Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta rufe fuskarta gaba daya idanunta kadai ake iya gani ta cikin kofar bakin kyallen
Ba kowa bace wannan budurwa ba face gimbiya walisa
A tarihin rayuwarsa ba'a taba kaishi kasa ba afilin daga
Amma sai gashi yau an sami budurwa mace wacce ta iya yi masa dukan
Da badon yayi da gaske ba sai ya fadi kasa
Dalilinta kawai na shiga wannan gasa shine tana son ta gwada jarumtakarta akan ta sarki aryan
Domin ta gani da idanunta tabbas sarki aryan ba kanwar lasa bane a fannin jarumtaka
Nanfa aka tsaya ana kallon kallo atsakaninsu ya tambayi kansa
Yace wannan wacce budurwace mai irin wannan karfin dukan
Daga can sai duk su biyun suka kwarara uban ihu sannan suka falfalo da gudun gaske
Kan juna suna masu kaiwa junansu mugayen hare hare cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta
Wohoho hakika fadan manyan dawa daban yake dana kanana
Ai kuwa suna fara fadan ne filin ya hargitse fiye da baya kai kace mutum dari ne suke kafsawa
Karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne, idan makamansu suka hadu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi
Kura kuwa ta turnuke tsakiyar filin tun ana iya hangosu har saida ya zama sun biya acikin kura sai kana da karfin ido sosai sannan zaka iya hangosu
Wohoho! !
Hakika irin wannan fadan ake cewa turnuku fadan iblisai

Sai gashi mutum biyu kacal sun debe gaba daya hankalin ýan kallo
Da zarar daya daga cikinsu ya kaiwa wani hari idan ya kauce takobinsa ta sauka akasa saidai kaga ya haifar da wani wawan rami
Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda iya yakinsu ya kusan zuwa daya tamkar a makaranta daya aka koyar dasu
Shi kansa sarki aryan yayi matukar mamakin yadda akayi ya kasa samun galaba akanta farat daya
Domin bai taba haduwa da mutum mai karfin damtsenta ba
Haka itama abangarenta tayi matukar mamakin yadda karfin damtsensa da nata suka kusan zuwa daya
Alhalin tunda take bata taba shafe dakiku sittin tana fada da wani ba ba tare da tayi nasara akansa ba face dan uwanta yarima walisu wanda yanzu take kan hanyar nemansa
Kai wani lokacin ma sai kaga har tashi sama suke kamar tsuntsaye suna kaiwa junansu hari a sama
Kai sai kayi zaton cewa mikiyoyi ne guda biyu suke fada
Saida suka shafe sa'a biyu suna wannan fafatawar ba tareda dayansu ya sami nasara aka daya ba
Bisa dole duk su biyun suka ja da baya suka tsaya suna kallon kallo kamar zakaru
Sai a sannan ne sarki aryan yaji akaron farko na rayuwarsa ya hadu da macen data burgeshi
Kuma yaji a yanzu babu abinda yake bukata face yaga fuskarta
domin tun daga kallon yanayin dirin jikinta dolene ta kasance kyakykyawar budurwa ta gaban kwatance
Dayin wannan tunani kawai sai ya kudurce a ransa cewa dolene sai ya san hanyar da yabi ya kwance bakin kyallen da bakuwar jarumar ta rufe fuskarta dashi don yaga wacece ita
Koda gama yin wannan tunani sai duk su biyun kamar hadin baki sukayi kukan kura suka kara afkawa junansu da harin daya zarce irin farko
Wannan karon sai duk su biyun suka sauya salon fadan da sukeyi suka fara hadawa da kai naushi gami da kutufo, hannu da kafa
Kai kace dama can sun kasance abokan gaba
sai gashi duk su biyun suna laftar jikin junansu shi kuwa sarki aryan a wannan lokaci burinsa kawai shine ya bude fuskar wannan bakuwar jaruma
