Join Our WhatsApp Group

MABUDIN WAHALA Complete Hausa Novel Document by MABUDIN WAHALA


MABUDIN WAHALA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 93954



MABUDIN WAHALA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Unknown ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 494.07 kb

File Type: txt

Views: 1122+

Download: 466+

Last download: 1 day ago

Description/Story: Novels BOOK
MABUDIN WAHALA 1**1
Wata rana yarinyar ajinsu nafsa taxo da wayar
hadset nan sauran yaran aji suka xagayeta
suna kallo babu kamar nafsa da tayi ma2kar
rudewa 2n daga lakain tasha alwashin
mahmuda yana xuwa xata ce masa GSM
takeso ya sai mata,bayan wata3 sai ka gashi
yaxo sunyi murna da ganin juna inda yaxo
mata da tsarabar 2raruka a ranar ne kuma ta
gabatar mishi da ba2n GSM yayi shiru yana
naxarin shirme irin na nafsa wai shin tasan ma
kudin GSM kuwa bare layin?to ko shi bai kai ga
mallaka ba 2kunna. Yayi yar gyaran murya
sannan yace me xakiyi da GSM?tace ni dai ina
so zan dinga bugawa mutane,yace wa gareku
mai waya?tayi shiru yace to ki bar ba2n GSSm
xan sai miki amma sai nan gaba in nima na
siya sai mu dinga yin wayar,tayi shiru yace
kinjini? Tace um naji amma fa yarinyar ajinku
tata mai kyau irinta nake so. Yace ita yarinyar
wa ya bata?tace saurayin ta mana yace kema
xan sai miki amma ba yanxu ba, ba haka taso
ba. Kwananshi hudu ya koma cikin haka su
nafsa sukayi canjin aji,wata rana suna bayan
gdansu ita dasu sunusi tana sanye da kayan
islamiya taki tafiya tunda mahaifinta ya koro ta
tace ita dai tana son waya don Allah cikinsu
wa xai sai mata? Fahat ya kira sunusi gefe
yace yarinyar nan fa yan iska ta maida
mu,kome sai tace muyi mata mun biye muna
mata kuma kai kasan kudin banxa muke
kashewa gara mu yagi rabon mu mu kyaleta,
sanusi yace to wace dabara xamuy mata?
Yace xan dauko wayar yayana a boye sai mu
nuna mata muce xamu bata amma sai in ta
yarda ta bamu kanta yanda take da shegen
son abin duniya yarda xatayi in mun cimma
burin mu saai mu gudu da wayar, sunusi yace
haka ne zamuyi maganin kwadayi sai mu kaita
dakina 2nda kaga gidanmu na cikin lungu
ne,nan suka tafa sannan suka dawo gurinta.
Itama tana dariya tace gulmar wa kukeyi?
Fahat yace ba gulma bane muna lissafin yanda
xamu hada kudi ne mu sai miki waya tace kai
aiko da har na mu2 baxan manta daku ba,
sanusi yace matsalarmu 1 yanxun kin samu
wani gaye kin share mu kuma shi ba saya miki
wayar xaya iya ba. Tace in kuna so ku sai min
kawai ku sai min ba ruwanku da wancan
kowanne da gurbin shi. Sukace hakane, fahat
yace tofa kin san rayuwar nan yanxu cudanni
ne in cudeki,sanusi yace sanar da ita kawai ba
wani xagaye xagaye,in xaki bamu kanki sai
muje dakina minti kadan ki amshi waya,tayi
shiru tana 2nani wannan shine ga koshi ga
kwanan yunwa. Kada ki damu mun baki xuwa
gobe da dare kiyi naxari inji fahat. Tace to
xatayi 2nani. Kaji wauta fa!
Sai da ta daidaici an tashi daga makaranta ta
nufi gida. Ikilima ta sanar da haule cewa ya
nafsa fa bata je makaranta ba maimakon haule
tayiwa nafisa fada sai ta balbale iklima da fada
wai bata son xaman lafya kuma bata san me
