Join Our WhatsApp Group

KOGON ANNOBA Complete Hausa Novel Document by KOGON ANNOBA


KOGON ANNOBA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8971



KOGON ANNOBA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Mansur Usman Sufi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137237071

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 50.88 kb

File Type: txt

Views: 1251+

Download: 213+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: KOGON ANNOBA
Littafi na Daya 1
Na Mansur Usman Sufi
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
KOGON ANNOBA Part A
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Mansur Usman sufi
Kananan yara ne mace da namiji kyawawa na gaban
kwatance ke ta faman tsala matsanancin gudu babu
sassauci saboda tsananin gudun da yaran keyi idan
kagani sai kayi tsammanin zasu fita daga duniyar ne, kai
duk sa'adda suka waiga bayansu idan sukayi arba da
abinda yake bayansu sai kaga sun kara zage damtse karfin
gudun nasu ya karu fiye da na dazu Babu abinda zai bawo
mutum mamaki face idan yaga yanda suke gudun sai ya
rantse yace basu kasance bil adama ba kallo daya zakayi
musu ka fahimci cewa sun kasance ya'yan wani
hamshakin attajiri ko basarake saboda suturun dake
jikinsu masu tsadar gaskene.
Haka dai suka cigaba da gudu domin tsira da rayukansu
daga sharrin abubuwan da suka biyo su babu alamun
tsoro ko firgici a tattare da fuskokinsu har suka iso wani
qasaitaccen birni ai kuwa sai suka kunna kai ta cikin wata
yar mitsitsiyar taga ba tare sa sun jira masu gadin birnin
sun bude musu kofar ba lokacin da abubuwan suka biyo
yaran suka sauka a birnin nanfa jama'a suka dinga guje
guje gamida iface iface kafin kace me gari ya kaure da
ihun jama'a mutane suka ringa rugawa izuwa gidajensu
suna debo makaman yaki a wannan lokacin sarkin dake
mulki a birnin yana zaune akan karagarsa fadar ta qawatu
ainun da kayan alatu nau'i nau' i daban daban dangin
zinare da azurfa hardama abinda ido bai taba ganiba duk
inda ka duba a fadar kawunan jama'ane rututu kamar
dandazon kiyasai.
.
A gefe guda kuwa sarki SIYAMUL ANSAR na zaune akan
kasaitaccen karagar mulki yana sanye da doguwar
alkyabba akansa yana sanye da kambun mulki da aka
sana'anta shi da zazzarar zinare da lu'u lu'u sarki siyamul
ansar ya kasance dogon mutum mai qirar samudawan
farko yana da kyakkyawar fuska da dan siririn gemu mai
tsawon kamu biyu wanda shine ya kara fitar da kyawun
fuskarsa kallo daya zakayi masa ka fahimci cewa ya
kasance gwarzon jarumi yan majalisansa na zaune bisa
shimfidu na alfarma wadanda idan mutum ya taka su
saboda tsananin taushinsu sai yaji tamkar kafafunsa zasu
nutse a ciki awannan lokaci babu abinda kunne keji face
guje gujen jama'a da kuma shirun da ya wanzu a fada
kamar mutuwa ta gifta sai can ga dakaru masu tsaron
kofa sun shigo fadar hankalinsu a tashe.
Koda ganin halin da suke ciki sai sarki ya dube su yace
shin meke faruwa ne cikin rawar murya daya daga cikin
dakarun ya budi baki dakyar yace ya shugabana muna
cikin gudanar da ayyukanmu na tsaron kofa sai ga su
yarima NAZMAR sun janyo mana wata gagarumar masifa
bana tsammanin cewa akwai wata halitta da ta tsira da
rayuwarta mu kanmu tsananin razana ya hana mu mu
tantance wace irin masiface. Kafin badakaren ya gama
rufe bakinsa sarki siyamul ansar ya zare sharbebiyar
takobi ya sare masa wuya nan take kan badakaren yayi
fitar burgu daga gangar jikinsa jini yayi kwaranya kawai
sai sarki siyamul ansar ya takarkare ya kwarara uban ihu
wanda ya firgita gaba daya jama'ar dake fadar kuma ya
amsa kuwwa izuwa cikin birnin sai daga bisani ya
murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa
nan take yayi umarni aka busa qahon yaki kafin wani
lokaci mayaka sunyi cincirindo a kofar gidan sarauta shi
ko sarki siyamul ansar sai ya shiga izuwa gidan sarauta
jimm kadan sai ya fito cikin shigar yaki mai natukar
kwarjini da ban tsoro.
