Join Our WhatsApp Group

YAR AIKIN KARUWAI Complete Hausa Novel Document by YAR AIKIN KARUWAI


YAR AIKIN KARUWAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 82279YAR AIKIN KARUWAI

Reading Time: 6 Hours

Added On: 03, Aug 2023

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08061929616

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 412.48 kb

File Type: txt

Views: 16277+

Download: 11496+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: [7/15, 5:48 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼


LITTAFIN KYAUTA NE


1-5Official

By
AsmaBaffa08061929616 Sabon layina


BISMILLAH

INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON RUBUTA SABON NOVEL DINA NA KYAUTA SABO DA JIN DADIN MASOYA NA,SANNAN FANS DINA INA BAKU HAKURI A BISA LAYINA NA DA YA SAMU MATSALA DOLE SAI SABO NA CANJA,DUK WACCE KE DA TSOHON LAYINA ZATA IYA GOGE SHI TAYI SAVING DA SABON, SANNAN WANDA SUKA SAN INA WANI GROUP NASU PLEASE KU BA ADMIN LAYINA TAYI ADDING DINA DA SABUWAR NUMBER TA

MASU BIBIYAR NOVELS DINA INA MATUKAR GODIYA MATUKA SANNAN IDAN AN FARA KARANTA NOVEL DIN NAN TO SHARHI NAKE BUKATA BA GODIYA BA,ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA DARASIN DAKE CIKIN LITTAFIN AMEEN.


LITTAFAN DANA RUBUTA SUNE

CIRANIN AMANA
MA'AIKACIYAR GOMNATI
KASUWANCINA
GASKIYA CE
KAMARSU CE DAYA
DUK INDA TA FADI
ME MAGANI
TUBABBIYA
HADIN KAI
JIN DADI SABO
MAFARKIN FARIDA
WARE BAIKO
AUREN MU

NA KUDI SUNE

RASHIN SA'A
TA GYARU
ADDUAR KAWA
YAR KWANGILA
GIDAN GWAURO
DANGIN RABI
DUNIYATA AAMNAH
BABU KAUNA
JIKAR MAGUZAWA


SADAUKARWA GA
DUKKAN YARAN TSUNTUWA

PAGE NAKI NE TAWAN
AIDA MAMAN TASNIM
Cikin dare misalin 1:40am na fito fitsari buta na dauka nabi ta jikin dakin Gwaggo wani uban nishi naji Wanda ban taba ji ba ana ihu washsh.....ahhhhhh......uhhhhhh......Ahhhhh zaka kashe ni....zaka kashe ni...Zan mutu....zaka kashe ni ...Ahhhh....wash...uhmmmmmm....zaka kashe ni...zaka kashe ni....zaka kashe ni.....tsoro ne ya kamani na sake kasa kunne tare da manna kaina a jikin kofar naji ihu da zaka kasheni Yana Kara ta'azzara,a fili nace karfa ayi kisan kai Muna nan gaskiya bai kamata ba ya kamata na Kai agaji waye zai kashe Gwaggo haka bazan kyale ba wallahi, kofar dakin na shiga kwankwasawa Shuru ba a bude ba amma Ina Jin Maganar Gwaggo tana zaka kashe ni wayyo....kofar na hau duka da karfin gaske Jin za ayi kisan kai

Cikin bacin rai aka bude na kutsa kaina ciki da sauri,cikin zafin nama na runtse idona ganin Gwaggo zigidir Babu komai a jikinta tana kokarin daura zaninta cikin sauri,Dagaci ma daga shi sai dankwalin Gwaggo Yana Kare gabansa ashe sex suke ana kwasar love ban sani ba,duk da haka ban gane ba nace au kuyi hakuri dama zuwa nayi na taimakeki Gwaggo naji kina ta cewa zai kashe ki zai kashe ki shine nazo kawo Miki dauki ashe kalau kike, kinci uwarki da ubanki shegiya annamimiya munafuka me labe cewar Gwaggo,Dagaci kasa magana yayi ya mako kofarsa ya kulle Saura kadan ya datse da hannuna, ai ji nayi Gwaggo taci gaba da zaka kashe ni tana nishi,tsayawa nayi a jikin kofar na dora Hannu a kai Ina salati nace shike nan Gwaggo zuwa gobe sai gawarta,kasa jurewa nayi na kai Hannu zan sake kwankwasa musu kofa sai kuma na fasa Kawai Ina jimami na tafi na bar wajen.

