Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

+++++++++++++ZUBAR DA JINI

++++++++++++++ 1 PART A

LBR
++++++++++++++HABIBULLAH KBR

Gaisuwa ta musamman ga ýar uwar mu wato ummu jawaheer
sannan ina tayata murnar auren da tayi sannan allah ya bada zaman lafiya

Jin jina

Ga dukkan makaranta wadanda suke bibiyarmu tun daga farkon littafi kuma suke yi mana comment wadanda bansan adadinsu ba
Mun gode allah ya bar zumunci

A wani zamani can baya mai tsawo daya shude alokacin da
duniya take cikin kuncin rayuwa Saboda gaba daya mutane da
dabbobi kai hatta sarakuna basu da kwanciyar hankali sakamakon yawan yawan zubar da jinin da akeyi a fadin duniya
Saboda ako da yaushe cikin farautar rayuwar juna ake
Wanda yafika karfi ya kashe ka ya kwashe dukiyar daka tara
A wannan zamani mafi yawan mutane jarumai ne kuma matsafa
Domin su kare kansu daga farmakin abokan gaba
Babu abinda
mutane sukafi so awannan zamani sama da suga jini ya gauraya da kasa yana gudu akanta
Namiji kuwa idan bai kasance gawurtaccen mayaki ba bai isa ya auri mace kyakykyawa ba
Face wani yazo har inda yake ya kasheshi ya kwaceta
Kai yaran da suke wannan zamanin a haka suke tasowa
Sai kaga an haifi jarirai guda biyu amma da zarar sun fara wayo sai kaga suna yunkurin kashe junansu
Mutane basu da burin da yafi suga jini yana gudu acikin kwata kamar ruwa
Duk sarkin kuwa da yake da bukatar shakatawa sai kaga ya hada
Rundunar yaki sun farwa wata kasar wacce suka fita karfi da yawan mayaka
Su yaketa sannan su kamo bayi su dawo dasu birninsu
Hakika duk inda lalacewa da rashin imani yakai to wannan zamani ya wuce haka
Acikin wannan zamani ne akayi wata babbar masarauta mai dumbin tarihi
Wacce ta shahara a yawan mayaka da kuma girman kasa
Kuma ubangiji ya azurtasu da tarin arzikin kasa mai dumbin yawa
Ana kiran wannan birni da suna madaril adfam
Birnin madaril adfam ya shahara wajen kasuwanci da saye da sayarwA
Kasancewar shine kadai birnin da zakaje kayi zamanka lafiya ba tareda fargabar 'yan harin sumame ba
Saboda tsananin zaman lafiyar da akeyi a birnin
Ba komai ne ya janyo haka ba face kasancewar sarkin garin adalin gaske ana kiransa da suna fadarul munnar
Kuma fasa taro tunda yake a tarihin jarumtakarsa ba'a taba yankarsa ba afilin daga
Sannan kuma ya tsani zalunci bashi da burin da yafi yaga
Ya kawar da zaluncin da yake faruwa acikin duniya amma ya kasa
har ya zamana girma ya fara kamashi kuma gashi bashi da da ko
guda daya wanda sai gaji karagarsa idan ya mutu
Don haka
wata rana ya tambayi wani amintaccen bokansa kan yadda zai yi duk bukatunsa su biya
Koda jin bukatun sarki fadarul munnar sai bokan ya bushe da dariya sannan
Yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa bukatunka duka zasu biya
Amma ina mai tabbatar maka da cewa ba kaine zaka kawar da zaluncin da akeyi acikin duniyar nan ba
Sai dai tsatsonka bincike ya nuna cewa matarka tana dauke da juna biyu
Nan bada dadewa ba zata haifi 'ya'ya guda biyu to wadannan 'yA'yan ne zasu cika maka burinka

Daga wannan rana sarki fadarul munnar ya zauna jiran ranar haihuwar matarsa wacce ake kira da gimbiya nursiba zata haihu