Koda suka sake shafe wasu dakiku masu yawa suna wannan fafatawar kuma gimbiya walisa taga ta kasa samun nasara akan sarki aryan
Sai kawai ta fusata ta shureshi sama kamar wani dan yaro tayi wulli dashi
Ai kuwa sai shima ya wulkila jikinsa kamar dan biri sannan ya diro kasa
Sannan shima ya daka wani mahaukacin tsallen yayo kan jarumar da nufin yasa hannunsa ya cire kyallen data rufe fuskarta dashi kota halin kaka
Cikin sauri gimbiya walisa ta sunkuya ya shuri iska sannan suka sake dawowa suka kara kachamewa da wani sabon fada
Ai kuwa ana fara fadan ne aryan ya sammaci jarumar ya doki kafafunta da kafarsa guda don ta fadi kasa
Aikuwa take ta sulale kasa zata fadi amma sai ta saka hannayenta ta tokare bata yarda itama taje kasa ba
Kai tun suna iyayin fadan a tsaye saida ya kai sun kasa tsayawa
Sai azaune suketa hadawa junansu jini da majina
Suna cikin wannan fafatawar ne kwatsam sai dan kyallen da walisa ta rufe fuskarta dashi ya kwance ya fadi kasa
Take anan gurin kowa ya gane ko wacece ita shi kuwa sarki aryan sai ya kame kamar wanda aka zare masa lakar jikinsa
Ya tsaya kyam yana kallonta ko kifta idanu bayayi, domin ji yayi akaron farko ya hadu da budurwar da zuciyarsa ta kamu da soyayyarta take fuskarsa ta fadada da murmushi
Ya manta da gurin da yake da kuma matsayinsa kawai sai ya dubeta yace
Yake wannan jaruma tabbas kece gimbiya walisa ýa agurin mai girma sarki fadarul munnar
Shin menene dalilin dayasa kika boye kanki agaremu ba tareda kin bayyana kanki ba domin mu hada taron yi miki barka da zuwa wannan birni namu mai albarka ?
Kuma me yasa na ganki ke kadai a wannan lokaci ba tareda dan uwanki yarima walisu ba?

Tabbas tun farkon fara fadana dake jikina ya bani cewa dole ina fada ne da gimbiya walisa
Domin duk manyan jaruman da suke wannan nahiya dama wasu nahiyoyin inada hoton fuskasu a masarauta ta
Da kuma salon yakin kowanne daga cikinsu, ni kaina na tabbata da ace mun cigaba da yaki dake nasan kece wacce zatayi nasara akaina
Domin sadaukantaka da sa'a acikin jininku yake ke da dan uwanki yarima walisu
Don yanzu hakama ýan kallo shaida ne kan cewa kece wacce tayi galaba akaina
Domin kin yi mini kyawawan duka har guda biyu ni kuma nayi miki daya
Saboda haka ayanzu ma kece kikayi nasara akaina kuma koda an ci gaba da fada yanzu tsakanina dake
To na rantse harda karagar mulkina kece zakiyi nasara akaina
Acan bangaren ýan kallo kuwa hankalinsu gaba daya ya tafi zuwa tsakiyar fili
Suna ganin abinda yake faruwa tsakanin sarki aryan da gimbiya walisa
Koda gimbiya walisa taji tambayoyin da sarki aryan yayi mata sai kawai tayi guntun murmushi wanda ya bayyana mata tsananin kyawunta
Sannan tace
Ya kai wannan adalin sarki ka sani cewa dalilin dayasa kaga ban sanar daku shigowata wannan birni ba shine
Yanzu haka na baro gidane domin gudanar da wani uzurine wanda mahaifina ya saka ni
Tambayar da kayi kuwa game da dan uwana yarima walisu shine
Yanzu haka bana tare dashi kuma ban san inda yake ba
Bayan haka ina neman afuwarka kan rashin shiga gasa da wuri da banyi ba nazo amakare
Amma na biya alkalin gasa gaba daya kudin tikitin da kuke bukata
Koda gama fadin haka sai kawai tayi girgiza ta zama wani farin hayaki sannan hayakin ya tashi sama cikin gajimare ya bace bat
Shi kuma sarki aryan sai ya daga kansa yabi hayakin da kallo har saidaya bace masa bat da gani
