Join Our WhatsApp Group

BUSA A MUTU Book 4 Complete Hausa Novel Document by BUSA A MUTU Book 4


BUSA A MUTU Book 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17703



BUSA A MUTU Book 4

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Nov 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 95.11 kb

File Type: txt

Views: 809+

Download: 413+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: BUSA A MUTU!!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part A

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke magana
Ayi Hakuri Munyi Iya Kokarinmu Amma bamu samu littafi na 3 ba.

KODA HUSNAILA TA GA YADDA MURAISU YA KASANCE
sai ta kamu da tsananin farin cíki. Ta shiga
kodashi tana mai cewa.
"Gaisheka Magajin MAZAN JIYA. Tabbas na yarda
da jarumtakarka da kuma horon da na baka, don haka bana
shakkar ka tari mayaka komai yawansu.
Ka sani cewa yanzu ne fa zan ga amfanin horon da na
baka na tsawon shekaru anan dajin Kirzufa.
Yanzu ne zan gani idan baka sha nonona a banza ba.
Idan har ka bani kunya ba ni ba kai har abada!"
Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta buga da
karfi bar kwalla ta cika masa idanu, ya dubi Husnaila ya ce,
"Ya ke Ummina ya za a yi kuwa na baki kunya alhalin
wannan ita ce ranar da na dade ina jiran zuwanta?
Lallai kuwa yanzu ne za ki san cewa baki yi
baibuwar banza ba.
Yanzu ne za ki san cewa ba ki yi haihuwar banza ba.
Yanzu ne za ki san cewa kin haifi jarumi dan jarumai,
kuma jikan JARMAI."
Koda Husnaila taji haka sai ta rungume Muraisu cikin
tsananin farin ciki tana mai sa masa albarka.
Daga can kuma sai ta janye jikinta daga cikin nasa
suka fuskanci juna ta ce, "Abu na biyu da nake son na sanar
maka shi ne mu kasance a cikin shiri koda yaushe. Da zarar
ka ji wani motsi a cikin dajin nan wanda bamu saba jinsa
ba, kawai ka fiddo wannan kah0 na farautarka ka bu:
busashi
domin sauran abokan gaba tare.
Da zarar mun yi arba da abokan gaba kada ka rigani
afka musu. Ka tsaya ka ga yadda ake yin yaki tukunna,
lallai za ka ga yadda zan ragargaji maza, sannan sai kaima
ka sa hannu. "
Muraisu ya gyada kai yana mai nuna gamsuwarsa.
Nan take Husnaila ta kama hannun Muraisu ta ja shi
izuwa cikin gidan nasu, Jairul da Hairul na biye da su a
baya tana mai cewa, "Yana da kyau, mu je mu zauna mu
huta tunda tun safe muke ta aiki".
Haka dai Muraisu da Husnaila da sauran dabbobii.
dajin Kirzufa suka kasance kullum a cikin shiri da jiran
zuwan abokan gaba kuma, a kullum din idan lokacin busa
Kahon BUSA A MUTU ya yi sai Muraisu yaje ya busashi.
Shi kansa Muraisu duk sa'adda zai busa kahon sai yaji
bankalinsa ya dugunzuma domin ya san cewa lokaci ne na
tashin hankalin komai da kowa da ke nahiyar gaba daya.
A ranar kwana na ashirin da daya ne da fara busa
kahon da rana tsaka su Muraisu suka jiyo sukuwar dawakai
barkatai da ihun mazaje ya cika dajin Kirzufa gaba daya.
A wannan lokaci Muraisu da Husnaila na zaune
cikin gidansu suna cin abincin rana.
Koda suka jiyo wannan hayaniya sai suka mike tsaye
zurmbur! Husnaila tayia wuf ta dauki mashinta, shi kuma
