Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gudu,
Ba tareda bata lokaci ba suka garzaya dashi zuwa ga dodo marugas
Koda dodo marugas ya kalleshi acikin wannan hali sai ya bushe da dariyar mugunta
Yayitayi kamar bazai daina ba
Daga can say ya nunawa wadannan dodannin wasu tsaunika guda biyu wadanda suke agefen wannan fili ya umarcesu dasu hau dashi saman wadannan tsaunikan sannan ya tsara musu yadda zasuyi dashi asaman
Ai kuwa ba tareda bata lokaci ba dodannin suka kama hanyar cika aikinsu
Tafiyarsu keda wuya sai kiyasul ausar ta dubeshi tace duk wannan da kakeyi ka manta ba'a rabashi da makaman yakinsa ba
Don haka zai fi kyau duk aciresu daga jikinsa
Dajin haka sai ya juyo ya fuskanceta yace
Duk nasan da haka amma ki tsaya kiga abinda zai faru nayi haka ne domin nayi adalci atsakaninmu

WANNAN SHINE BABBAN KUSKUREN DA SUKA AIKATA A RAYUWARSU
Lokacin da wadannan dodannin suka haye saman tsauni dauke da hassanul basari
Saida sukaje karshensa kawai sai suka sami wata katuwar kusa mai kauri
Wacce aka kafa a samansa suka daure sarkokin jikin hannunsa ajikin kusar
Sannan suka koma kan daya tsaunin jikin wani katon dutse suka daure sarkokin jikin kafafunsa ajiki
Shidai wannan dutse wanda suka daure kafafunsa ajiki bai zauna sosai ba
Domin da zarar an fiya turashi take zai goce daga gurin da yake zaune ya fado kasa ya tsinka duk abinda aka daure ajikinsu

Koda gama wannan aiki sai dodannin suka sauko kasa
Kamar yadda aka umarcesu ,ba tareda bata lokaci ba
Dodo marugas ya bada umarnin a fara shagali aikuwa nantake guri ya batse da dodanni suka fara yin shagulgula irin masu l
Saida suka rakashe suka cashe kowa yaci abinci da abinsha mai dadin gaske
Acan gefe daya kuwa inda su dodo marugas suke
Sai marugas ya dubi kiyasul ausar yace
Yake kawata yanzu dai ina fatan kin fuskanci irin kisan dana tsara zamuyi wa wannan makiyi namu
Saboda haka sai ki zaba ina kike so tsakanin
Daga kansa zuwa cibiyarsa
Ko kuma daga cibiyarsa zuwa kafarsa ?
Dajin wannan tambaya sai tayi wani murmshin jin dadi wanda ya kara bayyanar da muninta a fili tace
Aini duk jikin bil'adama babu ina nakeso kamar daga kansa zuwa cibiyarsa
Domin na zuki ruwan idonsa da bakina sannan na dinga zare hanjin cikinsa ina cineyewa da daidai da daidai
Dajin haka sai marugas yace ai shikenan amma nima ki sani babu inda nakeso sama da ina kika zaba
Amma tunda ni na baki zabi shikenan na hakura
Yana gama fadin haka sai ya umarci wadannan dodannin dasu hau saman tsaunin su turo wannan dutsen kasa
Ai kuwa take suka fara hawa kan tsaunin saida suka hau rabin tsaunin
Babu zato ba tsammani sai wani irin bakin hadari ya hado a sararin samaniya tareda iska mai sanyi
Kafin dakika biyu sai aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya
Koda wannan ruwan ya sauka akan fuskar hassanul basari sai take ya farka daga dogon suman da yayi
Koda ya bude idanunsa ya ganshi a tsakanin manyan tsaunika
Kuma an daura masa sarkoki hannu da kafa sai nantake ya takarkare ya kwallara kabbara
Wacce sautin kabbarar saidata ratsa dajin gaba daya
Take zuciyoyin dodannin suka buga da karfi saboda razanar da suka najin wannan kabbarar
Shi kuwa dodo marugas da kiyasul ausar duk sai suka mike tsaye suka kame kyam kamar gumaka domin sunfi kowa razana da jin wannan kalmar