Koda mutanen da suke filin sukaga wannan al'amari daya faru sai gaba dayansu suka cika da tsananin mamaki kuma suka dada tabbatarwa cewa itadin shu'umar yarinya ce
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A FILIN GASA BAYAN GIMBIYA WALISA TA BAR FILIN GASA
***** ******* ******* ******
Acan kuwa al'amarin gimbiya walisa koda tabar filin gasar
Bata baiyana ako'ina ba sai cikin gidan sarkin kasuwa yimana
Ranta a matukar bace domin bataso fuskarta ta bayyana ga mutanen gari ba
Ta gaba da gasar da takeyi domin ita kanta Jarumtakar sarki aryan ba karamin burgeta tayi b
Da kuma irin salon kalaman daya dinga furta mata kawai sai ta tashi
Ta tafi jikin madubi domin ta duba fuskarta, koda ta karasa gabansa sai taja da baya a tana mai zare takobin ta
Ba komai ta gani ba face fuskar sarki aryan fuskarsa cike da murmushi
Ya taho yana shirin rumgumeta akirjinsa sai daga baya ta fuskanci cewa idanunta ne suka nuna mata haka
Koda ta fuskanci haka sai kawai tayi murmushi taje ta sami waje ta zauna
Zamanta keda wuya sai tunanin dan uwanta yarima walisu ya kara fado mata aranta
Da kuma irin kalaman da wannan saurayin yake fada mata amafarki
Koda yin wannan dan tunani sai taji gaba daya hankalinta bai kwanta ba
Taji kamar ta tashi ta fice daga cikin garin ta tafi nemansa
Koda yin wannan tunanin sai kawai ta dauko madubin tsafinta ta shafeshi
Aikuwa koda ta shafeshi saiga hoton ko'ina na cikin duniya ya bayyana ajikinsa
Kuma gashi nan kowa yana gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali kamar yadda suka saba
Amma duk da haka sai taji hankalinta bai kwanta ba da zaman garin dolene tayi kokari ta fice daga cikinsa cikin kankanin lokaci
Kafin shirinta ya fara neman rushewa domin a yanzu ta fahimci akwai bakon al'amarin dayake shirin faruwa agareta
Tana cikin wannan tunanin ne kawai sai taji an kwankwasa kofar dakin da take ciki
Take tayiwa mai kwankwasawar izinin shigowa
Ba kowa bane ba face sarkin kasuwa yimana ya bude kofar dakin ya shigo fuskarsa cike da alamun damuwa karara akanta
Da shigowarsa sai ya sami waje kusa da ita ya zauna ya fuskanceta yadda suna iya kallon juna atsakaninsu
Tsawon ýan dakiku babu wanda yacewa daya kala,
Daga can sai yayi gyaran murya yace yake walisa tunda dai
Yanzu an gama wannan gasar to ina mai baki shawara daki kama hanya ki tafi gabatar da aikin da yake gabanki
Domin na fuskanci akwai alamun soyayyarki ta shiga zuciyar sarki aryan
Nasan cewa sarki aryan bai isa ya tilasta miki akan ki soshi ba .
Amma ita soyayya shegiyar abace domin tana da matukar hadari fiye da makami
Akoda yaushe soyayya tana iya shiga zuciyar mutum kuma da zarar ta shiga
Shikenan zata sa shi ya manta kansa da asalinsa daga karshe kuma tana iya sakashi ya rusa duk wasu burika nasa na rayuwa
Idan har kinaso ki cika burinki da kuma burin mahaifinki dolene ki gaggauta barin wannan birni tun kafin sarki aryan ya gano cewa a gidana kike zaune yazo ya sameki da kansa ya bayyana miki sirrin zuciyarsa
Kuma ayanzu zai iya haukacewa akanki har ya gwammace daya rasa komai nasa muddin zai sameki
Tunda kema da kanki kinji labarin abindaya faru akansu SADAUKI HASSANUL BASARI DA KUMA GIMBIYA BAHJHAT
Kodajin haka sai ta kara dubansa da sauri tace ai har yanzu ban karasa jin wannan daddadar hikayar ba
Ina mai rokonka don darajar iyayenka daka karasa bani labarin wannan hikayar yanzu kafin na tafi na bar muku wannan birni in tafi aikin da yake gabana
