Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shekawa barzahu, don haka lokaci yayi da nima zan saka muku akan abinda kukayi mini
Dajin wannan batu sai ta gyada kai sannan ta kwashe labarin komai ta bayyana masa Dakuma taimakon da takeso yayi mata
Kodajin wannan labari sai ya kame kam kamar gunki yana mai yin tunani acikin ransa
Daga can kuma sai ya ajiye gwauron numfashi yace
Lallai duniya abar tsoro ce, kuma ina matukar tausaya miki ke da mahaifinki
Kuma nayi miki alkawarin zan baki mazaunin da zaki zauna har zuwa
Sanda zaki bar wannan birni, sannan zan ruke miki wannan yaro amana,
Yana gama fadin haka sai ya kwallawa wasu kuyanginsa kira
Take kuwa sukazo gabansa suka russina ya dubesu yace
Inaso ku raka wannan bakuwar tawa zuwa dakin saukar baki na musamman
Sannan shi kuma wannan yaron ku kaishi can dakin da ýaýana suke kwana
Domin shima yanzu ya zama dana babu banbanci atsakaninsa dasu
Bayan haka inaso ku kai musu abinci mai kyau kuma isashshe
Wanda zai ishesu gaba daya
Kodajin wannan umarni sai dukkansu suka ce munji wannan umarni naka
Take suka tashi sukayiwa su walisa jagora zuwa can dakunan da aka umarcesu dasu kaisu
Bayan 'yan dakiku kadan aka kai kowa masukinsa
Dakin da aka ajiye walisa
Daki ne madaidai ci, wandake dauke da gado da dukkan kayan kawa acikinsa
Sannan kuma agefensa akwai bandaki wanda mutum zai shiga domin biyan bukatarsa

MAI ZAI FARU ACIKIN WANNAN BIRNI DA WALISA TA YADA ZANGO ACIKINSA
SHIN ZATA SHIGA GASAR JARUMTAKAR DA ZA'A GUDA NAR ACIKIN BIRNIN KO KUMA BA ZATA SHIGA BA
SHIN WAYE ZAI LASHE NASARAR WANNAN GASAR JARUMTAKAR TSAKANIN SARKI ARYAN DA KUMA JARUMAN GASAR?
DON JIN AMSOSHIN WANNAN TAMBAYA SAI MU HADU A LITTAFI NA 3
DON JIN KARASHEN WANNAN LITTAFI DAGA NI
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT++++++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++3 PART A

LBR

++++++++++++ HABIBULLAH KBR

Atakaice dai wannan daki an kawatashi daidai na rayuwar ka wanda bazaka takura ba acikinsa
Dukda dai bai kai dakinta ba, ba tareda bata lokaci ba
Ta shiga cikin bandaki tayi wanka domin ta huce gajiyar da take jikinta
Bayan ta fito ne taga tuni anzo an ajiyemata abinci mai mai da lafiya
Ba tareda bata lokaci ba ta zauna ta fara cin abincin cikin kwanciyar hankali ba tareda fargabar komai ba
Bata gama cin abincin ba taji ta fara jin barci sosai, don haka sai ta
Kwanta akan gadon da yake dakin domin yin barci aikuwa
Bata dade da kwanciya ba sai barci mai nauyi ya sace ta
Acikin barcin ne tayi mafarki da wani matashin saurayi
mai cikakkiyar kamala fuskarsa tana wani irin sheki da kyalkyaki kayan jikinsa kuwa duk farare ne
Ya nufo inda take hannunsa ruke da wata farar sanda ajikinta anyi wani irin rubutu wanda bata iya gane abinda aka rubuta ajikinta domin wani irin yare ne na daban wanda batama san sunansa ba
Kallo daya zakayi masa ka tabbatar da cewa gwarzon mayaki ne kuma namijin duniya
A saman kansa kuwa wasu fareren balbelu ne suke binsa
Duk inda yabi abin dai abin ban sha'awa, a hankali matashin saurayin yazo Inda take tare da yi mata murmushi
Her ta bude baki zatayi magana sai taji yace da ita
Yake gimbiya walisa ki sani aikin da kika daukowa kanki aikine mai matukar wahala
Kuma acikin wannan birnin da kike zaki fuskanci wani babban kalubale
Wanda har sai kinyi yaki da zuciyarki, sannan zaki sami nasarar abinda kika fito nema
Amma ina mai shawartarki daki kara zage damtse akan aikin dake gabanki
Ina tabbatar miki zaki sami nasara amma dolene sai kin cika wani sharadi
Cikin mamaki walisa tace dashi wanne irin sharadi ne wannan?
Saurayin yace
Zan sanar dake wannan sharadin idan lokacin hakan yayi
Amma yanzu zanyi miki taimako guda daya akan ciwon kunar da yake bayanki
Take taga ya taho gurin da take sannan ya runtse idanunsa
Tare dayin wani karatu sannan ya tofa mata agadon bayanta
Yin hakan keda wuya sai ta sa hannunta agadon bayan nata
Ko zataji wannan kunar amma bisa mamaki sai taji babu komai agadon bayanta ma'ana kunar wutar ta warke sumul
Cikin mamaki ta juyo ta dubi wannan saurayin tace kai wanene
Kuma me kake takama dashi? Tabbas wannan sihirin naka mai karfine
Kodajin haka sai saurayin yayi murmushi wanda ya kara fito da tsantsar kyawunsa
Yace mata ni bana tsafi kuma ban yarda dashi ba
Dangane da sanin ko waneneni kuwa da kike son sani
To nine………
Adaidai wannan lokacin ne taji ana hayaniyar mutane tana tashi
a kasan tagar da take kusa da gadon da take kwance
Hayaniyar ce ta zama silar farkawarta daga barcin da takeyi ba tare da taji sunan saurayinba