Washe gari kuwa
Shigowa gida nayi Ina rabe rabe a bango cikin wulakantattun kayana Atamfa ce amma kana taba ta zata yage kadan take jira doguwar riga ce,dankwali me santsi Wanda ake Kira da disco shine daure a kaina na zamge goshina sai kyalli yake,tsoro nake ji sabo da nayi laifi an aikeni ban dawo da wuri ba,Gwaggo da Aunty Amarya na samu a zaune gaban murhun gawayi,Dagaci Yana zaune a saman tabarma jikin dakinsa ba Wanda ya kulani Ina rabe rabe idona ya ciko da kwalla a tsorace na mikawa Gwaggo daddawar dana siyo Ina ja da baya Ina kyarmar jiki,ba Wanda ya kulani cikinsu ni sam gwara ma suyi fadan yafi sauki akan wannan shurun da Suka min,salin alin Gwaggo ta karbi sakon bata ce komai ba dole akwai wata a kasa,na gaza Shuru nace Gwaggo baki ce komai ba ko dan zagina kiyi mana,Aunty Amarya na kalla nace Aunty dan Allah ko ashar uku ce dan Allah,cikinsu ba Wanda ya kulani

Nasan wannan shurun nasu yafi komai bala'i a wajensu na rasa inda Zan saka kaina,gaban Dagaci na karasa tare da tsugunawa idona cike taf da kwalla,nace dan Allah ni kuyi min bala'i,Dagaci sai lokacin yayi magana yace a'a me za ace dake,da sauri na girgiza Masa Kai na furta a'a akwai abin fada dan Allah kuyi min fada,wallahi sai Kun Yi min fada sai kunyi fada aikena fa kuka yi na dade ban dawo ba ko zagina ai ya kamata kuyi shine hankalina zai kwanda,dan Allah Baba kuyi min fada,gaban Aunty Amarya na koma na durkusa na furta dan Allah ki zazzageni ku dakeni dan Allah,Dagaci na sake kallo Muka hada Ido nace ka balla ni dan Allah kayi min dukan kawo wuka, ni nasan da wannan shurun nasu muguntar da zasu min gwara su min dukan tsiya duk ranar da Suka yi wannan shurun to zanji jiki,banza suka min ba Wanda ya kulani,sai da na dame su Dagaci ya fisgo ni na saki ihu ya hau jibgata Kamar wani gardi ya samu sai da ya min lilis sannan Gwaggo ta miko min buhu dauke da masara a ciki tace dauki dan ubanki ki tafi nika ta sake hambareni sai da na Kai kasa sabo da azaba haka na dauki nikan na fice.

Cikin kauyen mu me suna rinjin tsangaya dake cikin karamar hukumar Ungoggo dake Kano state nake tafiyata cikin nutsuwa yau ma da sanyi na dake ni mace ce me sanyin hali babu sawa ba hanawa haka nake,dauke nake da buhu a kaina na dakko Mana garin tuwo daga wajen nika da kyar nake taka kafata sabo da gajiya gida na dawo na shiga gidanmu madaidaici me dauke da dakuna hudu da wani karamin daki da suke tara tarkace Wanda ke a zauren gidan Kuma shine dakin da nake kwana da Yar tabarma ta a gefe
Saukar duka naji a bayana a firgice na juyo Ina Sosa bayana a inda nake bayan na ajiye garin tuwon na zauna a jikin bango na rakube Ina hutawa, tana zazzaro min idanu Kamar zasu ballako su fado kasa tace tashi tsintacciyar mage maza kije ki karasa aikinki kaf bana son 'ya'ya na sun gama karatu sun dawo a samu matsala kaf garin nan babu kamarsu,ko akwai Wanda yayi makarantar gaba da secondary idan ba yarana ba munafuka kina kallona da idonki a soye Kamar an watsa waken suya, a hankali nayi kasa da kaina ina me runtse idona a cikin raina nace ya Allah yaushe zan fita daga wannan kangin Allah ka nuna min Iyayena ko dangina idan ma bazan gansu ba Allah ka hadani da Wanda zai rikeni a matsayin 'ya Kamar kowa,wani saukar azazaben rankwashi naji tace wai dan ubanki bada ke Gwaggo take ba,juyowa nayi naga Aunty Amarya ce a kaina yanzu wanda dazu Gwaggo ce take dukana ganin zasu yi min taron dangi na mike nace yanzu da me zan fara? Da kan uwarki zaki fara cewar Gwaggo dake jawo ruwa a rijiya, Dagacin garin nan ya shugo Wanda muke Kira da Baban Mairo,nidai aikin gyara gidan nakeyi Wanda gidane a kauyen na rufin asiri gidane na bulon siminti ko Ina ya sha siminti cikin dakuna Kuma tiles ne da bandaki idan ka shiga gidan baza kace a Kauye kake ba sabo da daidai misali Yana da kyau,Baban Mairo Yana kokari wajen kula da iyalinsa kaf garin yaransa ne suka fi kowa ilimi dana addini dana zamani banda ni tunda Ni tsintata akayi iyakata primary na iya karatun hausa da rubutawa matansa Aunty Amarya da Gwaggo Suka zugashi ya cireni sai Islamiyya Kawai nake zuwa da Yamma gashi har na Kai 21yrs a zaune ni banyi aure ba ni banje school ba sai aikin gida sabo da a garin ma duk kyan da Allah yayi min ba wanda ya taba zuwa wajena kowa cewa yake yi bazai auri marar asali ba babu Wanda ya sani ko yar shege ce ni sabo da mafi yawa Indai yaran halak ne ba a jefar dasu.

