Join Our WhatsApp Group

TAKOBIN JINI Complete Hausa Novel Document by TAKOBIN JINI


TAKOBIN JINI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17798



TAKOBIN JINI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Shuraihu Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08140419490

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 105.39 kb

File Type: txt

Views: 1160+

Download: 241+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: TAKOBIN JINI 1
Littafina daya 1 complet
Marubuci:- Shuraih Usman
(c) shuraih 99% 2016
TAKOBIN JINI »»
.
Littafin shuraih Usman
Part 1
Awani zamani can daya shude adaular larabawa
acikin wani babban birni maisuna ashdamir
Ashdamir babban birnine wanda yake karkashin
jagorancin sarki gulmanu gulmanu ya kasance
tun yana yaro azzalumine kuma hatsabibi don
ko acikin yara sa`oinsa tsoronsa ake
Wani abin mamaki shine allah yazuba masa
karf,ga jarumta don tun yana dan shekara goma
shabiyar yake kwace a hannun mutane ko
fatake da kun zaburo mai sai dai wasu bakuba
dan bai dauki ran mutun a bakin komai ba
mahaifiyarshi ta rasu shiyasa mahaifinshi yake
mutukar sonshi suna rayuwane awani kauye sai
suka yanke shawaran yin hijira zuwa birnin
ashdamir koda suka iso birnin . Bayan kamar
sati daya sai gulmanu yafara sana'anshi wato
zalunci todama sarkin wannan birni adaline
sunan shi asmir bin hubbal sarki asmir bayason
zalunci kuma bashida abokin gaba sai azzalumi
koda sarki yasamu labarin gulmanu da irin
zaluncin daya keyi sai ya umarci dakaru dasuje
sukamoshi. Baccin anka month shine sarki yasa
ai yekuwa kowa da kowa suzo fadan sarki aiko
nan take fadan ta cika da mutane makil sannan
wani bafaje yafara magana kamar haka. Yaku
jama'ar wannan birni mai Albarka kusani
wannan mutumin yaka sance yana aikata zalunci
acikin wannan birni dun haka hukuncin shi
bulala dubu sannan kuma musa shi agidan yari
na wata shida cur,wannan sai yazama darasi ga
yan gaba. Nan take aka mai bulala dubu sannan
aka wuce da shi gidan yari mahaifin sa yana
kuka yana neman gafara akan abashi danshi
haka amma ina yana kallo aka wuce dashi
Shuraih 99%
TAKOBIN JINI 1
Part 2
TAKOBIN JINI»»
Part 2
Bayan ankai gulmanu gidan yarine. Sabida haushi
da takaici mahaifinsa ya hadiyi zuciya ya mutu.
Da safiyar ranan ne labari ya riski gulManu ai
mahaifinshi ya mutu nan take ya runga kuka yana
birgima akasa. Bayan wannan rana gulmanu yana
cikin kurkuku sai yaga wani koren haske yana
fitowa kadan kadan kai har yamamaye cikin dakin
da yake amma ko alamar tsorata babu afuskan
gulmanu har koren hasken nan ya rikide yakoma
siffan wani kyamu shashshan tsoho babu riga ko
wando a jikin sa sai wani warki ta fatan zaki duk
jikinsa gashine. Ga wani kashin kwanyan mutum
a rataye a wuyanshi. Mutumin bata rai sannan
yace yakai gulmanu kasani cewa yadda kakeson
ganin bayan sarki Ashbir nima haka nake son
ganin bayanshi kai mahaifinka yakashe amma ni
yaya na guda biyu yaka shemin. Tsohon yace
gulmanu kayi sani cewa suna boka balbalin bala'I
ina rayuwane acan kan wani dutse anakiranshi
dutsen bala'I. Arayuwana ban san yafiyaba kuma
bani da imani koda miskala zarratin ne Ina
dawata kyakyawan mata wadda nake sonta ainun
amma garin haihuwa tarasu soyayyan danake
mata sai takoma wajen yayanta data haifa yan
biyu nasamu suna SAKRADIYYU da SAKRADISA
ina masifan son yayana har sukakai shekaru
Ashirin aduniya sannan nafara koya masu sihiri
kalakala. Wata rana suka ce mun nabarsu su je
farauta ni kuma na yarjemusu. Da suka fitane sai
sukakamo hanyar wannan birni. Har suka iso
suka shiga cikin birnin nan take suka fara amfani
sihirinsu suna kwace ,yima mata fyade dade
sauransu. Shikuma dokan wannan garin shine
duk wanda aka kama yacuci wani koya zalunci
wani ta hanyar amfani da sihiri to hukuncinshi
kisane. Ai kuwa nan da nan jama'an garin suka
gane su nan take suka kai kara wajen sarki. Sarki
ashbir yasa wani bokan shi mai suna KUMRU
bincike ai ko nan take boka kumru yace tabbas
magana wayannan mutanen gaskiyane ya shu
gabana. Nan sarki yace aje akamosu aiko nan
take a kaje aka kamosu sarki ashbir yatara
jama'an gari duka afada sannan. Aka kashesu.