MAI ZAI FARU A WANNAN LOKACI?
SHIN SUNA SAMUN NASARAR TSINKA SHI BIYU KO KO BASA SAMU
WANENE ZAI TSIRA A TSAKANINSU
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS**********ZUBAR DA JINI

*************8 PART A

LBR

************HABIBULLAH KBR

Take wajen tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta bakajin komai face sautin numfashinsu da kuma bugun zuciyarsu
Shikuwa hassanul basari da yake saman tsaunika adaure da sarkoki
Sai kurum ya hango wadannan dodannin da aka saka su tura wannan dutsen kasa suna kokarin hawa kan dutsen kallo daya yayi musu ya fahimci akwai wani tuggun da suke shiryawa akansa

Koda yin wannan tunani sai ya tattara karfinsa waje guda ya tsinka sarkar dake daure a hannuwansa tamkar ya tsinka igiya
Take kuwa ya sulmuyo kasa zuwa bangaren tsauni na biyu
Tun kafin ya karaso daidai inda wadannan dodanni masu yunkurin hawa kan dutsen domin su turo dutsen da zai tsinkashi
Tuni ya zare takobinsa yana zuwa daidai inda suke yasaka ya zabtare musu kawunansa
Take kawunan suka sulmuyo kasa tare da ganganr jikin
Koda ganin abindaya faru sai dodo marugas ya dakawa dakarunsa tsawa yace me kuke jirane da bazakuje ku shayar dashi gidauniyar mutuwaba ?
Kodajin wannan batu sai take dakarun suka zazzaro wasu zabga zabgan kibiyoyi wadanda akayisu da manyan reshunan bishiyoyi suka daddana ajikin bakarsu suka tabe sannan suka sakarwa hassanul basari
Aikuwa cikin bakin zafin nama hassanul basari yasaka takobinsa ya sake tsinka sarkokin da suka daure jikin kafafunsa ya sulmuyo kasa
Tun asaman ya dinga saka takobinsa yana kade wadannan kibiyoyi tareda zulle musu tamkar ba'a kan iska yake ba
Aikuwa yana dira akan doron kasa sai fada ya canja salo domin cikin kankanin lokaci ya zame musu guguwar annoba
Dukda cewa sunfishi girman jiki, amma sai hakan ya zamo na banza
Domin babu abindaya dingayi face tura rayukansu kiyama
Nanfa garin ya cika da iface iface babu sninda kunne yakeji face sautin gurnani da kuma koke koken dodannin nan
Dukda irin girman jikin da suke dashi saiys tashi abanza
Duk inda ya ratsa acikinsu saidai kaga jini yana feshi yana fansama akan doron kasa
Dodo marugas da kiyasul ausar kuwa tsananin mamaki ne ya kamasu
Saboda ganin yadda yake nuna tsantsar jarumtaka kuma yake yaki kamar jikinsa bana jini da tsoka bane
Musamman ma kiyasul ausar domin gani tayi hatta salon yakinsa ya sauya ba kamar sanin da tayi masa abaya ba
Kuma baya taba yarda ya zauna waje daya
Yana fadan ne tareda hadawa da tsalle tsalle, gami da zulliya .
Duk inda ya ratsa sai kaga mutuwa ta ratsa ta gurin cikin kankanin lokaci ya gama hallaka dodannin gaba dayansu
Sannan ya nufo inda su kiyasul ausar da dodo marugas suke
Takobinsa tana digar da jini nanfa suka fara kallon kallo atsakaninsu
Daga can sai dodo marugas ya kalli kiyasul ausar ya yi mata wata inkiya da ido
Ai kuwa take suka daka tsalle sama suka kai masa mugayen sara da nufin su tsargashi biyu kamar yadda sukayi nufinyi abaya
Cikin bakin zafin nama hassanul basari ya kauce makamin dodo marugas da hannun kiyasul ausar suka hadu wata irin kara mara dadin ji ta tashi sama tareda tartsatsin wuta
Kafin suyi wani yunkuri tuni ya shuri kafafunsu duk su biyun ya maka su da kasa