Tana farkawa daga barcin cikin sauri ta sanya hannunta ta shafo inda ciwon yake
Take kuwa taji gaba daya babu ciwon ajikinta amma duk da haka bata yarda ba
Sai da taje jikin madubi kasancewar akwai hasken farin wata
Ta duba bayan nata aikuwa saita cika da mamaki domin ko tabon kunar bata gani ba ajikinta
Take ta cika da tsananin mamaki fiye da farko akan wannan al'amari
Domin ki a tarihi bata taba jin labari kwatankwacin wannan ba
Amma sai ta bar zancen a zuciyarta ta dawo bakin taga domin taga abinda yake faruwa acikin birnin
Koda lekawarta sai tayi arba da jama'a suna gudanar da shirye shiryen wannan gasa kamar da rana
Ba komai bane ya haddasa haka ba face acikin daren ne
Sarki yasa akayi sanarwa cewa washe gari da safe za'a fara gudanar da wannan gasa
Wannan shine dalilin dayasa kowa ya katse barcinsa suka cigaba da baiwa kansu horon yaki
Saboda kawai kwadayin wannan dukiyar da zasu samu idan suka ci wannan gasar
Koda ganin wannan al'amari dai kawai tayi tsaki tace
Aikin banza yanzu kawai saboda dukiya suketa wahalar da kansu kan abinda basu da tabbacin samun nasara acikinsa
Abinda ta manta shine babu wanda yake da tabbas akan abinda zai faru dashi arayuwarsa
Kuma babu wanda yake da ikon canja kaddararsa, shiyasa ake cewa
Mai rabon shan duka sai ya sha, kuma nasara tana tare da mai nema
Haka dai walisa ta koma kan gadonta da nufin kwanciya barci
Amma sai taji ta kasa, domin hoton fuskar wannan bakon jarumin ce kawai takeyi mata yawo akan idanunta
Da kuma irin maganganun daya fada mata masu ratsa zuciya
Take ta tambayi kanta shin me yake nufi da wadannan kalamai nasa? Kuma wanene shi
Amsar data kasa baiwa kanta kenan,
Don haka saita rusa uban ihu har tasa hannu ta naushi ginin da yake kusa da ita
Saboda karfin naushin saida ginin ya huje hannunta ya fito waje ta baya
Hakadai jaruma walisa ta cigaba da zama tanata tunani kan abubuwan da suka faru acikin barcinta
Har safiya tayi
Sannan ta tashi ta shiga bandaki ta sake sabon wanka
Kafin ta fito daga wankan har anzo an ajiye mata abinci da abin sha,
Ba tareda bata lokaci ba kuwa ta zauna taci abincin dan kadan
Sannan taje ta dauki kayanta na yaki ta sanya ajikinta
Ta fito falon gidan, tana fitowa sai tayi arba da sarkin kasuwa yimana
Tareda yaro zaljus koda zaljus ta hango ta tana tahowa
Sai shima ya taho da gudun gaske ya rungume ta suka jera
tare suka sami kujeru suka zauna sannan suka gaggaisa
Zamansu keda wuya sai yimana yace da ita, yake wannan jaruma
Amma dai jiya da daddare kinji sanarwar cewa yaune za'a fara gudanar da gasar jarumta ko?
Kodajin haka sai take ta tuna da abin daya faru acikin barcinta
Don haka saita kwashe labarin komai ta fada masa sannan ta tambayeshi
Ko ya san fassarar wannan mafarki nata
Kodajin wannan labari sai kawai ya girgiza kansa yana dan tunani
Daga can ya kalleta yace
Yake wannan jaruma tabbas acikin acikin wannan mafarki naki akwai babban abin al'ajabi
Domin bantaba ganin aikin da akayi a cikin mafarki ba kuma ya faru agaske ba sai wannan
Don haka nake shawartarki daki yi taka tsantsan acikin wannan tafiyar taki kada ki yarda wani abu yazo ya rusa miki duk shirin da kika dade kina tanadi akansa
Daga yau har zuwa sanda zaki kammala shi
Saidai a yadda kika siffanta mini wannan jarumi inada kyakyawan zaton cewa
Dolene shima ya kasance sadaukin gaske kuma gagara badau ko kuma ince dodon maza kamar dai yadda
Iyayena suka taba bani labarin wani hamshakin sadauki
kuma jarumin jarumai, ko kuma ince dashi dodon maza,
wasu kuma suke yi masa kirari da fasa taro, abangaren talakawa kuwa suna yi masa lakabi ne da dodon azzalumai
Sarakuna kuwa suna kiransa da murucin kan dutse wanda bai fito ba sai daya shirya
Alokacin da sadauki hasanul basari yake raye yayi jarumtakar da har duniya ta nade baza'a taba mantawa dashi ba
Domin saidaya rikirkita gabaki daya azzaluman sarakuna da bokaye na zamaninsa