Dagaci dan Asalin garin Argungun ne Wanda tuntuni iyayensa Dake Fulanin tashi ne Suka dawo Kano Ungoggo me yana da kanne biyu Mata Talatu da Hafsa duk a garin suke aure da yaransu maza da Mata,Dagaci Raliya Gwaggo itace ta fari ya Aurota daga garinsu Argugun Haihuwar Farko ta haifo Maryam ana ce Mata Mairo,ta sake haifo Bilkisu ana ce Mata Gaji,sai Namiji Imrana sai Abdullahi ana ce Masa Audu sai lawan da Autansu Sagiru,duk yaran Gwoggo ne.
Duk suna kanana Dagaci ya Karo Auren Kubra ana ce Mata Aunty Amarya a bazawara ya aureta bata haihuwa shi yasa sun dade bata taba haihuwa ba sai dai yaran Gwaggo Kawai ganin Gwaggo yaranta ne Kawai shi yasa basa zaman kishi da Aunty Amarya sun hade kansu duk abinda daya tayi to dai dai ne,basu da Imani Basu da tausayi ko kadan,Dagaci ma haka daga shi sai Yaransa Indai ba yaransa ba to baya son wani da ci gaba ko a kauyen baya son kowa da samu sai iyalinsa.

Gwaggo ce ta bani labarin Lokacin da ta haifi Bilkisu Gaji kenan da watanni bakwai lokacin Kuma aka tsince ni jaririya a nannade cikin sabon zani cikin jini Wanda ko cibi ba'a gama yanke Mini ba a jikin wani masallaci yarinya ce Fara kyakyawar gaske, ana ta cecekucen waye zai dauka a kauyen kowa yaki karba,kowa yace bazai dauka ba Shima Dagaci yaki karba aka rasa me dauka Jamian tsaro Yan Sanda suna ta roko ko za a samu me dauka Kar a bari a kaini gidan raino amma kowa yaki,Gwaggo tana Jin labari tace yo tunda kowa baya so ni a bani idan na raineta ta girma na samu Yar aiki komai na gidan sai ta dinga yi min na huta idan Allah yayi me kashin arziki ce ta zama kadara na dinga Neman kudi da ita,Gwaggo da sauri ta falfalo tace a bata tana so,Hukuma ta bawa Gwaggo Amana akayi rubuce rubuce aka damka Mata jaririya bada son ran Dagaci ba haka na taso cikin tsangwama da bala'i a gidan tun Ina karama Gwaggo kullum ita da yaranta sai hantarata da zagina haka Dagaci da aka auro Aunty Amarya ma haka Suka dora da ganamin azaba iri iri kaf kauyen da yan uwan Dagaci sun tsaneni basa kaunar ganina haka Dangin Gwaggo dana Amarya bani da inda zanje naji sanyi wahala idan da sabo na saba har Muka girma tare da yaransu suma basa so na har dama dama Mairo ma gashi Allah ya bani kyau da cikar zati,kaf garin bani da masoyi Namiji cewar ni Yar shege ce bani da iyaye ba Wanda yake zuwa wajena zance har gashi Ina 21yrs a kauyen Gaji tana 21yrs Mairo tana 23yrs,Mairo da Gaji suna gama Secondary ya samo musu admission a poly Kaduna sukayi HND yanzu sun gama zasu dawo gida daga Hostel shine ake ta shirye shiryen tarbarsu Kamar zasu dawo daga kasar waje.

