Join Our WhatsApp Group

ZUBAR DA JINI Complete Hausa Novel Document by ZUBAR DA JINI


ZUBAR DA JINI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 65414



ZUBAR DA JINI

Reading Time: 5 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Habibullah Muhammad Kabara ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 372.17 kb

File Type: txt

Views: 674+

Download: 434+

Last download: 4 days ago

Description/Story: +++++++++++++ZUBAR DA JINI

++++++++++++++ 1 PART A

LBR
++++++++++++++HABIBULLAH KBR

Gaisuwa ta musamman ga ýar uwar mu wato ummu jawaheer
sannan ina tayata murnar auren da tayi sannan allah ya bada zaman lafiya

Jin jina

Ga dukkan makaranta wadanda suke bibiyarmu tun daga farkon littafi kuma suke yi mana comment wadanda bansan adadinsu ba
Mun gode allah ya bar zumunci

A wani zamani can baya mai tsawo daya shude alokacin da
duniya take cikin kuncin rayuwa Saboda gaba daya mutane da
dabbobi kai hatta sarakuna basu da kwanciyar hankali sakamakon yawan yawan zubar da jinin da akeyi a fadin duniya
Saboda ako da yaushe cikin farautar rayuwar juna ake
Wanda yafika karfi ya kashe ka ya kwashe dukiyar daka tara
A wannan zamani mafi yawan mutane jarumai ne kuma matsafa
Domin su kare kansu daga farmakin abokan gaba
Babu abinda
mutane sukafi so awannan zamani sama da suga jini ya gauraya da kasa yana gudu akanta
Namiji kuwa idan bai kasance gawurtaccen mayaki ba bai isa ya auri mace kyakykyawa ba
Face wani yazo har inda yake ya kasheshi ya kwaceta
Kai yaran da suke wannan zamanin a haka suke tasowa
Sai kaga an haifi jarirai guda biyu amma da zarar sun fara wayo sai kaga suna yunkurin kashe junansu
Mutane basu da burin da yafi suga jini yana gudu acikin kwata kamar ruwa
Duk sarkin kuwa da yake da bukatar shakatawa sai kaga ya hada
Rundunar yaki sun farwa wata kasar wacce suka fita karfi da yawan mayaka
Su yaketa sannan su kamo bayi su dawo dasu birninsu
Hakika duk inda lalacewa da rashin imani yakai to wannan zamani ya wuce haka
Acikin wannan zamani ne akayi wata babbar masarauta mai dumbin tarihi
Wacce ta shahara a yawan mayaka da kuma girman kasa
Kuma ubangiji ya azurtasu da tarin arzikin kasa mai dumbin yawa
Ana kiran wannan birni da suna madaril adfam
Birnin madaril adfam ya shahara wajen kasuwanci da saye da sayarwA
Kasancewar shine kadai birnin da zakaje kayi zamanka lafiya ba tareda fargabar 'yan harin sumame ba
Saboda tsananin zaman lafiyar da akeyi a birnin
Ba komai ne ya janyo haka ba face kasancewar sarkin garin adalin gaske ana kiransa da suna fadarul munnar
Kuma fasa taro tunda yake a tarihin jarumtakarsa ba'a taba yankarsa ba afilin daga
Sannan kuma ya tsani zalunci bashi da burin da yafi yaga
Ya kawar da zaluncin da yake faruwa acikin duniya amma ya kasa
har ya zamana girma ya fara kamashi kuma gashi bashi da da ko
guda daya wanda sai gaji karagarsa idan ya mutu
Don haka
wata rana ya tambayi wani amintaccen bokansa kan yadda zai yi duk bukatunsa su biya
Koda jin bukatun sarki fadarul munnar sai bokan ya bushe da dariya sannan
Yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa bukatunka duka zasu biya
Amma ina mai tabbatar maka da cewa ba kaine zaka kawar da zaluncin da akeyi acikin duniyar nan ba
Sai dai tsatsonka bincike ya nuna cewa matarka tana dauke da juna biyu
Nan bada dadewa ba zata haifi 'ya'ya guda biyu to wadannan 'yA'yan ne zasu cika maka burinka

Daga wannan rana sarki fadarul munnar ya zauna jiran ranar haihuwar matarsa wacce ake kira da gimbiya nursiba zata haihu