Muraisu sai ya dauki kuttun kwarinsa guda uku gami da
bakansa na gado ya ratayasu a kafadarsa, kuma ya ruga
izuwa Kofar gida. Yana fita ya fiddo kahonsa na farauta ya
busa.
Nan take karar kabon ta danne hargowar Dakarun da
suka shigo dajin gaba daya har suka yi turjiya gaba
dayansu da dawakansu a lokaci guda suka yi cirko-cirko
domin dukkaninsu sun razana, kuma sun zata ma kahon
BUSA A MUTU ne aka busa.
Wadannan Dakarun yaki dai da suka shigo cikin dajin
Kirzufa su dubu saba'in ne, kuma suna da nmatukar kwarjinı
da ban tsoro, suna dauke da mugayen makamai na yakı iri-
iri, har da ma kalar da mutum bai taba gani ba.
Ba wani bane ke jagorantar wadannan mayaka ba
face Sarki Zaidur, kuma shi ne akan gaba ya yi gagarumar
shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro, fuskarsa a
murtuke take ko kadan babu annuri a tattare da ita.
Nan da nan dabbobin dajin Kirzufa gaba dayansu
suka taru a gaban Muraisu da Husn aila, kuma sai ga Jairul
da Hairul sun jawo tawagar birirrikan dajin gaba daya.
Suna isowa suka zube kasa a gaban su Muraisu suna
kwasar gaisuwa. Husnaila ta dubi gaba dayan dabbobin ta
ce, "Ya ku abokan zama, kun sani cewa shekara da shekaru
muna zaune a cikin wannan daji duk mahalukin da ya shigo
cikin wannan daji baya fita a raye, kuma baya iya cutar da
mu.
To fa ku sani wannan karon al'amura za su sauya,
domin abokan gabar da suka shigo mana yanzu za su iya
cutar da mu, amma fa dayansu ba zai fita ba a raye.
Abinda nake so da ku shi ne, ku tsaya mu yi yaki da
ranmu da jikinmu, domin mu kare rayuwarmu da
mahallinmu"
Koda gama wannan jawabi sai Husnaila ta wuce kan
gaba tana rike da mashita, ai kuwa sai dabbobin daiin
suka bita a baya duuu!
Shi kuwa Muraisu sai yai sauri ya hau kan Zaki
Jandal, suka bi bayan su Husnaila.
Al'amarin su Sarki Zaidur kuwa, lokacin a tawagar
tasu gaba daya suka ja linzamin dawakansu suka yi tirjiya
sakamakon jin sautin kahon farautar Muraisu sai suka tsaya
suna raba idanuwa suna kallon gabas da yamma, kudu da
arewa suna jiran su ga ta inda mai kahon BUSA A MUTU
zai fito su afka masa gaba daya.
Idan mutum ya dubi fuskokin Dakarun gaba daya sai
ya ga alamun tsoro a tare da su, Sarki Zaidur ne kadai
zuciyarsa a kekashe, sai muzurai yake kamar zai ci babu.
Sarki Zaidur ya cika katon mutum mai kirar
samudawa, domin girman halittar jikinsa ta yi kusan biyun
ta Muraisu.
Ya kasance dogo, kakkaura kuma shima duk jikinsa a
murde yake tamkar curin nakiya. Kallo daya mutum zai yi
masa ya san cewa ya cika barde mai dakawa maza gumba a
hannu.
Gaba dayan jikin nasa a cike yake da layu da gurave
na tsafi, wanda ya gada tun iyaye da kakanni kuma bava
amfani da su face a yaki.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai su Sarki Zaidur
suka bango Husnaila a guje a durlafosu rike da mashi.
dabbobin dajin na biye da ita.
Har Dakarun yakin sun fara dariya bisa ganin mace
ce ke tunkarosu, sai kuma suka ga wadannan dabbobin daji
biye da ita duu! a baya, sai suka fara razana.
Koda ganin haka sai Sarki Zaidur ya dakawa Dakarun
nasa tsawa ya ce, "Me ku ke jira ne da su! Ma za ku afka