Fitowarsa da yan dakiku sai ga boka ZULWAL ya bayyana
acikin shigar yaki ya fadi kasa yayi gaisuwa sarki ya dube
shi tsananin fushi yana mai daka masa tsawa yace shin
kana ina ne masifa tatunkaro kasata ka gaggauta nemo
mana mafita domin tserar da ratukan al'ummar kasata
cikin ladabi boka zulwal yace ya shugabana kayi sani
cewa mafita dayace mafitar kuwa itace mu fita mu tari
wannan masifar tun kafin ta iso birninmu ina mai
tabbatar maka da cewa zamu samu nasara gama fadin
hakan keda wuya sarki ya kada linzamin dokinsa ya shige
gaba boka zulwal yabi bayansa take miliyoyin dakarun
yaki sukayi koyi dashi sarki siyamul ansar bn fanan siri ya
kasance mashahurin sarki kuma gagarumin attajiri da
babu kamarsa a kaf nahiyar baitul wahir yana da matar
aure guda daya kyakkyawar gaske mai suna NUZRA BIN
SHA'ARAN a rayuwar sarki siyamul ansar babu wani
rayuwar jin dadi da ya nema ya rasa face rashin haifuwa
duk da irin tarin dukiya da karfin mulki da yake dashi ya
tashi a banza domin bashida wanda zai gaji karagarsa
Akalla ya ziyarci manyan bokaye sama da dari akan
wannan matsala ta rashin haihuwa amma abu ya citra a
wani shekara ne ya ziyarci wani boka acan birnin KUBA
mai suna zulwal lokacin da sarki siyamul ansar ya
bijirowa da boka zulwal da buka tunsa na rashin haihuwa
sai kawai boka zulwal ya bushe da dariya har sai da ya
fado daga kan kujerar da yake zaune kuma idanunsa suka
ciko da kwalla al amarin da ya daurewa sarki siyamul
ansar kai kenan kuma ya fusata ya dakawa boka zulwal
tsawa yace dashi shin ina dalilin yin wannan dariya taka
cikin nutsuwa da biyayya boka zulwal ya koma akan
kujerarsa ya zauna yayi gyaran murya sannan ya fara
magana karo na farko muryarsa mai kama da kukan jaki
yana mai cewa asi ya huci zuciyarka ya sarkin sarakunan
masu isa kayi sani cewa ba komaine ya sanya ni wannan
dariya ba face bisa ganin yanda ka wahalar da kanka
wajen fadin bukatar da take tafe dakai ya sarki mai
cikakken iko kasani cewa tabbas ayanzu matarka na
dauke da juna biyu nan bada dadewa ba zata haihu kuma
ina mai farin cikin sanar dakai cewa 'ya'ya biyu zata haifa
mace da namiji sai dai inda gizo ke sakar shine 'ya'yan da
za a haifa maka zasu kasance hatsabibai marasa jin
magana wadanda sune zasu zamo ajalinka.