Cikin sauri duk su biyun suka mike tsaye suka kame kyam suna kallonsa cikin tsananin mamakin inda ya sami wannan gagarumin karfi
Daga can kuma sai suka daka tsalle sama lokaci guda suka watso masa wasu irin sihirtattun kibiyoyi masu yawan gaske
Lokaci guda kibiyoyin sukayi fitar burgu data cikin hannayensu sukayi kansa gadan gadan
Cikin wani irin mahaukacin gudu kamar kiftawar ido
Koda kibiyoyin suka sauka akansa sai duk suka kama da wuta suka kone kurmus
Sai suka sake watsa masa wutar tsafi don ta kone jikinsa kurmus ai kuwa kafin wutar ta sauka ajikinsa tuni sai ta daskare ta koma kankara itama kankarar saita narke ta zube kasa
Da ganin wannan abu daya faru sai suka sake watsa masa wasu manyan duwatsu na sihiri da nufin su turmushe shi
Aikuwa koda wadannan duwatsu suka isa inda yake sai duk duwatsun suka tarwatse
Suka zama gari garin ma sai ya tashi sama yabi iska
Saida suka gwada dukkan sirrikan tsafinsu akansa amma sukaga yaki tayi tasiri akansa
Koda sukaga haka sai nantake suka dungule guri daya
Tareda karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai duk su biyun suka rikide suka zama wata irin katuwar macijiya
Mai girman gaske
Itadai wannan macijiya tana da kawuna guda biyu hakama jelarta ta rabu gida biyu
Koda ta gama rikidewa zuwa wannan siffar sai nantake macijiyar ta wangame bakinta
Ta tsarto masa wani ruwan dafi mai matukar karfi
Cikin bakin zafin nama ya daka tsalle daga inda yake ya kaucewa dafin nata
Koda dafin nata ya sauka akan kasa sai take kasar gurin ta kama da wuta har tana zabalbala
Koda ganin wannan abu sai take hassanul basari ya mike tsaye zumbur ya yana mai gyara tsayuwarsa
Alamar ya shirya fafatawar su
Koda macijayar taga yadda ya tsaya agabanta shi kadai kamar an ajiye kyanwa agaban katon kare
Sai macijiyar ta wangame bakinta ta bushe da mahaukaciyar dariya
Tace kai karamar halitta tayaya kake tsammanin tunkarar mu a wannan siffa?
Ina mai rantsuwa da ruhin mai gidan mu a wannan karon baka isa ka sami nasara akanmu ba
Suna gama fadin haka sai macijiyar ta kai masa mahaukacin duka da jelarta
Kafin jelar tazo inda yake tuni ya sunkuyar da kansa kasa
Tareda karanta wadansu addu'o'i na musamman acikin zuciyarsa
Ya tofa ajikin macijiyar aikuwa take ta tarwatse ta koma ainihin siffar dodo marugas da kiyasul ausar
Duk jikinsu tayi fata fata da jini
Nantake suka rugo da gudun gaske kansa suka kacahame da azabbaben yaki
Fiye da hasa shen mai hasashe, tamkar zasu tashi daga kan doron kasa
Saiga hassanul basari ya shiga tsakanin kiyasul ausar da dodo marugas yana fafata yaki dasu shi kadai
Kuma dukda kasancewarsu su biyu sai gashi sun kasa samun nasara akansa harma ya hargiza musu tunaninsu
Sai a sannan ne dodo marugas yayi nadamar kin karbar shawarar da kiyasul ausar ta bashi na kashe hassanul basari tun yana cikin halin suma
saida suka shafe lokaci mai yawa suna fafata yaki atsakaninsu
Koda hassanul basari yaga suna neman bata masa lokaci sai kurum ya takarkare ya kwarara kabbara da karfi
Sannan ya karanta wata addu'a acikin zuciyarsa tareda kaiwa kiyasul ausar mummunan sara a tsakiyar kanta
Nantake sai takobin ta dara kanta gida biyu sannan ta fadi kasa matacciya
Koda ganin abindaya faru ga kiyasul ausar sai dodo marugas ya juya da baya da nufin shima ya gudu domin ceton rayuwarsa
Amma ina damar hakan bata samu ba agareshi domin saida yayi nisa acikin gudun nasa kawai sai hassanul basari ya jefa masa takobinsa
Take takobin taje ta cake agadon bayansa ta faso kirjinsa fa fito waje
Kawai sai shima ya fadi kasa matacce koda ganin wannan nasara daya samu sai kawai ya daga hannunsa sama yayiwa allah godiya
Sannan ya tashi ya kama hanyar fita daga cikin wannan daji
Haka dai yayita tafiya acikin wannan daji tsawon kwanaki saboda tsananin girmansa
Sannu ahankali har ya fice daga cikin wannan daji ya shiga daji na gaba
Tun daga wannan rana bai sake haduwa da wani abu mai cutarwa ba akan hanyarsa
Sai a cikin wannan daji inda ya fafata da manyan namun daji masu yawan gaske
Bayan wannan daji saidaya ratsa ta cikin manyan dajijjika guda goma
Masu mabanbanta halittu koma wadanne kalar nau'in bala'insu da ban
Har sai daya gama ketare wadannan dajijjikan sannan ya fara hango fadar boka sahibul ukub daga can nesa da inda yake
Koda yaga ya fara hango wannan fadar sai kawai yaji wani irin farinciki mara misaltuwa ya turnukeshi
Domin yanzu ne ya fara ganin biyan bukatarsa saboda haka sai ya kara sauri sosai don yaga ya isa cikinta da wuri
Saidaya shafe lokaci mai tsawo yana mai tsala azabbaben gudu
Amma bai isa inda wannan fadar take ba
Sai a sannan ne ya fuskanci cewa fadar ba'a kusa take ba tana can nesa da inda yake
Tsananin tsawon tsaunin da yake kaine yasa yake ganin fadar kamar a kusa dashi take

