Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai gashi suna kawo masa mugayen hare hare da makamansu

ME ZAI FARU A WANNAN FAFATAWAR ?
WANENE MAI NASARA A TSAKANINSU?
INA LABARIN ALJANI KHADIMUL ISLAM?
SHIN HASSANUL BASARI YANA SAMUN NASARAR DAUKE GIMBIYA BAHJAHT?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS***************ZUBAR DA JINI

****************8 PART C

LBR

**************** HABIBULLAH KBR

Lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin hassanul hassanul basari da wadannan dakarun na boka sahibul ukub
Sai suka kasance suna masu kai masa munanan hare hare ta kowanne sashi sama da kasa
Shi kuwa ya wanzu shi kadai a tsakiyarsu yana mai karewa tareda mai da musu martani
Nanfa ya zame musu kadangaren bakin tulu domin duk da wannnan yawa nasu sai ya zamo na banza domin sun kasa samun nasarar koda shafar fatar jikin
Kuma babban abinda yake firgita wadannan dodannin shine
Wannan hasken da yake fita daga jikin sandar tasa domin yasa ma basa iya ganin abinda yake gabansu
Saboda haka nema yasa duk bangaren da hassanul basari yakai duka da tsini ko kaifin sandar dake hannunsa
Duk wanda ya samu take zakaga ya kumbura sannan kuma yayi bindiga ya fashe
Cikin kankanin lokaci ya gigita su ya zame musu kamar guguwar annoba
Duk inda ya ratsa saidai kaga suna zubewa kasa kamar ana sassabe agona
Jini kuwa ya dinga fallatsa sassan jiki suka dinga yawo a saman iska
Ihun su da gurnaninsu ya cika filin gaba daya shi kansa
boka sahibul ukub yayi matukar mamakin yadda hassanul basari
yake da tsananin zafin nama juriya da bajinta kamar jikinsa bana jini da tsaka bane
Ba komai ne ya bashi wannan karfin ba face addu'o'in da yake karantawa acikin zuciyarsa
Cikin kankanin lokaci ya gama kashesu gaba ki dayansu guda daya baiyi saura ba acikinsu
Ya zamana daga hassanul basari sai boka sahibul ukub a tsaye suna kallon juna
Sahibul ukub har wani gyatsine yakeyi da fuska saboda matukar fusatar da yayi
Cikin shammace sai kawai ya shammaci hassanul basari ya watso masa wata iriyar bakar wuta ta tsafi
Cikin bakin zafin nama hassanul basari ya daka tsalle ya kaucewa wannan wutar
Take kuwa wutar ta nutse acikin kasa wanda sanadin hakan saida ta haddasa katon rami a gurin tareda girgizar fadar gaba dayanta
Kafin hassanul basari ya kara motsawa daga inda yake tuni ya bayyana a kusa dashi tareda kawo masa mahaukacin duka da wannnan sandar ta hannunsa
Nantake shima ya sanya tasa sandar ya kare wannan dukan
Sakamakon haduwar sandunan nasu ne ya haddasa wata irin tsawa da walkiya a agaba daya ilahirin gurin
Saboda karfin dukan saida hassanul basari ya durkushe kasa bisa kafafunsa
Shi kuwa sahibul ukub ji yayi gaba daya sandar tsafinsa ta dauki wani irin zafi sakamakon haduwa da sandar hassanul basari wanda a baya bai taba jin irin wannan sabon yanayi ba
Don haka sai ya fahimci tabbas akwai wani babban al'amari akanta
Koda gama yin wannan tunani sai nantake ya rintse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi
Ai kuwa yana gamawa sai nan wata iriyar iska mai karfin tazo ta shuri hassanul basari tayi sama dashi ta dinga wujijjiga shi
Kamar ba bil'adama cikin kankanin lokaci kuwa ya fara neman fita daga hayyacinsa
Don haka baisan lokacin daya kwala kabbara da karfi ba
Ai kuwa nantake sai wannan guguwar ta sakeshi
Kai a wannan lokaci saida sahibul ukub yayi sihiri sama da kala dubu domin yaga ya hallaka shi amma abu ya gagara
Don haka nantake yayi wani sihiri na karshe wanda yasa fadar gaba dayanta tayi duhu sosai yadda koda tafin hannunka ba zaka iya gani ba
Ba komai ne yasaka shi aikata hakan ba face yasan cewa dolene bazai gudu yabar fadarsa ba saidai acikin biyu ayi daya
Ko shi da hassanul basari wani ya kashe daya ko kuma dukkansu su biyun suyi ragas
Ai kuwa koda duhun ya gama mamaye fadar sai duk su biyun suka afkawa junansu da mahaukatan hare hare masu matukar hatsari da barazana ga rayuwa

