Join Our WhatsApp Group

ALLON SIHIRI 1 TO 9 Complete Hausa Novel Document by ALLON SIHIRI 1 TO 9


ALLON SIHIRI 1 TO 9

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 89725



ALLON SIHIRI 1 TO 9

Reading Time: 7 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 511.54 kb

File Type: txt

Views: 1614+

Download: 1192+

Last download: 4 days ago

Description/Story: ALLON SIHIRI
Littafi na daya(1)
Part 1

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
YANA TAFE bisa wani ingarman doki sanye da
tufafi na alfarma ya ratso ta cikin Birnin.
Duk inda
ya wuce saidai kaga jama'a nata kallonsa saboda
kwararan dalilai guda uku.
Dalili na farko
shine,tufafin dake sanye a jikinsa wanda babu
mai iya sanyasu face shahararren ATTAJIRI ko
kasaitaccen
BASARAKE mai amsa sunansa.
Dalili na
biyu kuma ya kasance kyakkyawan saurayi na
kwatance wanda dole 'yanmata su yaba.
Dalili na
uku kuwa shine ya kasance GWARZON NAMIJI
mai
kirar sadaukai.
Kash!rashin sani yafi dare
duhu,inda 'yan mata sun san matsalar wannan
kyakkyawan
sauarayi da sunce akai kasuwa.Haka
dai wannan saurayi yaci gaba da tafiya a cikin
babban birnin da ya shigo mai suna RAUHUL
BAHADAR yana tambayar hanyar da zata kaishi
izuwa fadar birnin ana nuna masa harya
iso.
Fadace kasaitacciya ta gani ta fada domin an
kashe dukiya
mai yawan gaske wajen ginata.Kaida
gani kasan cewa an shirya Aljannar duniya a
cikin
wannan gidan sarautar.
SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA na zaune bisa karagar mulki
fadawanta
sun kewayeta kuma fadar ta cika makil da jama'a
ana gudanar da harkokin mulki,sai ga wannan
bakon saurayi an
shigo dashi dakaru kimanin su
goma na zagaye dashi don tabbatar da tsaro.Ba'a
bari wannan bakon saurayi ya kusanci inda
karagar take ba har saida aka je aka gaya mata
cewar yazo ne yana son ganinta sannnan ta
bayar
da izinin a gabatar dashi,aka rako shi aka
gurfanar dashi da
tazarar kimanin taku goma a
tsakaninsu da ita.
Bayan dukkanin dakarun dake
cikin fadar sun tsaida hankalinsu a kansa kuma
sun dafe kufen takubbansu suna jiran ko ta
kwana.
Saurayin ya zube kasa bisa guiwoyinsa a
gaban sarauniya Akisatul Sauwar cikin biyayya ya
kwashi
gaisuwa.Cikin murmushi da annuri fuskar
Akisatul Sauwar ta karbi gaisuwar sannan tace,ya
kai wannan bakon saurayi ma'abocin kwarjini
mene ne ya kawika kasata kuma menene dalilin
dayasa kake son ka gana dani?
Lokacin da
saurayin yaji wannan tambaya sai ya sake
risinawa cikin ladabi
yace,ya shugabata ni dai
sunana YARIMA LUBAINU IBIN SALLUR.Mahaifin
a
shine Sarkin wani babban birni da ake kira
ZAMRUL a can wata nahiya dake yammacin
wannan nahiya taku.
Ba wani abu bane yasa na
baro kasarmu ba face neman inda kogin BAHAR
IMFAL
yake.Koda jin wannan batu sai gaba daya
mutanen dake fadar suka bude baki suna
kallonsa cikin tsananin al'ajabi kuma suna yi
masa
kallon mahaukaci.
Ba komai ne ya janyi hakan ba
face sanin cewa babu wanda zai bukaci zuwa
inda
kogin Bahar Imfal yake ba face wanda ya gaji da
duniyar yake
neman ajalinsa.
Duk da cewar Yarima
Lubainu ya lura da irin kallon da jama'a keyi
masa a cikin fadar sai ya basar ya sake duban