Ana cikin wannan hali ne wata rana kwatasam sai nakuda ta kama nursiba
Ta haifi ýan tagwaye guda biyu mace da namiji kyawawan gaske
Awannan lokaci sarki fadarul munnar yayi farincikin da bai taba yin kamarsa a tarihin rayuwarsa
Domin saida akayi sati biyu ana shagalin bikin murnar haihuwarsu
Kuma tun aranar da aka haifesu aka soma tsumasu da tsumin tsafi mai matukar karfi don ya zame masu rigakafi
Dukiya kuwa yayita rabar da ita ga talakawa bai san iya adadinta ba
Tun a sannan suka dauki soyayyar duniya suka dorawa wadannan jarirai nasu
Sannan suka rada musu suna walisa da walisu dadin dadawa wadannan jarirai suna matukar kama da iyayen nasu guda biyu kamar an tsaga kara
A duk sanda sarki zaije zaman fada taredasu yake zuwa akafadarsa
Wani lokacin ma sai kaga ya goya daya abayansa daya kuma ya rukeshi a hannu
Lokacin da walisa da walisu suka cika shekara biyar sai aka fara koyar dasu ilimin bokanci da kuma salon yaki
Kasancewar su yarane masu hazaka da kaifin kwakwalwa sai kaga duk abinda aka koya musu sun dauka tamkar zanen dutse
Kai saida takai ta kawo shi kansa wanda yake koyar dasu dabarun yaki sun fishi iyawa
Sannan aka mikasu hannun sarkin yakin birnin wanda ake kira da huram
Shi kansa sarkin yaki huram yana matukar mamakin irin kaifin kashin wadannan yara dana kwakwalwarsu
Domin a lokacin ma kowanne daya daga cikinsu yana iya yin aikin da karti ashirin sukeyi
Kuma ba tareda sun jigata ba. Abangaren mutanen gari kuwa
Babu abinda yake burgesu gasu walisa face yadda suka hade kansu kuma suke da matukar tausayi
Sabanin ragowar yaran zamanin
Tun a wadannan shekarun mutanen birnin suka tabbatar da cewa
Nanda wani lokaci zasu zama gwarazan zamani wadanda za'a kara dasu a fannin jarumtaka
Shi kansa sarkin yaki huram watarana da suka kebanta da sarki fadarul munnar acikin turakarsa
Ya fada masa cewa
Zaifi kyau shi da kansa ya horar da su walisa da hannunsa
Domin sai sunfi samun cikakken horon yaki a gurinsa
Da jin haka sai sarki fadarul munnar yayi murmushi sannan yace
Nasan da haka amma ka sani inaso ne sai kashinsu yayi kwari sannan zan fara horar dasu da kaina
Wannan dalilin ne yasa na fara mikasu gurin matemakinka sannan suka dawo gurinka
To kaga idan suka zo hannuna salo na daban zan koya musu

Sirrikan tsafi kuwa a gurin babban bokan birnin suke samu wanda ake kira da suna makassar
Boka makassar ya kasance hatsabibin boka wanda duk nahiyar babu kamarsa
Shine yake koyar dasu ilimin bokanci da sirrikansa
Bayan sun
cika shekara goma sha biyar sai labarin jarumtakarsu ya shiga ko ina acikin duniya kasashe da dama suka kara shakkar tunkarar birnin madaril adfam da yaki
Komai karfin dakaru idan su walisa suka tunkaresu sai sun tarwatsasu
Sannan su kama sarkin su su mikashi wajen mahaifinsu
Atakaice dai sai da suka zama guguwar annoba ko ina ka shiga labarinsu akayi
A ka idar birnin madaril adfam mace batayin mulki saidai namiji
Amma hakan baisa sarki fadarul munnar yana nuna banbanci ba atsakanin 'yaýansa
Wannan dalilin ne yasa suka shaku da junansu ko kadan basa taba rabuwa da juna

