Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Koda suka fito daga cikin gidan sarautar sai suka wuce kai tsaye izuwa bargar dawakai
Ta zabi wani ingarman farin doki matashi
Mai jini ajika ta dauka ta hau
Sai gashi dokin ya dace da ita kamar saboda ita aka halicci dokin
Daga wannan guri sukayi bankwana da sarki fadarul munnar
Ta kama hanya ta nufi hanyar fita daga birnin
Duk inda ta gifta sai dai kaga dakaru da mutanen gari suna rissinawa suna gaisheta
Tareda yi mata addu'ar samun nasara
Ahaka har ta fice daga cikin birnin gaba daya ta shiga cikin daji
Tana zabga azababben gudu
Tun tana cikin yankin birninsu har ya zamana ta fice daga cikin nahiyar gaba daya

Kuma duk inda ta hadu da mutane saita dauko hoton yarima walisu
Ta nuna musu shi ko sun ganshi akan hanyar su
Amma
ko sai daya bata hadu da wasu mutane wadanda suka ce sun taba haduwa dashi ba
0=====[============>
Can kuwa al'amarin yarima walisu tun daga lokacin da fatalwar boka sahibul ukub ta shiga jikinsa
Alokacin yana kwance acikin turakarsa
Abinda ya faru shine
Lokacinda dare ya tsala yana cikin sharara barci abinsa harda minshari
Kamar wanda bazai taba farkawa ba daga dogon barcin da yakeyi
Kwatsam sai yaji wata irin tsawa daga
Cikin sauri ya farka firgigit daga dogon barcin da yakeyi
Tareda zare takobinsa azatonsa wasu dakarun mamayar bazato ne suka kawo masa hari
Bisa mamaki sai yaga shi kadai ne acikin dakin babu kowa
Amma duk da haka ba'adai na wannan walkiyar ba
Don haka sai ya kwantar da hankalinsa domin ya zata hadari ne
Ya hado ake shirin yin ruwan sama
Amma sai yaga wannan tsawar bata tsayaba har ma dakin nasa gaba daya ya canja fasali
Ba kamar yadda yake da ba
Domin gani yayi komai na cikin dakin yana yawo akan iska
Sannan ya dinga jin kamar ana kyallara dariya daga cikin wannan tsawar da take tashi
Ba zato ba tsammani sai kawai yaji kamar an kama jikinsa an daure .yadda ko dan yatsansa bazai iya dagawa ba
Daga can kuma sai yaji an bushe da dariya wacce bai san daga inda take tasowa ba
Kuma duk wannan abu da yake faruwa shi kadai ne yake ji kuma yake gani
Duk hadiman gidan sarautar basa iya ganin komai
Ana cewa cikin wata kakkausar murya mai kama da kukan jaki
Yakai wannan jarumi daga yanzu babu wanda yake da iko akanka
Sai abinda muka saka ka kawai zakayi ko kanaso ko baka so
Dole ne ka zama bawanmu daga nan har karshen rayuwarka
Kuma dakaine zan cika burina na ganin duk wata teku ya rine da jinin bil'adama
Kafin yace wani abu sai kawai yaga wani irin haske mai kama da suffar bil'adama
Tsoho tukuf fuskarsa cike da furfura idanunsa kuwa jajaye ne wuluk babu alamar fari acikinsu
Yana tafiya akan iska tareda kyalkyala dariya ya taho gurinda yake
Yarima walisu yana ji yana gani amma bashi da ikon koda bude bakinsa
Balle yayi magana wannan tsohon matsafi yazo ya shiga gangar jikinsa
Take walisu yaji gaba daya jikinsa yayi sanyi kuma nantake gaba daya tunaninsa