sarauniya Akisatul Sauwara yace,Na sami labari
cewa akwai cikakken tarihin kogin bahar imfal a
wannan masarauta taki.
Akwai wani magani da nake so naje na samo a
cikin kogin
Bahar Imfal
kuma bokaye sun tabbatar mini da cewa saina
sami cikakken tarihin kogin idan ina son na sami
nasarar riskar inda yake har ma na sami nasarar
shiga cikinsa na debo maganin danake
nema.
Koda Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara da dukkanin
fadawanta da sauran jama'ar dake cikin fadar
suka bushe da dariya.
Al'amarin dayai mutukar
bashi mamaki kenan ya rinka kallon kowa da
kowa.
Daga can sai kuma sai Sarauniya Akisatul
Sauwara ta tsuke bakinta ta hade fuska tana mai
duba Lubainu
a cikin nutsuwa tace,Yakai wanna
dan Sarki kayi sani cewa abinda kake nema
daidai
yake da neman jaki mai kaho.Tabbas akwai
tarihin kogon Bahar Imfal a cikin gidan sarautar
nan,amma wani sashi ne daga cikin tarihin ba
gaba dayansa bane.
Mahaifina kafin mutuwarsa ya tabbatar mini da
cewa duk
abinda mutum yake
nema a cikin Kogin Bahar Imfal ba zai sameshi
ba
face ya karance gaba daya rubutaccen tarihin
kogin.Shidai wannan tarihi an rubutashi ne a jikin
wani Allo wanda aka rabashi gida uku.Akan
wannan Allo anyi yake yake marasa adadi,kuma
milyoyin
rayuka sun salwanta.A yanzu haka kaso
daya na wannan Allo ne a hannuna,kaso na biyu
yana hannun Sarki DARMASU na birnin
Kimras.
Daya kason kuwa na uku yana hannun
wani takadirin boka wanda ake kira Da suna
SARYANU IBINI DAUMUR.
Lokacin da sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan
a zancenta sai
Hankalin
Yarima Lubainu ya DUGUNZUMA ainun ya rasa
abinda yake masa dadi a duniya,cikin alamun
damuwa ya dubi Sarauniya yace,Ya shugabata
mene ne asalin tarihin wannan Allo mai dauke da
tarihin Kogon Bahar Imfal,kuma yaya akayi ya
rarrabu har kaso
uku?
Koda jin wannan tambya
sai Sarauniya Akisatu Sauwar tayi murmushi
tace,zan baka amsar wannan tambaya taka
amma
nima sai ka gaya min maganin da kake son ka
debo a cikin kogin Bahar Imfal.
Dajin haka sai
hankalin Yarima Lubainu ya sake dugunzuma fiye
da farko ya
kama kallon jama'a ya kasa cewa
komai.
Daga can sai ya dubi Sarauniya yace,yake
wannan sarauniya mai adalci kiyi sani cewa kin
tambayeni wani babban sirri na rayuwata wanda
bazan iya sanar dakeshiba anan cikin taro.Lallai
akwai bukatar mu kebe kuma bazan iya gaya
miki sirrin ba
face kinyi alkawarin taimakona bisa tawa
bukatar.Sa'adda sarauniya Akisatul Sauwara taji
wanna jawabi na Yarima Lubainu sai itama jikinta
yayi sanyi ta rasa abinda zatace,tayi shiru tana
tunani har izuwa tsawon yan dakiku,dagan can
kuma saita dago kai ta dubi Yarima Lubainu
tace,akwai bukatar
nayi tunanin da nazari zuwa
gobe,yanzu zan saka a kaika masaukin ka.
Kafin
Yarima Lubainu ya gama rufe bakinsa tuni
Sarauniya ta kirawo wani hadiminta ta umarceshi
daya tafi da Lubainu izuwa masauki.
Tana gama
fadin hakan ta mike tsaye daga kan karagar
mulkinta ta juya ta
shige izuwa cikin gidan
sarautar,dakaru da kuyangi na take mata baya
ana
buga tambura ana busa algaita.
Lokacin da aka kai
Yarima Lubainu masaukinsa sai aka karrama shi
ainun aka kaishi cikin wani daki na alfarma
