin sauri suka duƙa dukkan su suka haɗa mishi kujerar da zai zauna da jukkunansu .......
Zama yayi a kansu , gamida ɗaukan kafarshi ta ƙwarangwal ɗin ya ɗaurata ɗaya kan ɗaya kafin daga bisani yasa hannunshi a gefen kujerar , gamida karkacewa gefe, irin zaman sarakai.....

Cikin muryarshi maras daɗin sauraro, bakinshi ya fara fidda wani irin hayaƙi maras daɗin kallo, yafara faɗin", Sarauniya!!! Firgita tayi ta buɗe idanuwanta, ta kara mannuwa a jikin bishiyar, cikin ranta take tunani idan bata manta ba irin sunan da ake kiranta kenan a Cikin mafarkinta , a tsorace ta haɗiye wani irin yawu mai matuƙar ɗaci , kaɗan_kaɗan numfashinta yake fita tsabar firgice haɗe tsantsan tsoro.......

Wata irin dariya ya ƙara fashewa da shi kafin daga bisani yayi Shuru cikin Muryar shi maras daɗin sauraro ya fara faɗin,"sarauniyata!! A tunaninki zaki auri wani a duniya bani ba, a tunaninki zan bari ki iya auren bil'adama ne , ki sani hakkan bazai yuyuba keɗin ta wace nii kaɗai nine zan aure ki bakowa ba, ai nasha faɗa miki, amma baki yarda bazaki taɓa aure ba , nine me tsananin ƙaunarki ni zaki aura , ni zan zama mijinki ki haifa mun yara kyawawa ƙamari ki , nafaɗa miki karkii kuskura kice zakiyi aure amma kinƙi, to yanzu kin kaini bango yanzu ki kalleni na fito miki ta sigar da zaki fahimta , tunda tun a can baya na faɗa miki amma baki yarda ba , kinga yanzu munanan tare dake , zamiyi aure a cikin duniyar mu mai matukar daɗi ,ya ƙarasa maganar gamida bushewa da matsananciyar dariya .......
Zuwa yanzu ita kam ta yanke kauna da rayuwata , domin tasan baza ta taɓa rayuwa mai daɗi ba, wannan wacce iriyar ƙaddara ce , wai ace ita ce zata auri irin wannan halitta, cikin ranta take faɗin," Allah yayi gaggawar ɗaukan rayuwarta , can wata zuciyar tace mata," kina hauka ne in kika mutu anan cikin *DAJIN ƘWARANGWAL* ɗinan kika san me za su yi da gawarki can gara kiyi fata ki koma gida , ina yaso ki mutu a cikin gata , ayi miki sutura cikin mutunci.... tsawar da ya daka mata ne yasa ta farga daga dogon tunaninta.....

Cikin tsawa ya fara faɗin," saurauniya!!, me kike da bukata yanzu!!!!, na dai faɗa miki bazaki taɓa auren bil'adama ba , dani zaki rayu , dalilin da yasa na dan baki wahala shine bijrema Umarnina da kika yi ,sabida haka yanzu ki faɗamun me kikeso!! dan kinsan ina sonki ina ƙaunarki ki fadi duk bukatar ki Yanzu Yanzu ........ Cikin kyarma Muryar ta na rawa tace," gida , gida nakeso zuwa ! ,Wata shu'umar dariya ya ƙara bushewa dashi kana daga bisani yace bazaki tafi gida ba , muna nan tare har sai an ɗaura mana aure, anan zaki cigaba da rayuwa , yaƙarasa maganar yana bushewa da wata matsananciyar dariyar da yasata sakin fitsari a wando tsabar tsantsar razana,da tashin hankali kan maganar da ya faɗi , kasa cewa komai tayi , Sabida zuwa yanzu baza ta taɓa iya cewa komai ba, domin bakinta ma bazai iya motsawa ba ......


Sossai Ammi take matsanancin kuka , duk da mutanen da suke gefen ta kilowa na ƙokarin bata haƙuri haɗe da kalaman kwantar da hankali, cikin Muryar kuka da tsantsar damuwa Ammi tafara faɗin," ni babbar damuwar ma bansan halin da yarinyar take ciki , A'a tana raye ne ko tana mace duk ban sani ba, wallahi tallahi gara ace gawarta aka kawomin , nasan mutuwa ta Allah ce amma ace ranar bikin yarinya a nemeta a rasa , wannan wacce irin ƙaddara ce , ta ƙarasa Maganar cikin matsanancin kuka , kafin taci gaba da faɗin," duk muna ta murna Allah ya kawo mana lokacin ta, tunda ansha ƙoƙarin yin auren amma baya yuyuwa, ashe murna zata koma ciki , ohh ni indo na shiga uku , Allah ka baiyyana mun yarinyar nan , ta cigaba da kuka da shasheƙa hade da face majina da bakin sabon zaninta da ta ɗinka na biki .......
Nan duk gurin suka fara bata baki suna bata haƙuri haɗe da kalamana kwantar da hankali , suna faɗin," inshallahu za"a ganta in Allah ya yarda , Allah zai baiyyana ta , amma gaskiya ɓatan ta kam akwai ban mamaki a ciki , da ɗaure kai, mudai fatan mu Allah ya baiyyana wannan yarinyar , amma kam abun ba daɗi, nan suka dinga shawarwarin yanda zasu ɓullo wa Al_amarin .......


Abba ne zaune a kan taburma a waje , ya miƙe kafarshi haɗe da tafka uban tagumi yayi Shuru, da alama ya zurfafa cikin tunani......

Taɓo shi na kusa dashi yayi yace," Mallam Bello tunani ba abun da zai haifar maka , Addu,a za'a cigaba dayi tunda anyi neman anyi neman Allah bai sa ansamu yarinyar nan ba, muyi hakuri kawai mu miƙa al_amuranmu zuwa ga ubangiji inshallahu Allah zai baiyyana ta, kuma za'a ci-gaba da nemanta inshallahu har Allah ya baiyyana ta .......

Shiru Mallam Bello yayi kana daga bisani yaja dogon numfashi haɗe da furzar da wata iska yace...


Read / Download DAJIN KWARANGWAL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album