Dajin haka sai yimana ya gyada kansa kamar yanayin wani nazari daga can kuma sai yace ai shikenan sai mu karasa farfajiyar gidannan tunda anan na ajiye wannan kayataccen littafi
Da gama fadin haka sai ya shige gaba ya fice daga dakin
Sannan itama walisa tabishi. Abaya har suka isa farfajiyar
Da zuwansu sai duk su biyun suka sami guri suka zauna
Kawai sai yasa hannunsa ya janyo wannan littafin wanda HIKAYAR SADAUKI HASSANUL BASARI DA GIMBIYA BAHJHAT YAKE CIKI
ya bude daidai shafin da suka tsaya ya fara karantashi a fili kamar haka

****- ****** ****** ******
Lokacin da boka sahibul ukub ya rikide ya koma siffar bakar guguwa
Sai gaba daya fadar tasa ta dinga girgiza kamar zata tashi tabar kan doron kasa
Take guguwar ta ratsa ta cikin saman rufin fadarsa fit ta fice
Cikin abinda bai wuce kiftawar ido ba, sai gashi yana tsala azababben gudu a sararin samaniya kamar giftawar tauraruwa mai wutsiya
Duk garin daya zo giftawa ta gabansa saidai kaga ana ruwan duwatsu a garin
Halittun da suke rayuwa a yankin suna faduwa kasa matattu
Hakika duk inda cikakken mara imani yakai to boka sahibul ukub ya wuce wannan matsayin
Domin babu abinda yake sakashi farinciki dajin dadi sama da ya ga jini yana fantsama akasa, da kuma ganin ýan uwa suna kukan rabuwa da masoyansu
Shi kuwa in banda kyalkyala dariya babu abinda yake domin shi burinsa kenan
Yaga jini yana gudu akan kasa ,a haka cikin lokaci kankani ya isa birni shawana
Alokacin sarki mayasin yana kan karagar mulkinsa yana gudanar da harkon mulkinsa ga fadawa nan da mutanen gari duk a zazzaune babu wanda yake da matsala
Adaidai wannan lokacin ne boka sahibul ukub ya baiyana acikin birnin cikin sararin samaniya
Da zuwansa sai gaba daya sararin samaniyar birnin harma da makotansu tayi duhu
Kai sai kayi zaton tsakiyar dare ne, koda bayyanarsa sai kawai ya karanta wadansu dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya saiga wasu irin manyan bakaken mikiyoyi suna saukowa daga sararin samaniya
Kowanne daya daga cikinsu yakai girman bishiyar kuka
Suna da baki mai tsawo da kuma tsini wanda idan suka caki abu dashi take yake hudashi koda kuwa dutsene
Kafafunsu ma dogayene kamar na jimina sannan suna da farata masu matukar tsini
Adadin wadannan mikiyoyi yakai kimanin dubu biyar
Kuma dukkansu girman jikinsu daya babu wanda yafi wani daga cikinsu
Ai kuwa koda gama bayyanarsu sai nantake boka sahibul ukub ya umarcesu dasu dasawa mutanen birnin shawana wawa
Ai kuwa nantake mikiyoyin suka sauka kasa sukayi dirar mikiya acikin birnin
Suka dinga fadawa kan mutane suna ragargaza naman jikinsu
Babu ruwansu kai komai rashin imanin mutum dolene ya tausaya mutanen wannan birni
Ganin yadda wadannan tsuntsaye suka dinga farka cikin mutane suna hadiye kayan cikinsu
Da kuma soke idanunsu da tsinin hakoransu suna kwakule kwayar isonsu
Su tauneta saidai kaga mutum babu kwayar idanu jini yana zuba daga kurmin idanun yana ta faman ihu
Sannan wani mikiyar yazo ya karasa farke cikinsa ya kwakule kayan cikinsu
Sannan su tashi sama
Cikin kankanin lokaci birnin ya cika da iface ifacen mutane
Kuma gawarwaki suka barbazu ako'ina na cikin babu kyan gani

SHIN BOKA SAHIBUL UKUB ZAI SAMI NASARAR KASHE MUTANEN BIRNIN SHAWANA KUMA HAR YA DAUKE GIMBIYA BAHJHAT YA KAITA CAN FADARSA?