Ana cikin wannan hali ne wata rana kwatasam sai nakuda ta kama nursiba
Ta haifi ýan tagwaye guda biyu mace da namiji kyawawan gaske
Awannan lokaci sarki fadarul munnar yayi farincikin da bai taba yin kamarsa a tarihin rayuwarsa
Domin saida akayi sati biyu ana shagalin bikin murnar haihuwarsu
Kuma tun aranar da aka haifesu aka soma tsumasu da tsumin tsafi mai matukar karfi don ya zame masu rigakafi
Dukiya kuwa yayita rabar da ita ga talakawa bai san iya adadinta ba
Tun a sannan suka dauki soyayyar duniya suka dorawa wadannan jarirai nasu
Sannan suka rada musu suna walisa da walisu dadin dadawa wadannan jarirai suna matukar kama da iyayen nasu guda biyu kamar an tsaga kara
A duk sanda sarki zaije zaman fada taredasu yake zuwa akafadarsa
Wani lokacin ma sai kaga ya goya daya abayansa daya kuma ya rukeshi a hannu
Lokacin da walisa da walisu suka cika shekara biyar sai aka fara koyar dasu ilimin bokanci da kuma salon yaki
Kasancewar su yarane masu hazaka da kaifin kwakwalwa sai kaga duk abinda aka koya musu sun dauka tamkar zanen dutse
Kai saida takai ta kawo shi kansa wanda yake koyar dasu dabarun yaki sun fishi iyawa
Sannan aka mikasu hannun sarkin yakin birnin wanda ake kira da huram
Shi kansa sarkin yaki huram yana matukar mamakin irin kaifin kashin wadannan yara dana kwakwalwarsu
Domin a lokacin ma kowanne daya daga cikinsu yana iya yin aikin da karti ashirin sukeyi
Kuma ba tareda sun jigata ba. Abangaren mutanen gari kuwa
Babu abinda yake burgesu gasu walisa face yadda suka hade kansu kuma suke da matukar tausayi
Sabanin ragowar yaran zamanin
Tun a wadannan shekarun mutanen birnin suka tabbatar da cewa
Nanda wani lokaci zasu zama gwarazan zamani wadanda za'a kara dasu a fannin jarumtaka
Shi kansa sarkin yaki huram watarana da suka kebanta da sarki fadarul munnar acikin turakarsa
Ya fada masa cewa
Zaifi kyau shi da kansa ya horar da su walisa da hannunsa
Domin sai sunfi samun cikakken horon yaki a gurinsa
Da jin haka sai sarki fadarul munnar yayi murmushi sannan yace
Nasan da haka amma ka sani inaso ne sai kashinsu yayi kwari sannan zan fara horar dasu da kaina
Wannan dalilin ne yasa na fara mikasu gurin matemakinka sannan suka dawo gurinka
To kaga idan suka zo hannuna salo na daban zan koya musu

Sirrikan tsafi kuwa a gurin babban bokan birnin suke samu wanda ake kira da suna makassar
Boka makassar ya kasance hatsabibin boka wanda duk nahiyar babu kamarsa
Shine yake koyar dasu ilimin bokanci da sirrikansa
Bayan sun
cika shekara goma sha biyar sai labarin jarumtakarsu ya shiga ko ina acikin duniya kasashe da dama suka kara shakkar tunkarar birnin madaril adfam da yaki
Komai karfin dakaru idan su walisa suka tunkaresu sai sun tarwatsasu
Sannan su kama sarkin su su mikashi wajen mahaifinsu
Atakaice dai sai da suka zama guguwar annoba ko ina ka shiga labarinsu akayi
A ka idar birnin madaril adfam mace batayin mulki saidai namiji
Amma hakan baisa sarki fadarul munnar yana nuna banbanci ba atsakanin 'yaýansa
Wannan dalilin ne yasa suka shaku da junansu ko kadan basa taba rabuwa da juna

Ana cikin wannan hali ne wata rana aka wayi gari babu yarima walisu acikin birnin
Wannan al'amari ne yayi matukar razana sarki fadarul munnar
da gimbiya walisa da mahaifiyarsu
Babu inda ba jeba acikin birnin da makotansa ko za'a ga yarima
walisu amma sama da kasa ba'a ganshi ko an sami labarin wanda ya ganshi ba
Wannan al'amari ba karamin tayar da hankalin mutanen birnin madaril adfam yayi ba
Domin tunda ya taso a rayuwarsa bai taba zuwa wani gurinba face da izinin iyayensa ba
Babu wanda hankalinsa ya tashi fiye dana kowa face 'yar uwarsa gimbiya walisa
Domin tasan ita bata da ikon mulkar birnin madaril adfam sai shi
Tunda ita mace ce don haka shi kadaine yake da ikon gadon karagar birninsu
Sai da aka kwana biyu ana binkice a cikin nahiyar kuma aka baza hotunansa
Sannan aka saka kudi mai tsoka kan cewa duk wanda ya fadi inda yake za'a bashi su
Amma duk da haka ba'a sami wani gamsashshen labari ba
Shi kansa boka makassar babu irin binciken da bayyi ba don gano inda yarima walisu yake amma ya kasa
Wannan dalilin ne yasa aka tara manyan bokayen da suke nahiyar guri guda domin su hada karfi da karfe su gano inda yake
Wannan taron kuwa anyi shi ne a fadar sarki fadarul munnar
Bayan kowa ya gama hallara sai sarki fadarul munnar ya tashi ya fara jawabi kamar haka

