Join Our WhatsApp Group

KASUWAR RAYUKA 1 and 2 Complete Hausa Novel Document by KASUWAR RAYUKA 1 and 2


KASUWAR RAYUKA 1 and 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15532



KASUWAR RAYUKA 1 and 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 19, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 87.37 kb

File Type: txt

Views: 1267+

Download: 367+

Last download: 3 days ago

Description/Story: KASUWAR RAYUKA
Littafi Na Daya (1)
PART {A}
A WANI Zamani can baya mai tsawo da ya
shude,lokacin da ake kan tsakiyar cinikin
bayi,sa'adda sarakuna ke mulkin KAMA
KARYA,MULKIN ZALUNCI,a zamanin da mutum
bashi
da wani yanci na kansa face ya kasance sarki ko
mashahurin attajiri ko kuma gawurataccen Boka
ko Jarumi.Indai mutum bai taka wannan matsayi
ba'ana
sarrafashi tamkar dabba ba dan adam ba.A
wannan
lokaci kaf duniya babu kasar da tafi BIRNIN KISRA
Daukaka a harkar CINIKIN BAYI,domin basu da wata
sana'a wacce tafita.Sarkin dake mulkin Birnin Kisra
{DR ROKED}
Awannan lokaci ya kasance gawurtaccen sadauki
kuma gagarumin mayaki mai TARWATSA MAZA a
FILI FAM,ana kiransa da suna SARKI UZAIMA IBINI
SARZAF.Sarki Uzaima shine da kansa yake kwasar
dakarunsa na yaki kamar mutum dubu uku su tafi
FARAUTAR BAYI,kuma indai zai fita farautar bayi
baya kai hari a yankin kasarsa ko kasashen dake
makoftaka da kasarsa,yakan tafi wata nahiyar ne
gaba daya kuma mafi akasarin tafiye tafiyen nasa
yana yinsu ne akan TEKU.Duk sa'adda sarki
Uzaima
ya fita farautar bayi baya dawowa gida da kasa da
bayi dubu goma,kuma shi baya kamo yara ko
tsofaffi
sai matasan SAMARI da 'YAN MATA masu jini a
jika.Duk garin da yaje yakan sauka a bayan garin
ne
ya aikawa da sarkinsu wasika.A cikin wasikar sai
ya
bukaci a bashi bayi dubu goma cikin salama,idan
kuwa aka ki sai ya fakawa garin da yaki ya kama
duk wanda ya gadama a matsayin bawa koda
kuwa
sarkin garin ne da kansa.Kasuwar cinikin bayi ta
birnin Kisra tana cine bayan duk karshen mako
biyu.A duk wannan rana attajirai da sarakai suna
zuwa birnin na kisra daga kowanne bangare na
duniya domin siyen bayi saboda babu irin kalar
bawan da mutum bazai samu ba.A wannan rana
sarki Uzaima yana samun kazaman kudade masu
dimbin yawan dashi kansa yana mamaki.Saida
sarki
Uzaima ya shekara ashirin akan KARAGAR MULKI
yana wannan sana'a ta tara arziki wanda har takai
cewa yama rasa abinda zaiyi da kudin.Sau bakwai
yana sawa ana rushe fadarsa ana gina sabuwa,ya
zamana cewa duk duniya babu wata fada data kai
tasa kyawu da kawa.Sarki Uzaima ya tara
gonaki,gidaje,dabbobi da rumfunoni a kasuwa ba
adadi wanda shi kansa baisan iyakar adadinsu
ba.Wani iko na Allah sarki Uzaima ya kasance
mutum mai matukar koshin lafiya domin tunda ya
hau karagar mulki bai taba yin cutar datasa ya
kwanta ba koda tsawon yini daya saidai dan
gajeren zazzabi ko ciwon kai.Sarki Uzaima yana da
matar
aure guda daya jal.Wata kyakkyawar mace mai
suna
Suhaira wacce tun yana da shekara ashirin da
daya
akayi musu auren saurayi da budurwa tun zamanin
mahaifinsa.A yanzu Suhaira ta shekara goma sha
hudu da auren sarki Uzaima amma ko bari bata
taba
yi ba.Sarki Uzaima yana da kwarkwarori guda
ashirin da daya,kuyangi da bayi mata kuwa gasu
nan birjik amma dayarsu bata taba samun ciki