TSAKANIN SARKI ARYAN DA GIMBIYA WALISA WANENE YA KAMU DA SOYAYYAR WANI?
WANNE MATAKI SARKI MAYASIN ZAI DAUKA AKAN BAYYANAR BOKA SAHIBUL UKUB?

DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT
**************ZUBAR DA JINI

****************6 PART A

*****************LBR

HABIBULLAH KBR


Ihu da iface ifacen mutane ya cika birnin yimana gaba daya
Duk inda ka kalla babu abinda zaka gani face jinin mutane yana ta malala akasa
Kamar an bude magudanar ruwa babu abinda zai baka tausayi
Face ganin yadda za'a kashe da a gaban Mahaifinsa
Ko kuma akashe uba agaban dansa, babbar matsalar wadannan mikiyoyi Itace
Ko kadan makami baya tasiri ajikinsu kuma gasu da karfin tsiya
Domin koda ace cikin gida mutum ya shiga don ya buyar musu
Sai sun biyoshi ciki komai kwarin ginin gidan nasa kuwa
Domin suna iya rusa gini duk kwarinsa kamar mutum ya sami biskit
Shi kansa kukan wadannan mikiyoyi ya isa abin tsoro
Domin shi kansa yana iya razana mutane mai jin fitsari yayi a wando. Ba tareda ya sani ba
Ko mace mai ciki ta haife dan dake cikinta ba tareda lokacin haihuwarsa yayi ba
Awannan lokaci sarki mayasin yana tsaka da fadanci sai kawai ji sukayi
Saman rufin gidan sarautar ya fara girgiza yana zabtarowa kasa yana danne mutane
Take itama fadar ta hargitse kowa ya fara neman gurin buya amma ina sun makara domin ko sun buyan ba zasu kubuta daga sharrin mikiyoyin ba
Tunda suke basu taba ganin bala'i kwatankwacin wanda suke ciki yanzu ba
Kafin suyi wani yunkuri tuni mikiyoyin sun yaye rufin fadar gaba dayansa
Suka shigo ciki suka cin karensu babu babbaka nanfa gaba daya manyan gari suka cakude da talakawa har suna turereniya atsakaninsu don kawai su samu su tsira da rayuwarsu
Kai koda sarki mayasin yaga irin barnar da wadannan sihirtattun halittun sukeyi masa sai ya kwarara uban ihu
Sannan ya zare takobinsa ya tunkari wadannan mikiyoyi suka kachame da azababben yaki
Wohoho ai kuwa koda ya shiga cikin wadannan mikiyoyin sai ya dinga kai musu mugayen hare hare
Don ganin ya tarwatsa su da karfin tsiya amma abin da bai sani ba shine
Su wadannan mikiyoyi ba irin wadanda ya saba gani bane
Domin su an kirkiresu ne daga duwatsun wuta masu karfin gaske
Don haka babu wani makami wanda zaiyi tasiri ajikinsu
Koda ya shiga cikinsu sai kawai suka kachame da azababben yaki atsakaninsu
Amma duk abinda yake takobinsa taki tayi tasiri ko kadan ajikinsu
Kuma cikin kankanin lokaci ya gaji sakamakon yawan wadannan mikiyoyi
Don haka sai ya fara neman hanyar da zai gudu ba shiri ya tarwatsa su da karfin tsiya
Ya falfala da gudun gaske ya fito daga cikin gidan sarautar
Ai kuwa da fitowarsa sai yaga birnin ya cika makil da gawarwakin mutanen kasarsa
Babu ko mutum daya wanda yayi saura acikinsu sai shi kadai
Koda ya daga kansa sama sai yaga ta cika makil da irin wadannan mikiyoyi
Sai shawagi sukeyi kamar kudajen zuma
Nantake ya tuna da batun ýarsa wacce yake matukar kaunarta
aduniya wato gimbiya bahjaht
Wacce ya wulakantata agaban talakawansa ya kaita gidan kurkuku ya kulle kawai saboda ta kamu da soyayyar SADAUKI HASSANUL BASARI
Inda ace hassanul basari ya san irin danyen hukuncin daya yiwa masoyiyarsa gimbiya bahjaht ya tabbata sai ya dau mataki akansa
Inda ace kuwa ya barshi tareda ita kuma ya jawoshi jikinsa