wanda
ya kawatu ainun kuma aka kawo masa irin
abincinsu na
alfarma.
Bayan Yarima Lubainu yayi
wanka ya huce yar gajiyar dake jikinsa saiya
zauna
domin ya ci wannan abinci.Koda ya dauko lomar
farko yakai bakinsa sai tunanin gida ya fado
masa,nan take idanunsa suka ciki da kwalla ya
kamu da tsananin bakin ciki har hawaye ya zubo
masa.Bisa ba
komai bane ya fado masa a rai ba face
tunowa da masoyiyarsa YAZARINA.... pls Like nd
comments......ALLON SIHIRI
Littafi na daya(1)
Part 2
A can birnin Zamral Yazarina ta kasance
tauraruwar mata wacce babu kamarta a fagen
kyau,kuma tun suna yara ita da Yarima Lubainu
jininsu ya hadu sosai har suka fara girma suka
kama soyayya.Rana tsaka Yarima MANGUL da ga
Sarki Alkas dake mulkin kasar dake makwabtaka
da birnin
Zamrul yaga Yazarina ya rude kuma ya
dimauce a cikin begenta da kaunarta.Bisa
wannan
dalili ne mahaifinsa sarki Alkasa ya taso da
kansa
yazo har Birnin Zamrul ya nemawa dansa auren
Yazarina a wajen mahaifinta wanda ake kira da
ABU YAZARINA.Shi dai Abu Yazarina ya kasance
gawurtaccen
Attajiri a Birnin Zamral wanda babu
kamarsa a nahiyar,kuma duk sarakunan dake
nahiyar abokan kasuwancinsa ne.Lokacin da
Sarki
Alkas yazo birnin Zamral ya kadaita da Attajiri
Abu
Yazarina sai ya dubeshi yace,ya kai tsohon
abokina kayi sani cewa dana Yarima Mangul ya
kyallara ido
yaga 'yarka yayin da taje bikin cin
kasuwar birnina wacce aka saba yi duk
shekara.Ina mai sanar dakai cewa tun daga
wannan rana sai Yarima ya susuce tamkar wanda
ya zautu,ya zamana cewa dare da rana bashi da
wani aiki face ambaton sunan 'yarka.Kai sai
datakai cewa ya
daina ci da sha face anyi masa
hirar Yazarina an koda ta ana baiyana masa irin
siffofinta.Yakai abokina nazone neman alfarmar
ka amince a daura auren 'dana da 'yarka cikin
gaggawa domin ina tsoron cewa 'dana zai iya
rasa
lafiyarsa ko rayuwarsa muddin bai mallaki
Yazarina ba a
matsayin matar aure Koda Sarki
Alkas yazo nan a zancensa sai hankalin Attajiri
Abu Yazarina ya DUGUNZUMA ainun domin an
sashi cikin TSAKA MAI WUYA.Abu na farko dai
Sarki Alkas da Sarki Sailur duk abokansa ne
kuma
aminansa tun yarinta,babu wanda zai nemi
alfarma a wajensa
ya hanashi.Abu na biyu shine
ya san cewa 'yarsa Yazarina da Yarima Lubainu
sun dade suna soyayya tun suna yara kuma ya
sance cewa Yazarina tana tsananin son Lubainu
rabata dashi ba karamin aiki bane.Bayan Abu
Yazarina yayi tunani na tsawon 'yan dakiku sai ya
dago kai ya
dubi Sarki Alkas fuskarsa cike da
dumbin damuwa yana mai ajiyar zuciya sannan
yace,yakai abokina kayi sani cewa 'yata Yazarina
da Yarima Lubainu sunfi shekara goma sha daya
suna soyayya kuma gashi rana daya danka ya
ganta yana SO.Ka da sarki Sailur aminaine kamar
yadda muke
nida kai kaga bana son abinda zai
kawo lalacewar zumunci a tsakaninmu.Hakika na
tausaywa danka mutuka bisa halin daya shiga
saboda nasan illar soyayya gami da sharrinta
domin kuwa kwatankwancin hakan ya sameni a
lokacin danake neman auren mahaifiyar
Yazarina.Abinda nake
ganin za'ayi yanzu shi ka
labartawa Sarki Sailur wannan al'amari?
Koda jin
wannan tambya sai Sarki Alkas ya gyada kai
yace,kawai ce masa zanyi nazone akan harkokin
