Join Our WhatsApp Group

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2 Complete Hausa Novel Document by MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2


MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19871



MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 06, Jan 2024

Author: Aliyu Abubakar Sharfadi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 101.66 kb

File Type: txt

Views: 910+

Download: 382+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman

Part 1.


A littafi na farko idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a
inda Aljana Akisa ta dawo da Malukussaifi birnin Kaimaru daf da
rijiyar nan da Sarki Kamrunu ya sa aka jefa shi, ta yi masa
sallama ta tafi bayan ta ba shi hular sa wadda ya samo.


Malukussaifi ya tsaya yana tunanin yadda zai yi ya shiga
birnin Kaimaru saboda yana tunanin ko ya sanya hularsa ta bata
ko dakon garin nan wanda ake kira gammazi zai ganshi saboda na tsafi ne, haka dai ya tsaya yana ta tunani a bakin kofar shiga birnin Kaimaru.


Can kuma a cikin birnin Kaimaru Damatu yar bokanya
Akila tun ranar da Sarki ya sa aka jefa Malukussaifi a rijiya duk
ta rude, hankalinta ya tashi domin ta san ba makawa sai va
halaka,sai ta samu uwarta bokanya Akila ta ce da ita, "Ya ke
wannan uwa tawa ma'abociyar yawan hikimomi, da kin buga
kasa kin bani labarin Malukussaifi tun kafin zuwansa kuma har
kika gaya mini ai shi ne ma mijin da zan aura to amma ga shi
yau sarki zai halaka shi, saboda haka yanzu ya zama dole a kan
ki ki yi amfani da
irin hikimominki na tsafi ki kubutar da shi in kuwa ba haka to
lallai ni ma zan kashe kaina na huta da radadin begensa da yake
damuna."
Ko da uwar ta ji haka ita ma sai hankalinta ya tashi jin
yarta ta ce za ta kashe kanta sai ta ce, Ki yi hakuri, ki kwantar
da hankalinki, zan yi iyaka bakin kokarina sai na ga na kubutar da
shi da ga wannan halaka da ya abka." Haka tai ta yi mata dabara
Tana rarrashinta har zuwa wannan rana da Aljana Akisa ta dawo
da Malukussaifi bayan wannan garin
Awannan ranar bokanya Akila tana gida tana buga kasa tana
bokancinta, a cikin haka sai ta hango Malukussaifi a bayan gari
yana tunanin yadda zai yi ya shigo ba tare da Gammazi ya yi
masa komai ba. Ko da ta ga haka sai ta yi kiran yarta Damatu
ta gaya mata, Ai ga Malukussaifi can a bayan gari yana tunanin
yadda zai yi ya shigo. yanzu sai ki yi maza ki je ki same shi ki ce da shi ya shigo duk ta inda yake so domin kuwa gunkin nan
gammazi tuni na lalata shi. Suna cikin haka sai suka ji ana
bubbuga kofar gida, bokanya ta ce. To shi ke nan ma ya hutar
da mu, ga shi can ya shigo yana buga
kofa maza je ki. ki bude masa ya shigo," Damatu ta yi zumbur
ta mike ta nufi kofar gida ta zare sakata ta bude kofa. Ko da su
kai ido hudu da Malukussaifi sai suka rungume Juna suna
shisshidar numfahi irin na ma'abota bege, sannan suka shiga cikin gida wurin uwarta, ita ma ta yi masa
maraba a kai masa shimfida ya zauna sannan suma suka zauna
tare da shi. Zaman su ke da wuya bokanya Akila ta mika hannunta baya
ta jawo wani katon tire wanda yake cike da abinci da na sha iri-
iri, suka ci suka sha, amma Damatu ta kasa cin abincin saboda
bege tana zaune kurum ta kurawa Malukussaifi ido tana kallonsa
tana mai cike da buri da bege
Bayan da ya huta ya kwashe labarın duk abin da ya faru tun
da ga lokacin da aka jefa shi a rijiya har zuwa wannan rana da
