Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu da wani mugun nufin

Tambaya ta biyu kuma itace shin akwai ragowar tikitin shiga wannan gasa ayanzu haka?
Dajin wadannan tambayoyi sai basdar yayi shiru yana dan nazari daga can kuma sai ya dago da kansa yace ya shugabana
Game da tambayar ka ta farko itace
Su dai wandannan jarumai guda biyar sun fitone daga mabanbantan kasashe ne
Kuma tabbas na tabbata cewa rana daya suka iso wannan birni kuma aranar suka sayi tikitin gasa domin da hannuna na rubuta musu shaidar shiga gasa ajikin tikitin yanzu haka sun kai mako uku da rabi acikin birnin nan

Game da tambayar ka ta biyu kuwa itace yanzu haka tikiti guda daya ne kacal ya rage a hannuna wanda ba'a saya ba
Dajin haka sai sarki aryan yayi wani tattausan murmushi sannan yace
To wannan tikiti ba za'a barshi a banza ba ka ajiye shi a hannunka
Kuma kazo dashi filin gasa gobe da safe domin na tabbata ahalin yanzu tsugunne bata kare ba
Dole akwai ragowar wani bakon jarumin wanda zai zo domin sayen wannan tikiti
Da zarar kuwa an samu kada kayi jayayya dashi kawai ka
sayar masa amma ka tsuga masa kudi mai yawa sakamakon jinkirin da yayi na rashin zuwa da wuri
Dajin wannan umarni sai basdar yace
Angama ya shugabana yana gama fadin haka sai ya mike sukayi sallama da sarki aryan
Shima ya kama hanyar komawa can nasa gidan wanda yake tazararsa da gidan sarauta bata wuce tafiyar rabin sa'a ba