Al'amarina kuwa tun danaga sunyi sati basudawo
ba hankalina ya tashi na dauko madubin tsafina
naduba nan da nan naga duka abin daya faru
dasu nan na Kwala wani uban ihu wanda nikaina
bansan lokacin danayi shiruba hawaye nazuba a
kuncina nan ta ke nayi wani sihiri mai karfi na
jefawa boka kumru nan take ya tarwase acikin
fadan sarki ashbir don ni duk wani bokan na
hiyannan shayina yake nayi nayi in kashe sarki
ashbir amma abin yagagara kawai saina shiga
halwan tsafina yau ne futowana daga halwan tun
bayan shekaru ashirin da biyar kenan. Nan boka
balbalin bala'I ya sauke numfashi. Gulmanu yace
yanzu nimekake nema awjena nan boka balbalin
bala'I yace kasani acikin halwan tsafina naga
babu yadda za ai naga bayan abokin gabana har
saina zo na sameka mun hada karfi da karfe
sannan za mu iya ganin bayan shi
TAKOBIN JINI 1
Copyright
Part 3
Shuraih Usman 2016
TAKOBIN JINI »»
part 3
gulmanu ya takarkare yafashe da dariyar
mugunta. Wannan dariyar ita ta tabbatar da boka
balbalin bala'I cewa gulmanu ya amince da
bukatarsa. Ai ko sai boka balbalin bala'I yai nuni
da yatsansa izuwa gulmanu sai gulmanu yaji
wani kaman an tsikareshi ya dan lumshe ido
budewanshi keda wuya sai yaganshi acikin wani
babban gida. Wanda aka mamaye cikin gidan da
yakutu da lu'ulu' ga kilisai ta ko ina sai yai duba
hannun damanshi nan take yai arba da boka
balbalin bala'I akan wata karaga na zinari. Boka
balbalin bala'I yace kasani gulmanu gobe zamu
kai ma sarki ashbir likafanin mutuwan shi har
gida sannan kai na doraka akujeran domin
arayuwana i ina matokan son azzalumi da zalunci
shiyasa nake son na dauraka akujeran sarki
ashbir don kata aika ta zalunci. Amma kafinnan
ina so kaje kahuta. Bayan gulmanu yahuta sosai.
Sai ya kishingida don yadan runtsa amma ina
tunanin mahaifinshi. Ta hanashi runtsawa. Washe
gari bayan gulmanu yayi shiri irin namayaka. Sai
boka balbalin bala'I yashigo har dakin. Gulmanu
yace kasani gulmanu yau shine ranar daukan
fansa a kan abokin gabanmu don haka babu
tausayi acikin wannan tafiya tamu. Ai kuwa sai
boka balabalin bala'I yai wasu surutai sai ga
wata katuwar tsuntsu ta sauka akofar gidan
sannan boka ya umarci gulmanu daya hau
shiyananan zuwa. Bayan hawan gulmanu bayan
wannan tsuntsu sai tsuntsun yatashi yanausa
sararin samaniya sai gudu ya ke kaman baze
dainaba******Al'amarin sarki ashbir kuwa tunda
ya samu labarin gulmanu ya tsere agidan kurkuku
sai hankalinshi yatashi ainun nan yakirawo
bokanshi mai suna hibrussalal. Koda zuwan
hibrussalal sai sarki ashbir yace mai yakai boka
hibrussalal kayisani cewa yaronnan gulmanu
yasamu nasaran tserewa da ga gidan kurkuku don
haka inaso kadubo min inda yake sannan ka qara
dubomin wanda ya temaka masa don nasan ba
zai iya tserewa daga wannan kurkuku shi kadai
ba nan take boka hibrussalal yace ya sarkin
sarakuna ina son abani daga yau zuwa gobe da
safe.