Saboda gudun da yakeyi ko sau daya baya yarda ta zauna domin hutawa saidai don yin ibada da kuma kawar da wata lalurar amma hatta cin abinci ko shan ruwa a tsaye yakeyinsu
Kai tun har saida takai abincin guzurinsa da ruwan shansa duk sun kare
Saidai ya sami ýaýan itatuwa ya karanta addu'ar neman tsari sannan yaci
A haka har ya isa bakin tsaunin da kogon tsafin boka sahibul ukub yake
Koda ya daga kansa sama yayi nazarin tsaunin sosai sai yaga baya iya hango karsen tsaunin saboda tsananin tsawon da yake dashi
Koda ya tsaya ya tsaya ya karewa tsaunin nazari sai take ya kama tsaunin da hannayensa ya fara hawa kansa
Sai kace ba bil'adama ba domin idan ka hangoshi daga nesa sai kayi zaton cewa kadangare ne ba mutum ba
Saidaya yini cur yana tafiya akan tsaunin sannan ya isa karshensa
Take yayi arba da wata tangamemiyar fada mai girman gaske
Wacce aka kera kofarta da zallan dutsen lu'u lu'u mai hasken gaske
Ita kanta wannan fadar idan ka kalleta ta isa abin al'ajabi domin idan kaga irin girmanta sai kayi zaton cewa wannan tsuburi ba zai iya daukarta ba
Domin ita kadai ta isa a hade manyan birane irinsu birnin sin da birnin kisra aguri guda saboda matukar girman sa

MENE ZAI FARU ACIKIN WANNAN FADAR?
SHIN YANA HADUWA DS BOKA SAHIBUL UKUB.?
TAYAYA ZAI IYA CETO MASOYIYARSA GIMBIYA BAHJAHT DA KUMA BAWANTA UZUMNAL?
DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN*************ZUBAR DA JINI