Dajin wadannan kalamai sai walisa ta dubi yimana tace
Dama kasan tarihin wannan gwarzon mayakin. Naji sunansa abakin iyayena alokacin da zan rabu dasu naji har suna cewa shine
Sadaukin mayakin daya kashe boka sahibul ukub a wancan zamanin
Lokacin da sahibul ukub ya addabi duniya da bakin zalunsa
Kuma naji ance tsafi baya tasiri ajikinsa kuma duk abindaya sanya agabansa
Sai yayi nasara acikinsa wannan dalili ne yasa har ya mutu
Ba'a sami gawarsa ba, kuma babu irin binciken da matsafa basuyi ba
Domin su gano inda gawarsa ta boye da kuma tarihinsa
Amma abu ya gagara domin da suka matsa ayin binciken sai da madubin tsafin nasu
Suka dinga fashewa ,bisa dole suka hakura,
Amma kai kuwa ya akayi kasan tarihin jarumtarsa? Dajin wannan tambaya sai yimana yayi murmushi sannan yace
Kadafa ki manta ni asalin bafatake ne, kuma na gaji wannan sana'ane agurin mahaifina
Tun ina yaro, a wannan lokacin ne wata rana mun tafi yawon fatauci mukazo giftawa ta birnin misra
Bayan mun shiga cikin birnin ne muka kama shago acikin kasuwa
Muka baza hajar mu, muna cin kasuwa, kawai sai muka hango wadansu matasan yara guda biyu
'Yan kimanin shekaru 15 dauke da wata akwati sun gifta ta inda muke
Har sun wuce sai kuma suka dawo babban ya dubi mahaifina yace masa
Kaine shugaban wannan tawaga, sai mahaifina ya amsa masa da eh
Sai kawai yaron ya miko masa wannan akwatin yace da mahaifina
Mahaifin mu ne ya rasu kuma days mutu bai bar mana gadon komai ba sai na wannan akwatin
Yace damu mu sayar dashi ga mutumin kirki, wanda zai saye shi ba tareda ya zalunce mu,
Kuma yace kudin wannan akwatin zai isheni rayuwa dani da ýar uwata
Koda jin haka sai mahaifina ya mika hannu ya karbi akwatin
Sannan ya budeta
Koda ganin abindaya ke ciki sai mutane suka fara yiwa matasan dariya
Sai da mahaifina ya daka musu tsawa sannan suka daina
Kawai sai ya zura hannunsa ya dauko wannan littafin
Koda daukoshi sai ya kame kyam atsaye sakamakon ganin rubutun da akayi ajikinsa
Ba komai aka rubuta ba face
HIKAYAR SADAUKI HASANUL BASARI
anyi rubutun ne da bakin alakalami, cikin tsananin mamaki
Mahaifina yace dasu shin wanene mahaifin naku? Wanda ya iya rubuta wannan babban tarihi haka?
Dajin wannan tambaya sai macen tace mahaifin mu shine
Habibullah kbr, bai kasance komai a wannan garinba face talaka
Wannan shine dalilin dayasa ya bata rayuwarsa wajen binciko tarihin wannan namijin duniya ya rubuta kuma yanzu haka shi kadaine yake da wannan
kundun tarihi kuma yayi mana alkawarin
Indai muka sayar da shi zamu sami abinda zai ishemu gudanar da rayuwarmu
Kodajin haka sai nan take mahaifina ya kirgo dinare masu yawan gaske ya mika musu
Suka karba suna murna, amma mai makon mahaifina ya sayar da wannan littafi don ya sami riba sai yaki
Kawai sai ya ajiye shi a cikin dakinsa yake zama kullum
yana karanta shi don ya debe masa kewa Saboda labarin
Ni kaina nayi matukar mamakin dalilin daya hanashi sayar da wannan littafi
akwai tsantsar abin al'ajabi da jarumtaka gami da soyayya acikinsa
Kuma har sanda ya mutu bai daina karanta littafinba aduk sanda yake bukatar debe kewa
Bayan ya mutu ne nima na gaji wannan littafi
Kuma nima na zauna na karantashi daga farko har karshe
Sai a sannan ne nasan dalilin daya hanashi sayar da littafin
koda jin wannan labari sai tace dashi
Yakai yimana ina neman alfarmar idan kana da lokaci ka bani tarihin wannan sadaukin duniya idan bazaka damuba
Dajin haka sai yayi dariya sannan yace
Ai wannan labarine mai matukar yawa da kuma dadin gaske
Amma zanyi kokari na takaice miki wannan labari kafin
lokacin fara gasa yayi idan kuma har lokaci yayi to zamu
tsayar da wannan labarin mu tafi kallon wannan gasar jarumta
domin bazan iya hakura da kallon wannan gumurzun mazan ba
Yana gama fadin haka sai yayi gyaran murya sannan ya fara labari kamar haka