Aljana Akisa ta dawo da shi ya gayawa bokanya da yarta kuma
ya nuna musu hular da ya samo. Bayan haka ya kara da cewa,
To ni fa ba zama ne ya kawo ni ba. yanzu ina dabarar yadda
zan yi na dakko littafin nan na Halwanu
Bokanya ta amsa masa da cewa. to ai yanzu wannan abu
mai sauki'ne tun.da ga wannan hula taka, ai za ta taimaka maka
kwarai Yanzu yau shauran kwana biyar ranar zuwa bautar
wannan littafi ta zo sai ka bari a wannan ranar zan fita tare da
kai ka saka hulanka yadda babu wanda zai ganka idan mun je
mun yi sujjada Sai kawai ka dauko ka fito." Ya yi na'am da
wanan shawara ta ta suka ci gaba da zama har kwana biyar wato anar fita bautar ta zo.
A Wannan ranar bokanya ta yi shiri ta fita izuwa fada sauran
bokaye. na biye da ita, cikinsu hadda Malukussaifi, amma babu
wanda yake ganinsa saboda ya saka hularsa. Da zuwansu fada Suka tarar wuri ya cika macik da jama'a,bokanya akila da Jama'arta suka nemi wuri suka zauna shi kuwa Malukussaifi ya je
gaban Sarki ya zauna babu wanda ya ganshi jim kadan Sarki yà yi umarni a tashi a tafi wajen bauta,
Sarki da bokanya da duk sauran jama'ar gari aka tashi aka
Qunguma zuwa wajen bautar littafi. Da zuwansu Sarki da kansa
ya sa makulli ya bude kofa suka shiga da duk sauran jamaa,
Sannan ya kuma dakko wasu 'ya'yan makullan ya bude adaka ta
farko ya bude ta biyu ya bude ta uku ya ga littafi yana nan
yadda yake, nan ya sunkuya yana mai wa littafi sujjada.
Ko da Malukussaii ya ga haka duk sun sunkuya sai ya nufo
wannan littafin kafin ya kai ga inda littafin yake sai littafin ya
fado gabansa, ko da Sarki da sauran jama'ar dake kusa suka ji
motsin fadowar wannan littafi, duk sai suka mike suka ga littafi
na gewayawa amma ba su ga kowa a wurin ba. Sai suka tsaya
Suna kallo , shi kuma Malukussaifi da ya ga haka sai ya sa hannu
ya dau littafin yana dauka sai
jama a suka daina ganin littain.
koda ganin haka Sarki Kamrunu ya yi wa mutanensa tsawa ya
umarce su da su fita duk inda wannan littafi ya shiga su nemo
masa shi. Ran Sarki ya baci hankalinsa ya tashi idanuwansa suka
kada sukai jazur kamar an hura wuta. Haka jama'a sukai ta jewa
har dare' ba su ga iittafi ba, a karshe dai suka zo suka gaya wa
Sarki cewa sun gaza samo wannan littafi.
Sarki ya juya ya dubi bokanya Akila ya ce,Ya ke
ma'abociyar yawan hikimomi da dabaru na mika wannan lamari
a hannunki, ki san duk yadda za ki yi ki ga kin gano inda
wannan littafi ya shige." Da akila ta ji wannan magana ta Sarki sai ta
ce ai wannan abu ne mai sauki, da sannu zan binciko maka
inda wannan littati yake, kai sai ma na kawo maka wanda ya
dauke shi nan gabanka." Haka dai ta yi tai wa Sarki kalamai na
na
lami, da kartafa gwuiwa har iyarsa ta yi sanyi sannan ya sallami
jama'a kowa ya tafi zuwa gidansa.
bokanya Akila na komnawa gida Sai ta tarar da Malukussaifi yana zaune ga hula ga littafi a gabansa, ta nemi wuri ta zauna.
Zamanta ke da wuya sai ya ce,To ni fa yau bukata ta ta biya
tun da na samu littafin nan gobe zan kama hanyar komawa garin
mu, kuma ina matukar godiya ga dukkan irin taimakon da ki kai
min ba zan taba manta wa dake ba."
Da ta ji haka sai ta ce, "I, ai kuwa lallai bukatarka ta biya,
amma kuma ni ma ina so ka cika mini burina kamar yadda naka
ya cika. Burina kuwa shi ne ka auri 'ya ta Damatu ma'abociyar
kyawu kafin ka bar garin nan. Wannan kawai shi ne bukata ta."
