Join Our WhatsApp Group

RIJIYA GABA DUBU Book 4 Complete Hausa Novel Document by RIJIYA GABA DUBU Book 4


RIJIYA GABA DUBU Book 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11640



RIJIYA GABA DUBU Book 4

Reading Time: 0 Hours

Added On: 21, Nov 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 61.04 kb

File Type: txt

Views: 1155+

Download: 369+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Hudu (4)
Part A
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Kyan Alkawari cikawa Saboda haka zamu cigabaa kamar yadda mukace

Marubucin yaci gaba da cewa....

Su kuwa waɗanda suka zabi jarumi zambaru a matsayin jaruminsu na caca sai suka fara tsalle gami da murna, domin sun san cewa kakarsu ta yanke saka dan sun gama zamowa manyan attajirai. Yayinda wadanda suka zabi jarumi Imhal kuwa a matsayin jarumin gasarsu sai suka fara kuka sannan suka kamu da tsananin bakin ciki saboda sun san cewa karayar arziki ta zo masu.

Lokacin da Zambaru ya tunkaro Imhal rike da wannan lafceciyar takobin tasa, kuma ga Imhal in kwance a kasa ya kasa miƙewa saboda karyewar da kafarsa ta yi, sai hankalin Gimbiya Shumaira ya dugunzuma ta ji kamar ta dafe kanta ta kwala uban ihu, kafin ta ankara tuni hawaye sun fara sartu a bisa kumatunta, tana daga idanu da sarki Taryan sau taga yana yi mata murmushi sannan yayi mata rada da cewa ki kwantar da hankalinki yake yata ai kada mage ba yankawa bane, wannan yaro Imhal dan baiwa ne baza a ci shi da yaƙi faraddaya ba sai rai ya baci.
A bangaren Sarki Gurzalu da Gimbiya Lumairat kuwa sun tabbatar da cewa karshen Imhal yazo domin dai gani kuru-kuru a zahiri an fi karfinsa, sannan fadan ya nuna cewa bashi da sauran kataɓus, haka ma sauran yan kallo da dukkanin attajirai da suka sanya kudin cacarsu akanshi jikinsu yayi sanyi, Wannan karon kuɗin da suka sanya a kanshi ya ninka na farko, saboda ganin yadda ya lashe gasarsa akan sadauki Darwaz jarumin da babu kamarsa a duk faɗin birnin Misra. Zambaru na karasowa daf da Imhal ai kawai ya kawo masa wawan sara a wuya da nufin ya tsinke masa kai, cikin bakin zafin nama Imhal ya kauce wa saran, saboda karfin saran da kuma nauyinta sai da takobin tasa ta nutse a cikin kasa kamar haka akayi aka sakata, kafin Zambaru ya zaro takobin tasa tuni Imhal yasa kafarsa mai lafiyar ya doki tsakiyar fuskarsa, saboda tsananin karfin dukan sai da Zambaru yayi taga-taga kamar zai fadi amman ya turje, duk kuwa da tsananin girmansa gami da karfinsa, take hancinsa gami da bakinsa suka fashe suka kama yoyon jini.
Al'amarin da ya baiwa yan kallo mamaki kenan, sai kawai akaga Imhal ya yunkura ya mike tsaye yana dingishi sakamakon karayar dake a kafarsa, daga cikin an kallo ne aka cillo wa jarumi Imhal wani dogon icce, cikin sauri Imhal ya cafe shi ba tare da ya ga wanda ya jefo masa ba. Nan take ya karya icce gida hudu ya daure karyayyar kafar ta shi. A daidai wannan lokaci ne kuma Zambaru ya miƙe daga durkuson da yayi yana mai shafa fuskarsa, koda yaga ya shafo jini a hannunsa sai ya fusata ainun ya takarkare ya kwarara uban ihu irin wanda yayi a karon farko, su kuwa jama'ar dake cikin wannan fili sai suka kaure da shewa gami da yiwa jarumi Imhal tafi bisa ganin irin jarumtakar da ya yi da kuma juriya, ya kasance ga shi dai ya karye amman ya ɗora kansa kuma ya ci gaba da gumurzu. Duk da cewar shi kansa Jarumi Imhal ya karaya amman sai da yaji dadi kwarin gwiwa da jama'a suke bashi, da kuma yadda yan kallo keta masa jinjina.