Yayin da boka zulwal yazo nan a jawabinsa sai hankalin
sarki siyamul ansar ya dugunzuma fiye da kowane lokaci
ya dubi boka zulwal yace ya sarkin bokaye shin babu
wata hanya da za abi 'ya'yan da zan haifa basu kasance
hatsabibaiba? boka zulwal ya nisa yace ai bakin alkalami
ya bushe lallai wannan al amari haka zai kasance koda jn
wannan batun sai sarki siyamul ansar ya sunkuyar da
kansa kas yana mai zurfafa cikin kogon tunani abu na
farko daya fado masa arai shine yanzu babu wata mafita
face kayi murna da wadannan yara da za a haifa maka
domin sune zasu gajeka bayan ranka tabbas bakada
nadama koda sun zamo ajalinka ai da ace wani ne zai gaji
karagarka gwara ace dankane na cikinka can kuma wata
zuciyar tace ka cigaba da bincike ya za ayi ace 'ya'yan
mutum sune zasu kasance ajalinsa lokacin da sarki
Siyamul ansar yazo nan a tunaninsa sai ya dago da kansa
ya dubi boka zulwal yace tabbas na amince 'ya'ya na su
zamo ajalina matukar zasu gajeni bayan raina.
Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar ya
debi dukiya mai yawa ya bawo boka zulwal saboda
tsananin murna sai da boka zulwal ya dinga birgima
akasa tamkar wanda ya samu ciwon hauka domin tunda
yake a rayuwarsa bai taba samun dukiya mai yawanta ba
kumama yana da wani babban buri akan dukiyar yana
son ya hada wani maganin tsafi da ita tun daga wannan
rana sarki Siyamul ansar ya kasance cikin tsananin farin
ciki kuma ya zamana dare da rana baya rabuwa da
uwargidansa nuzra yana bata gudunmuwa wajen rainon
juna biyun har ta sauka lafiya ta haifi 'ya'ya biyu kyawawa
mace da namiji aka rada musu suna NAZMAR da
HULAISA murna a wajen sarki kuwa ba a cewa komai
domin a wannan rana ya dinga rabon dukiya da 'yanta
bayi da barori sannan sai da akayi kwanaki ashirin ana
shirya walimar farin ciki manyan sarakunan duniya sun
sauka abirnin domin taya shi murna hakan ya sanya a
wannan lokaci ko kasa mutum ya kasa sai an siya saboda
kawai ana farin ciki kuma ya zamana sarki bashida wani
abokin shawara face boka zulwal tabbas masu iya
magana sunyi gaskiya da sukace sannu sannu bata hana
zuwa sai dai a dade ba a jeba sai gashi kwance tashi
Yarima nazmar da gimbiya hulaisa shekara uku a duniya
kasancewar yanayin jikinsu irin na mahaifinsu ne sai ya
zamana idan ka gansu lokacin da suka shekara uku sai
kace sun shekara biyar da haihuwa.
Tun suna wadannan shekaru suke nuna hatsabibancinsu
domin basa iya zama waje guda ko an kulle su a daki sai
sunyi dabaru sun fita awasu lokutan idan suka rasa
hanyar da zasubi su fice daga gidan sarautar sai su hada
rigima tsakanin dakarun dake tsaronsu sannan su sulale
su fice daga sarautar domin akwai wani lokaci da sukaje
suka tsokano wata qatuwar damisa ta biyosu har cikin
gari ta dinga hallaka mutane sai dakyar da sidin goshi aka
samu akayi maganin damisar kai in takaice maka kafin
Nazmar da Hulaisa su shekara shida sun janyowa birnin
masifu guda talatin kuma duk lokacin da hakan ya faru
sai an samu salwantar rayuka da dukiyoyin al'umma wani
abu da zai baka mamaki shine tunda aka haifi su yarima
Nazmar arzikin kasar ya kara bunkasa amma sai dai
mutane basu da kwanciyar hankali domin har kullum
gani sukeyi su Yarima nazmar zasu janyo masifar da zata
zamo ajalinsu ko asarar dukyarsu duk irin dakarun da
sarki Siyamul ansar zai sanya domin tsaron su Yarima
amma cikin hikima da basira sai Yarima nazmar sun
samu nasarar gudowa shi kasansa sarki duk lokacin da ya
tuna cewa su Yarima nazmar ne ajalinsa sai takaici ya
turnuke shi har ya zubar da hawaye duk cikin mutanen
birnin walau yan majalisa babu wanda ya iya kawowa
sarki korafi su Yarima nazmar saboda ganin irin soyayyar
da akeyi musu kuma babu wanda yake kaunar su domin
ta sanadin su attajirai sun zamo talakawa wadansu sun
zamo marayu. Duk lokacin da sarki ya samu labarin su
Yarima nazman sun janyo wata masifa sai ya kara sanya
matakan tsaro aturakarsa domin hanasu fita daga gidan
sarautar.