Ana cikin wannan hali ne wata rana aka wayi gari babu yarima walisu acikin birnin
Wannan al'amari ne yayi matukar razana sarki fadarul munnar
da gimbiya walisa da mahaifiyarsu
Babu inda ba jeba acikin birnin da makotansa ko za'a ga yarima
walisu amma sama da kasa ba'a ganshi ko an sami labarin wanda ya ganshi ba
Wannan al'amari ba karamin tayar da hankalin mutanen birnin madaril adfam yayi ba
Domin tunda ya taso a rayuwarsa bai taba zuwa wani gurinba face da izinin iyayensa ba
Babu wanda hankalinsa ya tashi fiye dana kowa face 'yar uwarsa gimbiya walisa
Domin tasan ita bata da ikon mulkar birnin madaril adfam sai shi
Tunda ita mace ce don haka shi kadaine yake da ikon gadon karagar birninsu
Sai da aka kwana biyu ana binkice a cikin nahiyar kuma aka baza hotunansa
Sannan aka saka kudi mai tsoka kan cewa duk wanda ya fadi inda yake za'a bashi su
Amma duk da haka ba'a sami wani gamsashshen labari ba
Shi kansa boka makassar babu irin binciken da bayyi ba don gano inda yarima walisu yake amma ya kasa
Wannan dalilin ne yasa aka tara manyan bokayen da suke nahiyar guri guda domin su hada karfi da karfe su gano inda yake
Wannan taron kuwa anyi shi ne a fadar sarki fadarul munnar
Bayan kowa ya gama hallara sai sarki fadarul munnar ya tashi ya fara jawabi kamar haka

Yaku manyan dirakun wannan nahiya dukkanku kunsan babban bala'in daya taso mini acikin wadannan kwanaki
Na batan magaji na wannan birnin wato dana walisu
Babu irin binciken da bamuyi ba domin gano inda yake amma mun kasa sani
Adalilin hakane yasa na taraku gaba daya domin yin shi wannan aikin
Inada tabbacin cewa idan kuka hada karfi da karfe zaku samo mana mafita akan wannan al'amari
Idan kuwa har kukayi wannan aiki zan baku dukiya mai dumbin yawa
Domin kowa acikin ku akwai irin baiwar da yake da ita
Da wannan kalami nake umartarku daku fara yin wannan gagarin aiki
Yana gama fadar haka yayi shiru da bakinsa ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya
Nantake duk bokayen suka dukufa suka fara bincike mai zurfi
Saida kowannensu ya jike sharkaf da gumi kamar an watsa musu ruwa
Jikinsu kuwa ya soma rawar dari, idanunsu sukayi jazur
Fadar kuwa tayi tsit kamar babu mai rai acikinta har suka shafe dakiku masu yawa
Sannan dukkansu suka dago da kansu jikinsu a sanyaye
Suka dubi mai gidansu boka makassar
Shi kuma ya kalli sarki fadarul munnar jikinsa duk yayi sanyi sannan yace
Ya shugabana dole saidai kayi hakuri da danka yarima walisu
Domin yanzu haka bama musan inda yake ba
Saidai bincike ya nuna mana cewa yana raye acikin duniya
Yanzu haka ruhin wani hatsabibin boka ne ya shigeshi wanda ya shafe shekaru masu daruruwa da mutuwa
Shidai wannan boka tunda aka halicci duniya ba'ataba samun
Shu'umin matsafi ba kamarsa domin yana iya yin tsafin da zai janyo hallakar birane da dama a cikin abinda bai wuce dakika guda ba
Kuma yana iya samar da hasken rana acikin tsakiyar dare
Kuma tunda yafara sabgar tsafinsa bai taba taka kasa ba ko kwanciya da zama akanta ba
Sai dai akan iska
Kuma duk inda yake da burin zuwa saidai kawai kaga ya
bayyana agurin koda kuwa tafiyar takai tsawon tafiyar shekara dubu
Ana kiransa da suna sahibul ukub
Azamaninsa saida takai ga cewa mafi yawan kasahen duniya da sarakuna shi suke bautawa amatsayin abin bautarsu
Saidai wasu kebantattun mutane mabiya wani addini wadanda basu da yawa acikin duniya
Babban burinsa a duniya shine ganin ya mayar da ita ta koma rayuwar ZUBAR DA JINI
Sannan yaga teku ta rine da jinin bil'adama
Kuma ta dole ya dinga tilastawa mutane suna yakar masoyansu suna kashesu da hannayensu
Ko kuma ya da da mahaifinsa
Ko dan uwa da dan uwa, ko miji da mata
Yace dole sai wani ya kashe daya sannan ya shanye jinin
Shi kuwa ya zauna yayita kyalkyala dariya
Bisa dole wannan mummunar dabi'a ta dinga shiga cikin zukatan mutane
Har ya zamana cewa suma babu abinda suke sha'awa sama da suga jini yana yawo akan turbaya