Ya juye ya manta ko wanene shi da asalinsa da kuma mahaifarsa
Nantake yaganshi yana tafiya akan iska ba kan kasa ba
Ahaka ya dinga ratsawa ta cikin ginin gidan sarautar tasu
Kuma duk inda ya gifta babu wanda yake iya ganinsa
Domin ta gaban dakarun ya dinga wucewa wasuma ratsawa ta jikinsu
Ya dingayi yana wucewa ahaka har ya bar cikin birnin
Kuma wata irin tafiya ya dingayi ta ban al'ajabi domin tafiya mai tsawo
Yana tamkar gudun kibiya haka yake yawo acikin iska
Ahankali har ya bayyana agaban wata katuwar bishiyar kuka
Acikin wani irin bakin daji itadai wannan bishiyar kukar ta kasance katuwar gaske
Domin komai karfin idon mutum bai isa ya ita ganin karsheta ba
Koda zuwansa gaban wannan bishiyar sai kawai kasar gurin ta dare gida biyu
Wata iriyar katuwar kofa ta bayyana akasanta kamar kofar gari
Nantake ya shiga cikin wannan kofar har yakai karshenta
Wohoho hakika wanda baiyi yawon duniya ba bai morewa idonsa kalloba
Sai gashi ya bayyana acikin wata katuwar fada mai girman gaske
Kai da ganin yadda wannan fadar take kasan cewa an dade ba'a shigo cikinta ba
Domin gaba daya komai na cikin fadar a lullube yake da yana da kuma kura
Nantake walisu ya dubi gaba daya fadar da kwayar idanunsa
Take wata iriyar iska mai karfi ta fito daga cikin idanun nasa
Ta karkade gaba daya yana da kuma kurar da suke cikin fadar
Sannan gaba daya kurar ta bace gaba dayanta
Bayan nan kuma sai wani irin ruwa ya fito daga cikin idanun nasa
Ya wanke komai na cikin fadar kuma atake komai ya bushe kamar ruwa bai taba sauka ajikinsu ba
Bayan komai ya koma yadda yake sai ya tafi kai tsaye zuwa inda wata kujerar tsafi take ya zauna akanta tareda dora hannayensa akan cinyoyinsa
Bayan 'yan dakiku sai yaji jikinsa ya fara karkarwa
Take ya fadi kasa ya fara farfadiya
Bakomai ne ya jawo hakaba face alokacin ne ruhin boka sahibul ukub yake da bukatar fita daga jikinsa
Nantake wannan hasken ya fita daga jikinsa shima ya dawo hayyacinsa
Koda ya dawo cikin hayyacinsa yayi arba da ruhin boka sahibul ukub
Sai ya daka masa tsawa tareda cewa
Wai shin kai wanene kuma me kake nufi dani sannan inane kakawo ni nan?
Ka gaggauta saki na ko kuma yanzun nan na hallaka gaba daya
Dajin haka sai ruhin boka sahibul ukub ya bushe da dariya sannan yace
Kai yaro hakika kana yaudarar kanka ne domin da ace ka sanni da bazakayi wannan maganar ba
Nine kadai atarihin duniya shu'umin dagaba daya duniya suke bauta masa
Domin babu wanda yake da karfin sihirin da nake dashi
Kuma nine wanda ya gagari duniya gabaki dayanta har ya zamana
Kowa yafi tsorona fiye da yadda yake tsoron mutuwarsa
Yanzu kai tayaya kake tsammanin zaka kasheni bayan dama can ni mataccene?
Kaine zaka zame mini gangar jikina awannan zamanin
Domin na ci gaba da BUWAYAR SADAUKAI da kuma
manyan SARAKUNA da kananun BOKAYEN wannan zamanin naku
Wadanda gaba daya sihirin nasu baifi cikin cokali ba
Ballantana kuma kai kanka ta taya kake tsammanin zaka iya tarata da yaki? Bayan na dade da shudewa ?