nafsa ta tsare mata ba take nuna mata tsana.
Iklima tace Allah ba tsana bace haule yaya
nafsa bata san xuwa makarantar islamya kuma
ko taje in anyi mana kara2 batayi sai suru2
daga ance ta karanta xatace ita bata iya
ba...nafsa ta jibga mata dundu na kasa din
kema dan ubanki kina wani yi ne? A daran
ranar suna xaune suna cin abinci suna hira
ikilima dai tana jinsu nafsa tace yauwa haule
saurayina yace xai bani wayar nan da ta shigo
ta yayi shine nake tsoro kada baba ya gani yayi
min fada. Haule ta kalli gurinda iklima take tace
sai dai in ikli ce xata fada kin san ta da
shegiyar gulma. Iklima tace ina ruwa na ni?
dama ni ina fada ne don ayi mata fada ba wai
don bakin ciki ba,in ba sakarai ba wanene xai
ki nashi da karuwa? Haule tace ke dai kika sani
ta dubi nafsa ki amso kinji babanku nuna masa
xa ayi? Shi da komai baya son cigaba ikli ta
dube su kamar tayi magana sai ta kauda kai ta
fasa. Maganar haule ta sake bawa nafsa
kwarin gwiwar baiwa su fahat kanta don su
bata waya duk da cewa bata xayyane ma
haulan bukatar samarin nata ba,yanxu dauwar
ta daya mahmu wanda ko yaushe in yaxo
girinta nasihar shi da ita ta kula mishi da kanta
sannan baya sonta roki kowa kome sai shi don
yace mata kwaday da roko suna karya
mu2mcin ya mace tare da jefa ta cikin kowane
irin hali don shi kanshi yanda nafsa ke rokonsa
baya ga tsananin sonta da yakeyi da 2ni ya
kama gabanshi. Ta yanke shawarar 2n2bar
kawarta safina,safina tace banxa ki yarda inda
nice ma wallah da 2ni na karbi wayar,nafsa
tace ina jin tsoron kada mahmud ya sani ne
safina taja tsaki kinjiki da wata banxar magana
to kece xaki gaya mishi? Nfsa tace ke naji fa
ance suna ganewa in basu sameki budurwa ba
safina tace to in ya gane sa me?nasan ma
2nda yana mutuwar sonki baxayi magana ba.
Nafsa ta dauki shawrar shirme gurin kawarta
don haka lokacin islamiya sai ta jira su bayan
gidansu kamar yadda suka shirya suka nuna
mata waya amma baxa su bata ba sai komai
ya kammala. Nan kuwa ta bisu dajin su sunusi
(A'uzubillah musa idanu kan yayan mu).
Bayan anyi abinda xa ayi taci wuya gurinsu
daga karshe suka gudu basu bata wayar ba
gashi kuma babu damar ta kai kara gurin kowa
ta tona asirin kanta,faruwar wannan lamari sai
yasa nafisa jin kai tare da ganin cewa ta girma.
Daga nan kuma ta xama karyar duk wanda
xaya taya ta in dai xai bata kudi xata bishi.
Nan fakudi suka dinga ci ita da haule,ta dinga
tsara sababbin dinkuna takalma da kayan
shafa,waya kuwa wani Alhaji da ta bishi ne ya
sai mata sabuwa dal ga mayukan kara fari
gami da dade fatar jiki.
Duk wannan lamarin mahaifinta bai sani ba
2nda baya yini gidan,sannan in ya lura da
bakon abu a gurinta yayi magana sai tace
mahmuda ya sai mata. Iklima kuwa duk tasan
abinda nafsa keyi kai ko haule ta sani kudin da
take kawo mata ne baxa su bari ta kwabe ta
ba. Cikin haka ne mahmud yaxo minna shi
kanshi yayi matukar mamakin yanda lokaci
kadan nafisa tayi ,ugun wayewa bai soma
tsorata da lamarinta ba sai ranar da taxo
dakinshi da rana yana bacci sai kawai yaji
hannunta a fuskarshi. Ai da ya tashi ya rufe ta