Duk wannan abu da yake faruwa tsakaninsu gimbiya bahjaht da bawa zamnal suna can gefe daya a daure suna kallo
Kuma boka sahibul ukub ne da kansa ya daure su ajikin wata
dirkar gini tareda rufe musu bakunansu bayan ya dawo dasu ainihin suffarsu
Acan kuwa al'amarin manyan gwarazan kuwa koda duhu
Ya mamaye fadar sai suka afkawa junansu da gagarumin yaki
Fiye da wanda sukayi da farko domin wannan shi ake cewa gumurzun sadaukai
Karar haduwar makamansu ta cika dodon kunne duk wanda
ya kaiwa wani farmaki idan ya kauce duk abinda da suka sama
saidai kaga take sun dagargazashi Hakama idan ganuwar
ginice komai girmanta saidai kaga sun raba ta biyu kamar an bara tuffa
Wani irin tartsatsin wuta ya cika ilahirin gurin
Tartsatsin wuta kuwa ya dinga fallatsa a ko'ina sanadin hakane yasa wuta ta dinga kamawa ako ina
Kamar anayin gobara saiga karfi yana neman yazo daya
Domin kowanne daga cikinsu yana matukar jin jiki shi kansa
hassanul basari saida yayi mamakin irin karfin damtsen da sahibul ukub yake dashi
Daga karshe saiya kaddara azuciyarsa cewa lallai wannan karfin damtsen ba nasa bane aikine duka na sihiri

Abinda bai sani ba shine boka sahibul ukub ya dade yana baiwa kansa horon yaki mai tsanani saboda gudun zuwan irin wannan rana
Kuma shima tun yana yaro karami allah yayi shi mai karfin gaske
Domin tun kafin ya fara samun sihirin tsafi da karfin
damtsensa yake zaluntar yara sa'anninsa kai har dama
wadanda suka girmeshi kuma tun farkon fara wannan fafatawar tasu duk sihirin tsafinsa ya daina tasiri
Wannan dalilin ne yasanya
Hatta sarkokin daya daure su gimbiya bahjaht duka suka tsitstsinke
Amma dukajsu sai suka buya suka ki yarda su fito suna kallon wannan bakin artabu
Ba komai ne ya hanasu fitowa ba face ganin yadda manyan dirakun gini suke zubuwo kasa suna turmushe duk abinda yake gurin
Wuta kuwa ta dinga ci a ko'ina acikin fadar kamar ana zuba mata makamashi
Saida suka shafe sa'o' masu yawa suna wannan fafatawa ba tareda dayansu ya sami nasara akan wani
Don haka sai sahibul ukub ya wullar da sandar dake hannunsa gefe daya
Ya tsaya cak cikin nuna alamun yarda da kansa yace
Ya kai wannan matashin saurayi kuma abokin gabata
Na fuskanci cewa idan zamu shekara muna wannan fadan namu da makami babu wanda zai yi nasara akan wani
Don haka nake ganin idan har ka yarda da kanka ka ajiye naka
makamin kazo mu gwada ýar kashi Kodajin haka sai shima
hassanul basari yayi murmushi sannan ya ajiye sandarsa
agefe daya ya fuskanci sahibul ukub suka afkawa junansu da fada mai matukar muni
A wannan lokaci sai fadan nasu ya banbanta fiye da farko
Domin nan da nan suka fara hadawa junansu jini da majina saboda yadda suke kaiwa junansu
Bugu da naushi, hannu da kafa
Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda sahibul
ukub yake iya shanye dukan da hassanul basari yake iya
kai masa duk da cewa kuwa tsufa ya fara kamashi ,har ma yake iya maida martani
Haka shima hassanul basarin yake iya shanye dukkan hare haren da sahibul ukub yake kai masa