*****************8 PART B

LBR
*****************HABIBULLAH KBR

Lokacinda hassanul basari ya karewa fadar kallo sosai yana
nazarin ta sai ya kula da cewa kofar fadar gaba daya bata
da makulli wanda ake budeta dashi Don haka babu shiri sai ya
fara shafa jikin kofar yana dada yin dogon nazari akanta
Koda gama yin dogon nazari akanta sai nantake ya daga
takobinsa ya sara da karfi ajikin kofar take yaga takobin tasa
ta karye gida biyu tare da tashin wata irin tsawa gami da walkiya alokaci guda
Koda ganin wannan al'amari sai ya fuskanci cewa karfin damtsensa bai isa ya bude masa kofar wannan fadar ba
Don haka sai ya daga hannayensa sama ya fara yiwa allah
kirari yana kuma rokonsa akan ya bashi nasarar bude wannan kofar
Bai jima da fara wannan addu'ar ba sai kurum yaga wani dan karamin tsuntsu yazo giftawa ta bakin kofar
Koda tazo daidai bakin kofar sai fuka fukinsa guda daya ya shafi kofar
Take wata irin kara ta cika dajin gaba dayansa kofar kuma ta bude kanta da kanta
Saida kofar ta shafe ýan dakiku sannan kofar ta gama bude kanta
Take yayi arba da cikin fadar wacce aka kawata ta fiye da kima
komai na cikin fadar anyi shine mara kala kamar haske ko kuma ince kamar ruwa haka yake

Domin komai ka kalla kana iya ganin cikinsa ba tareda ya
boye maka komai ba fadar tayi tsit baka jin sautin komai wanda yake giftawa ta cikinta
Ba tareda bata lokaci ba shima yasa kafarsa ya fara shiga

cikin fadar ba tareda fargabar komai ba kamar yana tafiya acikin gidansa
TABBAS RASHIN TSORO BAIWACE DAGA UBANGIJI
DOMIN IDAN HAR YA BAKA WANNAN BAIWAR BABU ABINDA ZAI TABA BAKA TSORO ACIKIN AL'AMURANKA
Lokacin da hassanul basari ya kutsa kai cikin wannan fadar saiya dinga tafiya yana mai kallon kowacce kusurwa ta cikin fadar
Yana mamakin yadda boka sahibul ukub ya iya sawa akayi masa ginin haske acikin fadarsakamar yadda yake gani da idanunsa
Sannan kuma yana hadawa da neman gimbiya bahjaht saidaya shafe sa'a biyu yana tafiya kwatsam sai yayi kicbus da wani murgujejen zaki mai girman gaske wanda tunda yazo duniya bai taba ganin halitta maigirmansa ba
Hatta shi kansa wannan zakin an kerashi ne da siffar haske domin hatta kayan cikinsa da haske akayisu
Har ma ana iya ganin gudun da jinin jikinsa yakeyi
Cikin idanun wannan zaki kadai ya isa ya razana mutum
Domin jajur yake sai ka zata garwashin wutane ke ci a cikinsa
Koda bayyanar wannan murgujejen zakin sai kawai ya wangame bakinsa yayi ruri irin wanda yake firgita namun daji dashi a cikin daji
Wanda sanadiyar wannan rurin nasa sai da wuta tayi tartsatsi daga bakin nasa kamar an watsawa kalanzir wuta
Duk inda wannan zakin ya taka acikin fadar sai dai kaji kasar gurin tayi girgiza saboda matukar nauyinsa
Sannu a hankali zakin ya fito daga sakon da yake ya tsaya nesa kadan da hassanul basari suka tsaya suna kallon kallo atsakaninsu
Tun da aka ajiye wannan zakin acikin fadar nan bai taba fita daga cikinta ba
Kuma bai taba ganin wata halitta data taba shigowa inda yake ba
Don haka shi babu abindaya sani face boka sahibul ukub domin hatta su gimbiya bahjaht baisan an shigo dasu ba tunda suna cikin akwati lokacin
Shi kuwa hassanul basari mamaki ne ya kamashi saboda ganin tsarin wannan fadar
Da kuma halittar wannan zakin da yake gabansa
Amma koda ya tuna cewa sha'anin tsafine kuma duk tsafi karyane
Sai kawai yaji ya daina mamaki akan wadannan abubuwa
Yana cikin wannan tunani ne ba zato ba tsammani sai kawai yaga wannan zakin ya falfalo da gudun gaske ya nufo inda yake
Kafin ya ankara tuni zakin ya daka tsalle sama ya bangajeshi da kirjinsa
Saboda karfin dukan saida yayi sama sannan ya fado kasa
Jikinsa ya bugo da kasa yaji kamar duk kashushuwan jikinsa sun kakkarye ,har saida yayi tumbudin jini daga cikin bakinsa
Kafin ya mike daga inda yake tuni zakin ya sake dako tsalle ya dira akansa yana kokarin kama kan fuskarsa da bakinsa ya gatsa
Koda ya fahimci mugun nufin wannan zakin akansa
Sai yayi caraf yasa hannayensa biyu ya kama kan zakin suka
kachame da kokawa atsakaninsu
Wohoho nanfa karfi ya fara ranarsa domin duk irin kokarin da
wannan zakin ya dingayi don yaga ya sami nasara akan hassanul basari sai ya kasa
Domin yaki yarda fuskar zakin ta sauka akan tasa fuskar
Nantake jijiyoyin jikinsa suka tashi sukayi burdin burdin kamar an jera jijiyoyin bishiya