dashi
ba.Duk wannan irin ni'ima da Allah ya baiwa Sarki
Uzaima ta mulki,jarumta,d
ukiya,daula,mata da
ingantacciyar lafiya sai ta zama ta banza,domin
duk
sa'adda ya tuna cewa bashi da magaji sai ya shiga
daki ya kulle kansa yayi ta kuka har sai ya gaji da
kukan barci ya sace shi bai sani ba.Allah shine
mai
iko!Gashi dai duk wata daukaka ta duniya an
baiwa
sarki Uzaima amma sai aka hanashi haihuwa dimin
a nuna masa cewa shima fa ba kowa bane face
bawan Allah.Bokaye da likitoci barkatai sun
tabbatarwa da sarki Uzaima cewa lafiyarsa kalai
kuma zai iya haihuwa amma babu wanda yasan
yaushe ne zai samu haihuwar,kuma babu wanda
yasan macen da zata sami wannan sa'a ta haihu
dashi.A tsawon shekaru ashirin da sarki Uzaima ya
kwashe yana kai hare hare izuwa kasashen ketare
bai taba zuwa garin daya kasa samo nasara
ba,kuma bai taba yin gumurzu da wani jarumi ya
sami nasarar koda lakutar jikinsa ba bare ace
gashi anyi masa wani babban rauni saboda tsabar
KARFINSA,JARUMTAKARSA DA SA'ARSA.A ranar da
sarki Uzaima ya cika shekara arba'in cif a duniya
ne
ya zamana cewa ya sami shekaru ashirin akan
karagar mulki,bisa wannan dalili yasa aka shirya
gagarumar walima ta musamman,kuma ya gayyaci
gaba dayan sarakunan dake nahiyarsa domin suzo
su tayashi murnar cika shekarunsa na haihuwa
arba'in da kuma cikar shekara ashirin akan
KARAGAR MULKI.Baya ga wannan Walima kuma
saiya shirya gagarumar gasa ta yki akan cewa duk
jarumin daya sami nasarar yi masa rauni ko ya
kaishi kasa to ya fadi duk abinda yake so walau
dukiya ko wata kadara tasa zai bashi.Lokacin da
wannan labari ya bazu a nahiyar,sai
sadaukai,jarumai da mayaka sukayi ta tururuwa
izuwa cikin birnin kisra domin shiga wannan gasa
duk da cewa da yawansu sun firgita da al'amarin
sarki Uzaima,sun san cewa babu wanda ya taba
samun galaba akansa amma saboda kwadayin
ladan
da sukaji za'a baiwa mutane sukayi kundunbalar
shiga wannan gasa. ¤ ¤ ¤
DR KABEER LAWAL UMAR ROKED
A YAMMA da Birnin Kisra akwai wata karamar kasa
da ake kira da NURUL AMSAR.Sarki dake mulkin
wannan kasa ya kasance adali,kuma tsoho ne
tukuf!
Har ma takai cewa ya kwanta CUTAR AJALI saboda
tsufan nasa.Shi dai wannan sarki ana kiransa da
suna SA'AD IBINI HUSEIN.Saboda birnin Nurul
Ansar
tana makoftaka da birnin Kisra sai ta sami kariya
daga sharrin mahara da yan FARAUTAR BAYI.Don
haka akwai cikakken kwanciyar hankali da zaman
lafiya a birnin.Kuma Allah ya albarkaci birnin da
arzikin noma,kuma sannan sarki Sa'ad yana
matukar
biyayya ga sarki Uzaima,hakan yasa duk shekara
yake aika masa da kyautar amfanin gona mai
yawan gaske da kuyangi.Bisa wannan dalili ne ko
kadan
sarki Uzaima bai taba sa ido akan kasar Nurul
Ansar
ba,kai har ma zuba dakarunsa yayi akan bodar
birnin domin su basu tsaro daga yan kawo harin
sumame.Sarki Sa'ad yana da matan aure
shida,amma kuma 'yarsa guda daya ce
jal!A duniya wata kyakkyawar budurwa ta gaban
kwatance mai suna ARYALA.A Duniya babu abinda
sarki Sa'adda ke SO da KAUNA sama da gimbiya
Aryala,amma tunda aka haifi Aryala aka boyeta
saboda tsananin Kyawunta.Kai!Hatta Barori da
hadiman gidan sarautar babu wanda ya taba ganin
fuskar Gimbiya Aryala bare ya tsegunta irin
kyawunta saboda kullum ana rufe fuskarta ne da