da fada tamkar xai dake ta yace kina hauka ne
nafisa kike taba ni? Taco to menene a cili
masoyina kaifa xan aura. Ya dauki rigarshi
yana sawa don ganin yanda ta tsura wa
kirjinshi idanu sannan yace amma ai ba a
daura ba tace sai ka dinga yi tamkar baka
waye ba yace wai ku me kuka dauki wayewa
ne?wlh kun jahilci wayewa naki ganin rashin
kunya da fitsara ita ce wayewa?to in haka kika
dauka bakima waye ba kuma fita daga dakina.
Nan ta xube tana rokon mahmud har da
hawaye yace wa yasan me kikayi da bana
nan?nan ta shiga rantsuwar bata kome.
*****Nafsa tana masifar son mahmud don haka
2nda ya dao ta kashe wayarta ta boye ta
kuma aje harkokinta. Yana tafiya ta koma ruwa
tuni ta daina xua islamiya baban ya daka ya
gaji bokon ma tana xua ne kawai saboda
mahmud ne ya sakata tasan in bata xua xasu
haura sama dashi ita kua da ta rasa shi gara
ta rasa ranta haka take ji a cikin xuciyarta.
Kwanci tashi mahmud sun gama service ya
dira minna. Nafsa kusan ta fisi murna ana
xaton shi kenan yanxun sai dai ya soma aiki
suyi auransu su fantama amma sai taji shuru.
Shi kuwa mahmud ya nemi aiki har ya gaji
kowa yasan irin yanda kasar namu take aiki
saida hanya,shima mahaifin shi yabi ta
sanayya amma duk ba a dace ba dan haka sai
yaba mahmud shawarar tunda gashi da shagi
a waje xaya xuba masa kayan masarufi yana
saidawa sannan xa ayi bikin shi 2nda yana da
gidaje sai ya xabi daya a gyara su xauna da
matar. Mahmud yaji dadi sosai ya nuna
murnarshi ya samu nafsa yace xa a xo
maganar auren su cikin sauri tace ka samu aiki
din ne?yace a'a shago xa a bude min kofar
gidan mu. Tayi dim!cikin xuciyarta tana
maimaita shago kuma?ita kam ba xata auri
mai shago ba. To ki auri wa?xuciyarta 2t
tambayeta. Tasan tabbas bata iya auran kowa
sai mahmud dinta to amma shago?masu kudi
da yayan masu kudi sun sha nuna suna sonta
amma saboda sonshoi duk ta share. Yace kinyi
shiru?ta dan taba baki gaskiya ni ka bari ka
samu aiki sannan nima na gama kara2na. Ya
tsura mata idanu nafsa na tabbata xan iya rike
ki koda ban samu aiki ba kara2nki kuwa xaki
cigaba. Tace to kabari 2kunna sai nan gaba
kadan. Yace to amma banga kina murna ba?
tace uhum kaima kasan ko ban nuna ba ina
cike da farin ciki. Bayan ya tafi ta shiga gida
babansu yana nan bare ta gaya ma haule don
haka sai ta nufi dakin su.
Tuni iklima tayi barci itama ta xube kan
tabarmarta ta shiga 2nani anya xata iya auren
mahmud baya aiki?itadakeson ta auri miji mai
katon gida da ka2war mota?shago fa,kanti
mijinta xai dinga xama,kai mahmud ma ya bata
kunya duk ajinshi da ji ji da kanshi ya tsaya a
kanti?wata xuciyar ta sake xugata da cewa duk
kyanki duk yangarki ki xama matar me saida
suga da kulla madra lallai kawayenki irin su
safina xasuy miki dariya,dubi Alhaji sani mai
son auren safina har ya 2ro kudin gaisuwa
gdansu dubu hamsin,sadaki sai nawa?jibi barin
kudin da yake musu ita da iyayenta amma ita
don kawai soyayya sai ta wulakanta?kai da
sake!gashi duk cikin friends dinsu tafi kyau
amma bari gari ya waye ta sanar da haule. Gari
yayi haske tana xaune ta xuba tagumi ko
sallah batayi ba dama ita in ba matsa mata