Ka sani cewa indai bana jikinka to sihirin tsafi na ba zai taba yin tasiri ba
Amma kuma idan duk duniya zasu taru basu isa su hanani shiga jikin ka ba
Kafin ya gama fadar abinda yake bakinsa tuni jarumi walisu
Ya dako tsalle daga inda yake ya kawowa ruhin boka sahibul ukub
Mummunan sara da nufin ya tsargeshi gida biyu
Bisa mamaki sai yaga takobin ta ratsa jikinsa ta wuce kamar
Ya sari haske ba tareda yaga jini ajikin takobinba kawai
Sai yaji boka sahibul ukub ya sake bushewa da wata mahaukaciyar
Dariya fiye da wacce yayi a baya wacce tasa fadar ta fara amsa kuwwa da amo
Komai na cikinta ya fara girgiza kamar zai rufto kasa
Harsaida yayi shiru sannan komai ya koma kamar yadda da yake abaya
Ya sake kallon walisu yace
Kai yaro kadaka taba yaudarar kanka da tunanin ganin karshena
Domin nine sa gudu kuma ki gudu duk hatsabibancin mutum ko aljan yana shakka haduwa dani
Kuma ina mai tabbatar maka da cewa ni din nan murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya
Daga yanzu acikin wannan fadar zaka ci gaba da zama har iya karshen rayuwarka
kuma ina mai tabbatar maka da cewa bazan bari ka mutu da wuri ba
Dole sai bukata ta gama biya ta ganin na zama cikakken gagara badau
Koda ruhin boka sahibul ukub ya gama fadar haka sai nantake ya tarwatse
Ya sake dawowa ya shiga jikin walisu faruwar hakan keda wuya
saiga launin fuskarsa ta sauya daga launin mutanen arziki zuwa ta azzalumai
Take wasu irin zabga zabgan fukafukai suka fito daga jikinsa
Sannan ya mike ya tashi sama ya ratsa ta jikin wannan ginin fadar
Ya luluka. Cikin sararin sama cikin azababben gudu kamar iska
WANNAN SHINE DALILIN DAYA SA GABA DAYA BOKAYEN DUNIYA SUKA KASA GANO INDA YARIMA WALISU YAKE
Babu inda jarumi walisu ya nufa face wani katon birni
Wanda ake kiransa da suna keraya, birnin keraya babban birnine
kuma karkashin mulkin wani azzalumin sarki mai suna ukibanu
Yana da matukar karfin sihiri da kuma karfin damtse
Kuma shima ya dauki ZUBAR DA JINI ba abakin komai ba
Hatta talakawan birninsa irin halinsu kenan wannan dalilin ne yasa
Kowa baya shakkar mutuwa akullum zubar da jinin bil'adama ake acikin Wannan birni

Wata rana suna zaune ana tafiyar da harkokinsu na yau da kullum
Kuma a wannan lokaci wani katon kakkarfan mutum
Mai kirar mutanen farko ya kamo wadansu dattijai guda biyu
Da kuma 'ya'yansu yara kanana ya daure su a tsakiyar kasuwa
Yana sa wuka yana yankan naman jikinsu yana gasawa acikin wuta
Sannan ya jefawa wadansu karnuka da suke bayansa su cinye
Su kuma wadannan daurarun mutanen sai kuka sukeyi
Gefe kuma ragowar mutanen gari ne sun tsaya suna kallonsu
Suna ta kyalkyala musu dariya don ko kadan babu alamar tausayi akan fuskokinsu

ME KAKE GANIN ZAI FARU A WANNAN BIRNI?
KUMA SHIN WALISA ZATA HADU DA DAN UWANTA JARUMI WALISU?
WANNE IRIN TASHIN HANKALI MUTANEN DUNIYA ZASU SHIGA SAKAMAKON BAYYANARSA?
SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
DAGA
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++++++1 PART C

LBR
++++++++++++ HABIBULLAH KBR

Kai wasuma har faduwa suke saboda dariya mazansu da matansu
Har ma zugashi wannan azzalumin sukeyi akan ya kara tsananin azabar da yake yiwa wadannan daurarrun
Wannan itace al'adar mutanen wannan gari indai kai ba jarumi bane
Koda yaushe irin wannan abu zai iya faruwa dakai domin bakin zaluncin su
Suna cikin wannan bakar al'adar tasu ne kawai sukaji wata iriyar
Bakar guguwa ta taso daga sama wacce ta haddasa tashin kura acikin birnin gaba dayansa
Wani irin bakin hadari ya tokare sararin samaniya kai kace ruwan sama za'ayi
Nanfa hankalin mutane gaba daya yabar kan wannan bakin azzalumi
Suka daga kawunansu sama suna kallon abinda yake shirin faruwa
Kafin su ankara sai sukaji wata irin tsawa mai karfi ta amsa kuwwa
A gaba daya birnin kamar zata fasa dodon kunne kai saboda
ma karfin karar saida suka durkushe kasa suka sa hannuwansu suka toshe kunnuwansu
Sannan suka tashi suka fara gudun neman wajen tsira
Daga can kuma sai kasa ta fara tsagewa mutane suna ruftawa cikinta
Nanfa hankalin gaba daya mutanen birnin ya tashi suka
Gudu suka bar kallon wannan bakin azzalumin domin
Shima gudun ceton ransa yayi bai san inda ya nufa ba
Mutane kuwa garin gudu wasu har fadawa suka dingayi
Cikin ramuka ba tareda sun sani ba, wasu kuma suna sane suka dinga jefa 'yan uwansu
Domin suma su tsira da rayukansu, manyan gine ginen birnin ma suka dinga zabtarewa suna fadowa kan mutane
Ana cikin wannan haline kawai sukaga kasa ya tsage
Ta haifar da wani wawakeken rami wanda basa iya ganin karshensa
Ta cikin ramin kuma sukaga jarumi walisu ya fito jikinsa
Dauke da manya manyan fukafukai har a wannan lokaci bai daina kyalkyala dariya ba
Koda sukayi arba da walisu sai suka kara firgita fiye da ko yaushe
Yana gama fitowa daga cikin ramin sai sukaga ya sunkuya yasa hannunsa guda daya
Ta shake wuyan wannan azzalumin mutumin take wuyan ya zabtare kamar zabira akasa aka yanka wuyan nasa da ita
Sannan ya juya kan wadannan daurarun mutanen suma ya firge musu kawunansu
Faruwar hakan keda wuya jini yayi tsartuwa daga jikin dungulmin wuyan nasu
Koda ganin abindaya faru sai mutane suka rusa uban ihu
Suka fara guje gujen neman wajen tsira amma ina babu damar hakan
Domin duk inda suka nufa saidai kaga walisu yayi nuni da hannunsa
Zuwa inda mutum yake saidai kaga kokon kansa ya fita daga jikin wuyansa
Jini yayi fallatsi a sama, ana cikin wannan artabune kawai sai dakarun sarkin garin suka iso karkashin
Jagorancin sarkin garin ukibanu koda sarki ukibanu yaga
Irin mahaukaciyar barnar da jarumi walisu yake masa
Saiya kwallara uban ihu sannan ya umarci dakaru masu kibiya dasu harbi jarumi walisu
Take kuwa suka cika umarni suka zaro wasu dogayen kibiyoyi suka harbowa jarumi walisu
Hakika rashin sani yafi dare duhu inda wadannan dakarun sun san abinda zai samesu da basuyi yunkurin cutar da walisu
Saidai su koma kan maigidan nasu
Ai koda suka harba kibiyoyin sararin samaniya sai kawai sukaga
Kibiyoyin sun dawo ta saman kansu suka fasa kokon kansu
Sannan suka hudo ta kasan duburarsu take sukayi mutuwar tsaye