Suna cikin fadan ne kawai sai sahibul ukub ya shammace shi ya debo wani garin magani ya watsa masa a cikin idanunsa
Nantake kuwa hassanul basari yaji wani irin zafi da zugi sun
ratsa cikin idanun nasa da kwakwalwarsa
Har ma yaji
idanunsa gaba daya sun daina gani Koda ganin wannan
gagarumar nasara daya samu sai ya bushe da wata iriyar
mahaukaciyar dariya wacce ta amsa kuwa acikin fadar tasa gaba daya
Sannan ya dubi hassanul basari yace lallai yaro kayi kuskuren. Kawo kanka ga halaka
Kai in banda ma rashin basira irin taka tayaya zaka yarda makiyinka wanda kuke yakar juna dashi zai baka shawara kuma ka yarda
To yanzun nan zan kashe ka kuma da zarar na kasheka dukkan sihirin tsafina zai dawo da dukkan abubuwan
dana rasa sanadin ka bayan nan kuma na sa a dauki wannan
sandar taka mai matukar sihiri irin naku ma'abota addinin musulunci a konata
Bayan nan naje can sansaninku na kama gaba daya kabilar ku acikin dakiku nayi musu kisan wulakanci wanda ko a tarihi ba za'a dinga tunawa dasu ba
Abu na karshe kuma da zan fada maka shine zan aure wacce kake burin aura wato gimbiya bahjaht
Yana gama fadin haka sai ya tashi yana dingishi ya dauki sandarsa ta tsafi
A wannan lokaci gaba daya hassanul basari baisan inda kansa yake ba saboda tsananin azabar da yake sha
Take ya jefo wannan mashin da nufin yayiwa hassanul basari kisan farat daya dashi
Idan ya mutu sai ya kafe gawarsa a saman fadar tasa
Kwatsam ba zato ba tsammani kafin tsinin sandar ya sauka
ajikin hassanul basari tuni gimbiya bahjaht ta fito daga inda
take idanunta na zubar. Da kwalla ta taho cikin azababben gudu ta sha gaban hassanul basari
Take tsinin sandar ya fasa kirjinta tareda zuciyarta ya faso ta gadon bayanta
Nanfa ta kwallara uban ihu saboda tsananin zafi da zugin da taji sannan wani irin jiri ya debe ta ta sulale ta fadi
Karar sautin ihun natane ya ratsa cikin kunnuwan hassanul basari ya gane cewa lallai wani abinne ya faru ga masoyiyarsa
Ai kuwa nantake yaji duk wani zugi da yakeji ya fice da cikin idanunsa
Bai san sanda ya daka tsalle ba daga inda yake shima ya shuri nasa sandar ya jefawa sahibul ukub shi
Take sandar ta tafi ta fasa makogaron sahibul ukub ta faso ta wuyansa ya fadi kasa yana shure shure

Cikin sauri hassanul basari ya taho kan gimbiya bahjaht wacce take kwance jini yana zuba daga kirjinsa
Sannan shima uzumnal din ya taho kan gimbiya bahjaht yana zubar da kwalla domin irin wannan ranar yake jiye mata tsoro tun daga ranar data fada soyayya da hassanul basari
Ya dauki kanta ya dora akan cinyarsa yadda suna iya kallon juna dukkan su hawaye na zuba daga idanunsu
Yace da ita
Me yasa zakiyi mini haka kinsan irin kuskuren da kika aikata kuwa ?
ko kinsan cewa rayuwarki tafi tawa mahimmanci bai kamata ki sayar da rayuwarki saboda ni ba
Dajin haka sai itama tasa hannunta ta goge hawayen da yake zuba akan fuskarsa tace