Bayan Zambaru ya gama miƙewa tsaye gami da yin wannan kururuwar mai firgita kowa sai kawai ya daga takobins sama ya riketa da hannu biyu ya tsaya cak! A inda yake ya kura wa Imhal idanu.
Koda ganin haka sai shima Imhal ya daga tasa takobin sama ya riketa da hannu biyu kamar yadda Zambaru ya yi suka ci gaba da kallon kallo, a wannan lokaci makada suka fara kada gangunansu filin ya sake hargitsewa da hayaninyar kida gami da surutan jama'a, tsawon kusan dakika dari uku da ashirin maroka da makada sunata zuga wadannan Jaruman gasar, daga can sai Zambaru ya rugo da mugun gudu, cikin tsananin mugun nufi izuwa kan Imhal, yana gudu kasa na rawa, nan take filin wajen ya hau girgiza shi kuwa jarumi Imhal ko motsawa bai yi ba daga inda yake ba, kawai sai ya cigaba da kurawa Zambaru idanu yana jiran isowarsa tunda shi bashi da ikon yin gudun amman ya tsaida hankalinsa sosai akan Zambaru yana jiran yaga ta inda zai kawo masa hari, kowa a wannan filin gasa hankalinsa a tashe yake domin babu wanda yake da tabbacin cewa ga wanda zai samu nasara.
Koda Zambaru ya iso daf da Imhal sai suka kacame da sabon azababben fada tamkar yanzu ma suka fara, ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta, amman fa karfin saran Zambaru ya ninka na jarumi Imhal a jahiri kowa ya tantance.
Duk sa'ad da ya kawo wa Imhal sara da wannan labceciyar takobi tasa koda Imhal ya kare saran nasa sai dai aga yana durkushewa kasa saboda nauyin saran. Amman saboda naci gami da kwarewa haka yake dagowa da sauri ya ci gaba da artabu yana mai mayar da martani.
Sai da suka shafe kusan rabin sa'a a haka dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin ɗaya ba.
Ko da ganin irin tsantsar jarumtakar da Imhal ke nunawa gami da juriya da naci har sai da "yan adawarsa ma suka ji ya burgesu ba su san sa'adda suka rinka yi amsa tafi gami da jinjina ba. Kai hatta attajiran da suka zuba dubunnan kudadensu a gasar akan Zambaru sai da suka koma goyon bayan Imhal basu sani ba, suna masu kiran sunansa.
Lokacin da Sadauki Zambaru yaga gaba daya yan kallo sun daina yi masa jinjina, zuga gami da tafi kowa ya koma kaunar Imhal sai ransa ya baci ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, cikin shammata ya gabza wa Imhal wani wawan naushi a fuska, saboda karfin naushin sai da imhal yayi katantanwa sau uku a wuri daya a lokacin ne kuma hakorinsa na sama yayi fitar burgu gami da gudan jini, sai kawai aka ga ya sulale kasa a matukar galabaice cikin mugun yanayi mai kama da birkicewar hankali.
Shi kuwa sadauki Zambaru sai ya kurma uban ihu na murnar samun nasara, sannan yaci gaba da dukan Imhal hannu da kafa, cikin kankanin lokaci kuwa ya galabaitar da shi ainun fuskar Imhal ta kumbura tayi suntum har ya zama cewa baya gani sosai da idanunsa sai dishi-dishi kuma tun yana yunkurin mikewa tsaye har sai da ya kasa ya baje kasa wanwar yana mai fidda numfashi sama-sama.
Tuni a wannan lokacin Gimbiya Shumaira ta sunkuyar da kanta kasa tana sharbar kuka domin ta fidda ran cewa Imhal zai iya tsira da rayuwarsa, kai hatta ita knta Gimbiya Lamirat wacce ta tsani Jarumi Imhal kamar yadda ta tsani mutuwarta sai da taji ta kamu da matukar tausayinsa.
Lokacin da Sadauki Zambaru yaga ya samu wannan gagarumar nasara ne sai ya ci gaba da kurma uban ihu yana yi wa kansa kirari, kawai sai yazo ya durkusa a gaban jarumi Imhal ya kamo gashin kansa yana mai dago da kansa sama da nufin ya dora kaifin takobinsa a bisa wuyansa da nufin yayi masa yankar rago a gaba kowa, tabbas kowa dake wannan fili ya fahimci manufar zambaru, kuma bakin ciki ya turnuke jama'a bisa ganin cewa za a yiwa wannan gawurtaccen jarumi kisan wulakanci a banza.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai akaga jarumi Imhal ya gabza wa Zambaru naushi a bisa makoshinsa, saboda karfin naushin sai da Zambaru ya yi sama sannan ya fado kasa a matular galabaice yana kakarin mutuwa.