Alokacin da giyar zalunci take dibarsa ne yaga mabiya wannan addinin marasa yawa sune kadai suka ki karbar wannan mummunar al'ada tasa kuma suka ki su bauta masa
Sai ya fara shirin yakarsu, watarana sai yayi karo da wani babban malaminsu kuma jarumin gaske
ana kiransa da suna hasanul basari bin maharaz

Suka fafata dashi daga baya ya hallaka shi boka sahibul ukuba din
Tun daga wannan lokaci aka huta da bakin zaluncin sa
Amma kuma duk da haka mutane suna kwaikwayon
Irin rashin imaninsa, har zuwa wannan zamanin da muke ciki
Shi kuwa ruhin boka sahibul ukuba tun daga sanda ya mutu ya koma kan wani tsauni ya zauna
Cikin wani kasurgumin daji
Mai cike da bakaken aljanu marasa imani ya cigaba da zama acan
Domin tun sanda yake raye ya taba yin binciken cewa
Bayan mutuwar sa da shekaru masu yawa za'a haifi wasu
Tagwayen jarirai masu matukar jarumtaka wadanda zasuyi shura acikin duniya
To duk sanda wadannan jarumai suka bayyana ruhinsa
zai iya shiga jikin daya daga cikinsu ya cigaba da gudanar
da rayuwarsa da mulkinsa na zalunci

Ya shugabana to kaji labarin wannan hatsabibin kuma takadirin boka
Yanzu haka ruhinsa yana jikin danka yarima walisu don haka
komai zaiyi ba'a cikin hayyacinsa zaiyi ba
dalilin
dayasa yaki shiga jikin walisa shine ita ya kasance macece shi kuma kaga namijine
Yanzu idan duniya zata taru babu wanda zai iya sanin inda walisu yake
Kuma babu wanda ya isa ya iya tunkararsa da yaki face ya sami nasara akansa
Kuma daga yanzu duniya zata shiga cikin tashin hankali fiye da wanda take ciki yanzu
ZUBAR DA JINI zai kara yawaita a duniya kasa zata rine da jinin bil'adama
Ya shugabana ka sani cewa dukda walisu ya kasance dane shi a gurinka
Idan ta raya masa zai iya zuwa nan fadarka ya kasheka ya kawo karshen mulkinka

Koda boka makassar yazo nan a zancensa sai sarki fadarul munnar yayi tagumi yana nazari na dan tsawon lokaci
Sannan ya dago kai ya dubeshi yace
Lallai akwai gagarumin tashin hankali agaba wanda zai haddasa zubar da jini
A duniya kuma bai kamata a ku tsaya mu zuba ido wannan abu ya faru ba
Dolene mu mike tsaye muyi maganin wannan bala'in domin zai addabi duniya ne baki dayanta
Idan har mukayi sakaci da wannan al'amari zaizo daga baya muma ya addabe mu

Shin yanzu amatsayin ku na manyan bokaye ta wacce
hanya kuke ganin zamu tunkari wannan bala'i?
Kodajin wannan tambaya sai boka makassar ya girgida kansa
Kamar ba zai ce komaiba daga can kuma yace
Hanya dayace kawai zamubi domin mu hana wannan bala'in tasiri
Hanyar kuwa itace dolene mu tashi 'yar uwarsa gimbiya walisa tayi kyakykyawan shiri ta fita farautarsa itama
Domin bincike ya nuna cewa duk duniya itace zata iya tunkararsa da yaki kasancewar karfin damtsensu daya ma'ana ita dashi kar ta san kar ne
Banbancin su kawai shine karfin sihiri
Domin hana shi ai watar da zaluncinsa har zuwa sanda zai sami lafiya ya rabu da wannan matsalar fatalwa

Ya shugabana ka sani cewa bamu da wani zabi face yin hakan
A koda yaushe zai dinga farwa manyan birane da kanana yana kashe mutane
Maza da mata yara da tsofaffi kuma babu yarda zasu iya dashi domin karfinsa na musamman ne
Koda duniya zasu taru basu isa su iya hanashi aiwatar da abinda yayi niyya ba
Saidai kasancewar gimbiya walisa zata hanashi yin tasiri
Babu wanda yasan inda zai fara zuwa kamar yadda babu wanda yasan inda yake a halin yanzu