0=======(::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::>

A wani zamani can baya mai tsawo daya shude acan nahiyar larabawa
Anyi wata babbar kasa mai suna fasawana, birnin fasawana ya kunshi manyan birane wadanda suke karkashinsa
Sarkin da yake mulkin wannan babban birni adalin gaskene ana kiransa da suna mayasin kuma sadauki uban sadaukai
Sarki mayasin yana da ýa guda daya wacce ta kasance kyakkyawar gaske
Da duk nahiyar babu mai kyawunta, wasuma suna hasashen cewa
Ba mutum bace ba ita, wasu kuma suna cewa wai ýar abin bautarsu ce
Shiyasa ya halicceta da kyawun dayafi na dukkan matan wannan karni
Ana kiranta da suna gimbiya bahjaht, ko kadan gimbiya bahjaht bata kasance jaruma ba sabanin mahaifinta
Amma duk da haka mahaifinta yana matukar kaunarta fiye da yadda yake kaunar kansa
Hatta bacci baya iyawa sai yaje cikin turakarta ya tabbatar da lafiyarta kalau
Ýa ýan sarakuna da dama sun nemi aurenta amma taki yarda
Tace ita har yanzu bataga saurayin daya burgeta ba
Domin Ita da kanta takeso ta zabarwa kanta wanda zata aura