Lokacin da sarki Siyamul ansar da dakarun yakin suka fita
daga kofar gari sai sukayi arba da wadansu irin jibga
jibgan tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance
suna da jiki irin na zaki amma kawunansu sun kasance na
rakumin dawa suna dauke da kafafuwa guda shida akalla
girman kowannensu yakai na qatuwar giwa fuka fukansu
manya manya ne masu dauke da wadansu irin gashi mai
kama da takobi awajen kaifi da tsini hakika ba karamin
jarumi bane zaiyi arba wadannan tsutsaye face sai ya
razana ainun yayi nadamar wamzuwarsa agaban kasa
koda tsuntsayen su kimanin dubu sukayi arba da su sarki
Siyamul ansar sai suka saki fukafukansu suka sauka
aturba lokacin da dakarun sarki Siyamul ansar sukayi
arba da wadannan tsuntsaye sai suka razana ainun da
yawa daga cikinsu basu san sa adda suka saki fitsari a
wandonsu ba kuma suka yunkura zasu koma da baya sai
sarki Siyamul ansar ya daka musu tsawa suka tsaya cak
jikinsu na tsuma gaminda karkarwa shi kansa sarki
Siyamul ansar sai da yaji tsoro da razana sun darsu a
zuciyarsa domin a iya tsawon rayuwarsa bai taba gani ko
jin labarin tsuntsaye masu tsananin girma da ban tsoro
kamarsu ba nanfa dawakai suka dinga haniniya suna
zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda
tsananin dimauta su Yarima Nazmar kuwa lokacin da
wadannan tsuntsaye suka biyo suka shiga birnin suka
wuce kai tsaye izuwa turakarsu suka fara sharar bacci
abinsu kai kace babu wani abu da ya faru agaresu al
amarin da ya bawo kuyangi da barorin gidan sarautar
mamaki kenan har wadansu suka raya zuciyarsu cewa
anya kuwa su Yarima nazmar mutanene ba aljanu ba? ita
kuwa mahaifiyarsu sai hankalinta ya dugunzuma ta kasa
tsaye ta kasa zaune kawai sai ta dinga kai komo cikin
turakar hawaye na zuba daga idanunta......
Zan Cigaba insha Allah
Admin Dr. Goni S AbubakarKOGON ANNOBA Part B
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Mansur Usman sufi
Lokacin da aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Siyamul
ansar da wadannan jibga jibgan tsuntsaye sai ya zamana
babu wanda yayi yunkurin afkawo abokin gabarsa
awannan lokaci gaba daya mayakan dake wajen
hankalinsu atashe yake shi kansa sarki Siyamul ansar
hankalinsa atashe yake fiye da kowa yayi karfin hali ne na
irin masu manyan sarakuna koda sarki Siyamul ansar
yaga tsuntsayen sunki yunkurin afka musu sai ya umarci
wasu dakaru dari biyar da su dana bakarsu su harbawa
tsuntsayen take dakarun sukabi umarnin suka dana
bakarsu suka harbawo tsuntsayen yayin da kibiyoyi guda
dari biyar suka sauka akan tsuntsayen sai akaga
tsuntsayen sun tsaya cak ko gezau basuyi ba hasalima
idan kibiyoyin suka sauka akansu sai dai tartsatsin wuta
ya tashi kibiyoyin su zube kasa saida dakarun suka karar
da kibiyoyinsu sannan tsuntsayen sukayi wani irin kuka
mai firgita manyan jaruman duniya suka afka musu da
yaki take tsuntsayen suka yanyame miliyoyin dakarun
kamar yanda dandazon kudaje ke yanyame kwallon
mangwaro duk inda ka duba sune birjik babu abinda
suke face hurowa dakarun wata dunkulalliyar wuta
abakinsu ko su hallakasu da wadannan tsinin gashin dake
fukafukansu masu tsananin kaifi da tsini.