Rigar jikinsa kuwa ta yage kamar ansa reza an yanka ta biyu
Nanfa suka yita kokawa wannan ya danne wannan wancan ya danne wannan
Da kyar hassanul basari ya samu ya bambare zakin daga jikinsa
Take zakin ya sake tasowa kansa suka da nufin ya sake yi masa abindaya yi masa da farko
Koda zakin yazo daidai inda hassanul basari yake sai hassanul basari ya kaiwa zakin mummunan duka da nufin ya tarwatsa kan zakin tun a saman
Ai kuwa cikin mamaki sai yaga hannunsa ya ratsa ta cikin fuskar zakin ya wuce
Ba tareda ya cutar da shi zakin ba, shikuwa zakin tuni yasa faratansa ya yanki hassanul basari a akan kafadun hannuwansa
Take wajen ya dare jini yayi tsartuwa daga gurin

Take ya kwarara ihu da karfi ba tareda daya sani ba saboda tsananin zafi da zugin da yaji
Cikin sauri ya dauki yagaggiyar rigarsa ya daure damatsan nasa da ita domin tsayar da jinin da yake zuba
Sannan ya sake juyowa ya fuskanci zakin alokacinda suffar zakin ta fara kara girma daga yadda take
Kafin wani lokaci girmansa ya ninka yadda yake da kuma a wannan lokaci wata irin bakar wuta ta dinga fita daga cikin bakinsa
Har hassanul basari yana iya jiyo hucin wutar daga inda yake
Kwatsam sai yaga zakin ya nufo inda yake da gudun gaske yana so yazo ya konashi da wutar bakinsa
Koda ganin wannan abu sai shima ya falfala da gudun gaske izuwa bayansa domin ya tserewa zakin
Nanfa suka kasa tseren gudu atsakaninsu mai ban al'ajabi
Hassanul basari ya dage iya karfinsa domin ganin ya gujewa wannan zakin
Shi kuwa zakin ya dinga binsa domin ya sami abincin kalaci
Duk da tsananin gudu irin na hassanul basari a wannan lokaci saida ya raina gudun nasa domin duk sanda ya zuyo da idanunsa baya sai yaga tazarar dake tsakanin sa da zakin bata wuce taku dayaba
Saida suka shafe dakiku masu yawa suna wannan tseren kawai sai hassanul basari ya tuna cewa
Duk wannan gudun da yake bada komai yake yinsa ba face karya
Domin shi shine gaskiya wannan zakin kuma karya ce ba gaskiya ba
Koda yin wannan tunani sai nantake ya karanta addu'ar neman tsari acikin zuciyarsa
Sannan ya tsaya da gudun da yake ya juyo ya shammaci zakin ya tofa ajikinsa
Koda yin haka sai take zakin ya kama da wuta ahankali jikinsa ya kone kurmus ya fadi kasa matacce
Cikin farinciki hassanul basari ya yi godiya ga allah daya bisa wannan taimakon gaggawa da ya kawo masa
Ba tareda bata lokaci ba ya kama hanyarsa yaci gaba da shiga cikin fadar
Saida ya sake wuce wasu fadojin daban daban sannan ya isa fadar karshe a cikin fadojin
Gaba daya ita wannan fadar ta banbanta da sauran
Domin babu komai acikinta face wasu irin manyan munanan gumaka
Wadanda kallonsu kadai ya isa ya razana mutum komai karfin zuciyarsa
Dukkansu suna ruke da miyagun makamai kamar ace kyat su kaure da fada a tsakaninsu
Acan karshen fadar kuwa boka sahibul ukub ne a zaune bisa kan karagar mulkinsa wacce ya sana anta ta da haske
Kamar yadda aka fada tun farko baya zama akan wani abu face haske domin haka ka'idar tsafinsa take
Ya zauna yayi zaman kasaita hannunsa daya ruke wata irin zabgegiyar sandar tsafi
Daya hannun kuwa ya dorashi akan cinyarsa ,fuskar sa kuwa a murtuke take kamar an aiko masa da sakon mutuwa
Agefen kujerar da yake kuwa wadansu irin sihirtattun
karnukan tsafine a tsaye suna kallon kowacce kusurwa ta fadar don tabbatar da tsaro
Tun daga nesa hassanul basari ya kurawa boka sahibul ukub ido kuma ya nufi inda karagarsa take fuskarsa a murtuke cike da TSANANIN GABA
Haka shima sahibul ukub din sai ya tsaya ya kurawa hassanul basari idanu har saidaya kusan zuwa daidai inda karagarsa take
Kawai sai hassanul basari yaji motsin wani abu a bayansa
Cikin sauri ya juya don yaga abindake faruwa bisa mamaki sai yaga wadannan gumakan daya wuce duk ruhi ya shiga jikinsu
Suna wani gurnani mara dadin ji haka suma wadannan karnukan guda biyu suma duk suka maida hankalinsu zuwa ga hassanul basari
Koda ganin wannan abu sai boka sahibul ukub ya bushe da dariya
Yayi tayi kamar ba zai daina ba saboda farin ciki sai daya yita kyalkyala dariya kamar ba zai daina ba
Daga can sai ya mike tsaye daga kan karagar tasa ya nuna hassanul basari da sandan sa yace