Kashe gari kuwa tun da duku dukun safiya gimbiya walisa ta farka
Domin tanaso taji karashen hikayar sadauki hassanul basari tare da gimbiya bahjaht,
Don haka tana farkawa saita shiga bandaki ta wanke fuskanta
Sannan ta fito falon gidan ko zataga sarkin kasuwa yimana azaune
Kamar yadda ta sameshi jiya da safe amma kash..
Sai aka sami akasi shima a wannan lokaci bai farka daga barcin da yake ba,
Sakamakon jiya da dare idanunsa soyewa sukayi ya kasa yin barci da wuri bayan ya rabu da ita
Bisa dole gimbiya walisa ta hakura dajin wannan labari
Ta koma cikin dakin da aka sauketa ta sami gefen gado ya zauna
Tana ta tunani acikin zuciyarta kwatsam sai tunanin dan uwanta yarima walisu ya fado mata azuciyarta
Ta tambayi kanta shin ina ya shiga yanzu gaba daya na daina jin duriyarsa?
Kodai yana can wata nahiyar daban yana aikata ta'addancinsa ne?
Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai taji ba zata iya hakuri ba
Kawai sai ta yi nuni da hannunta jikin bangon dakin da take
Tare da karanta wadansu dalasiman tsafi marasa dadin sauraro
Faruwar hakan keda wuya sai ga hoton duk abubuwan da suke faruwa acikin duniya ya bayyana ajikin bangon dakin
Ga shinan komai yana tafiya daidai cikin kwanciyar hankali
Bata sami walisu a daya daga cikin nahiyoyin da tsafinta ya nuna mata
Koda gama ganin wannan al'amari sai take taji hankalinta ya kwanta
Sannan ta shiga cikin bandaki tayi wanka kafin ta fito har anzo an ajiye mata abincin karin kumallo
Ba tareda bata lokaci ba ta zauna taci abincinta sannan ta debi makaman yakinta ta sanyasu ajikinta
Bayan nan kuma ta dauko wata doguwar riga mai launin kore ta sanya ajikinta tare da sanya bakin kyalle ta rufe fuskarta dashi kamar yadda ta sabayi
Hakika wannan shiga da tayi ba karamin yi mata kyau tayi ba
Nantake ta fito daga cikin dakin ta tafi can falon gidan
Da isarta sai ta tarar da sarkin kasuwa yimana azaune tareda zaljus
Cikin fara'a ya dago kai ya dubeta yace sannunki uwar son jin labari
Ai yanzu sai ki wuce mu tafi kallon gasar jarumta kafin lokacin ya wuce
Yana gama fadin haka sai ya mike ya shige gaba su kuma suka bishi abaya
Gimbiya walisa ce abayansa ruke da zaljus ahannunta
Haka suka jera tare suka fice data cikin gidan bayan sun fita ne masu tsaron kofar suka jawo kofa suka
saka wani katon makulli suka rufe gidan dashi awannan ranar birnin fasawana ya cika fiye da kullum
Badon komai ba mutane suka hallara ba face don kawai suga jarumtakar wadannan zaratan jarumai guda biyar
Kai harda ma wadanda basa zuwa kallon wannan gasa saida suka halarci birnin awannan rana
Saboda haka ne ma sarki aryan ya umarci dakaru dasu kulle kofar shiga garin
Ta yadda babu mai shiga ko kuma mai fita
Bisa dole wadanda basu sami damar shiga birnin ba suka hakura suka koma garuruwansu
Haka dai su jaruma walisa sukayita kutsawa ta cikin mutane
Duk inda suka gifta sai kaga ana buda musu hanya badon komai ba
Sai don Darajar sarkin kasuwa da mutane suke gani
Sannu ahankali suka karasa filin gasa wanda ya cika ya batse da jama'a babu masaka tsinke
Da kyar da makyarkyata suka samu aka buda musu hanya suka shiga cikin filin gasar
Yimana ne kadai ya sami gurin zama acikinsu
Domin dama tuni ya biya kudin hayar kujerar tun kafinsu gimbiya walisa su iso birnin
Don haka kai tsaye ya shige cikin rumfar da aka tanadar musu
Ya sami guri ya zauna, su kuwa su walisa sai suka koma can gefe daya suka tsaya cikin ýan kallo
Basu jima da zamaba afilin gasar sai suka fara jiyo sautin busar algaitu tare da bugun ganguna suna tashi daga can nesa dasu
Koda jiyo sautin sai fa gaba daya mutane suka maida kallon su zuwa hanyar da sautin yake tahowa
Sannu ahankali saiga sarki aryan ya iso filin cikin shiga ta kasaita da takama
Ya rataya wata doguwar alkyabba ajikinsa wacce tayi matukar yi masa kyau
Abayansa kuma ya rataya wasu tagwayen takubba guda biyu
Koda jama'a suka ganshi cikin wannan gagarumar shigar yaki
Sai suka kaure da ihu da shewa wadansu kuma suka fara yi masa tafi gami da jinjina
Kai kace gaba daya mutanen duniyar ne suke kodashi
Kai hatta wadanda suke makobtaka da birnin fasawana suna jiyo sautin kirarin da ake masa
Da isowarsa filin gasar sai ya wuce zuwa kan karagarsa ya zauna
Har asannan mutane suna tsatstsaye basu daina kirarin da sukeyi masa ba
Harsaidaya daga musu hannu sannan sukayi tsit kamar mutuwa ta gifta saboda yadda suke tsananin biyayya agareshi
Sannan ya tashi yayi musu barka da zuwa tareda jawabi
Sannan ya umarci alkalin gasa da yayi musu bayanin yadda tsarin gasa yake
Take kuwa alkalin gasa ya mike tsaye yayi musu bayani kamar yadda ya saba
Amma awannan karon sai ya fadawa jaruman gasa cewa
Ya halatta duk wanda ya sami galaba akan abokin gwaminsa to ya kashe shi
Domin a sami damar tsayar gagara badau guda daya acikin su
Koda jin wannan sabon tsari sai mutanen dake gurin suka cika da tsananin mamaki suka fara kallon juna domin wannan shine karon farko da aka fara shigo da irin wannan dokar cikin gasa
Abangaren jaruman gasar kuwa wannan hukunci ba karamin dadi yayi musu ba domin yanzu ne kowanne daga cikin su zai cika burinsa akan danuwansa
Koda mutanen ýan kallo sukaga babu abinda daya dami jaruman gasar sai suma suka saki jikinsu tundasu kallo ne kawai nasu
Ba tareda bata lokaci ba alkalin gasar ya dauko wasu jemammun fatoci kana wadanda aka rubuta sunayen jaruman gasar ajiki kuma aka nannade fatocin yadda babu ta yadda zakaga rubutun da yake ciki aka watsasu agaban jaruman gasar sannan aka umarcesu da su dauki guda daidai take kuwa suka cika umarni
Sannan suka warware faton da suke hannunsu aikuwa saiga sunan warshanu da hamukas ya fito a cikin wadanda zasuyi karawar farko
Koda ganin haka sai take alkalin gasa ya umarci ragowar mutum ukun da babu sunansu dasu fita daga cikin filin
Ba tareda bata lokaci ba kuwa suka cika umarni
Sannan aka umarci mai buga gangar gasa da ya buga
Nantake ya daga wata katuwar sanda ya bugata ajikin wata katuwar ganga
Take kuwa wani sauti mai kara ya bayyana ya cika filin gasar gaba daya