Da ya tabbata shi kadai zai iya karesu daga sharrin wandannan mugayen halittu kamar yadda ta
karesu daga sharrin wannan basamuden dodon
Kodayin wannan
tunani sai nantake yaji nadama tazo masa akaron farko na abindaya aikata
Koda gama wannan tunani sai kawai ya yi kukan kura ya
daina gudun ceton ransa domin ya tabbatar da cewa mutuwa zaiyi
Ya tunkari wadannan mikiyoyin ya cigaba da kai musu sara da suka
Ba karamin kokari sarki mayasin yayiba a wannan karon
Amma kuma duk kokarin sai ya zama na banza domin ko guda daya daga cikinsu ya kasa kashewa kuma tuni sun fara ji masa ciwuka
Ana cikin hakane wani katon mikiya ya taho ta bayansa
Ya caka masa faratun kafarsa agadon bayansa suka fito da kirjinsa sannan yayi sama dashi
Nantake sarki mayasin ya kwarara uban ihu saboda zafin fitar rai
Kawai sai ya saki takobinsa ta fadi idanuwansa suka kakkafe ya zama gawa
Ai kuwa take mikiyoyin suka dasa masa wawa kowa yana cirar abinda yake bukata
Kafin kace kwabo sunyi masa filla filla ma'ana sun gama cinye naman jikinsa saura kashushuwa kadai ne suka rage
Amma kowa na garin babu wanda bai mutuba, koda ganin irin mutuwar wulakancin da sarki mayasin yayi
Sai boka sahibul ukub ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta amsa kuwa agaba daya ilahirin rusashshen birnin
Kai hardama biranen da suke makobtaka dasu,kawai sai ya dauko mushen kan shaho ya kafe a tsakiyar garin
sannan ya sake rikidewa ya kara komawa bakar guguwa
Ya tafi can gidan kurkukun darul maut wadannan mikiyoyi suna biye dashi abaya
Idan ka gansu sai kayi zaton dandazon kudajen zuma ne
Cikin dakika guda suka isa kurkukun darul maut aikuwa
Suna isa sai wadannan mikiyoyin suka saki fuka fukansu suka sauko kasa

Awannan lokaci gimbiya bahjaht tana cikin dakin da aka daureta
Shikuwa uzumnal yana can adaure dakaru sunata gana masa azaba
Kwatsam adaidai wannan lokaci sai ji sukayi wani irin sautin kukan tsuntsaye mara dadin ji ya cika gidan kurkukun gaba dayansa
Kafin su ankara tuni mikiyoyin sun tarwatsa rufin fadar sun faso cikinta
Suna ta cinye komai da kowa dake cikii,nanfa itama wannan kurkuku ta hargitse ta cika da ihun mutane domin kowa ganin mutuws yake muraran agabansa
Kafin cikar dakika hudu har sun gama cinye komai na kurkukun
Abu biyune kadai basu taba wadannan abubuwa kuwa ba komai bane su ba face gimbiya bahjaht dakuma hadiminta uzumnal
Aikuwa koda mutuwar kowa dake cikin kurkukun sai duk wadannan mikiyoyin suka bace bat kamar basu taba wanzuwa ba
Kawai sai wata iska mai karfi tazo ta shuri su gimbiya bahjaht tayi sama dasu har zuwa inda boka sahibul ukub yake
Da isarsu daidai inda yake sai ya tsaya ya kare musu kallo sama da kasa
Sai ya bushe da dariya, wacce kararta ta zagaye nahiyar gaba daya sannan yace
Nayi farincikin samunku araye domin yanzu daku zan tafi can fadata
Har sai masoyinki hassanul basari ya kawo kansa sannan zan hadaku gaba daya nayi muku kisan gilla
Dajin haka sai bahjaht ta dubeshi fuskarta a murtuke tace
Karya kakeyi azzalumin banza ka sani inamai tabbar maka da cewa kai baka isa kayi galaba akan mu ba muddin kukayi ido hudu da kai da hassanul basari ina yi maka rantsuwa da ubangijinsa sai yayi nasara akanka
Koda boka sahibul ukub yaji ta rantse da ubangijin da hassanul basari