Dajin haka sai sarki fadarul munnar ya girgiza kansa yayi
shiru kamar an aiko masa da sakon mutuwa kwallar bakin ciki ta zubo daga idanunsa
sannan yace
Lallai duk mai rai zai dinga ganin kazantar duniya kala kala tareda abubuwan al'ajabi
Wannan wanne irin tashin hankali ne
Wai ace dan uwa zai fita duniya takanas domin farautar dan uwansa
Lallai mai rai baya rabuwa da ganin abubuwan al'ajabi
Wannan al'amari ba karami bane
Don haka yanzu yanzu za'a kirawo gimbiya walisa domin tasan
wannan al'amari kuma tayi shiri Yana gama fadar haka sai
ya kira sarkin gida ya tura shi yaje turakar gimbiya walisa ya kirawota
Da isowarta
Sarki ya kwashe labarin duk abinda ya faru da kuma hukuncin da suka yanke ya fada mata

Koda gama jin wannan al'amari saita faa she da kuka sannan
ta fice daga cikin fadar ta nufi turakar mahaifiyarsu ta kwashe labarin komai ta fada mata
Dajin wannan mummunan labari sai nan take gimbiya nursiba
Ta fadi kasa sumammiya
ME ZAI FARU NAN GABA
SHIN WALISA ZATA AMINCE DA WANNAN TAFIYAR?
MU HADU A KASHI NA GABA DAGA
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++++++1 PART B