Kafin ya mike zaune tuni Imhal ya rarumi takobinsa ya daka tsale daga inda yake zaune yayi sama kamar tsuntsu, bai dira a ko ina ba sai a kan ruwan cikin zambaru, kawai sai ya soka wa Zambaru takobi a cikin bakinsa take takobin ta faso keyarsa ta lume a cikin kasa, jini ya dinga malala ta cikin takobin tamkar idaniyar ruwace ta balle.
Imhal ya mike tsaye da kyar daga kan gawar Zambaru yana layi sai kawai akaga ya sulale kasa sumamme, nan fa filin gasar ya kaure da shewa, masu murna da tsalle na yi, masu rawa na yi. A guje likitoci suka suka karasa kan Jarumi Imhal, dakaru na kewaye da su dan tabbatar da tsaro, nan fa suka shiga yi masa magani domin ceto rayuwarsa.
Gawar sadauki Zambaru kuwa sai da karti majiya karfi mutum talatin suka taru sannan suka iya dauketa.
Cikin tsananin tashin hankali Sarki Gurzalu ya shiga cikin masaukinsa ya kama zarya kuma yana kai kawo zuciyarsa cikin kunci kamar ya dafe kai ya fashe da kuka bisa ganin yadda al'amura suka chakude masa, abu na farko da yafi dagula masa lissafi shine rashin sanin barawon da ya sace masa kambun sihirinsa, abu na biyu kuma shine ganin yadda lokacin karawarsu da Jarumi Imhal ya ke kara karatowa, tunda saura wasa uku kacal su hadu a filin gasar, ga shi kuma tsananin sa'ar Imhal din daya samu akan sadauki Imhal ta bashi mamaki, domin gaba daya filin babu wanda ya taba tunanin cewa Imhal zai tsira da rayuwarsa har ya lashe wannan gasa, amman sai ga shi yayi wa zambaru kisan farat daya.
Sarki Gurzalu na cikin wannan hali ne na kaikawo a cikin kuryar daki, sai ga Gimbiya Lamirat ta shigo cikin dakin, koda ta shigo taga sarki cikin wannan hali sai hankalinta ya tashi, ta karaso gareshi ta kama hannayensa ta rike ta jashi izuwa kan wata doguwar kujera suka zauna tare sannan ta dubeshi ta ce "Ya kai Abbana na san abinda ke damunka, amman ina so ka kwantar da hankalinka, ka yi sani cewa jarumi Imhal ba zai tsallake karo na uku a wannan gasa ba."
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Sarki Gurzalu ya dubeta ya ce "Mene ne hujjarki na fadar hakan, shin kin san jarumin da zasu fafata da shi ne, kuma kina da tabbacin cewa shi jarumin sai ya samu nasara akan Imhal din?"
Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Lamirat ta yi murmishi ta ce Kwarai kuwa nasan jarumin, kuma ina da yakinin cewa a halin yanzu ko kai bana zaton zaka iya samun nasara akan sa."
Koda jin haka sai sarki Gurzalu ya cika da tsananin mamaki, sannan kuma ya bushe da dariya ya ce Haba yake yata, hakika na fuskanci cewa har yanzu kina wasa da al'amarina, bakisan cewa na wuce duk yadda kike zato ba, ai duk da cewa bana tare da gurun tsafina babu wani jarumi da zai iya rabani da wannan kambun na jarumta a duk fadin wannan duniya, sai dai ko muyi ragas ni da shi. Yau dai saura kwana uku rak bokayen garin nan su gano mani barawon kambuna, kuma ban san ranar da zanyi karo da Jarumi Imhal ba, tunda dai ga shi ya sake samun karaya a kafarsa, kuma dole ne yayi jinya ta yan kwanaki.