Washe gari da safe Dagaci ne ya kwala min Kira bayan na gama aikina da sauri na saka slifas dina dan Madina naje nace baban Mairo gani na durkusa har kasa kudi ya miko min yace maza jeki cikin garin kano ki siyo min Lemon kwali da ruwan roba ki hau machine saura ki zauna baki dawo da wuri ba ki tsaya karuwancin naki karba nayi bance komai ba na shiga daki na dakko Hijab dina blue na dora a saman doguwar rigata ta kodaddiyar Atamfa ta maroon,Gwaggo na samu tana juya Miya nace Gwaggo na tafi cikin gari,Tsaki taja tace to ko ki dawo lafiya ko Kar ki dawo lafiya Rabi Ina ruwana Rabi kike ko Rabi Kudirar Allah ko? Aunty Amarya dake linke Kaya tace Wai Rabi Miracle haka ake ce Mata a makaranta bakar kinibabba munafuka Yar shege anyi cikin Shege an jefar a bola,inda sabo na saba haka na fice Babu me Napep ko Daya a kauyen dole machine na hau na Shiga cikin garin kano bakin wani katon shago nace ya tsaya a nan,Me machine din ya sanni na sanshi garinmu daya nace dan jirani Musa naje na dawo,yace to ni Kuma na shiga ciki na Fadi abinda nake so aka ebo min na siyo zan fito kenan Naga wata katuwar mota me kyau tayi parking wani mutum kyakyawa baki ya fito daga motar shi baza a kirashi da matashi ba sannan baza a kirashi da babban mutum ba,tunda ya fito yake kallona kamar maye,da sauri na tafi na dane saman machine din da muka zo tare,da Sauri mutumin yace dan Allah malam me machine tsaya,nace Kai Musa muje,Mutumin yace karka tafi zan baka kudi,Musa ya tsaya cak da machine na bata rai cike da masifa nace Musa muje nace fa,Musa yace Allah ya gani bazan tafi ba kina ji dai yace zai bani kudi haka Kawai ki cuceni ke nawa zaki bani? to ba inda zani,kinga dan Allah ki saurare shi yayi sauri ya barmu mu tafi,baki na turo gaba tare da kallon mutumin nace Ina jinka,Murmushi ya saki yace Kawai kwatancen gidanku zaki bani idan nazo sai na fada Miki dalilina na tsaida ku,Shuru na Masa har ya gaji da tsaiwa yace Ina jinki princess,Harara na watsa masa,Musa zancen ya karbe ya Fara Masa kwatancen gidanmu yace idan kazo kauyen namu kace gidan su Rabi Yar tsuntuwa ko gidan Dagaci,Murmushi mutumin yayi yace nice name sunana Alhaji Mas'ud amma kowa da Alhaji Kutama ya sanni, baki na tabe Ina kallo ya bawa Musa dubu biyu,Musa sai Murna Yana godiya yace zaku iya tafiya,sai lokacin Musa yaja machine muka tafi Yana murna,nace Wlh Musa kayi asara tirrr da Kai,dariya ya sake yi tare da furta ba komai naji.

Ina sauka a kofar gidanmu na biya Musa kudinsa na shige gida da sauri,Ina shiga Dagaci ya hauni da masifa da bala'i,Gwaggo tazo ta fisge ledar lemukan tare da dungure min kai tana furta gantalalliya anyi gadon karuwanci,Aunty Amarya tace yo matar da aka tsinta yashe a titi cikin jini ai kinsan bata da uba Yar shege ce ai,bance komai ba sai ga Mairo da Gaji sun fito daga daki ashe fitata suka shugo gida,Gaji ta kalleni tace jaraba ja'iba haihuwar kwararo na tsaneki wlh Gwaggo ban San ya akayi Yar shege take da kyau haka ba,kalli duwawunta Lodi guda Nawa Kuwa sai kace Kullin Sugar gata Fara Ni Kuwa wankan tarwada Mairo ma haka,duk inda tazo ta tsaya Muka tsaya dole ita za a dinga kallo,kalli duwaiwaka sun Bude,Aunty Amarya tace ai sabo da maza ne yasa Kwankwaso ya bude inda Zaki San Yarinyar nan tasan...


Read / Download YAR AIKIN KARUWAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

10 months ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

10 months ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

8 months ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

7 months ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

7 months ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album