LBR
+++++++++++++++HABIBULLAH KBR

Take gimbiya walisa ta rusa uban ihu karar ihun nata ne
Ya amsa kuwwa har zuwa can cikin fada cikin sauri sarki fadarul munnar
Ya falfalo da azababben gudu cikin turakar
Da zuwa sai ya debi ruwa ya yayyafawa gimbiya nursiba
Take kuwa ta farfado daga suman da tayi tanamai ajiyar dogon numfashi
Ta kalli sarki fadarul munnar tace
Shin da gaske ne yanzu shi kenan na rabu da dana walisu?
Kan sarki fadarul munnar a kasa yace kwarai kuwa abinda walisa ta fada miki gaskiyane
Babu yadda zamu iya akan wannan al'amari face mu hakura mu tura 'yar uwarsa
Ta bishi cikin duniya domin nemansa ta wannan hanyace kadai zamu iya samu mu dawo da dan mu zuwa garemu
Idan ba haka ba kuwa mu dashi har abada domin bazai taba yarda cewa
Mu iyayensa ne ba kuma duk sanda ta raya masa zai iya dawowa nan birnin mu ya yake mu
Kuma bamu da abinda zamu iya yi masa awannan lokaci
Koda jin haka sai nan take hankalin gimbiya walisa ya tashi tashiga tunani a cikin zuciyarta
Bata san sanda zancen zuci ya fito fili ba tace
Yanzu shikenan ni da dan uwana mun zama abokan gaba da samu dinga farautar juna ?
Shakka babu dolene ki aikata haka domin ceton miliyoyin rayuka daga hallaka
Idan kuwa kika ki to tabbas zanyi nadamar haihuwarki
Domin burina kawai shine ganin an sami zaman lafiya a duniya an daina ZUBAR DA JININ da akeyi
Ina mai umartarki da ki kasance cikin shirin wannan tafiya kisa aranki cewa zaki ceto dubban rayuka ne daga hallaka
Yana gama fadin haka sai ya juya ya nufi hanyar zuwa fada yanayi mata nuni data biyo bayansa
Nantake kuwa ya bishi abaya har suka isa cikin fada duk inda suka gifta dakarune suke rissinawa suna gaishesu
Da isowarsu cikin fada sai suka sami guri suka zauna
Sarki fadarul munnar yayi gyaran murya sannan yace
Yaku wadannan bokaye duk naji irin bayanin da kukayi
Kuma na gamsu dashi sosai amma inaso idan akwai
wani taimako da zaku iya yiwa walisa to inaso kuyi matashi yanzu
Koda sukaji abinda sarki fadarul munnar ya fada sai duk suka tsaya suna nazari
Daga can sai dukkansu suka hadu waje daya suka tattara hannayensu
Suna masu karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya
Saiga wani irin karanin dutse ya bayyana a tsakiyar hannunsu
Shidai wannan dutse girmansa baifi tafin hannu ba
Sannan wani irin shudin haske yana tashi daga jikinsa
Boka makassar ya tashi da kafafunsa yazo gaban gimbiya walisa ya mika
Mata wannan dutse sannan yace wannan dutsen zai taimaka miki sosai acikin wannan tafiya
Duk sanda kikaga wannan shudin haske ya juye zuwa ja
To tabbas akwai wani bala'i da yake shirin faruwa a wannan yankin
A yanzu kuma kinga babu bala'in daya fi na dan uwanki a wannan duniya
Karki kuskura ki rabu da wannan dutse koda yaushe ya kasance ajikinki
Koda kuwa barci zakiyi domin yana daga cikin abubuwan da zasu taimaka miki
Cikin sauri takarbi wannan dutse ta sakashi acikin aljihu ta ajiye
Sannan sarki fadarul munnar ya debi dukiya mai yawa ya baiwa wadannan bokaye
Ya sallame su suka kama hanya suka tafi kowa ya shiga sabgarsa
Kai tsaye sarki fadarul munnar da gimbiya walisa suka koma cikin gidan sarauta hanyar da zata kaika dakin sarki
Koda suka kusa zuwa kofar dakin sai suka yi arba da gimbiya nursiba
Atsaye a bakin kofar idanunta cike da kwalla
Take tazo ta rungume walisa sannan tace
Zanyi kewarki yake 'yata zanso ki dawo wannan birni namu a raye
Daga wannan farautar mutuwar da zaki fita
Kodajin haka sai walisa ta janye jikinta daga na mahaifiyarta tace
Haba ummi na bai kamata ki fidda rai dani ba ki sa aranki cewa dole zan dawo wannan birni
Kuma inayi miki alkawarin bazan dawo ba sai tareda dan uwana yarima walisu
Domin shine babban burin mahaifina tunda shine yake da gadonsa bani ba
Dajin haka sai kwalla ta zubowa sarki fadarul munnar
Take yaji tausayin gimbiya walisa ya kamashi don haka sai
Kawai ya bude kofar turakarsa ya shiga
Ashe suma sun kula da wannan hawayen daya zubo daga idonsa
Cikin sauri suka biyoshi abaya sannan walisa tace
Ya abbana kayi hakuri idan maganar dana fada ta bata maka rai
Ka sani cewa ban fada bane domin nufin cutar dakai ba
Cikin murmushi ya dubeta yace.
Yake 'yata ko kadan baki bata mini raiba saidai tausayi
Da kika bani na ganin cewa baki da gadon karagata
Nima bani da yadda zanyi akan haka domin haka ka'idar mulkin birnin mu yake
Da ace ki namiji ce to da tabbas kece zaki gaji kujerar mulki na
Yana gama fadar haka sai yaje ya dauko wata akwati acan kasan gadonsa
Ya budeta sai gashi ya zaro wani irin bakin sulke mai kaurin gaske
Tareda wata iriyar takobi itama baka kamar yadda sulken yake
Ya taho zuwaga walisa ya mika mata wadannan kayan sannan yace
Ga wadannan kaysn ki rikesu a hannunki zasuyi miki amfani sosai acikin wannan tafiya
Nima na gajesu ne awajen mahaifina kuma nima yanzu na mallaka miki su
Daga yau har zuwa sanda zaki dawo
Nantake walisa ta karbi wadannan kayan ta saka ajikinta
Sannan ta nade gashinta guri daya ta saukeshi ya zuba akan kafadunta
Ta juyo ta rungume mahaifiyarta
Nan dai sukayi bankwana da juna ta juya ta fice daga cikin turakar tana waiwayen mahaifiyarta
Shikuwa sarki fadarul munnar sai ya biyota abaya yana rakata
Sannan yana kara karfafa mata gwuiwa akan aikin dake gabanta


Please Login or Register in order to submit comment