kasuwancinmu nida kai.Abu Yazarina ya gyada
kai
yace,ba za'ayi haka ba domin nan gaba wani abu
ya faru sai
yayi zaton munyi masa duk
munafunci.Abinda za'ayi yanzu shine ka tashi
muje fada musa ayi mana iso a wajen sarki mu
fito zahiri mu baiyana masa duk abinda ke
faruwa
dominmu hada basirarmu waje guda mu yanke
hukuncin da zai fi dacewa bisa adalci.Ba tare da
gardamar
komai ba kuwa Sarki Alkas ya amince
da wannan shawara.Na take Attajiri Abu Yazarina
yasa aka fito da keken doki suka hau aka tafi
dasu
izuwa fada.Da isarsu fadar suka tura akayi mus
iso a wajen sarki.Na take Sarki yasa aka shigar
dasu har cikin turakarsa saboda aminci.Bayan
sun gaisa sai
Attajiri Abu Yazarina ya zaiyane masa
koma dangane da abinda ya kawoso.Koda Sarki
Sailur yaji jawabinsa sai shima Hankalinsa ya
DUGUNZUMA ainun fiye da nasu.Saida ya jima
yana tunani har ya mike tsaye ya kama kai kawo
yana ta tunanin mafita.Daga can kuma ya dawo
ya zauna ya
fuskancesu su biyun yace,ni inda
tason raina ne zan iya tilastawa Yarima Lubainu
akan ya hakura ya barwa Yarima Mangul
Yazarina
amma idan akayi masa haka ba ayi masa adalci
ba tunda ya riga Mangul son Yazarina,asali ma
sun shafe shekaru masu yawa suna yin
soyayar.Ni a nawa
tunanin shawarar dana yanke a cikin
zuciya itace kawai a shirya musu gasa wanda ya
lashe shine zai aureta.Koda jin wannan batu sai
hankalin Sarki Alkasa dana Attajiri Abu Yazarina
Ya DUGUNZUMA.Cikin kaduwa Abu Yazarina ya
dubi Sarki Sailur yace,wace irin gasa kenan za'a
shirya musu?
Sarki Sailur yace,tunda dai duk su
biyun sun kasance GAWURTATTUN JARUMAI
masu
TARWATSA MAZA a filin daga kawai suyi yaki da
junansu wanda duk ya kashe wani Yazarina ta
zama tasa.Kafin Sailur ya gama rufe bakinsa tuni
Sarki Alkasa ya daka masa tsawa yace,ashe ka
sami tabin
hankali ban sani ba?
Ta yaya zamu sa
'ya'yanmu suyi gasar kashe junansu akan
soyayyar 'ya mace alhalin su kadai garemu?
Na
sani cewa a duniya babu abinda kake so sama
da
danka Yarima Lubainu kamar yadda nima nake
tsananin son Yarima Mangul.Menene hujjarka ta
yanke wannan
hukuncin?
Koda jin wannan
tambaya sai idanun sarki Sailur suka ciko da
kwalla har hawaye ya zubo masa sannan ya dubi
sarki Alkas yace,yakai abokina kayi sani cewa
mutum na iya rasa 'da ya sami wani amma
zumuncin daya kullu a tsawon shekara da
shekaru a
tsakaninmu idan ya zube ba zai taba debuwa
ba har abada.Na gama yanke hukunci don haka
ka koma gida ka shaidawa danka cewa idan har
son da yake yiwa Yazarina na gaskiya ne to yayi
shiri yazo nan birnin domin suyi gasar kashe juna
nan da ranar karshe ta wannan watan,kaga
kenan bai wuce
kwanaki goma sha hudu ba masu
zuwa.Ina maka fadan komawa gida lafiya.Koda
gama fadin haka sai Sarki Sailur ya mike tsaye
ya
fice daga cikin turakar ya barsu su biyu a zaune
cikin tsananin kaduwa da mamaki.Nan dai suma
suka mike tsaye jikinsu a sanyaye suka fice daga
cikin
turakar....Like nd comments pls
10 hrs · PublicALLON SIHIRI
Littafi na daya(1)
Part 3
Da la'asar sakaliya Sarki Sailur ya tura aka
kirawo
Yarima Lubainu suka kadaita a wani wuri na
musamman acikin gidan sarautar inda sarke ke