akayi ba da ba2n sallah bata cika maida
hankali ba,iklima tana gefe tana azkar din safe
nafsa ta daga murya tace haulr,mahaifiyarsu
dake gndn murhu tana hura wuta ta nufo dakin
tace kiran me kike min? Ta shigo dakin ko lin
samo wani abinne?ai ni 2nda wannan shegen
saurayin naki ya dawo kika jefa mu cikin talauci
kinki sauraron masu baki abin arxiki sai shi
kyautar shi bata wuce dubu 2 itama sai ayi
sati2 ba a baki ba. Nafsa tace mahmud ne
xaya 2ro jiya yake ce min yan gdansu xasu zo.
Haule ta tabe baki xasuxo ba2n auranku?
Nafsa tace eh amma damuwata bai fa samu
aiki ba,shagon kayan masarufi babansu xaya
bude masa. Haule tace tabdi jam!lallai kin
kama tashar daji ance miki kayan masarufi
suna daurewa ne?da kun cinye sai ku tsugunna
shikenan a shiga wahala da ko yaushe ina rayo
ki cikin tsalelen gda
In xakixo gidannan kixo mana cikin dirkekiyar
mota cike da kayan masarufi ki biya mana
makka yan gulmar cikin layin nan masu miki
sharrin kina yawon banxa suji kunya. Nfsa tace
nima nafi son mjin da xan huta amma ina
matukar son mahmud ne,haule tace son banxa
ai wannan xamanin so shine kudi yarinya baki
da wayo nafisa tace to kuma ni baxan iya
korarshi ba ne, haule ta gyara xama kin san
hausawa suna cewa kora da hali yafi kora da
dukan sanda canxa mishi xakiyi kwata kwata
har ya gaji ya tafi ina mai tabbatar miki da kin
dasa wa xuciyar ki tsanarshi xakiji ya fice miki
a xuciya. Nafisa tace to xankoyi haka in sha
Allah,haule ta fita tana murna gami da yiwa
nafsa kirarin da takan yi mata yarinya guda
tamkar da dubu yarinya mai tsada.
Shikuwa mahmud 2ni an bude shago an xuba
kaya sannan mahaifinsa ya saya masa mashin
don xuwa babbar kasuwar minna don saro
kaya 2ni kuma ya soma cinikin shi. Lura da
yayi nafsa bata son ba2n shago shiyasa ko
yaxo baya mata,cikin haka ne wata asabar da
hantsi kawayen nafsa safina da mama zee
suka xo wucewa sai suka ganshi a bakin
shago motar fiyo wata tana sauke mishi safina
ta taba mama zee dubi saurayin Nafsa
baby,mama zee ta kalle shi kina nufin wannan
ne mahmud din? Safina tace shine mama zee
tace kai amma nafsy beby taji haushi shagon
sa ne? Safina tace kila shagonsa ne baxata
fada ba kada muy mata dariya amma xo mu
karasa mu gaisa suka karasa aka gaisa sukace
gidan mutiniyar taka xamuje ta cigaba da cewa
ka bude shago ne? Wallahi a nan muke dan
samun na rufin asri inji shi,suka dubi juna da
mama zee suka ce Allah ya taimaka. Ya bude
fridge ya kwaso maltina 2 da dogon biskit yasa
cikin leda gashi ku dan sha safina tace daga
gaisuwa sai mu karya jari yace a'a ba ba2n
karya jari ku dai na gode da gaisuwa
Safina taki karba Mama zee ce tasa hannu ta
karbe tare da cewa Babu karya batun maltina
kai dai mun gode Allah ya kawo kasuwa. Suka
tafi suna tuntsura dariya. Mama zee tace
yanxun duk yanga da jan ajin da Nafsa Beby
take yiwa Alhazawannan saboda wannan ne?
Safina tace kin dai ganshi don kyau yana da
kyau kuma ya hadu amma kyau da haduwa
shine aljihun mu2m. Mama zee tace ashe dai
kin gane,nifa ba ruwana da wai so ko
kyau,kyawun mu2m ni a gurina bai wuce ya
sakar min kudi ba. Da wadannan hirarrakin