Faruwar hakan keda wuya sai nantake su warshanu suka falfala da gudun gaske kan juna cikin mugun nufi

ME ZAI FARU ACIKIN WANNAN GASA?
SHIN IDAN BOKA SAHIBUL UKUB YA JE BIRNIN SHAWANA ZAI SAMI NASARAR SATO GIMBIYA BAHJAHT DAGA GIDAN KURKUKUN DA MAHAIFINTA YA RUFETA?
ANYA KUWA SARKI ARYAN ZAI SAMI NASARA ACIKIN WANNAN GASA?
WANNE IRIN SIRRI WADANNAN JARUMAN GASA SUKA BOYE ACIKIN ZUKATANSU?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA NA WANNAN KAYATACCEN LABARI
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT*******************ZUBAR DA JINI

***************** 5 PART B

LBR

********* HABIBULLAH KBR

Tun kafin su karasa kan juna sai kowannensu ya daka tsalle yakaiwa abokin fadansa
Mummunan harin bazato
Cikin bakin zafin nama sai kowannensu ya kacewa harin
Sannan suka duro akan kasa, kai idan ka gansu a wannan lokaci sai kayi zaton cewa
Warshanu sai yiwa hamukas kwaf daya ya kasheshi
Take warshanu ya dubi hamukas yace gaskiya wannan ranar sa'a tace
Domin kuwa tuntuni nakeson ganin bayanka amma damar hakan bata samu ba
Don haka saika shiryawa mutuwa acikin wannan fili kuma a hannuna
Dajin wannan batu sai shima hamukas yayi dariya shima yace
To ai shikenan duk irin burikan mu dayane don haka ka shiryawa tarar mutuwa a hannuna….
Kafin ya gama fadin abindake bakinsa tuni lamakus ya shammaceshi ya sake kawo masa wani wawan saran da rakobinsa
Inbadon yayi saurin kaucewaba da tuni takobin ta shafce masa wuyansa
Amma duk da haka saida takobin ta shafce masa saman gashin kansa
Kafin lamakus ya kara kawo masa wani harin tuni shima yasanya kafafunsa
Ya fyalli kafafun lamakus duka biyun take lamakus ya fadi kasa
Cikin bakin zafin nama hamukas y gyara rukon takobinsa
Sannan ya daka tsalle yakaiwa lamakus shura da nufin ya huda ruwan cikinsa da ita
Cikin bakin zafin nama lamakus ya kaucewa sukar daya kawo masa
Koda ganin wannan abu daya faru sai take ýan kallon da suke wajen suka fara koda gwanayensu tsakanin lamakus da hamukas
Sannan yayi alkafira ya mike tsaye zumbur tareda shurar takobinsa
Ya nufi hamukas suka kachame da azababben yaki mai matukar muni
Kai da gani kasan cewa ba wannan gasarce ta fara hadasu karo da juna dole dai akwai wata kullalliya akasan zuciyarsu
Koda lamakus yaga wankin hula zai kaishi dare sai kawai ya
shammaci hamukas ya debi kasa ya watsa masa a ido
Take idanun hamukas suka rufe ya daina ganin abindake gabansa
Kafin yayi wani yunkuri tuni lamakus ya soka masa wuka acikinsa ta faso ta gadon bayansa
Nantake wani gudan jini yayi fitar burgu daga bakinsa
Koda lamakus yaga ya sami wannan nasarar sai kawai ya bushe da dariyar mugunta
Yana cikin dariyar ne kafin ya ankara sai ji yayi an jefo takobi ta cake ta cikin kansa ta faso keyarsa
Take jikinsa ya kame kamar gunki ahankali sai yaga ba kowa bane yayi masa wannan mugun kisanba face hamukas
Shima fuskarsa cike da murmushin mugunta yana cewa
Ai baka isa na mutu a hannunka ba saidai muyi mutuwar ragas ni da kai
Atare duk su biyun suka fadi kasa sunata shure shure har rai yayi halinsa
Ganin irin wannan mutuwar mazajen faman ce tasa gaba daya mutane suka kara maida hankalinsu cikin filin gasa domin ganin yadda zata kasance a fafatawar gaba
Ba a dadeba sai alkalin gasar yasa aka sake kawo masa wasu jemammun fatun guda uku wadanda acikinsu akwai rubutun sunayen jaruman gasa guda biyu aka zube agabansu kowa ya dauki guda daya
Wadannan mutum biyun ba kowa bane face warshanu da kuma markus
Sunan jaruma marfuza wacce da alama itace zata kara da jarumin da yayi nasara tsakanin mutum biyun