Duk da kasancewar birnin fasawana ta kasance babbar
kasa ce kuma ta kunshi kabilu daban daban ,da addinai kala daban daban
Sarki mayasin bai hana kowa gudanar da addininsa ba
Saidai acikin biranen da suke karkashinsa akwai wani
dan karamin kauye wanda adadin mutanen cikinsa basu wuce mutum dari uku ba
Gaba daya mutanen kauyen mafarauta mazansu da matansu wadanda
Suka dogara da sana'ar farauta, ana kiran jama'ar wannan kauye da suna banu sudais
Kuma suna kan bin turbar addinin musulunci ne

Asalin wannan kabila sun kasance basu da tsayayyen gurin zama
Domin suna yawone acikin dajijjika duk inda suka tarar zaiyi
dadin rayuwa sai su yada zango acikinsa na tsawon
kwanaki sannan su tashi su kara gaba Duk sanda sukazo
giftawa ta wani babban birnin sai su wakilta shugabansu
Wani dattijo mai suna maharaz akan ya shiga cikin garin ya
sayar musu da fatun dabbobin da suka tara saboda kowa ya yarda da amanar sa
Maharaz ya kasance yana da da guda daya wanda ya kasance
kyakkyawan da babu irinsa aduk fadin nahiyar kuma sadaukin gaske
Domin tun yana dan shekara shida idan ya fita farauta baya taba dawowa sai ya kamo manyan dabbobin daji irinsu zakuna da dai sauransu kamar guda goma acikin sa'a guda
Idan kuwa ya fara zabga gudu baya taba gajiya har tsawon makonni biyar
Karfin gudunsa kuwa idan yanayi kamar na giftawar tauraruwa mai wutsiya haka yake yinsa
Idan ya saka hannunsa ya naushi dutse dashi saidai kaga dutsen ya dagargaje
Ba tareda shi hannunsa yayi koda kwarzane ba, idan kuwa yana gudu acikin daji mai yawan bishiyoyi saidai kaga yana tsalle. Asamansu kamar wani dan buri
Idan kuwa yayi nutso akasan teku sai ya yini aciki yana iyo ba tareda ya dago kaiba koda sau daya
Kai saboma da wannan baiwa tasa wasu cewa sukeyi shi ba mutum bane aljani ne shi, domin tun yana shiga cikin daji farauta sai suma dabbobin suka firgita da lamarinsa
Ya zamana cewa da zarar sun hangoshi daga nesa ya nufo cikin dajin
Sai nantake kaga sun fara gudun ceton ransu domin suma sun gama firgita da lamarinsa
Bama su kadaiba hatta manyan 'yan fashi da suke suke tare dajijjika Sun san labarinsa
Duk wadannan abubuwa suna faruwa ne tun yana karamin yaro
Lokacin daya cika shekaru ashirin kuwa sai kyawunsa da jarumtakar sa suka ninku fiye da da kuma acikin
wannan shekarun ne Mahafinsa maharaz ya mutu lokacin daya mutu mutane sunyi matukar bakin ciki musamman ma shi hasanul basari
Domin tun tasowarsa mahaifinsa kadai ya sani domin mahaifiyarsa ma ta mutu tun lokacin data haifeshi
Bayan rasuwar maharaz ne sai aka nada shi amatsayin shugaban wannan kabila, aka dora masa duk alhakin kula da kowa
A rayuwarsa gaba daya baisan wata aba wai ita soyayya ba
Domin labarinta kadai yakeji abakin mutane
Kuma 'yan mata da dama sun nemi da yayi soyayya dasu amma bai taba yarda da bukatunsu ba
Ana cikin hakane wata rana bayan kabilar su sun tara fatun dabbobin daji masu yawan gaske

Suka wakiltashi kan ya tashi ya shiga cikin babban birninku wato birnin fasawana don ya sayar musu dasu
SHIN JARUMI HASANUL BASARI ZAI SHIGA BIRNIN SHAWANA?
SHIN WANENE HASANUL BASARI?
YAYA MAGANAR GASAR JARUMTAR DA ZA'A GABATAR A BIRNIN FASAWANA ?
DON SANIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN++++++++++++++++ZUBAR DA JINI