Yaku manyan dirakun wannan nahiya dukkanku kunsan babban bala'in daya taso mini acikin wadannan kwanaki
Na batan magaji na wannan birnin wato dana walisu
Babu irin binciken da bamuyi ba domin gano inda yake amma mun kasa sani
Adalilin hakane yasa na taraku gaba daya domin yin shi wannan aikin
Inada tabbacin cewa idan kuka hada karfi da karfe zaku samo mana mafita akan wannan al'amari
Idan kuwa har kukayi wannan aiki zan baku dukiya mai dumbin yawa
Domin kowa acikin ku akwai irin baiwar da yake da ita
Da wannan kalami nake umartarku daku fara yin wannan gagarin aiki
Yana gama fadar haka yayi shiru da bakinsa ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya
Nantake duk bokayen suka dukufa suka fara bincike mai zurfi
Saida kowannensu ya jike sharkaf da gumi kamar an watsa musu ruwa
Jikinsu kuwa ya soma rawar dari, idanunsu sukayi jazur
Fadar kuwa tayi tsit kamar babu mai rai acikinta har suka shafe dakiku masu yawa
Sannan dukkansu suka dago da kansu jikinsu a sanyaye
Suka dubi mai gidansu boka makassar
Shi kuma ya kalli sarki fadarul munnar jikinsa duk yayi sanyi sannan yace
Ya shugabana dole saidai kayi hakuri da danka yarima walisu
Domin yanzu haka bama musan inda yake ba
Saidai bincike ya nuna mana cewa yana raye acikin duniya
Yanzu haka ruhin wani hatsabibin boka ne ya shigeshi wanda ya shafe shekaru masu daruruwa da mutuwa
Shidai wannan boka tunda aka halicci duniya ba'ataba samun
Shu'umin matsafi ba kamarsa domin yana iya yin tsafin da zai janyo hallakar birane da dama a cikin abinda bai wuce dakika guda ba
Kuma yana iya samar da hasken rana acikin tsakiyar dare
Kuma tunda yafara sabgar tsafinsa bai taba taka kasa ba ko kwanciya da zama akanta ba
Sai dai akan iska
Kuma duk inda yake da burin zuwa saidai kawai kaga ya
bayyana agurin koda kuwa tafiyar takai tsawon tafiyar shekara dubu
Ana kiransa da suna sahibul ukub
Azamaninsa saida takai ga cewa mafi yawan kasahen duniya da sarakuna shi suke bautawa amatsayin abin bautarsu
Saidai wasu kebantattun mutane mabiya wani addini wadanda basu da yawa acikin duniya
Babban burinsa a duniya shine ganin ya mayar da ita ta koma rayuwar ZUBAR DA JINI
Sannan yaga teku ta rine da jinin bil'adama
Kuma ta dole ya dinga tilastawa mutane suna yakar masoyansu suna kashesu da hannayensu
Ko kuma ya da da mahaifinsa
Ko dan uwa da dan uwa, ko miji da mata
Yace dole sai wani ya kashe daya sannan ya shanye jinin
Shi kuwa ya zauna yayita kyalkyala dariya
Bisa dole wannan mummunar dabi'a ta dinga shiga cikin zukatan mutane
Har ya zamana cewa suma babu abinda suke sha'awa sama da suga jini yana yawo akan turbaya

Alokacin da giyar zalunci take dibarsa ne yaga mabiya wannan addinin marasa yawa sune kadai suka ki karbar wannan mummunar al'ada tasa kuma suka ki su bauta masa
Sai ya fara shirin yakarsu, watarana sai yayi karo da wani babban malaminsu kuma jarumin gaske
ana kiransa da suna hasanul basari bin maharaz