Take duk su biyun suka shiga cikin filin suna wani irin gudu mai kama da sauri sauri
Suna masu dagawa ýan kallo hannu taredayi musu jinjina kai her suna hadawa da tsalle tsalle saboda yadda suka kagu da a ce su fara fadan kamar ba dayane daga cikinsu yake daf da mutuwa ba, shigarsu cikin filin keda wuya sai wani badakare ya buga kararrawar fara gasa
Take karar kararrawar ta cika dodon kunne hatta ýan kallo saida suka sa hannuwansu
Suka toshe kunnuwansu dasu
Su kuwa su markuz babu abindaya damesu domin zare makamansu kawai sukayi suka afka kan junansu suka kachame da masifaffen fada
Cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta tamkar jikinsu bana jini da tsoka baneba
Suna fara fadan nasune suka hargitsa tsakiyar filin gasar kura ta tashi ta turnuke su ya zamana ba'a iya ganinsu saidai karar karafkiyar makamansu kawai ake iya ji tareda tartsatsin wuta wanda yake tashi
Hakika idan karfi ya hadu da karfi to abin bazaiyi kyau ba
Su kansu ýan kallo saida hankalinsu ya tashi suka mimmike tsaye domin ganin yadda zata kaya atsakaninsu
Su kadai suka tafi da gaba daya hankalin masu kallo
Saboda fadan nasu ya zama abin al'ajabi ganin yadda warshanu
Yafi markus girman jiki da kuma murdewa shikuwa markuz ya kasance matashin saurayi
Amma ya hana warshanu samun damar da zaiyi galaba akansa
Ba komai ya janyo hakan ba face tsananin zafin naman da yake dashi
Su kansu ýan kallo sunyi mamakin irin wannan zafin naman nasa
Koda suka shafe wasu sa'o'i suna wannan kafsawa sai fadan ya canja launi
Domin dukkansu sun fara hadawa junansu jini da majina
Amma sai kaga sun shanye dukan kamar jikinsu bana jini da tsoka bane ba
Ba komai ne ya janyo haka ba face dukkansu sun kasance kar ta san karce a tsakaninsu
Tun tuni sun sha haduwa abaya suna fafatawa don ganin sun halaka daya daga cikinsu amma damar hakan bata samu ba
Ba komaine ya haddasa wannan gaba atsakaninsu ba face
Wata rana sa'adda suka shiga daji farauta
Sai sukaci karo da wata katuwar barewa awannan lokaci suma shine farkon haduwarsu domin dukkansu farautace sanaa'rsu
Don haka basu saba da juna sosaiba,
Da ganin wannan barewa sai duk su biyun suka bita da gudun gaske domin su kure mata gudu su kamata
Itadai wannan barewar ta saba haduwa da mafarauta iri iri
Don haka ta saba yin gudun ceton rai
Don haka koda taga su warshanu sun biyota saita fyalle kafafunta ta ruga da gudun gaske
Su kuma suna biye da ita
Wohoho ! Nanfa aka kasa mahaukacin tseren gudu atsakaninsu
Duk inda suka barewar ta dauke kafarta nan suma suke sauke nasu kafafun
Ta zararsu bata wuce taku kai harsaida suka wuce dajin da suke ciki suka kara nausawa wani dajin da yake gaba da nasu a wannan lokaci sun gaji likis dagasu har barewar
Koda markus yaga cewa yana bata lokacinsa ne wajen bin wannan barewa kawai sai
Ya dana kibiyarsa ajikin baka
Ya saita tsakiyar cikin ta ya harba. Take kuwa kibiyar ta tafi da gudu ta huda tsakiyar cikin barewar ta fadi kasa matacciya
Cikin murna duk su biyun suka karasa suka dauki barewar suka gurata
Awannan lokaci yunwa ta gama kama cikinsu kamar ransu zai fita saboda yumwa da kuma kishirwa a sannan battar ruwansu tayi karkaf
Koda markus yaga haka sai ya mike ya dauki takobinsa tareda battar ruwansa kuma ya karbi ta warshanu
Ya tafi nemo musu ruwan da zasu sha saida ya gama zagaye dajin da kyar ya samu korama guda daya ta ciko battocinsu da ruwa ya dawo
Koda dawowarsa inda suke zaune sai ya tarar warshanu ya tattara gaba daya naman barewar da sauran kayan da markus ya bari ya sace su ya gudu dasu