Yakai wannan jarumi ka sani cewa tabbas na jinjina maka kan yadda ka isa ketare duk hadarurrukan da suke kan hanya har ka iso nan cikin fadata
Amma ka sani cewa duk wannan nasarar daka samu daidai take da cigaban mai hakan rijiya domin wannan guri shine ajalinka
Don babu wanda yake da ikon shigowa cikin nan fadata ya fita lafiya saida izinina
Duk abinda nake bukata shi ne yake faruwa a wannan fadar
Don haka ina matukar tausaya maka domin yadda ka fito domin neman cikar muradinka wato gimbiya bahjaht haka zaka mutu ba tareda bukatarka ta biya ba
Kuma agaban idanunta zaka mutu a matsayin kaskantacce
Kuma duniya zata manta da tarihin sadaukantakarka har abada ba za'a taba tunawa da kai ba……..
Tun kafin ya karasa maganar da yake fada tuni hassanul basari ya tareshi tare da daka masa tsawa yace
Karya kake tsohon la'ananne baka isa ka kashe koda sauro
ba face da izinin ubangijin musulunci Ina mai gargadinka
daka gaggauta sakar mini masoyiyata da kuma yaronta
sannan ka karbi addinin musulunci ka ajiye shirka da kuma tsafi domin duk karyane
In ba hakaba kuwa tabbas dolene ka dandani zakin mutuwa
Dajin haka sai sahibul ukub ya bushe da dariya sannan yace
Ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa sai mu zuba mu gani idan ka gama da wadannan saika juyo inda nake domin muyi gaba da gaba
Yana gama fadin haka saiya umarci dodannin nan dasu afka masa
Nantake kuwa suka falfalo da azabbaben gudu suka afka masa
Suna wani irin gurnani mara dadin ji da cika kunne wanda
ka iya zautar da tunanin mai sauraro

Tun kafin su karaso inda yake tuni yayi sauri ya zaro wannan
farar sandar da malan ramadan ya bashi wanda yana zarotane hasken jikinta ya mamaye fadar gaba ki dayanta
Nanfa suka kachame da azabbaben yaki atsakaninsu

Please Login or Register in order to submit comment