Yakai masoyina duk wannan abu da nayi ba komai baneba akan abinda kayi
Ka sani Cewa na zabi na mutu kai ka rayu domin kai kafi cancanta daka rayu
Domin kaine ka fara sayar da rayuwarka domin ceton tawa
rayuwar da kuma miliyoyin rayuka Idan har na kuskura
ka mutu duk wahalar daka sha abaya ta tashi a banza
domin sahibul ukub zai aureni ne kuma zai cigaba dw gudar da zaluncinsa adoron kasa
Na sani kaine kadai zaka iya hanashi aiwtar da wannan mugun nufin nasa
Idan har na kuskura ka mutu to tabbas nima zan biyo bayanka
Kuma ina godiya agareka bisa wannan sadaukar da rayuwarka da kayi domin tawa
Yanzu haka duk irin alkawarukan daka daukar mini tabbas
na gani ka cika mini su har dama wadanda bakayi mini ba suma ka cika
Don haka nima zan cika maka alkawarin dana daukar maka
Ina rokonka daka gaggauta shigar dani wannan addini naka kafin ajalina ya riskeni
Domin yanzu na gamsu cewa babu wani addini na gaskiya face addinin musulunci
Koda jin haka sai nantake farin ciki ya lullube zuciyarsa
Ba shiri ya karanta mata kalmar shahada itama ta maimaita
Tana gama biyawa sai duk jikinta ya sandare idanunta suka kafe ta mutu
Koda ganin wannan al'amari sai nantake ya fashe da kukan gaske
Yana cikin kukan ne ya jiyo kakarin boka sahibul ukub acan gefe daya
Ba shiri ya tashi ya koma inda yake ya daga hannunsa zai gabza masa naushi da nufin yayi masa fashin albasa
Kawai sai yaga sahibul ukub din yayi masa murmushi sannan yace
Ina tayaka murnar samun nasara akaina a wannan lokaci
Amma ka sani kamar ka kashe macijine baka sare sare kansa ba
Domin domin ruhina zai tafi can wata nahiyar ne, inda babu wanda ya sani
Sai bayan shekaru daruruwa zan sake bayyana ajikin wani hamshakin sadaukin
Da kuma dukkan karfina har ma nafi yanzu shara da bunkasa
na sani cewa kai ba zaka kai wannan lokaci ba shi yasa nake baka labari
Idan har ka isa kaima sai ka biyoni wannan lokacin domin
ka hanani idan har ka iya biyoni wannan lokacin kuma ka kasheni to shikenan ba zan sake bayyana ba na mutu har abada

Koda gama fadin haka sai nantake ya sandare kawai sai wani haske ya fito daga cikin jikinsa mai siffarsa ya tashi sama yana kyalkyala dariya
Ya ratsa saman rufin fadar ya fice

Hassanul basari na cikin kallon wannan hasken ne kawai sai yaji uzumnal yace
Yakai wannan sadauki tabbas nima na gamsu cewa addinin ka shine gaskiya don haka ina rokonka nima ka shigar dani cikin addinin nan naka
Koda jin haka sai nantake farin ciki ya lullube hassanul basari ba tareda bata lokaci ba ya biya masa kalmar shahada
Ya maimaita sannan dukkansu suka fito daga cikin fadar boka sahibul ukub suka sauko daga kan tsaunin da fadar take kai
Suka sami waje sukayi mata suttira suka bunneta tareda yi mata addu'o'i
daga wannan guri ya nemi alfarma agurin uzumnal
daya koma can farkon wannan daji ya hadu da aljani
khadimul islam ya daukeshi ya kaishi can sansaninsu domin ya koyo ibada acan sannan ya sanar dasu cewa shi ba zai sami damar dawowa ba
Anan suka rabu kowa ya kama hanyarsa daban ya tafi
Hassanul ya koma can wani daji daban a tsakanin wasu kananun duwatsu
Gurin ya kasance mai matukar ni'ima da dadin rayuwa yaci gaba da rayuwarsa akullum babu abinda yake face ibada da kuma begen masoyiyarsa gimbiya bahjaht har ya tsufa ajalinsa ya riskeshi bai yarda ya sake haduwa da wani bil'adama ko aljani ba
Wannan dalilin ne yasa har yanzu ba sake ganinsa ba kuma ba'a sami labarin inda yake ba