Saidai kawai kaga jini yana bulbulowa ta kasan duburarsu kamar ruwan fanfo
Nantake suka sulale kasa matattu koda ganin abindaya faru ga wadannan dakaru
Saiya kwarar uban ihu ya falfalo da gudun gaske zuwa kan walisu
Koda yazo baifi taku hudu ba atsakaninsu sai sarki ukibanu
Ya daka tsalle da nufin ya kaiwa walisu harin bazato
Koda takobin ta kusa sauka akan wuyan jarumi walisu
Sai wani irin tiririn hayaki ya fita daga jikinsa ya shiga jikin sarki ukibanu
Take jikinsa ya sandare a saman kamar wanda ya kasance dama can ba'a taba halittarsa ba
Daga can kuma sai jini ya dinga fita daga cikin kowacce kofar gashi da take jikinsa
Kafin cikar dakika biyu duk jinin jikinsa ya gama fita kuma yazama gawa
Koda yaga ya gama da sarkin garin sai ya koma kan mutanen birnin
Yaci gaba dayi musu kisan gilla,
Kaico ! Kai komai rashin imanin mutum idan yaga yadda
walisu yake yiwa mutane kisan gilla dolene ya tausaya musu
Saidai kaga kawai walisu yana nuni da hannunsa yana
Fizgewa mutane kawunansu gaba daya garin babu abinda kakeji face
Koke koken mutane yara da tsofaffi amma shi babu abindaya dameshi
Cikin abinda bai wuce dakika ashirin ba ya gama hallakar
da duk mutanen birnin yayiwa kasa ado da jininsu kai hatta jikin ginannika
Babu abinda zaka gani face jinin mutane wanda yayiwa ginin fenti
Kasa kuwa gatanan ta rine da jinin bil'adama ya cudanya da jini
Koda gama aikata wannan munnar barnar tasa sai ya dauko kokon kan wata mujiya ya tsireta ajikin mashi sannan ya bude fukafukansa ya tashi sama tamkar bai taba wanzuwa abirnin ba
WANNAN SHINE LABARIN JARUMI WALISU
0======[=========≠=====>
Acan kuwa al'amariin jaruma walisa tun daga sanda
Ta baro gida ta fito neman dan uwanta jarumi walisu
Sai ta shiga cikin manyan dajijjika da kogunan duwatsu
Ko zataganshi ko kuma ta sami labarin inda yake amma harta gama karade wadannan dajijjika bata hadu da shi ba
Fargabar da takeyi acikin zuciyarta itace wanne birni zataje ta hadu da walisu
Kuma ta yaya zata iya hanashi ai watar da mummunar dabi'arsa
Tana cikin tafiyane acikin daji kawai sai ta jiyo karnin jini
Daga can nesa da inda take, take ta juyar da linzamin dokinta
Zuwa inda take jiwo wannan karni, koda ta karasa sai taga gurin ya
Cika makil da wakilan wasu manyan sarakunan sunzo
Domin suga abindaya faru a wannan guri, kowa acikin su
Ya toshe hancinsa da hannunsa saboda tsananin karnin da yake tashi awannan birni
Koda walisa ta iso wannan guri saita cika da tsananin mamaki
Ta sami wani daga cikin mutanen da suke gurin wanda ya kasance dattijon mutum tace
Wanne irin bala'i ne ya faru a wannan guri, ko kuma wasu bakaken aljanun ne
Suka kawo musu harin bazato?
Kodajin wannan tambaya sai wannan mutumin ya kalleta yace
Dukkanmu nan bamuda masaniyar amsar wannan tambaya taki
Domin gaba dayan mu bamusan faruwar wannan al'amari ba
Kuma ina mai tabbatar miki da cewa ba aljanu ne sukayi wannan abuba
Saidai wani shararren matsafin domin sarki ukibanu hatsabibin mutumne
Shine yake mulkin gaba daya aljanun da suke wannan nahiya
Don haka kinga aljanu basu isa suyi masa wannan mummunan kisa ba
Kodajin haka sai zuciyar walisa ta buga da karfi tace acikin zuciyarta
Anya kuwa wannan ba aikin dan uwana walisu baneba?