wata bakar Hula wacce idanunta,bakinta da
hancinta
kadai ake iya gani,kuma mahaifinta ne ya bada
wannan umarni saboda wani sirri da bokansa ya
gaya masa.Lokacin da Aryala ta fara tasowa sai
Sarki Sa'adda yaga ashe Allah yayi mata baiwa ta
sadaukantaka,domin tun tana shekara shida a
duniya take iya dagashi sama ta fyada da kasa a
lokacin da yake koya mata kokawa.
Doctor kabeer kemagana
Koda gain
wannan al'amari na ban mamaki sai sarki Sa'ad ya
sake killace Gimbiya Aryala aka dauketa ita da
mahaifiyarta aka kaisu can wani gidan sarki dake
can bayan gari.In banda dakarun dake gadin gidan
babu kowa a cikinsa face Aryala da
mahaifiyarta.Anan ne kuma sarki Sa'adda ya rinka
zuwa da kansa yana koyawa gimbiya Aryala yaki.A
sannan ne fa ya sake ganin abin al'ajabi daya
shallake tunaninsa.Ba komai ya gani ba face yadda
a kwana uku kacal Aryala ta lakanci sarrafa takobi
fiye dashi.A cikin sati uku kuwa sai gashi tana
baiwa
kanta horon yakin da ba'a taba koya mata ba,sai
gashi har tashi sama take kamar tsuntsuwa tana
kaiwa iska SARA DA SUKA.haka dai Gimbiya Aryala
da mahaifiyarta ZALIMA suka cigaba da rayuwa a
cikin wannan gida na bayan gari su biyu kacal
tsawon shekara goma sha biyu.A tsawon wannan
lokaci Aryala bata da wani aiki wanda yafi baiwa
kanta horon yaki da kuma fita daji farauta a
sirrance ba tare da dakarun gidan sin sami
ba.Daidai da
rana
daya Gimbiya Aryala bata taba cire hular fuskarta
ba
ta kalli kanta a madubi bare taga kamanninta.Bata
cire wannan hula face idan zatayi wanka ko zatayi
barci,saboda dokace sarki ya kafa mata.Gimbiya
Aryala ta kasance tana tsananin son sarki Sa'ad
don
haka tana matukar biyayya a gareshi saboda haka
bata yarda ta sabawa umarninsa.Duk sa'adda
Gimbiya Aryala ta tuna cewa itafa yar sarki ce kuma
mai jiran gado,amma gashi an kawota wani gida
dake cikin kungurmin daji an ajiyeta tare da
mahaifiyarta tsawon shekaru goma sha biyu ba
tare
datasan dalili ba,kuma sannan an kafa mata dokar
rufe fuskarta a koyaushe har yakai cewa ita kanta
batasan kamannin kanta ba.An nisantata da
jama'a,bata ma san yadda ake tafiyar da al'amarin
rayuwa ba face abinda mahaifiyarta ta koya
mata,sai
tayi kuka na takaici da bakin ciki a duk sa'dda ta
zauna tana tunani akan wannan lamari na
rayuwarta.Abu daya ne yake sa zuciyarta tayi sanyi
a duk sa'adda ta kasance a cikin wannan hali,kuma
ba komai bane face duk sa'adda ta tafi farauta daji
tayi gumurzu da wata dabbar mai hadari ta kasheta
sai ta tsinci kanta a cikin dimbin farin ciki,tayi
murna
bisa ganin jarumtakar da Allah ya bata.A duk
lokacin
da Gimbiya Aryala ta tambayi mahaifiyarta dalilin
da
yasa aka killacesu a cikin wannan gida dake daji
aka
hanasu rayuwa a cikin gari da gidan sarauta sai
kawai taga hawaye ya zubowa mahaifiyarta
Zalima,sannan tace da ita kiyi hakuri yake 'yata
lokaci yana nan zuwa da zamu koma cikin gari
kuma a sannan ne zaki gaji mahaifinki ki haukan
KARAGAR MULKINSA!!!Duk sa'adda Gimbiya Aryala
taki wannan batu daga bakin mahaifiyarta Zalima
sai
ta kamu da tsananin mamaki,ta dubeta tace,saboda
me bazamu koma yanzu ba?Yake Ummina ki tuna fa
cewa yanzu mahaifina ya tsufa tukuf,kuma gashi
yana yawan yin rashin lafiya,har ta kai cewa yanzu
sau biyu rak yake iya kawo mana ziyara gidan