Babu yarda bokaye da sarakuna da masana tarihi basuyi ba domin ganin wannan guri ba amma sun kasa
Haka shima boka sahibul ukub babu wanda yasan inda yake

WANNAN SHINE KARSHEN HIKAYAR SADAUKI HASSANUL BASARI DA KUMA IRIN SOYAYYAR DA SUKAYI A ZAMANINSU

YA LABARIN GIMBIYA WALISA DA DAN UWANTA WALISU?
SHIN HASSANUL BASARI YANA SAKE BAYYANA A WANNAN ZAMANIN?
WANENE SAURAYIN DA WALISA TA GANI ACIKIN BARCINTA ?
KUMA YA SOYAYYARTA DA SARKI ARYAN ZATA KASANCE?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS*************ZUBAR DA JINI

*******************9 PART A

LBR
HABIBULLAH KBR

Koda sarkin kasuwa yimana yazo karshen HIKAYAR
SADAUKI HASSANUL BASARI DA GIMBIYA BAHJAHT sai a sannan suka lura cewa har dare yayi kuma gari ya waye
Saboda yadda suka dingajin sautin carar zakaru
Don haka sai yimana ya dago da kansa suka hada idanu da gimbiya walisa sai yaga idanunta sun cika da kwalla
Da alama ta jima tana kuka bai sani ba koda suka hada idanunsu
Sai yace da ita yake ýata kinji yadda wannan hikaya take da
kuma abubuwan al'ajabin data kunsa Tabbas soyayya
abace mai dadi wacce take tafiya da kuma zautar da wadanda suka fada cikinta
Kuma tafi komai samar da kwanciyar hankali a zukata
Itace take iya maida mai ido ya zama makaho, mai kunne kuma
ta mai dashi kurma ya dainajin komai sai zancen wanda yake so
Mutum baya sanin farin ciki ko bakin ciki sai ya fada tarkon soyayya
Amma kuma duk wannan dadin da take dashi sai ta zama hatsari mai girman gaske

Ga duk wanda yake da burin zama wani hamshakin ko kuma
yake bukatar cika wani buri nasa Takan iya saka mutum ya rasa duk dukiyarsa, daukakarsa, matsayinsa
Irin haka ta faru akan mutane da dama kamar su sadauki hantaru da dai sauransu
Idan har kinaso ki cika burin mahaifinki to dolene ki hakura
da batun soyayya idan yaso daga baya idan bukatar
ki ta biya sai ki fuskanci sabuwar rayuwar da take shirin tunkarar ki ta soyayya
Ina fatan yanzu kin fahimci duk dalilan da suka saka
nake shawartarki daki ajiye batun soyayya agefe daya
Kodajin haka sai walisa tasa hannayenta ta goge hawayen dake zuba daga ciki
Sannan tace
Gaskiya tunda nake ban taba jin labarin soyayya wanda
ya ratsa zuciyata kamar wannan hikayar ba
Hakika
yanzu na gamsu da duk sharwarin da kuma kokarin da kake na ganin ban fada tarkon soyayya ba
Amma ina da wata tambaya kuma inaso ka bani amsa
iya gaskiyarka kada kayi mini karya shin yanzu kai ka yarda
da cewa addinin su hassanul basari shine addinin gaskiya ba wanda muke kai ba?
Dajin wannan tambayar sai sarkin kasuwa yimana yayi shiru kamar ba zaice komai ba daga can kuma sai ya dago da kansa ya dubeta yace