Lallai akwai abin al'ajabi acikin wannan al'amari, tana cikin wannan
Zancen zucin ne ta iso inda gawar sarki ukibanu take
Har a sannan yana sandare a sama bai fado kasa ba
Saidai takobinsa ita kadaice ta fadi daga hannunsa
Wannan abin ne ya tabbatar mata da cewa lallai wannan aikin walsu ne
Tace acikin ranta shin ina ya kamata taje inda zata hadu dashi?
Dolene tayi saurin hanashi aikata wannan mummunar barnar da yake yi
Tana gama wannan zancen zuci sai kawai ta yanke shawarar
Shiga cikin wani birnin da suke makwabtaka da wannan birni

0=====[=========≠====>
Birnin kufa babban birnine wanda yake cike da kabilu kala kala
Kuma yana karkashin mulkin wani hamshakin sarki matashi
Maisuna kalkus,
Kalkus amini ne ga marigayi sarki ukibanu kuma akwai shakuwa
Mai tarin yawa a tsakaninsu domin tun suna yara suke abokan taka da juna
Har zuwa girmansu, kuma ya sami labarin abindaya faru a birnin da abokinsa yake mulki wato ukibanu
Kuma har yaje da kafafunsa ya gani da idonsa abindaya faru
Don haka sai ransa yayi matukar baci ya hada dakarun sa masu yawa
Yayi shirin fita neman wanda yayi wannan danyen aiki da kansa
Har sun fito kofar gidan sarautar kawai sai sukayi kicibus
Da babban bokan birnin wanda akewa lakabi da shamshan
Shidai shamshan ya kasance dattijone mai shekaru kimanin tamanin da biyar
Fuskarsa cike take da furfura, sannan yana da matukar kwarjini
Kallo daya zakayi masa kasan cewa ya sha gwagawar mayar duniya
Hannunsa ruke yakeda wata sandar tsafi irinta shahararrun matsafa
Cikin sauri boka shamshan yazo gaban sarki kalkus ya russina yace
Ya shugabana ina mai shawartarka da kada kayi gaggawar wannan tafiya
Domin bincike na ya nuna mini cewa idan har ka fita daga cikin birnin nan ba zaka dawo a raye ba wannan aiki dake gabanka
Daidai yake da fita farautar mutuwar ka
Koda jin wannan batu sai sarki kalkus ya kwarar uban ihu saboda bakin ciki
Bisa dole ya hakura ya koma cikin gidan sarauta boka shamshan yana biye dashi abaya
Da isarsu cikin fadar sai sarki ya sami guri ya zauna
Sannan shima boka shamshan ya zauna suna fuskantar juna
Bayan sun danyi shiru na kankanin lokaci sai bokan ya katse shirun da yake tsakaninsu da fadin cewa
Ya shugabana ba komai ne yasa na hanaka fita daga cikin birnin nan ba
Face binciken danayi yanzu akan wannan al'amari shine yayi matukar razanani
Domin babu irin binciken da banyi ba akan na gano
Wanda ya aikata wannan mummunan aiki ba amma na kasa
Kai dana tsawaita bincikema sai madubin tsafin nawa ma ya fashe gaba daya
Tun da nake ban taba ganin al'amari mai firgitarwa ba face wannan
Sai dai idan mukayi amfani da kwakwalwar mu zamu iya gano
Silar faruwar wannan abu gasu sarki ukibanu
Idan har zaka iya tunawa tun daga sanda aka haifemu
Irin haka bata taba faruwa ba a wannan duniya saidai
Kuma mun sami labari daga gurin kakanninmu cewa
A shekarun baya an tabayin wani hatsabibin boka wanda a wannan zamanin
Babu wanda ya kaishi shu'umanci har zuwa yanzu
Duk rashin imanin mutum bai isa ya kwatanta rashin imani ko irin azabar sa ba
Wannan daliline yasa ake masa lakabi da sahibul ukub
Wasu kuma sunayi masa lakabi da tauraruwa mai wutsiya saboda ganinsa ba alheri bane