Takobin jini 1
Copyright
Part 4
Shuraih Usman 2016
Takobin Jini 1
TAKOBIN JINI»» . Marubucin Littafin Shuraih usman .
part Washe gari koda boka hibrusallal yazo fada
sai ya kwashi gaisuwa. Agun sarki sannan sarki
ashbir yace boka hibrusallal menene sakamakon
binciken dakayi jiya. Boka hibrusallal yace kayisani ya
sarki mai Adalci cewa jiya bayan narabuda kai babu
inda nazame sai kokon bincikena. Sannan boka yai
shiru sarki ashbir yace to ina jin ka mene sakamakon
don na kagu da inji meke faruwa. Boka hibrusallal.
Alkaluman tsafina sun nuna min wani babban masifa
da ke shirin faruwa acikin wannan birni namu nan da
nan hankalin sarki ashbir ya dugunzuma ainun yace
ma boka kadena kwanekwane kawai kafads min
meyake shirin faruwa acikin kasata sai boka
hibrusallal yace wato maimartaba bawani bane ya
taimaki gulmanu har ya tsere daga kurkuku ba illa
tsohon abokin gabanmu wato boka balbalin bala'I
yanzu haka sun hada karfi da karfe wato karfin tsafi
da karfin damtse zasuzo suya keka sannan gulmanu
yahau karagan mulkinka. Koda jin wannan batu sai
kowa da ke cikin fadan hantarsa ta kada akafara kace
nace. Sannan sarki ya dakamusu tsawa sannan aka
natsu. Sarki yace yanzu suna inane. Sai boka yace
yanzu sunanan acan dutsen bala'I. Kuma kasani daga
can zuwa nan tafiyar kwana biyar ne kaga muna da
lokacin da zamuyi shawara. Da jin wannan maganan
sai sarki ashbir yace yanzu meye abun dayakamata
muyi. Sai boka hibrusallal yace shawarata itace
muma mutaresu dayaki na san tauraruwa zahlu
zatabamu nasara Tauraruwa zahlu itace duk yan
nahiyar suke bauta mata. Sarki ashbir yace lallai boka
hibrusallal. Kakawo shawara dun haka sarkin yaki
kadibi dakaru dubu biyar kutsaya abakin kofar gari
kuhana kowa fita sannan kuhana kowa shiga.wannan
shine abin daya wakana abirnin ashdamir
*********** Al'amarin boka balbalin bala'I kuwa
yana rabuwa da gulmanu bai zame ko ina ba sai wani
daki inda shima ya sake tsuma kanshi acikin tukunyan
tsafi har tsahon kwana daya sannan ya fito koda
yafito sai ya kama karanto wasu dalasimai na tsafi ai
sai. Ya bace bat kaman bai taba wanzuwa awajenba
********** ********* Gulmanu kuwa tunda yahaau
kan wannan tsuntsu ta lula da shi sararin samaniya.
Yana cikin tafya kenan sai yaga kaman wani abu yana
yawo asaman dayalura sosai sai yaga ashe boka
balbalin bala'ine nan suka kwashe kwana uku suna
tafiya asararin samaniya sai arana ta biyarne suka
yada zango abayan birnin ashdamir nan boka
balbalin. Bala'I yace ma gulmanu ya shirya yanzu
zasu shiga garin. Aikuwa nuni kadai bokabalbalin
bala'I yayi da tafin hannunshi sai wani haske ya bai
bayesu can sai hasken yayaye nan suka tsinci kansu
akofan fadan maimartaba sarki ashbir ga dakaru nan
fululu tako ina suna kai da kawowa nan da nan boka
balbalin bala'I ya bace batt shikuma gulmanu koda
ganin haka sai yashigi wayannan dakaru dasara
dasuka duk inda gulmanu yayi saide karinga ganin
sassan jikin dan adam suna faduwa can sai dakarun
sukaga in akacigaba ahaka to lallai zai iya qarar da su
sai su ka mai zobe sannan wani ya wurgomai raga ai
kuwa yai sa'a ragan tada baibaye gulmanu nan suka
rufumai suka mai daurin huhun goro suka dauko shi
basu tsaya dashi ako ina ba sai agban sarki ashbir
koda sarki yaga gulmanu acikin sarka sai yai
murmushi yace yau kazo hannu kuma gobe za'a
yankema hukuncin kisa agban kowa da kowa***
TAkobin jini 1
Copyright
Part 5
Shuraih Usman 2016
TAKOBIN JINI�� .