Tabbas kinyi tambaya mai girma wacce duk wanda ya fiya
furtata to rayuwarsa zata shiga hatsari kuma dolene
manyan sarakuna da matsafa su dinga farmakin rayuwarsa
amma kuma ya zame mini dole na amsa miki ita
Azahirin gaskiya duk kan wadannan addinan da muke kansu addinai ne na karya wadanda aka ginasu kan son zuciya, zalunci, kyamatar juna da kuma nuna banbanci tsakanin talaka, mai kudi da kuma talakawa
Dukkan su wasu daga cikin tsageran aljanu ne suka kirkireshi domin su dinga bautar da mutane agaresu
Wasu kuma sun riki wadannan addinaine domin su tara dukiya da bayi kota wacce irin hanya
Atakai ce babu wani addinin gaskiya face addinin musulunci
Domin shine addinin da a koda yaushe yake nuni da a aikata gaskiya sannan kuma abar barna da zalunci
Duk wannan rashin kwanciyar hankali hankalin da ZUBAR DA JININ da akeyi duk anayinsane saka makon rashin riko da wannan addini
Kodajin wannan bayani sai walisa ta girgiza kanta tana mai tunani akan abubuwan daya fada mata
Daga can sai tace
Ai kuwa indai hakane babu abinda ya fiye mana sauki a rayuwar mu face mu ajiye son zuciyar mu mu karbi wannan addini
Amma inda matsalar take shine babu wanda yasan inda za'a sami mabiya wannan addini
Don haka yanzu zan fice na bar wannan birnin naku na shiga cikin duniya na ci gaba da neman wannan dan uwa nawa
Sannan kuma na hada da cigiyar ma'abota wannan addinin na musulunci
Kodajin haka sai yimana ya ja da baya a firgice yace
Me zakiyi a gurin wadannan mutane?
Walisa tace
Idan har na hadu dasu to nima zan karbi wannan addini nasu ne
Dajin haka sai yimana yaja da baya a razane yace
Ina mai shawartarki idan har kinaso ki cika burin ki da wuri da kada ki karbi wannan addini
Ki bari harsai kin gama cika burin ki sannan ki karbi addinin musulunci

Koda jin haka sai walisa ta kyalkyale da dariya sannan tace
Lallai yanzu na fahimci cewar kaima kana daga cikin mutanen daka lissafa masu son zuciyar su
Akan me kake tunanin zanki karbar gaskiya idan tazo mini?
To ka sani ko yanzu nayi arba da ma'abota addinin musulunci saina karbeshi na ajiye addinin tsafin da na gada tun iyaye da kakanni
Domin tun ina yara mahaifinmu abinda yake koya mana shine yaki da zalunci da kuma kafa gaskiya a duk gurin da babu ita
don haka idan har kana ganin zaka iya hanani abinda naga dama to ina mai umartarka daka dauki makaman yakinka
Amma bayan haka ina godiya agareka abisa bani gurin zama da kayi cikin amanarka

Koda gama fadin haka sai walisa ta mike ta kama hanyar fita daga cikin
Shi kuwa sai yabita da kallo ya rasa yadda zai yi ya hanata fita
Koda fitowarta a wannan karon saitaki ta daura kyallen da take rufe fuskarta dashi
Kawai ta kutsa kanta cikin ta nufi hanyar da zata fita daga cikin birnin gaba
Duk inda ta ratsa saidai kaga mutane suna kallonta wasu suna barin ayyukansu suna komawa gefe suna tseguminta
Domin sunyi matukar mamakin yadda ta iya karawa da sarkinsu ba tareda ya sami nasara akanta ba
Ita kuwa sai tayi burus dasu har ta kusan zuwa bakin kofar garin sai kawai ta tuna cewa tunda ita kadaice ya kamata yanzu ta nemi wani abin hawan don rage tafiya
Koda gama wannan tunani saita wuce kai tsaye zuwa kasuwa ta sayo wani farin ingarman doki kosashshe ta haye kansa ta sakar masa linzami ta nufi kofar fita daga birnin
Tafiya ýar kadan tayi daga inda take sannan ta isa bakin kofar birnin
Aikuwa tana zuwa ba tareda gardamar komaiba dakaru suka bude mata kofa ta fice daga birnin gaba daya ta nausa cikin ta ci gaba neman dan uwanta yarima walisu