musu ku zo mn da kan wannan hatsabibiyar mace wadda
ta haifo mana alakakai a cikin wannan daji".
Kafin Sarki Zaidur ya gama rufe bakinsa tuni
Dakarun su dubu saba'in sun sakarwa dawakansu linzami
sun sukwanesu a guje sun yi kan Husnaila da dabbobin.
A wannan lokaci ne kasa ta kama girgiza saboda
karar sawayen dawakai da na dabbobi.
Inda ace mutum yana nan a lokacin da za ayi wannan
mugun gamo yana kallo sai ya yi tsammanin cewa yakin
duniya ne ya barke.
Ai kuwa runduna biyun na haduwa aka kacame da
azababben yaki, ya zamana cewa karar karafa, ihun mazaje
da rurin dabbobi ya cika dodon kunne.
Ana haduwa aka cakude, aka ruguntsume da
azababben zazzafan yaki mai matukar muni.
Babban abinda ya tayarwa da Dakarun Sarki Zaidur
hankali shi ne, dabbobin tsalle suke suna dira akansu suna
jehosu kasa daga kan dawakai, kafin su yi wani yunkuri
tuni sun turmushesu sun yagalgalasu.
Kalilan ne daga cikin Dakarun suke da matukar zafin
naman da suke iva kaiwa dabbobin sara da suka suna yi
musu lahani.
Amma saboda naci da taurin rai irin na dabbobin sai
ka ga sun mike sun ci gaba da yakin duk da cewa jini na
zuba a jikinsu.
Duk wannan bakin artabu da ake yi Sarki Zaidur na
Asaye akan dokinsa yana kallo kawai, AA Misau ke magana domin ya fahimci
bangaren da ke samun nasara, amma ya kasa, domin yakin
ya zamo KARE JINI, BIRI JINI. Shi kansa yadda yaji
bokansa ya bashi labarin masifar dabbobin dajin Kirzufa
sai ya ga ma ashe ya fi haka.
Yana cikin kallon abinda ke fdaruwa ne jarumi
Muraisu ya durfafo wajen bisa Zaki Jandal. Jandal na yin
wata irin tafiya a hankali cikin takama da kasaita ya ratayo
kwari da bakansa.
Tun daga nesa Sarki Zaidur ya kurawa Muraisu idanu
cikin tsananin mamaki.
oms Ba wai kwarjininsa ne ko Zakin da yake kansa bane
suka bashi mamaki, kamanninsa ne da suka zo iri daya sak
da na ubansa marigayi Sarki Muraisu.
Nan fa Sarki Zaidur ya fara aiyanawa a ransa yana
mai cewa, "Anya kuwa Wannan ba Sarki Muraisu bane ya
yi fatalwa?"
Wata zuCiyar kuma sai ta ce da shi, "Ai kuwa inda
Sarki Muraisu ne ko dai fatalwa ya yi ya kamata ace
fuskarsa ta nuna manyanta tunda kusan shekaru goma sha
takwas ke nan da mutuwarsa"
Koda Muraisu ya kara matsowa kusa, sai ya raba
idanunsa A waje biyu, ya zamana cewa yana kallon
gumurzun da mahaifiyarsa Husnaila take ya ga yadda ta
zama tamkar shaidaniya a tsakiyar wadannan Dakaru, sai
sokesu take da mashinta suna faduwa kasa oatattu, kuma
da mashin nata take kare sara da sukansu.
Kai har tashi sama takea ansu tarmkar tsuntsuwa mai
fuka-fukai. Sannan kuma sai yc dubi Sarki Zaidur wanda
ke tsaye bisa dokinsa a gefe daya suna kallo-kallo.
Sa'adda Sarki Zaidur ya ga irin 6arnar da Husnaila
take yiwa Dakarunsa da kuma barnar da dabbobin dajin ke
yiwa Dakarun nasa sai ya fusata ainun, ya dirgo kasa daga
kan dokinsa yana mai zare takobinsa ya falfala da gudun
tsiya izuwa inda ake wannan gunurzu.
Yana isa cikin turmutsitsin taron ya tarwatsa
dabbobin dajin, loakci guda ya soki wadansu Damisoshi
guda uku, ya sari giwaye biyu ya bazar da su kasa sannan
yasa kafarsa ya make wani Zaki da wata Kura duk suka