yake bautawa sai ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa sannan yace
Lallai yarinya kin tafka babban kuskure da har kika yarda da ubangijin musulunci kuma har kike tunanin zai iya taimakon hassanul basari har ya sami galaba akaina
Ina tabbatar miki da cewa inda ace gaba daya mutanen duniya dama na wasu duniyoyin zasu hadu domin
yakata basu isa su sami nasara ba akaina ballantana kuma wani mutum guda daya wanda bashi da sihirin komai a tare dashi
Amma nayi mamakin abinda shi hassanul basari yayi miki wanda yasa har kikayi saurin yarda dashi kika bijirewa mahaifinki
Har kuma yasa ki kika fara yarda da ubangijinsa ,kike nema ki bijirewa addinin da kika gada ke da iyayenki na bautar gumaka
Wanda duk duniya shine addinin gaskiya
Kodajin wannan batu sai kawai sai tayi murmushi sannan tace
Babu wani abu dayayi mini kawai dai ni da kaina naji na gamsu da addininsa fiye da wanda naga iyayena sunayi
Domin da idona naga karfin ubangijinsa alokacin daya taimaki hassanul basari ya bashi karfin daya iya kashe masifar maridin daka aiko mana
Tabbas yanzu na gane ko wanene kai,
Kaine boka sahibul ukub wanda naji sunanka abakin maridin dodon daka turo domin ya baje birnin mu
Ganin maridin naka ya kasa samun nasara ne akanmu yasa kayi tattaki da kanka kazo har birnin mu ka ruguzashi
Shine yanzu kazo nan domin ka daukeni ka kaini can fadarka domin kayi garkuwa dani……. .
Tun kafin ta karasa maganar da takeyi sai boka sahibul ukub ya daka mata tsawa
Wacce tasa taji kamar zuciyarta zata faso kirjinta ta fito waje
Kawai sai yace da'ita wannan kuskure nane da har na tsaya ina cacar baki dake
Kinyi sa'a inada buri akanki amma badon haka ba da yanzu take zan hallaka ki dake da hadimin naki
Yana gama fadin haka sai ya hura musu wata irin iska daga cikin bakinsa
Take iskar ta Shiga cikin jikinsu gaba daya
Sai gashi duk su biyun sun fara kankancewa suna zama kanana
Kafin dakika biyu su cika har sun kankance sun zama kamar girman jinjirayen maguna
Sannan ya dauko wata ýar karamar akwati duk su biyun ya zurasu aciki
Sai gasu duk su biyun sun zauna acikinta kamar suna cikin daki ba tareda sun matsuba
Sannan ya zura akwatin acikin aljihunsa, ya kara rikidewa zuwa siffar bakar guguwa
Ya kama hanyar komawa fadarsa

WANNAN SHINE ABIDAYA FARU ACIKIN BIRNIN SHAWANA BAYAN BOKA SAHIBUL UKUB
YA SHIGA CIKINSA YA KASHE KOMAI DA KOMAI NA CIKIN SA
SANNAN YA SACE GIMBIYA BAHJAHT DAGA GIDAN KURKUKU YA TAFI DA ITA CAN FADARSA WACCE TAFI KO'INA NA DUNIYA HATSARI
0======(::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Acan kuwa al'amarin jarumi hassanul basari tun daga ranar da suka gana da gimbiya bahjaht sanda ta kawo masa ziyara lokacin yana cikin daji
Sai ya koma gida cikin farinciki da begen gimbiya bahjaht domin a wannan ne farkon fara yin soyayyarsa kuma sai tayi masa mugun kamu
Ma'ana ta shiga zuciyarsa da karfi yaji ayanzu duk duniya babu abinda yake so kuma yake burin gani kamar gimbiya bahjaht
Kai tsaye ya kama hanyar komawa gida yanata tunanin gimbiya bahjaht da kuma begenta acikin zuciyarsa
Domin ko iskace tazo giftawa ta kunnensa babu abinda yakeji face sautin muryarta
Hoton fuskarta suka dinga yi masa gizo akan idonsa
Ahaka ya koma sansaninsu cikin

Please Login or Register in order to submit comment