++++++++3 PART B

LBR

+++++++++++++++HABIBULLAH KBR

Take kuwa jarumi hassanul basari ya karbi wannan fatun dabbobin ya kama hanyar sa abinsa
Abinka da wanda ya kasance mai kuzari, cikin azababben gudu
Yake tafiya saboda burin yaje birnin shawana ya dawo da wuri
Cikin lokaci kankani ya isa birnin shawana, ka sancewar kowanne daga cikin su yasan wanene shi hakane yasa basu tsaya tuhumarsa ba suka bude masa kofa ya shiga
Da shigar sa cikin birnin kai tsaye sai ya nufi hanyar da zata kaishi kasuwa
Kasancewar da yawa daga cikin mutanen birnin masu shiga daji farauta duk sun sanshi, kai hardama wadanda basa shiga labarin jarumtakarsa yaje musu harma an sami wasu kwararrun masu zane suna zana taswirar fuskarsa suna sayarwa a cikin kasuwar garin
Aikuwa da shigowarsa cikin birnin sai mutane maza da mata suka dinga fitowa sunata rububin ganinsa
Wasu tsananin kyawunsa ne da sukaji ana fada ne yake burgesu
Wasu kuma sadaukantakarsa da kuma baiwar da yake da itace take basu sha'awa
Kai idan kaga yadda suketa rububin kallonsa awannan lokaci saika dauka cewa dan sarauta ne shi,
Shi kansa saidaya tambayi kansa yace
Wai menene yasa mutane suketa faman kallona ne kamar basu taba ganin mutum ba
Ko kuma kayan da suke jikinane basuyi mini kyau ba?
Wata zuciyar kuma tace dashi kai wata kila kuma soyayya ce tasa suke yi maka haka
Dayin wannan tunani sai yace godiya ta tabbata ga ubangijin daya bani irin wannan farin jinin
.
++++++++++++++++++++++