Koda jin wannan batu sai Lamirat ta dan yi guntun murmushi ta ce "Ai al'amarin Jarumi Imhal yana da matukar shammata gami da ban tsoro, domin wannan karaya tasa zata iya warkewa a kowanne lokaci, ka duba fa yadda wannan lafcecen rauni na kirjinsa ya warke a cikin kwanaki uku kacal, alhali muna zaton cewa sai ya shafe sama da kwana bakwai yana jinya."
Sa'adda da Gimbiya Lamirat ta zo nan a zancenta sai Sarki yayi ajiyar zuciya gami da dan guntun murmushi Ya ce babu komai lokaci zai warware mana komai.
Yana gama fadin haka sai kawai ya shige cikin kewaye ya bar Gimbiya Lamirat zaune tana mamaki da tunanin abinda mahaifinta ya taka da har yake irin wannan lafazi.
Acan wani ɓangare na gidan sarauttar kuwa Gimbiya Shumaira ce tare da Gimbiya Muzaira zaune a cikin lambun sarki Taryan suna cin yayan itatuwa suna firarsu cike da nishadi amman duk hadiman gidan dake kai kawo basa iya jin abinda suke tattaunawa a tsakaninsu albarkacin wannan gurun sihirin dake daure a kugun Muzaira wato gurun Sarki Gurzalu, a cikin hirar tasu ce Muzaira ta dubi Shumaira cikin alamun damuwa ta ce Ya ke kawata wai shin mene ne yake damun kine, alhalin gashi danki jarumi Imhal yana samun nasara ko yaushe a cikn wannan gasa ta kambun jarumtaka, kuma ga shi kin samu nasarar raba Sarki Gurzalu da babban abin dogoronsa wato kambun sihirin da yake amfani da shi wajen cika dukkanin burikan rayuwarsa.
Lokacin da Muzaira ta ji wannan tambaya sai ta kawo gwauron numfashi ta ajiye fuskarta tana mai nuna damuwa da takaici ta ce Ya ke wannan yar sarki ki yi sani cewa har yanzu bani da kwanciyar hankali, duk da cewar na raba sarki Gurzalu da wannan gurun nasa na tsafi saboda shi mutum ne mai basira da hangen nesa, duk yadda zai yi yaga bayan makiyansa sai yayi, inba don bashi da ikon komawa birninsa ba a cikin wannan lokaci da tuni ya gano duk abinda nake ciki.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Shumaira ta dubi Muzaira ta ce Ya za'a yi ya gano abinda kika shirya alhalin kina tare da abin dogaronnasa.
Muzairat ta ce ai yana shiga cikin dakin halwar tsafin nasa ba zai yi sama da sa'a daya ba zai gano komai, yanzu babban abinda ke tayar mani da hankali shine ban dan irin tuggun da sarki Gurzalu zai shirya ba a ranar da zai fafata da Imhal ba, nasan dole ne ya dauki mataki gami da mugun shiri akan hakan tunda baya tare da kambun sihirinsa.
Kodajin wannan batu sai Muzira ta ce amman kin dada tayar mana da hankali saboda na fiskanci cewar rayuwar Imhal na cikin mugun hadari, ni ina ganin cewa dole ne ki taima wa Imhal wajen tsare lafiyarsa da rayuwarsa a ko yaushe kuma a duk inda yake.
Koda jin wannan batu sai Muzaira ta yi murmushi ta ce ai mahaifinki yana matukar kokari akan haka, ni nawa babban taimako sai a filin gasa, ni yanzu matsalata guda daya ce jal kuma ba komai bane face batun tsoho Imzanu wanda na baro a cikin gidana shi kadai, sa'adda da na barshi yana matsananciyar rashin lafiya duk da cewa nayi masa magani kafin na taho nan, kuma babu abinda zai nema ya rasa a gidan koda kuwa zai shafe shekara a gidan, hakika zaman kadaicinsa na damuna a gidan.
Koda Shumairat ta ji wannan batu sai ta yi ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya ta dubi Muzaira ta ce Kwantar da hankalinki yake Ummul Imhal, ni ina ji a jikina cewa har a gama wannan gasa zaki koma gida ki iske wannan tsoho wanda ya raini Imhal, alfarma daya nake nema a wajenki ina son a daren yau ki shigar da ni har dakin da aka kulle imhal domin in ban ganshi a halin da ake ciki ba nasan cewa ko barci ba zan iya yi ba.
Kodajin...


Read / Download RIJIYA GABA DUBU Book 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album