Ko da ya ji wannan magana sai ya ce shi sam wannan ba za ta
yiwu ba, domin ya riga ya yi alkawarin ba zai auri wata ya mace
ba har sai ya auri Shamatu 'yar Sarki Afarahu, haka sukai ta
jayayya da shi da ita, amma sam ya ki yarda.
Can ita kuma Damatu tana daga dakinta, tana jin duk irin
jayayyar da suke yi, ko da ta ji ya ce ba zai aure ba ta, sai ranta
ya baci hankalinta ya tashi, haka ta raba dare tana tunani, can sai
ta tashi ta shiga dakin da Malukussaifi yake kwance, sai ta tarar
da shi ya yi nisa a cikin barcinsa, sai ta dauke hular nan tasa ta
yi kokarin ta dauke littafin ammna sai tai gudun kar ya farka
saboda da shi ya tada kai sai ta hakura ta koma dakinta da
hular.
Gari na wayewa Malukussaifi ya farka daga baricinsa ya
duba ya ga bai ga hularsa ba, nan da nan ya tambayi bokanya ko
ita ta dauka, ta ce ba ta dauka ba. Suna cikin haka sai Damatu
ta shigo ta ce masa, "Ni ce na dauke hular kuma ba zan baka ita
ba, har sai ka aure ni." Da jin wannan sai ya yi shiru, can sai ya
tuna da hudubar da Shaihu Jayyada ya yi masa ta cewar ya
dogara ga Allah, a dukkan lamarinsa.
Nan da nan sai ya fusata ya ce, Ba zan aure ki ba, hula
kuma ki rike, ni na dogara da Allah shi zai kubutar da ni." Ya
tashi ya yi musu sallama ya kama hanyar sa ta komawa gabar
kogin nan da dabbar nan Hashisha ta kawo shi.
Ita kuma bokanya Akila bayan da rana ta dan daga, sai ta yi Shiri ta tafi fada. Da zuwanta ta fadi gaban sarki ta yi gaisuwa ta
nemi wuri ta zauna, zamanta ke da wuya,sai Sarki ya dube ta ya
Ce Ya ke mai yawan hikimomi ya labarin littafi me kika gani
game da shi kuma?"
Akila ta ce, Ai wato wanda ya dauki wannan littafi ai
yanzu ma ga shi can ina kallonsa ya kama hanyar zuwa bakin
kogi, yanzu maza ka sa a bi shi a kamo shi."
Nan da nan Sarki ya yi tsawa, sadaukai mayaka duk suka
mike ya umarce su da cewa maza su bi wannan mutumin su
kamoshi. Nan da nan suka daurawa dawaki sirada suka hau, kimanin mutum dari biyar suka bazama neman Malukussaifi.
Shi kuma can Malukussaifi ya samu kwana biyu yana tafiya
cikin dajin yana Cin ya'yan itatuwa, yana shan ruwan
kwazazzabai. A rana ta uku, yana cikin tafiya sai ya ji karar
kofaton dawaki suna biye da- shi. Ko da ya waiga ya hango
mutanen nan da Sarki ya turo a sukwane kan dawaki, sai ya ranta
a na kare, ya yi ta gudu suna biye da shi har dare ya yi. Sai ya
Zo wani waje mai duwatsu cikin duhun dare, ya kwana karkashin
wani dutse duhu ya boye shi Su kuma mutanen nan su kai ta
neman sa amma ba su gan shi ba, sai suka tsaya suka tattare
hanyoyi suna jira gari ya waye Su kama shi
Da Malukussaifi ya ga haka sai ya yi tunanin a kan cewa
yanzu dabbar nan Hashisha tana kwance a gabar kogi, tana jira
rana ta bullo. A nan sai ya yi ta rokon Allah yana fatan ya boye
shi, ya wuce ba tare da mutanen nan sun ganshi ba. Allah ma ji
rokon bawañsa, ya amsa addu arsa. Haka ya fito ya ratsa ta cikin
mutanen nan ya wuce amma ba su gan shi ba.
Da zuwan Malukussaifi gabar kogi ya tarar da dabbar nan
Hashisha tana kwance. ya yi tsalle ya dafe gashin ta ya yi lif
Can su kuma mutanen dake neman sa, da gari ya waye 'suka
duba ba su ganshi ba, sai suka rika bin sawunsa cikin yashi har
kusa da gabar kogi. A wannan lokacin ita kuma wannan dabbar ta fara ruri ta mike, mutanen nan duk Suka juya a firgice saboda jin
kukan Hashisha, suna cewa, Aiya, wannan ai ya hadu da
Hashisha ta lashe, ai sai mu koma mu ga ya wa Sarki.


MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman

Part 2.



Haka suka
Koma gaban sarki a sukwane suKa shaida masa ai wanda ya dau
littafin Hahisha ta lashe shi.
Bayan faduwar rana Hahisha ta kwanta a waccan gabar
Malukussaifi ya sauka ya kama hanyar komawa hasumiyar
Shaihu Jayyada.


Da zuwansa ya yi masa sallama, Shaihun ya
amsa ya yi marhabin da zuwan Malukussaifi kuma ya kwashe
labarin duk abin da ya faru gareshi a tafiyarsa ya gaya masa,
kamar yana nan akai ya gaya wa Malukussaifi.


Sannan kuma ya
tuna masa da cewa shi gobe zai mutu, idan ya mutu, ya yi masa
wanka ya sa likkafani ya rufe shi, sannan kuma zai ga wasu
mutane sun zo jana' izar sa ka da ya yi wa kowa magana daga
cikinsu.


Haka kuma bayan an gama zai ga sun koma, kada ya
waiwaya har sai ya daina jin motsinsu, sannan ya binne Shi ya
yi tafiyarsa.


Asuba na yi Shaihu Jayyada ya cika, Malukussaifi ya aikata
komai kamar yadda ya umarce shi. Bayan ya gama tsaf. ya kamo
dokinsa ya yi masa sirdi ya hau ya kamo hanyar komowa kasar
Duwar.


kasar Sarki Afrahu inda aka raine shi.
Can kuma a kasar Duwar din Sa'adunizzanji ya kosa da rashin
dawowar Malukussaifi ubangijinsa. Wata rana Sarki Afarahu
yana fadarsa tare da sauran jama'a, ga boka Sakaradiyyuna na
zaune a gefen sa sai Sa'adunizzanji ya shigo fadar cikin fushi nan
da nan Sarki da sauran jama'a duk suka mike tsaye cikin rawar
jiki.


Sa'adunizzanji ya numfasa ya ce da Sarki, Wato kun tura
uban dakina neman wani littati kun tura shi ga halaka ko, to nan
da yan kwanaki kadan idan bai dawo ba na rantse da tauraruwa
zahallu duk garin nan sai na halaka ku." Ya juya ya fice a fusace.


Ko da ya fita sai Sarki Afarahu cikin dimuwa ya dubi
Sakaradiyyuna ya ce, Ka gani duk kai ka jawo mana wannan bala'in. Boka Sakaradiyuna ya ce da Sarki Afarahu, Kwantar da
hankalinka, wannan ni zan sabbaba abin da zai halaka shi."


Nan sai boka Sakaradiyyuna ya rubuta takarda zuwa ga dan uwansa boka Sakaradisa dake can fadar babban Sarki
Saifu'aradu. Ya kwashe labarin duk irin abubuwan da suka faru
game da lamarin Malukussaifi har zuwa inda ya nemi auren
Shamatu da yanda ya tura shi ya zo da kan Sa'aduninzanji, ya
kuma gaya masa yanzu ma ya tura shi ya nemo littafin Halwanu.


Sannan kuma ya ce da shi ya gayawa babban Sarki
Saifu'radu wannan labari, ya kuma gaya masa idan har wannan
yaro ya auri Shamatu to zai zamto sanadiyyar rushewar mulkinsa
sannan kuma zai mai da su bayi, addu'ar nan da Annnabi Nuhu
(AS) ya yi ta tabbata a zamaninsu.


Ya kuma ce ya gaya wa Sarki ya aiko wa da Sarki Afarahu
da kyauta ya kuma nemi auren Shamatu domin ya kare mulkinsa
daga kubucewa daga hannunsa. Ya kuma ce ka ga ko da wannan
yaron ya dawo mana a kan bukatarsa, sai mu ce ya taho wajen
babban Sarki ya karbeta, ballantana ma na san yanzu wannan
yaron ya halaka tuni.


da ya gama rubuta takarda sai ya bai wa wasu bayi su bakwai
ya ce su tafi can kasar babban Sarki Saifu'aradu su kai wa dan uwansa boka Sakaradisä wannan takarda nan da nan bayin nan
suka kama hanya kwanci tashi, har suka isa wanan kasa.

Da
zuwansu suka kai wa boka Sakaradisa wannan takarda, ya karba
ya bude.ya karanta ta sai ya mayar ya ajiye yana jiran gari ya
waye da safe ya tafi da ita fada ya karantawa Sarki Saifuar'adu
ita.


Waye war gari ke da wuya, boka Sakaradisa ya shirya ya tafi
fada, ya kwashe laberin dake cikin takardar nan kaf ya gaya wa
Sarki, kuma ya kwadaitar da shi auren Shanmatu. Ya umarce shi
da ya nemi aurenta kamar yadda aka rubuta a cikin takardar nan
Ko da Sarki ya ji haka nan da nan, sai ya sa aka kawo wasu
manyan adaku çike da dinari guda hudu, ya kuma sa aka kawo wesu adakun guda biyar cike da kayan ado irin na mata da abubuwa iri-iri na daga nau'in dukiya, sannan ya sa aka kirawo
wanj babban Sadauki daga cikin mayakansa, wanda ake kira manadihu, tsawonsa Kamu saba'in ne ga shi da manyan idanuwa jajaye, ga shi baki mai katon kai da gajeren...


Read / Download MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN Book 2
avatar
abdulrasheed-yusuf

4 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album