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN GIMBIYA WALISA DA SARKIN KASUWA YIMANA
****** ********* ********
A can kuwa al'amarin yarima walisu tun lokacin da fafata yaki da ýar uwarsa wato gimbiya walisa kuma yayi mata alkawarin ba zai sake kai wani farmakin ba harsai lokacin data sami lafiya
Sai ya koma can cikin kogon tsafinsa ya zauna yana ta tunani kala daban daban
Acikin tunanin ne kawai sai ya tuna da tsohuwar rayuwarsa tabaya
Wato shekaru dubunnai baya lokacin yana kan sharafin mulkinsa da zaluncinsa
Har ya zamana ko sunansa aka ambata agurin mutane take suke rudewa har su saki futsari awando ba tareda sun sani ba
Sannan ya tuna da batun masoyiyarsa wato gimbiya BAHJAHT wacce babu mace mai kyawunta duk duniya a wancan zamanin kuma shine ya kasheta da hannunsa
Har zuwa abubuwan da suka faru tsakaninsa da SADAUKI HASSANUL BASARI
Koda gama wannan tunani sai ya takarkare ya kwarara uban ihu
Wanda sanadinsa har saida komai na cikin fadar ya dinga bindiga yana fashewa
Har saida yayi shiru sannan komai ya koma kamar yadda yake abaya
Har dama wadanda suka lalace sai suka hade suka koma kamar yadda suke
Kawai sai ya fara zancen zuci yana cewa
Duk yadda akayi wannan takadirin sadaukin ya dade da shekewa barzahu
Don haka nima ya zame mini dole na binciko gawarsa na nemota a duk inda take
Domin in zuba masa garin maganin da zan tashe shi kuma ya zama bawana
Tahanyar yin hakan ne kadai zan huce bakin cikin rabani
da tsohuwar rayuwata mai dadi da yayi
Koda gama fadin haka sai ya karasa kan karagarsa ta tsafi wacce aka sana'anta ta da haske ya zauna akanta
Take yayi nuni da hannunsa zuwa jikin bangon fadar tasa
Nantake saiga taswirar ko ina na duniya ta bayyana ajikin bangon fadar
Amma babu hoton inda gawar hassanul basari take
Koda ganin haka sai ya kara tsananta binciken sa akan haka
Kai sai da takai cewa ma maimakon hoton wani abu ya fito
Sai bangon ya fara baki yana neman tsagewa yayi bindiga
Bisa dole ya hakura da binciken ya yanke hukuncin ya tashi ya fita da kansa domin neman gawar hassanul basari basari da kansa ko ta halin kaka

Koda gama fadin haka sai nantake ya sake mikewa tsaye
Wasu irin manya manyan fuka fukai suka fito daga cikin jikinsa
Kawai sai ya mike tsaye nantake ya kada fuka fukansa ya tashi sama
Sai da yayi kololuwa acikin sarararin samaniya yadda hatta manyan duwarwatsu kananu yake kallonsu a kasan sa
Kawai sai ya tsaya cak yana tunanin gurin daya kamata ya fara zuwa
Sai daya dan debi ýan dakiku yana nazari kawai sai ya kada fuka fukansa ya nufi gabashin dajin
Cikin tsala azababben gudu

WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA YARIMA WALISU BAYAN FAFATAWARSU DA WALISA

***** ****** ********
Al'amarin gimbiya walisa kuwa lokacin data shiga cikin daji akan ingarman dokinta
Koda ta fita daga cikin birnin saita sakarwa dokin linzami
Cikin tsala azababben gudu ta nausa cikin daji ba tare da sanin inda ta dosa ba
Duk inda ta gifta saidai kaga kura tana tashi sakamakon
kartar kasa da kofaton dokinta yake Kuma tana tafiyar
ne tana karanta dalasiman tsafi na daure kasa domin
gajarce doguwar tafiyar dake gabanta A haka ta dinga
ratsawa ta cikin manyan dajijjika masu matukar hatsari kuma duk tana iya ketare su da karfin damtsenta dana sihirinta
Saboda haka sai data shage kwanaki tana

Please Login or Register in order to submit comment