nan,shin bakya tsoron AJALI zai iya riskarsa muna
nan bamu sani ba?Yake mahaifiyata keda kanki
kinsan irin tsananin son da nake yiwa Abbana,don
haka ko zai mutu inason ya mutu akan kafaduna
ina
rungume dashi.Koda Gimbiya Aryala tazo nan a
zancenta sai hawaye ya zubo mata daga
idanunta.Itama mahaifiyarta Zalima ta kamu da
tsananin tausayinta ta kama zubar da hawayen
suka
rungume juna suna masu ci gaba da kukan.
Toh ai shikenan
Nima tsananin jin tausayin su yasa na tsaya ina
jimami.
....
Dafatan yayi kuma zakuyi liking da
commenting kamar yadda kuka saba.. Sannan zan
cigaba kaman yadda na saba Insha
Allah.
............
... By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOOKASUWAR RAYUKA
Littafi na Daya (1)
Part B.
Suka rungume juna suna masu ci gaba da
kukan.Tun daga wannan rana sai da sarki sa'ad ya
shafe sati biyu cur!bai kawowa su Gimbiya Aryala
ziyara ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinsu
kenan,kawai sai Gimbiya Aryala ya mike tsaye ta
kama shiri zata fita.Cikin firgici mahaifiyarta Zalima
ta sha gabanta tace,ina zakije?Koda jin wannnan
tambaya sai hawaye ya zubowa Gimbiya Aryala
tace,ya za'ayi naci gaba da zama tsawon sati biyu
ba tare danaga Abbana ba?Bamu san halin da
yake
ciki ba a yanzu yana raye ko baya raye bamu sani
ba.Dole ne yanzu naje cikin gari na shiga har fada
domin nasan abinda ake ciki.
KABEER LAWAL UMAR ROKED
Gimbiya Aryala na gama fadin hakan sai ta juya ta
nufi bakin kofa da
nufin taje inda bargar dawakai take ta kama daya
ta
hau.Koda ganin haka sai Zalima ta ruga tasha
gabanta ta rungumeta kuma ta fashe da kuka tana
mai rokonta akan ta kara hakuri lallai sarki bazai
barsu haka ba.Nan fa gardama ta karke a
tsakaninsu,Gimbiya Aryala nacewa sai ta tafi,ita
kuma Zalima tana riketa tare da rokonta akan ta
hakura da zuwa.Suna cikin wannan hali ne
kwatsam!Sai akaji haniniyar doki a kofar gidan
alamar cewa manzo yazo daga fada.A Guje Zalima
da Gimbiya Aryala suka ruga izuwa kofar
gidan,suna
zuwa kuwa sai sukaga ashe wani hadimin sarki ne
na jikinsa yazo.Take hadimin ya sauko daga kan
dokinsa,koda yazo gaban gimbiya Aryala sai ya
zube bisa guiwoyinsa yayi mata gaisuwa irin wacce
ake yiwa sarki.Duk da cewa fuskar gimbiya Aryala
a
rufe take saida Hadimin yaga alamun tsananin
tsoro
akan fuskarta domin ja tayi da baya a firgice tana
mai dafe kirjinta ta dubi hadimin tace,meya faru ga
Abbana?Hadimin yayi murmushi sannan yace sarki
nanan a raye,amma yana kwance cikin jinya,kuma
shine ua aikoni gareku yanzu.
Sarki yace a shaida
muku cewa yaune ranar dazaiyi murabus ya baki
KARAGAR MULKINSA don haka sai ku shirya mu
tafi.Koda jin wannan batu sai Gimbiya Aryala da
mahaifiyarta Zalima suka kamu da tsananin
farinciki
gami da mamaki.Nan da nan cikin kankanin lokaci
Zalima da Gimbiya Aryala suka yi shiri suka debi
yan kayan dasuke bukata suka hau dawakai
biyu,hadimin yayi musu jagora suka durfafi hanyar
dazata kaisu cikin gari.Tunda suka fara wannan
tafiya sai Gimbiya Aryala ta tsinci kanta a cikin
tsananin farin ciki don haka sai ta rinka kalle kallen
daji tana ta murmushi cikin annashuwa.Koda suka
iso kofar gari kuma taga yadda gaba dayan garin ya
sauya da sabbabin gine gine sai hawaye ya zubo
mata saboda rabon data taka kasar garin yau