baje a kasa wanwar ko shurawa basu yi ba, saboda tsananin
karfin dukan nasa.
Al'amarin da ya firgita gaba dayan dabbobin dajin ke
nan suka ja da baya suka koma can bayan Husnaila. A
lokacin ne suma Dakarun yakin na Sarki Zaidur suka koma
bayan Sarkinsu, aka fara kallon-kallo tsakanin Sarki Zaidur
da Husnaila.AA misau ke magana
Kawai sai Sarki Zaidur ya juyo ya dubi Dakarun nasa
ya ce, "Ina masu kwari? Ku harba kibiyoyin wuta".
Kafin Sarki Zaidur ya gama rufe bakinsa tuni
Dakarun sun kunna wuta a kasa sun fara dodana
kibiyoyinsu akan wutar.
Koda Husnaila ta ga abinda ke shirin faruwa, sai ta
falfalo da matsanaicin gudu ta daka wawan tsalle sama
izuwa kan wadannan Dakaru masu kwari ta hau sokesu da
mashinta.
Koda Sarki Zaidur a ga haka sai ya ruga da gudu
izuwa ga Husnaila domin ya kawar da ita, ai kuwa sai
jarumi Muraisu ya zaburi Zaki Jandal da gudu.
Kafin Sarki Zaidur ya iso inda Husnaila take tuni
Muraisu ya sha gabansa ya daka tsalle daga kan Zaki
Jandal ya doki kirjin Sarki Zaidur da kafa funsa biyu.
Duk da irin azababben karfi na Muraisu sai karfin
dukan nasa ya kasa kai Zaidur kasa, amma sai da ya ja da
baya taga-taga har taku uku, sannan ya tsaya cak yana mai
kallon Muraisu cikin murmushi.
Al'amarin da ya matukar baiwa Muraisu mamaki ke
nan domin komai girman bishiya mna idan yai tsalle ya
doketa da kafafunsa sai ya kaita kas, amma yau gashi ya
kasa kai mutum kas.
Nan fa ya sha jinin jikinsa ya tabbatar da cewa ya
gamu da gamonsa.
Sarki Zaidur ya kwarara uban ihu wanda ya firgita
komai da kowa da ke cikin dajin gaba daya har aka daina
yakin aka ja da baya aka zuba musu idanu shi da Muraisu,
Nan take kwalla ta cika idanun Sarki Zaidur, ya dubi
Muraisu a fusace ya ce, "Ya kai wannan dan marigayi
Sarki Muraisu, kayi sani cewa ka yanke min farin cikin
rayuwata tunda ka kashe mini dana sakamakon kabon da
ka busa don baka ne naji tsoron wannan daji na Kirzufa ya
fita daga raina, shi yasa na fito da dukkan shirina domin na
kashe duk wata halitta da ke cikin wannan daji kuma na
koneshi kurmus yadda za a manta da fargabarsa har
abada, "
Kafin Sarki Zaidur ya gama rufe bakinsa tuni
Husnaila ta tari numfashinsa ta ce, "Kafin kasa a manta da
fargabar wannan daji na Kirzufa ni da dana sai mun sa an
manta da duk irin zaluncin da kuke yi a wannan nahiya.
Shin ka manta ne cewa shekara da shekaru babu
Zaman lafiya a kowanne birni cikin wannan nahiya?
Sace-sace da kisan rayuka ya yawaita a ko ina amma
saboda abin bai taba shafarku ba ko wani naku shi yasa
kuka bar talakawa a cikin masifa, sai yanzu da ka rasa
danka wanda ka fi so fiye da komai shi ne za ka yi kokarin
shafe dajin Kirzufa da abinda ke cikinsa?
To ka sani cewa dajin Kirzufa da mu masu
mallakinsa mun fi karfinka.
Da sannu zamu karkade duk azzaluman da ke wannan
nabiya".
Koda jin wannan batu sai Sarki Zaidur ya kara fusata
ainun ya kwarara uban ihu a karo na biyu ya ruga izuwa
kan Husnaila da Muraisu suka ruguntsume da sabon
azababben yaki, suma Dakarun yakin nasa sai suka fara
fadawa dabbobin dajin aka dada rincabewa.