Acan cikin gidan sarautar shawana kuwa yau gimbiya bahjaht ta tashi cikin tsananin nishadi, da kuma son fita rangadi domin ta zagaya kasuwar garin nasu da kafafunta domin dama ta saba a duk rana irin wannan takan debi dakaru da fita rangadi cikin birnin
Saboda tana matukar jin dadi taganta acikin mutane kowa yanata rububin kallonta kamar zai cinyeta, ta zama tauraruwa guda daya tak acikin dubunnan mutane don haka sai taji girmankai ya shigeta
Don kowa daina kasuwancinsa yakeyi ya taho hanyar da take wucewa domin yaga tsananin kyawunta
Kai wasu ma daga wasu garuruwan suke tahowa saboda yadda labarin kyawunta ya zaga ko'ina acikin nahiyar
Tun da duku dukun safiya ta tashi ta caba kwalliya wata kuyanga tazo ta caba mata kwalliya ta gaban kwatance domin ta dada daukar hankalin mutane
Sannan kuyanginta guda goma suka kawo mata kwanikan abinci kala daban daban
Suka ajiye mata suka fita, fitarsu keda wuya sai wasu kuyangin suma guda goma suka shigo da abubuwan sha kala daban daban sannan suma suka fice daga cikin turakar tata,
Fitarsu keda wuya gimbiya bahjaht ta zauna akan teburan abincin taci dan kadan domin bata fiye cin abinci da yawa ba
Wannan ne dalilin dayasa koda yaushe cikin ta yake sumul kamar bata cin abinci
Tana gama cin abincin ta tashi ta kara zuwa gaban madubi
Ta tabbatar da cewa kwalliyar tata tayi kyau kuma zata dauki hankalin mutane acikin birnin
Sannan ta kamo hanya ta daga cikin turakar tata ta nufi hanyar da zata kaita turakar mahaifinta
Duk inda tazo giftawa acikin gidan sarautar saidai kaga dakaru suna zubewa har kasa suna gaishe ta
Ahankali har ta isa cikin turakar mahaifinta
Da zuwa saita iskeshi zaune akan kujera ya zauna jikinsa gaba daya yayi sanyi da alamun damuwa karara akan fuskarsa
Cikin fara'a ta karasa gareshi cikin gudu ta fada kansa
Sannan tace dashi ya abbana shin menene dalilin dayasa naga fuskarka cike da damuwa awannan rana ?
Dajin wannan tambaya sai sarki mayasin ya dubeta yace
Yake ýata tunda kiyi sani cewa zuciyata gaba daya bata amince da wannan rangadi da zaki fita ba, domin inaji ajikina cewa akwai wani abu da zai faru dake acikin wannan rangadin
Ina mai baki shawara da kar ki fita wannan rangadi ki jira sati mai zuwa sai ki fita
Dajin wannan batu sai jikinta yayi sanyi amma sai ta dubeshi tace
Ya abbana hakika kamar yadda kake jin wani abu zai sameni to tabbas hakane
Ammani abinda jikina yake bani zai faru dani a wannan rangadi na alheri ne
Wanda zai sa zuciyata ta kwanta kuma nutsuwa ta sameni har abada
Ina mai rokonka da kada ka hanani fita wannan rangadi
Dajin haka sai shima jikinsa yayi sanyi domin bayason
Ya hanata abinda duk tayi niya, don haka sai yace
To shikenan na amince amma zan hadaki da dakaru masu yawa
Wadanda zasu rakaki wannan rangadi don su tabbatar da tsaron lafiyarki
Take sarki ya kira sarkin yakinsa mai suna ukairu ya umarceshi daya debi dakaru masu yawa su rakata wannan rangadi
Take kuwa ya cika umarni bayan fitarsa da ýan dakiku sai gimbiya bahjaht ta tashi Ta bishi abaya
Fitarta keda wuya sai ta riski dakaru sunyi sahu sahu suna
Jiran isowarta, don haka bata bata lokaci ba ya shige gabansu ta tsaya
Sannan wasu kuyangi kimanin su dari suka tsaya abayanta
Suka ruke doguwar rigarta wacce take jan kasa da hannayensu
Wasu kuma suka ruke mata lema saboda kare mata zafin rana
Sannan suka dunguma suka shiga cikin gari kamar yadda ta saba
Koda sukayi tafiyar ýan dakiku saita cika da mamaki domin gani tayi a wannan rana ba'a cikaba wajen kallonta kamar yadda aka saba
Duk da cewa kuwa akwai mutane da yawa wadanda suka tsaya kallonta, wadanda suka hada maza da mata ,yara da manya,
Amma kuma ba'a cikaba kamar yadda aka saba ba, domin a saninta duk sanda ta fito wannan rangadi wasu mutanen ma basa samun gurin tsayawa
Don haka saidai su hau kan katangu su tsaya kamar ana gabatar da wani gagarumin bikin shekara
Kodayin wannan nazari sai taji zuciyarta ta buga da karfin gaske
Tace a ranta anya kuwa ba maganar mahaifina bace take shirin faruwa ba?
Domin naga gaba daya al'amura sun sauya ba kamar yadda nasansu abaya sukeba
amma sai wata zuciyar tace da ita
A'a bahjaht kada ki karaya kawai ki ci gaba da tafiya tunda dai akwai sauran tafiya agabanki kafin ki isa kasuwa wata kila kowa yana kasuwar yana jiranki
Da gama wannan tunani saita sami kwarin gwuiwa
Adaidai wannan lokacin ne taga mutane suna dawowa daga hanyar kasuwa
Don haka sai tasa aka kira mata wata budurwa daga cikinsu
Take kuwa wani badakare yaje ya zo mata da wannan budurwa
Gimbiya bahjaht ta tambayeta shin menene yake faruwa acikin kasuwar birnin?
Take kuwa kuyangar ta kwashe labarin komai ta fada mata cewa
Ai wani bakon jarumi ne ya shigo birnin wanda labarin tsantsar jarumtakarsa
Da kyawunsa suka cika nahiyar gaba daya shine ya shigo birnin
Mutane suke rububin kallonsa don su ganewa idanunsu
Kodajin wannan labari sai zuciyar ta ta buga da karfi take ta sallami wannan budurwa
Sannan taji wani irin kishi ya kamata, tace aranta wai jarumin da take jin labarinsa
Abakin kuyanginta shine ya shigo har cikin birnin mu ya kwashe mini gaba daya mutane na,
Ya zama dole naje gurinsa na hanashi shigowa cikin wannan birnin aduk irin

Please Login or Register in order to submit comment