Cikin kankanin lokaci waje ya cikada ihun mazaje gamida
karar karafkiya karafe gamida haniniyar dawakai
mutuwar sadaukai ta cigaba da yawaita awajen nanfa aka
kacame da azababben yayi tsakanin kowane bangare har
yazama an shafe tsawon rabin sa'a su sarki Siyamul ansar
basu samu nasarar kashe ko daya daga cikin tsuntsayen
ba sai dai kaga tsuntsu ya wangame bakinsa ya hurawo
badakare wuta sai dai kaga nan take badakare da dokinsa
sun kama da wuta sassan jikin dakarun ya dinga shawagi
a sararin samaniya kura ta turnuke kamar hadari ya
gangamo akece da ruwan sama mala'ikan mutuwa ya
wanzu yana shawagi asama dawakai suka dinga haniniya
suna zubar da mahayansu kai duk inda daya daga cikin
tsuntsayen ya sanya gaba sai dai kaga dakaru suna
zubewa kasa matattu kamar ana sassabe agonar auduga
sarki Siyamul ansar ya wanzu yana kare kansa yana saran
tsuntsayen cikin bakin zafin nama juriya da jarumtaka.
Yayin da yaga yanda dakarunsa ke hallaka sai takaici ya
turnuke shi ya takarkare ya kwarara uban ehu ya dire
daga kan dokinsa ya tari wani tsuntsu guda daya suka
kacame da yaki idan tsuntsun ya wangame bakinsa ya
huro masa wuta sai kaga sarki Siyamul ansar ya kaucewa
harin cikin bakin zafin nama idan wutar ta zuba a kasa sai
kaga wajen ya haddasa wani wawakeken rami mai zurfin
gaske Lokacin da tsuntsun yaga ya kasa samun nasara
akan sarki Siyamuk ansar ta hanyar kone shi da wutar
bakinsa sai kawai ya dinga kai masa yakushi da zaqo
zaqon paratan hannunsa da nufin yayi fata fata da sassan
jikinsa. Faruwar hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar
ya fara gano lagon tsuntsun domin yanzu takobinsa ya
fara tasiri akan tsuntsun dan ayanzu takobinsa na samun
nasarar yankar jikin tsuntsun duk inda takobin ya sara
ajikin tsuntsun sai dai kaga ya dare jinina kwaranya.
Abangaren boka zulwal kuwa yana iyakar kokarinsa
wajen yakar tsuntsayen amma babu abinda ya daure
masa kai sama da yadda karfin sihiri baya tasiri ajikin
tsuntsayen face tsagwaron karfin damtse duk inda mai
kallo ya duba ba abinda zai gani face gawarwakin dakaru
fululu kwance cikin jini wasu a babbake suna kauri jini
kuwa ya cakude da kasa babu kyan gani ana cikin wannan
yaki ne wannan tsuntsu ya samu nasarar yankar sarki
Siyamul ansar da faratansa a cinya take inda ya yanke shi
ya haddasa wani qaton rauni jini ya kwaranya saboda zafi
da zugin da sarki Siyamul ansar yaji bai san sa'adda ya
sandara uban ihu ba ya saki takobin dake hannunsa cikin
tsananin zafin nama ya daka tsalle daga inda yake tamkar
an harbashi daga cikin baka ya dira akan wuyan tsuntsun
ya sanya hannayensa biyu ya kama kan tsuntsun ya
murde iyakar karfinsa nan take wuyan ya karye ji kake
rukuss sarki Siyamul ansar ya daka tsalle karo na biyu ya
sauka daga kan tsuntsun take tsuntsun ya fadi kasa yiff
tamkar an jefar da giwa ko shurawa baiyi ba.
Yayin da tsuntsayen sukaga abinda...


Read / Download KOGON ANNOBA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album