Tun daga wannan rana gaba ta shiga tsakaninsu duk a inda suka hadu basa taba rabuwa sai sun hadawa junansu jini da majina
Koda suka shafe sa'o'i suna wannan fafatawa sai kawai
Suka ja da baya taku hudu suna nazarin junansu
Daga can kuma lokaci guda sai suka daka tsalle asama suka kaiwa junansu munanan hare hare
Take kuwa duk su biyun sukayi ragas kowa ya sami nasarar
Sarewa junansu kawuna take kuwa duk su biyun suka rikito kasa matattu
Koda ganin irin wannan mummunaf mutuwa da sukayi sai duk ýan kallo suka mike tsaye zumbur saboda tsananin mamakin irin wannan al'amari, take filin gasar ya cika da kace nace din mutane sakamakon ganin yadda karshen wannan gasa yake
Domin ta riga ta bayyana cewa jaruma marfuza itace zata kara da sarki aryan wanda ya saba lashe nasarar gasar
Idan har aka cigaba da gasar a haka to dole babu wanda zaiyi nasara acikin gasar domin saidai suyi ragas dashi
Wannan shine dalilin daya haddasa wannan hayaniya acikin filin
Basuyi shiru ba saida sukaji an buga kararrawa sannan kowa ya dawo hayyacinsa
Sukayi shiru kamar mutuwa ta gifta ta tsakiyarsu in banda sautin numfashi babu abinda kunnuwa ke sauraro
Daga can sai alkalin gasa ya mike ya kalli ýan kallo yace
Yaku jamaa'r wannan guri dukkanku kunga abubuwan da suka faru da idanunku
Acikin jaruman wannan gasa babu wanda ya rage face jaruma marfuza
Don haka Itace wacce zata kara da mai girma sarki aryan
Duk wanda yayi nasara acikin su shine wanda ya lashe nasarar wannan gasa kuma shine zai karbi kambunta
Kafin ya gama jawabin da yakeyi tuni jaruma marfuza ta shiga tsakiyar filin gasar ta tsaya
Hannunta kuwa rike da wata zabgegiyar takobi mai matukar kaifin gaske
Hakika jaruma marfuza kyakykyawar budurwa mai kira mai kyau
Domin ta kasance fatar jikinta wankan tarwada ce kugunta acike yake
Tana da gashi wanda ya zuba har kasan kafadunta
Idanuwanta fararene sol, da kuma digon baki atsakiyarsa
Hakika marfuza kyakykywace abar fada amma duk da kyawunta gimbiya walisa tafita
Domin ita farace fatarta amma farin ba mai haske sosai ba
Gashin kanta ya sauka har wajen mazaunanta saboda hakanema yasa take daureshi agadon bayanta
Sannan kuma tafi jaruma marfuza tsawo