Suka fafata dashi daga baya ya hallaka shi boka sahibul ukuba din
Tun daga wannan lokaci aka huta da bakin zaluncin sa
Amma kuma duk da haka mutane suna kwaikwayon
Irin rashin imaninsa, har zuwa wannan zamanin da muke ciki
Shi kuwa ruhin boka sahibul ukuba tun daga sanda ya mutu ya koma kan wani tsauni ya zauna
Cikin wani kasurgumin daji
Mai cike da bakaken aljanu marasa imani ya cigaba da zama acan
Domin tun sanda yake raye ya taba yin binciken cewa
Bayan mutuwar sa da shekaru masu yawa za'a haifi wasu
Tagwayen jarirai masu matukar jarumtaka wadanda zasuyi shura acikin duniya
To duk sanda wadannan jarumai suka bayyana ruhinsa
zai iya shiga jikin daya daga cikinsu ya cigaba da gudanar
da rayuwarsa da mulkinsa na zalunci

Ya shugabana to kaji labarin wannan hatsabibin kuma takadirin boka
Yanzu haka ruhinsa yana jikin danka yarima walisu don haka
komai zaiyi ba'a cikin hayyacinsa zaiyi ba
dalilin
dayasa yaki shiga jikin walisa shine ita ya kasance macece shi kuma kaga namijine
Yanzu idan duniya zata taru babu wanda zai iya sanin inda walisu yake
Kuma babu wanda ya isa ya iya tunkararsa da yaki face ya sami nasara akansa
Kuma daga yanzu duniya zata shiga cikin tashin hankali fiye da wanda take ciki yanzu
ZUBAR DA JINI zai kara yawaita a duniya kasa zata rine da jinin bil'adama
Ya shugabana ka sani cewa dukda walisu ya kasance dane shi a gurinka
Idan ta raya masa zai iya zuwa nan fadarka ya kasheka ya kawo karshen mulkinka

Koda boka makassar yazo nan a zancensa sai sarki fadarul munnar yayi tagumi yana nazari na dan tsawon lokaci
Sannan ya dago kai ya dubeshi yace
Lallai akwai gagarumin tashin hankali agaba wanda zai haddasa zubar da jini
A duniya kuma bai kamata a ku tsaya mu zuba ido wannan abu ya faru ba
Dolene mu mike tsaye muyi maganin wannan bala'in domin zai addabi duniya ne baki dayanta
Idan har mukayi sakaci da wannan al'amari zaizo daga baya muma ya addabe mu

Shin yanzu amatsayin ku na manyan bokaye ta wacce
hanya kuke ganin zamu tunkari wannan bala'i?
Kodajin wannan tambaya sai boka makassar ya girgida kansa
Kamar ba zai ce komaiba daga can kuma yace
Hanya dayace kawai zamubi domin mu hana wannan bala'in tasiri
Hanyar kuwa itace dolene mu tashi 'yar uwarsa gimbiya walisa tayi kyakykyawan shiri ta fita farautarsa itama
Domin bincike ya nuna cewa duk duniya itace zata iya tunkararsa da yaki kasancewar karfin damtsensu daya ma'ana ita dashi kar ta san kar ne
Banbancin su kawai shine karfin sihiri
Domin hana shi ai watar da zaluncinsa har zuwa sanda zai sami lafiya ya rabu da wannan matsalar fatalwa

Ya shugabana ka sani cewa bamu da wani zabi face yin hakan
A koda yaushe zai dinga farwa manyan birane da kanana yana kashe mutane
Maza da mata yara da tsofaffi kuma babu yarda zasu iya dashi domin karfinsa na musamman ne
Koda duniya zasu taru basu isa su iya hanashi aiwatar da abinda yayi niyya ba
Saidai kasancewar gimbiya walisa zata hanashi yin tasiri
Babu wanda yasan inda zai fara zuwa kamar yadda babu wanda yasan inda yake a halin yanzu

Dajin haka sai sarki fadarul munnar ya girgiza kansa yayi
shiru kamar an aiko masa da sakon mutuwa kwallar bakin ciki ta zubo daga idanunsa
sannan yace
Lallai duk mai rai zai dinga ganin kazantar duniya kala kala tareda abubuwan al'ajabi
Wannan wanne irin tashin hankali ne
Wai ace dan uwa zai fita duniya takanas domin farautar dan uwansa
Lallai mai rai baya rabuwa da ganin abubuwan al'ajabi
Wannan al'amari ba karami bane
Don haka yanzu yanzu za'a kirawo gimbiya walisa domin tasan
wannan al'amari kuma tayi shiri Yana gama fadar haka sai
ya kira sarkin gida ya tura shi yaje turakar gimbiya walisa ya kirawota
Da isowarta
Sarki ya kwashe labarin duk abinda ya faru da kuma hukuncin da suka yanke ya fada mata

Koda gama jin wannan al'amari saita faa she da kuka sannan...


Read / Download ZUBAR DA JINI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album