shekara goma sha biyu kenan.Kawai sai Gimbiya
Aryala ta sauko daga kan dokinta ta debi kasa da
hannayenta biyu ta shinshinata sannan tayi ihu cikin
murna.
DOCTOR KABEER LAWAL UMAR ROKED
Al'amarin daya firgita hadimin sarki
kenan,yayi sauri ya tsaida dokinsa ya sauko ya
kama Gimbiya Aryala ya tasheta tsaye da sauri ya
dubeta yace,haba ya shugabata,ayau fa zaki zama
sarauniyarmu yaya zaki rinka yin abu na kaskanci
irin haka?Koda jin wannan batu sai Zalima ta dubi
Hadimin ta bushe da dariya tace,yakai SHUBARU
ka
kyale 'yata tayi farin cikinta ta more domin tana
begen birninta ne.Nan dai Shubaru ya kamawa
Gimbiya Aryala Dokinta ta sake hawa suka cigaba
da
tafiya suka kunna kai izuwa cikin garin.Har suka
isa
gidan sarautar babu wanda ya gane ko su waye.Kai
tsaye aka wuce dasu Gimbiya Aryala izuwa fadar
sarki.Al'amarin daya basu mamaki kenan har
Gimbiya Aryala ta dubi hadimi Shubaru cikin
mamaki
da rashin fahimta tace saboda me zaka nufi fada
damu maimakon ka kaimu turakar sarki muga
halin
da yake ciki?Hadimi Shubaru yace,ai sarki yana
fada
yana jiranku.Gama fadin hakan keda wuya kuwa
sai suka iso bakin kofar fadar aka bude musu suka
shiga.Suna shiga suke iske fadar a cike makil da
fadawa da kuma mutanen gari babu masakar
tsinke.Take suka hango sarki Sa'd zaune akan
karagar mulki yana rike da sandarsa ta mulki.Kallo
daya Gimbiya Aryala da Zalima suka yiwa sarki
Sa'ad suka gane cewa yana jin jiki,kawai karfin hali
yayi harma ya iya fitowa fadar ya zauna.Koda
jama'a
sukaga matar sarki Zalima da 'yarta Gimbiya
Aryala
sun durfafi inda sarki sa'ad ke zauna sai suka cika
da tsananin mamaki saboda jama'a da yawa sun
zata cewa Zalima ta mutu tun shekaru goma sha
biyu bayan ta tafi garinsu gaida iyayenta.Wannan
itace jita jitar da akayi ta yadawa har ma ana cewa
jaririyarta data haifa ma ta mutu.A wannan lokaci
Gimbiya Aryala tana sanye da wata doguwar riga ce
ta talakawa wacce mahaifiyarta ce ta dinkata da
hannunta,kuma takalmin dake kafarta mana fate
ne
kalar na talakawa.Duk da cewa fuskar Gimbiya
Aryala a rufe take,amma kyawun siffar jikinta sai
daya dimauta gaba daya mutanen dake fadar
musamman mazaje.Koda sarki sa'ad ya hango
matarsa Zalima tare da 'yarsa Gimbiya Aryala sun
shigo cikin fadar,sai fuskarsa ta fadada da
murmushi,kawai sai akaga sarki sa'ad ya yunkura
cikin matukar karfin hali ya mike tsaye sannan ya
taka matattakalar dake gabansa ya sauko kasa
daga
kan tudun da Kargar Mulkinsa take yazo ya tare su
Zalima duk su biyun sai suka fada kan kirjinsa
suka
rungumeshi suna kuka.Take shima sarki sa'ad
zuciyarsa ta karaya har hawaye ya zubo
masa.Al'amarin daya kara baiwa kowa mamaki
kenan.Bayan sarki sa'ad ya dan jima kankame
dasu
Gimbiya Aryala,daga can saiya janye jikinsa daga
cikin nasun sannan ya fuskanci jama'a yace,yaku
jama'ar birnin nurul ansar da yawanku kun san
kowace ce wannan a hannuna na hagu.To ga
wadanda basu santa ba ina mai sanar dasu cewa
wannan itace matata guda daya jal a duniya wato
Zalima wacce ake ta yada rade radin cewa ta mutu
a can garin su kimanin shekaru goma sha biyu da
suka gabata baya.Wannan budurwa kuwa da kuke
gani a hannu na na dama ba wata bace face 'yata
guda daya jal tilo a duniya,wato gimbiya Aryala.