Adaidai wannan lokacin ne shima sarki aryan ya mike tsaye ya sauka daga kan karagar mulkinsa
Sannan ya cire hular sarautar da take kansa, tare da cire doguwar alkyabbar da take jikinsa
Take saiga siffarsa ta bayyana
Cikin shigar wani irin jan sulken yaki tareda wasu jajayen adduna guda biyu
Wadanda ya dauresu a saman kafadunsa, kafarsa kuwa tana sanye da wani irin farin takalmi wanda yazo masa har kasan gwuiwarsa
Kallo daya zakayiwa sarki aryan kasan cewa dolene ya kasance jarumin gaske kuma sa maza gudu
Duk da cewa jikinsa a rufe yake cikin sulke amma hakan bai hana ganin irin murdaddiyar surar jikin da yake da ita
Dadin dadawa kuma ga baiwar kyawun da ibangiji yayi masa
Koda gama cire alkyabbar da take jikinsa sai ya nufi cikin filin gasar
Yana wata irin tafiyar kasaita kamar toron giwa, nanfa ýan kallo suka dada rushewa da ihu suna masu yi masa kirari
Yayinda makada suka fara yi masa kirari suna zugashi
Koda ya shiga cikin filin gasar sai yaja tunga ya tsaya
Yana mai fuskantar jaruma marfuza tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku shida ba
Suka tsaya suna kallon kallo atsakaninsa da ita tareda zagaya junansu rike da makamansu a hannuwansu
Daga can kuma sai sukayi kukan kura suka afkawa junansu da mugayen hare hare
Wadanda suka hada da sara, suka, naushi da bugu hannu da kafa sai kace ablisai
Wohoho hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace rana bata karya,
Domin kuwa gashi a zahiri ta bayyana wadanda suka biya kudi domin ganin irin jarumtakar da sarki aryan yake da ita sun fara more kudinsu da suka zuba domin kallon wannan gasa
Suna fadan ne cikin nuna salo da kwarewa tabbas jaruma marfuza itama ta cika jarumar gaske wacce ta saba shiga gwagwarmaya arayuwarta
In badon haka ba da tuni sarki aryan ya sami galaba akanta
Domin ya fita karfin damtse nesa ba kusa ba. Abu dayane kawai yake taimakonta har take iya yaki dashi
Wannan abu kuwa ba komai bane face ita ta kasance mace ce mai zafin nama da kuma juriyar wahala
Don badon haka ba da tuni sarki aryan ya sassarata da addunan da suke hannunsa saboda karfin saran da yake kawo mata
Haka shima lokuta da dama sai yayi da gaske yake iya kare harin da take kawo masa
Saboda tana da matukar shammace, amma wani abu guda shi sarki aryan ya fuskanta dan gane da ita jaruma marfuza
Wannan abu ba komai bane ba face, duk da cewa shi yana kaima hari domin ganin ya rabata da numfashinta
Sai yaga ita ko kadan bata kai masa harin da zai rasa rayuwarsa
Saidai ma yaga tanayi masa wani irin tattausan murmushi wanda shi kansa ya kasa gane dalilin murmushin
Har ya tambayi kansa cewa shin wannan murmushin da takeyi mini na raini ne ko kuma na soyayya?
Domin kuwa jiya ma naga tayi mini irinsa sa'adda aka tashi daga zagayen farko na gasar
Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan kuma yaji gaba daya bai amince da wannan murmushin da take yi masa ba
Don haka saiya kara zage damtsensa wajen kai mata mugayen hare hare masu karfi
Wanda inbadon tana da juriya ba da bazata iya kare hare haren nasa ba
Hakika sarki aryan jarumi ne wanda ya amsa sunansa jarumi