Marubucin Shuraih
Usman
Part
. . Bayan sarki yasa ankai gulmanu
kurkuku an kulle can sai gulmanu yafara sakesake
acikin ranshi. To shi Boka balbalin bala'I dama ya
yaudarenine yana kan wannan sakesaken ne sai ya ji
motsi ta bayanshi wai ga wan dazaiyi kenan abin
mamaki ba sai yayi kicibis da boka balbalin bala'I ba
Haba ba sai gulmanu ya fara kokarin balle sarkan da
aka daureshi da itaba. Boka balbalin bala'I ya bushe
da wata mahaukaciyan dariya wanda tasa gulmanu ya
dena kokarin balle sarkannan. Ya dauki lokaci mai
tsawo yana wannan mahaukaciyar dariyan na shi
sannan yai turbune fuska izan ka ganshi zaka rantse
bai taba dariya aduniya ba Yace ya kai gulmanu kayi
sani cewa ina sane na aikata ma haka. Gulmanu ua
tunzura sannan ya ce lallai kacika maci amana kuma
matsoraci. Ashe duk harbin iska ne kake tayi wai kai
za ka kashe sarki ashbir amma ga shi anzo ka gudu
nanemeka harnagaji sannan baka taimakamin
dakomiba Koda jin haka sai boka balbalin bala'I
yasake bushewa dawata mahaukaciyar dariya can sai
kuma ya juyar da dariyar izuwa murmushi. Sannan
yace Gulmanu kai yarone shiyasa bazaka hangi abin
dana hanga. Kayisani cewa wani tarkone na dana ma
sarki ashbir kuma yafada. Wato kaga kama kannan da
akayi suna zaton kai kadaine kazo. Sannan yanzu haka
nasan sarki ashbir yananan yana bacci cikin
kwanciyan hankali mukuma. Sai muyi amfani da
wannan daman wajen halakashi sannan kuma inaso
kadauka azuciyanka nayi haka ne don tseratar da
rayuwanka Nan take boka ya balle ma gulmanu
wannnan sarkan sannan yakama hannun gulmanu ba
sai ga su a bakin kofan turakan sarkiba. Gulmanu ya
kashe masu tsaron kofan. Sannan ya kutsa kai cikin
turakan ba sai ga sarki kwance ba yana ta minshari.
Nan gulmanu yadaga takobinshi sama bai sauketa
ako'inaba sai a wuyan sarki ashbir aiko Nan kan sarki
tai sama to adaide wannan lokacin matan sarki mai
suna suraila. Ta make abakin kofan tana jin duk abin
da gulmanu kefadi koda ta fahimci gulmanu ya kashe
mijinta saita kwarara wani uban ihu sannan taruga
aguje koda gulmanu ya ji ihu sai ya fita da gudu yabi
bayan suraila yana bintanne kwatsam sai yaji an
dagashi sama an buga da kasa waigowan da zai yi
kenan sai yaga wata majaujawa tanufo shi gadan
gadan da niyyar halakashi bawannan bane ya tsorata
gulmanu. Ganin majaujawan sam bai tsoratar da
shiba illa Rashin ganin marikinta domin a iska
majaujawan ta ke zuwa koda ya rage bai fi tiki biyu
majaujawan ta fille maikaiba Sai yaga majaujawan
tana komawa dabaya. Nan sai boka balbalin bala'I ya
bayyana yana rike dawani babarbara katuwa sannan
boka hibrussallal shima ya bayyana ahannun shi na
dama yana rike da majaujawa hannun hagu kuwa
wata
makekiyan garkuwane.
Takobin jini 1
Copyright
Part 6
Shuraih Usman 2016
TAKOBIN JINI»»
. Marubucin Littafin Shuraih usman .
Part . .