shakatwa.Bayan Yarima Lubainu ya zube kasa a
gaban sarki Sailur ya kwashi gaisuwa sai sarki ya
dubeshi fuskarsa a daure yace,yakai dana kayi
sani cewa kai
ba rago bane,kuma baka kasance
matsoraciba.Baya ga haka ban taba umartarka
dayin
wani abu ka kasa yi ba,saboda haka yanzu na
shirya
gasar yaki tsakanin da Yarima Mangul akan
soyayar
da kuke yiwa Yazarina.Wanda duk ya sami
nasarar
kashe wani a cikinku shine zai auri
Yazarina.Koda jin wannan
batu sai Yarima Lubainu ya cika da
tsananin mamaki kuma hankalinsa ya
DUGUNZUMA
ainun ya dubi sarki cikin kaduwa yace,yakai
Abbana
ina dalilin yanke wannan danyen hukunci dakayi?
Koda jin wannan tambaya sai sarki Sailur ya
kwashe
duk abinda ya faru tsakaninsu dasu Attajiri Abu
Yazarina da
kuma hujjarsa ta yanke wannan
hukunci.Dajin haka sai jikin Lubainu yayi sanyi
yayi
shiru izuwa tsohon 'yan dakiku,daga can sai
kuma
hawaye ya zubo masa yace,yakai Abbana kayi
sani
cewa Yarima Mangul abokinane tun yarinta
bazan
iya kashe shi ba da hannuna amma kuma ba zan
kaucewa
umarninka ba.Lallai zanyi wannan
gasa.Koda jin wannan batu sai Sarki ya fusata
ainun
ya dakawa Lubainu tsawa yace,idan har kaki yin
wannan yaki da dukkan karfinka da jarumtakarka
a
bakacin auren mahaifiyarka!Yana gama fadin
haka
ya mike tsaye yayi tafiyarsa yabar Yarima
Lubainu a
zaune cikin tsananin damuwa da tashin hankali
saboda yasan halin mahaifin nasa baya magana
biyu.Saida Yarima Lubainu ya dade a zaune a
wannan wuri yana kukan takaici.Yana cikin
wanann
hali ne yaji an dafa kafadarsa ta baya.Cikin firgici
ya waigo da
sauri kawai sai yaga she mahaifiyarsa ce
ZUHAIMA tsaye a kansa tana zubar da
hawaye.Cikin
hanzari Yarima Lubainu ya mike tsaye suka
rungume juna kuma suka cigaba da kuka
tare.Daga
can sai Zuhaima ta janye jikinta daga nasa suka
fuskanci juna ta dubeshi cikin nutsuwa da
murmushi tace,yakai
'dana na sanka tun kana yaro karami duk
abinda kasa a gabanka saikayi nasara.Nasani
cewa
ko kadan baka sin yin wannan gasa da abokinka
Yarima Mangul amma ya zama dole kayi ta tunda
baka da wani zabin.Lallai kayi wannan gasa da
dukkan karfinka da jarumtakarka kamar yadda
mahaifinka ya
umarceka domin bana son na
rasaka.Idan kuwa na rasaka nima bazan dade ba
a
cikin wannan duniya.Koda jin wannan batu sai
Yarima Lubainu ya kara kankame jikin Zuhaima
yacigaba da kuka yana mai cewa lallai bazan
yadda
ki rasani ba domin nafi kaunarki fiye da komai a
wannan
duniya hatta Yazarina kuwa.Wannan shine
abinda ya faru a birnin Zamral.
¤¤¤••••••••••••••••••••¤¤¤
A can birnin DARUL HUNZUL kuwa lokacin. da
sarki
Alkas ya isa gida sai ya kirawo Yarima Mangul
da
mahaifiyarsa tare da dukkan fadawansa ya sanar
dasu irin
hukuncin da sarki Sailur ya yanke bisa
neman auren kyakkyawa Yazarina dayaje
nemawa
Yarima.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa
ya
dugunzuma ainun shi kuwa Yarima Mangul
farinciki
ne ya lullubeshi ya kama ihu da murna domin
yana
ganin cewa tamkar ya mallaki Yazarina ne.Duk
dacewa yana
kaunar Yarima...


Read / Download ALLON SIHIRI 1 TO 9

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

5 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album