Ai kuwa yana canja salon fadan nasa sai nan da nan cikin kankanin lokaci ya rikita jaruma marfuza
Tun tana iya maida martani har ta kasa ya zamana cewa
Kokarin kare kanta daga mutuwa kawai takeyi
Koda ýan kallo suka ga irin wannan karfi irin na sarki aryan sai
Nantake suka fara zuga shi sunayi masa kirari suna zugashi kan cewa shine
Kadai jarumin da babu kamar sa awannan nahiya
Har suna ikirarin cewa idan akwai wani jarumin daya rage ya fito su ganshi
Haka dai sukayita yi masa kirari kala daban daban wanda hakan yasa gimbiya walisa
Wacce take cikin ýan kallo taji wani irin kishi ya turnuketa
Acan tsakiyar filin gasa kuwa tuni sarki aryan ya gama samun galaba akan jaruma marfuza domin harya tara mata jini ajikinta
Tun tana iya kare farmakinsa har ta kasa takobinta ta fadi kasa acan gefe daya
Cikin zafin nama sarki aryan yasa kafarsa guda ya doketa da ita
Take tayi sama saboda karfin dukan ta fadi can gefe daya yayinda wani gudan jini ya fita daga cikin bakinta
Kawai sai yazo daidai kanta ruke da takobinsa ya tsaya tana kallon kaifin takobin
Ya kalleta yace sai kiyi hakuri ýar budurwa mugun nufin da kuka shigo dashi cikin wannan birni duk nayi maganinsu
Don haka ke kadaice kika rage kuma zan kaddamar da hukunci akanki
Koda marfuza taji abindaya fada sai itama tayi murmushin karfin hali irin wanda ta saba yi masa abaya sannan tace
To me kake jira? Kayi sauri ka kasheni ni, ko ba komai zan zamo mai matukar farinciki kan cewa na mutu a hannun masoyina wanda zuciyata ta dade da nutsewa cikin soyayyarsa
Yakai wannan sarki ka sani cewa ba na shiga wannan gasar don burin samun dukiya bane
Na shiga ne kawai don na sami damar da zan furta soyayyata agareka ne
Don haka ina mai rokonka daka gaggauta kasheni idan har kasan ba zaka karbi soyayyata ba
Don ruhi na ya kwanta cikin jin dadi, ka sani babban farin cikina shine ka kasheni da tafin hannunka.
Kodajin kalaman data fada sai sarki aryan ya kwarara ihu cikin bacin rai ya daga takobinsa sama da nufin ya sare mata kanta
Ba zato ba tsammani sai yaji an dako tsalle daga cikin ýan kallo a sama an jera masa zafafan duka da kafafu atsakiyar kirjinsa
Saboda karfin dukan saida yayi baya taga taga zai fadi amma sai yasa hannuwansa ya tare
Bai yadda ya fadi kasa ba sannan ya mike ya juyo don ganin wanda yayi masa wannan mummunan dukan
SHIN WANENE YA DAKI SARKI ARYAN?
SHIN SARKI ARYAN ZAI KARBI SOYAYYAR JARUMA MARFUZA?
WANNE HUKUNCI ZA'A YANKEWA WANDA YA DAKI SARKI ARYAN?
SHIN INA GIMBIYA WALISA?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR

KUYI HAKURI AKAN JINKIRIN POST DIN DA KUKA GANI HAKAN TA FARUNE SAKAMAKON RASHIN LAFIYAR DA NAYI

LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT***********ZUBAR DA JINI

********************5 PART C

LBR

**********-HABIBULLAH KBR

lokacin da sarki aryan yaji an gabza masa kwararan naushi akirjinsa
Har saida yaja da baya ya kusan faduwa kasa amma sai ya saka hannayensa
Ya kare bai yarda yaje kasa ba sannan yayi alkafira ya mike tsaye domin ganin wanda yayi masa wannan zazzafan dukan
Kawai sai ya cika da mamaki domin ba komai ya gani ba face budurwa
Wacce

Please Login or Register in order to submit comment