suka isa gidansu nafsa sun gaisa da haule
sannan suka shga dakin su nafsa tana kwance
tana shirga bacci,mama zee ta dada mata
duka tare da cewa tashi shegiya kasa uwar
bacci kin kwanta kina ta shegen bacci, ta mike
da sauri ta xuba musu idanu tayi murmushi
tare da cewa wlh kunyi masifar ban tsoro na
dauka baba na ne,nan suka shiga hirar duniya
mama xee tace um bari insha maltina ta, safina
tayi karaf tace ke yar gari munga masoyin ki
shine ya bamu ashe shago gare shi? Nafsa ta
tabe baki tace ashe har an bude shagon?
Mama zee tace mun sheda mun sha maltina.
Safna tace wlh nafsy beby zakiyi nadama a
rayuwa matsawar kikace xaki auri wannan
mahmud din. Mamaxee tace barta ma dinga
xuwa gdanta muna bata kwance,nafsa cikin
masifa tace na wuce nan safeena son mahmud
ne kawai ke dawaiyniya dani na rasa yadda
xanyi kuma nima ina 2nanin auranmu bazaya
yiwu ba matsawar bai samu aiki ba. Mama zee
ta dafata Hajiyan Allah share shi xakiyi ki kama
na gaske, nafisa tace nima shawarar da na
yanke kenan.
Ckn kwanakin mahmud ya soma ganin chanji
gurn nafsa zuwanshi ya kai sau 3 cikin satin
amma sai ace bata nan,ranar na hudunne ta
fito fuska daure yayi yayi yasan me ke damunta
amma tace ba komai shi kuwa tamkar ta kara
mishi sonta ne cikin xuciya. Cikin kwanakin
yayi ta fama ta yarda magabatanshi suxo
gdansu sam taki, karshe ma ta da taga yana
so ya matsa mata sai tace gaskiyar magana
baxanyi aure yanxun ba in xaka jirani in gama
kara2 to,in baxa ka iya ba je ka nemi wata.
Kalmar ta firgita mahmuda ta kuma hana shi
bacci kenan in yana sonta dole ne ya jirata da
yabi duk yanda xaibi bai samu amincewarta
karshe sai ya hakura kan cewa xai jiratan.
Koda yaxo mata da ba2n bata ji dadi ba
hakanan da ta sanar da mahaifiyar ta itama
bata ji dadi ba, karshe tace barshi shine
wahalalle.
Malam Usaman mahaifinta shine da kansa ya
samu mahmud lokacin da yaxo tadi yana
jiranta kusan minti 40 bata fito ba Mahmud ya
tsugunna ya gaida Baban su Nfsa. Malam
usman yace yauwa mahmud daman ina son
ganinka ya kara matsowa kusa da mahmud
nafisa ta shaida maka cewa ina nemanka
kuwa?yayi shiru sai kuma yace eh ta fada min
shi yayi haka ne dan kawai ya rufa mata asiri.
Malam usman yace ta sanar dani yanda kukayi
kace sai ta gama makaranta ko? Gaban
mahmud ya fadi bai dai ce kome ba ya cigaba
da cewa naso ace kunyi auranku 2nda nafsa
ba wani xuwa makarantar take ba sai asarar
kudi da kakeyi. Mahmuda ya kalaci miyau ya
hadiye yace nima naso hakan amma nafisa ce
ta dage kan cewa sai ta gama makaranta.
Malam usman yace oho dama ita ta dage kan
haka?to shikenan in kaje gida ka 2ro min
manyanka cikin jin dadi yace to,baban nafsa ya
shige gda,nan ya samu nafsa sai lokacin xata
fito ta gama mishi wulakancin nan ya hau ta da
fada ita da uwarta yace haule na sani...


Read / Download MABUDIN WAHALA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

3 Comments On MABUDIN WAHALA
avatar
amina-ibrahim-4

6 months ago

Reply

Good

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to amina-ibrahim-4

aha

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album