Duk inda ya baiyana sai yayiwa kasar gurin ado da jinin mutanen da suke rayuwa agurin
Har wasuma nayi masa kirari da guguwar annoba
Babu irin salon zaluncin da bai sani ba
Domin duk azzaluman da kake ganin sun cika zalunci to shi suke kwaikwaya
Inta kaice makama duk duniya a wancan zamanin saida suka koma bauta masa
Na sami labari agurin kakana cewa shi wannan bokan
Ya taba haduwa da wani sadaukin jarumi ma'abocin addinin musulunci ana kiransa da suna hassanul basari
Suka fafata kazamin yaki dashi daga baya ya sami nasarar
Hallaka boka sahibul ukub, saidai ba anan gizo yake sakar ba
Domin an kashe maciji ne ba'a sare kansa ba,
Saboda ita kanta gangar jikinsa bacewa tayi ba'a sake ganinta ba
Saidai masu bincike sun tabbatar da cewa nan da wasu shekaru masu zuwa zai sake bayyana da wata bakuwar fuskar wacce ba'a santa ba
Don haka idan mukayi tunani akan abindaya faru zaka ga cewa
Duk cikin nahiyar nan in banda kai babu mutum mai karfin damtsen ukibanu
Sannan kuma shi mutum ne mai tsananin karfin sihiri
Idan kayi la'akari da irin kisan da aka dinga yiwa mutanen birnin keraya
Zakaga cewa kisan ba'ayi amfani da makami ba alokacin yinsa
Kuma da ace da karfin damtse akayi wannan fafatawa
Dolene labari yazo har nan ya samemu har muje mukai musu dauki
Ballantana ma uwa uba cewa
Nayi amfani da gaba daya sihirina amma na kasa ganin wanda ya aikata wannan barna
Abisa wannan daliline yasa na tabbatar da cewa boka sahibul ukub ne
Ya dawo a cikin wannan zamanin da muke ciki
Idan kuma baka yarda ba inaso ka danyi hakuri daga nan zuwa kwanaki biyu
Zaka gasgata maganata, kai in takaicemaka hatta shi kan wannan mujiyar daka gani an ajiye atsakiyar birnin keraya itace shaidar da boka sahibul ukub yake bari aduk inda yakai hari
Abinciken da nayi yanzu na gano cewa akwai wata budurwa
Wacce ta baro gida domin neman shi boka sahibul ukub din
Domin tsafi ya tabbatar da cewa itace zata hanashi aikata wannan zaluncin
Tabbas itama jarumace ta hakika amma kuma bata da karfin sihirinsa
Zatasha wahala duk lokacin da suka hadu da ita amma
duk wuyar da zata sha ba zata mutu ba
Saboda akwai alaka mai karfi atsakaninsu
Dajin haka sai hankalin sarki kalkus ya tashi ya tambayi shamsal yace
Shin a ina zan sami wannan budurwa inje in tareta mu hada karfi da karfe
Mu kawo karshen sahibul ukub?
Dajin wannan tambaya sai boka shamshan ya bushe da dariya sannan yace
Ai zaifi kyau kahakura ka zauna acikin masarautar nan taka don wanda yayi karo da sahibul ukub to kamar yayi karo da ajalinsa ne
Koda jin haka sai sarki kalkus ya daka masa tsawa yace
Kai karya kake yi dolene nima na fita nemansa da kaina domin na kare kimar kasata
Nanfa boka shamshan ya fara kokarin shawo kansa amma yaki hakura
Ya kama hanya ya fita daga gidan sarautar
0======[=========≠=====>
Lokacin da walisa ta kama hanya da nufin idan ta sami wani garin ta yada zango acikinsa
Tana cikin wannan tafiyar ne ta iso bakin wata katuwar korama
Wacce ruwa yake gangarawa cikinta a wannan lokaci daga ita har wannan dokin nata sun gaji saboda

Please Login or Register in order to submit comment