...

....
By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWÀR RAYUKA!!!
Littafi na Dàya (1).
Part C
Wannan budurwa kuwa da kuka gani a hannuna
na dama ba
wata bace face 'yata guda daya jal tilo a
duniya,wato
Gimbiya Aryala.Koda sarki sa'ad yazo nan a
zancensa sai gaba dayan mutanen dake fadar suka
mike tsaye cikin tsananin mamaki suka kurawa
Gimbiya Aryala Idanu.Nan take sarki yasa hannu ya
cire hular dake kan fuskar gimbiya Aryala,jama'a
sukayi arba da tsananin kyawun fuskarta tata,ai
hatta
yan'uwanta mata dimaucewa sukayi saboda
tsananin kyawunta.Nan take sarki sa'ad ya kama
hannun
gimbiya Aryala yajata izuwa kan karagarsa ta mulki
yaje ya zaunar da ita sannan ya cire KAMBUN
SARAUTARsa na danyen zinare da lu'u lu'u dake
kansa ya dora mata akanta,sannan ya mike mata
sandarsa ta mulki ta karba.Kawai sai ya zube kasa
a
gabanta yayi gaisuwa mai nuna MUBAYA'A.Koda
ganin haka sai gaba dayan jama'ar dake cikin fadar
suka zube kasa gaban Gimbiya Aryala suna masu
jadda mubaya'arsu kamar yadda sukaga sarki
sa'ad yayi suna cewa cikin hadin baki munyi
MUBAYA'A
a
gareki ya sarauniyarmu!!!
KABEER LAWAL UMAR ROKED
Nan fa suka yi ta fadan
hakan har muryoyinsu suka cika birnin gaba
daya,jama'ar dake cikin gari ma da basu zo fadar
ba a wannan lokaci saida suka jiyo,kuma labari ya
riskesu da gaggawa cewa ai 'yar sarki sa'ad na
nan
a raye bata mutu ba,kuma gata nan ma a fada har
yayi murabus ya dorata akan karagar...


Read / Download KASUWAR RAYUKA 1 and 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album