Wannan karon sai masu kwari da baka suka sami
damar harba kibiyovin wuta, nan fa wuta ta rinka kama
Sassan wurare a cikin dajin, ai kuwa sai giwaye suka fara
aikinsu na kashe wutar suna zuko ruwa da bakunansu a
cikin koramu da koguna suna watsawa akan wutar.
Da zarar sun kashe wutar sai su ga an sake kunna
wata. Jairul da Jairul kuwa, sai suka jagoranci sauran 'yan
uwansu biririka suka rinka debo manyan duwatsu suna
jefawa abokan gaba, sai dai ka ga an fasawa Badakare kai
ko goshi jini yai tsartuwa ya sulale kasa daga kan dokinsa,
kafin ya mike tsaye dabbobin sun turmusheshi sun
yagalgalashi.
Kamar yadda dabbobin ke wannan 6arna haka suma
zakwakuran mayakan Sarki Zaidur ke ragargazar wasu
daga cikin dabbobin suna saransu da sukarsu da takubba da
masu gami da kibiyoyi.
Haka dai yaki ya kara tsamari ainun ya zamana cewa
komai kallon kurillar mutum bai isa ya gano bangaren da
ke samun nasara ba sai dai ya ce KARE JINI, BIRI JINI
ake yi.
A bangaren Sarki Zaidur da su Muraisu kuwa, labari
ya sha bamban, domin idan suka sareshi ko suka sokeshi AA Misau ke magana
sai dai su ji kamnar dutse suka sara, shima kuma idan ya sare
su sai dai yaji kamar karfe yake sara, domin KAIFI DA
TSINI baya tasiri a jikinsu su duka, amma kuma sai ya
zamana cewa ya fi su karfin dantse da zafin nama don haka
sai ya zame musu alakakai suka rasa yadda za su yi su sami
nasara akansa.
Hatta takobin da ke hannun Muraisu wacce ya kar6a
8 hannun wani Badakare da ya make tuni ta dakushe
saboda saran Sarki Zaidur.
Lokacin da Sarki Zaidur ya fahimci cewar KAIFI DA
TSINI ba zai yi tasiri a jikin Muraisu da mahaifiyarsa ba sai
ya yi wurgi da takobin bannunsa ya shigesu da dukkan
karfinsu ya fara kai musu naushi da bugu da hannayensa da
kafafunsa.
Duk da cewa suna kokarin karewa da mai da martani
sai ya fara kuntatasu har ma ta kai cewa ya doki tsakiyar
mashin Husnaila da hannunsa.
Nan take mashin ya 6alle, ya raba gida biyu, sannan
ya fisge takobin da ke hannun Muraisu ya mutsittsiketa da
bannu daya tamkar takarda ya dukunkune, ya ja da baya
yana mai gyara isayuwa gami da dunkule hannayensa biyu.
Al'amarin da ya firgita Muraisu da Husnaila ke nan
suka Rara tabbatar da cewa lallai sun gamu da uban
sadaukai.
Kawai sai Muraisu da Husnaila suka dubu can inda
ake ta fafata yaki da dabbobinsu, suka ga lallai kare jini biri
jini ake yi, sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka kamu
da tsananin bakin ciki.
Muraisu ya dubi Husnaila ya yi ma ta inkiyar ta koma
gefe daya ta kyaleshi da Sarki Zaidur.
Cikin alamun firgita tayi masa nuni da cewar ba za ta
iya ba, sai dai su hada karfi su yakeshi. Kamar hadin baki
kuwa sai Muraisu da Husnaila suka ruga da gudu izuwa
kan Sarki Zaidur suna masu kurma ibu cikin mugun nufi.
Sarki Zaidur ya tsaya cak a inda yake ko motsawa bai
yi ba. Koda suka iso daf da shi suka kawo masa naushi da
bugu sai ya goce cikin zafin nama suka naushi iska. Kafin
su ankara tuni Zaidur ya gabzawa Husnaila wawan naushi a
fuska.
Saboda karfin naushin...


Read / Download BUSA A MUTU Book 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album