Sai boka bal balin bala'I yai furta wasu
dalasimai nan da nan wata bakar wuta mai tafasa ta
kawo ma boka hibrusallal wani wawan sura da niyan
ta lullubeshi koda boka ya gahaka sai shima yai wasu
surutai wanda shi kadai yasan meyafada nan take
wannan bakar wutan ta bace kaman bata taba
wanzuwa awajen ba wannan ne ya basu daman
rabuwa har da yar tazaran zira'I tara sannan boka
balbalin bala'I ya bushe da dariya sautin muryarsa
duk t dauka acikin gidan sarautan lokaci guda kuma
ya tsuke baki kaman bai taba dariya aduniya ba yace
kasani hibrusallal kadebo ruwan dafa kanka kuma ina
mai rantsuwa da tauraruwa zahlu ko burbushin ka
baza a tararrba. Karo na farko kenan da gulmanu
wanda tun farkon gumurzun yana wajen yasaka
aranshi lallai boka hibrusallal taimakonsa yake. Batun
gaskiya dai boka hibrusallal bai da karfin sihirin boka
balbalin bala'I amma saboda zuciya irin na boka
hibrusallal yadake sannan yace kayisani yakai
wannan azzalumin boka yau karshen zaluncinka tazo
ina mai tabbatar maka ko kayi nasaran kasheni to
kasani watarana kaima sai ka....... Bai gama rufe baki
ba yaji wata zafi ta mamaye sassan jikinshi. Nan boka
balbalin bala'I yakece da dariya hannunsa na nuni
izuwa boka hibrusallal nan boka hibrusallal yafara
yankwamewa yana shanyewa har takai yakoma
kaman jariri koda gulmanu yaga haka sai yace acikin
ranshi cewa boka balbalin bala'I bakaramin hatsabibi
bane shikuwa boka hibrusallal nan take kasa ta
shanye shi gaba daya in badon a gaban gulmanu
wannan abun yafaruba da sai ya rantse babu wani
mutum daya taba wanzuwa awajen Sannan boka
balbalin bala'I ya sauke hannunshi tare da yin wata
irin huci ba sai gulmanu yaga kayan jikinsa sun canja
sunkoma kayan sarakai ba wadda ko acikin sarakan
sai antona. Gulmanu yatashi daga zaunen dayake ya
tsaya akan kafafunsa sannan yace waye zai jadani
nine gulmanu ibn hubruz azzalumi kuma uban
Azzalumai. Bayan gari ya waye jama'an gari suka
tsinci kansu acikin wani yanayi na bakin ciki sabilida
kashe Adalin sarkinsu da Akayi aka kafe kanshi acikin
wata itaciya. Ga badaya jama'an gari suka yi sahu
sahu afada don ganin waye ya kashe sarkinsu ya haye
kujeransa bayan yan mintoci sai ga boka balbalin
bala'I ya bayyana a tsakiyan fadan sannan aka ga gari
yayi duhu can da duhun yayaye. Gulmanu ya bayyana
da kayan sarauta nan da nan jama'a suka fara ihu
suna suna cewa bazamu yadda ba suna kan fadin
haka sai wata iska mai karfi tatashi sama tana tashi
sai ga kawunan mutane nan burjik akasa koda
jama'an gari suka ga abin dayafru da yan uwansu
wayan da suke gaba gaba sai sukai tsit sannan wata
dariya ta barke sanda mai dariyan yayi ta ishesshi
sannan yai shiru bawani ke dariyan ba illa Gulmanu.
Sannan yace kuyisani ya ku mutanen birnin ashdamir
daga nine sarkinku kuma duk wanda yaki yin muba yi
a agareni abin daya faru ga wa yennan shine zai faru
agaresa. Sannan sarki gulmanu ya shige gidan
sarauta. Jama'a suka watse.
Takobin jini 1
Copyright
Part 7
Shuraih Usman 2016
TAKOBIN JINI .
Marubucin Littafin Shuraih Usman .
Part . .
Al'amarin gimbiya suraila kuwa tun da ta
samu ta fice daga cikin birnin Ashdamir sai ta yanki
daji taita gudu har tsawon sa'oi. Goma sannnan wani
mugun gajiya ya lullube matA gabobin jiki taji bazata
iya ma tafiyaba,can dai dataga babu yadda zatayi
tafiya ya zamar mata wajibi sai ta cigaba da tafiya
tana yi tana layi kamar wadda ta kurbe tulunan giya
guda biyar !kamar daga sama saI taji karar zubar
ruwa , Nan take farinciki ya lullubeta taji ma dukkan
gajiyan dake jikinta sun kau ahaka ta karisa bakin
wannan korama ,. Wannan korama takasance babban
kogi ne ma'abocin zubar da ruwa shi wannan kogin
yana saman wani tsauni ne yayin da ruwan cikinsa ke
gangarowa zuwa kasa wannan ruwan dake kasan
shine ya samar da koramar da suraila ta tunkara
cikin farinciki tana ji kaman tabace ne ta bayyana
atsakiyar wannan korama sabida kaguwa da tayi da
kuma kishirwa ta...


Read / Download TAKOBIN JINI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album