Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farincikin sake ganin gimbiya bahjaht
Da isarsa sai kowa ya kame aka zauna aka zura masa idanu
Domin kowa yasan cewa ya fitane domin yin farauta
Amma sai gashi ya dawo shi kadai ba tareda ya farauto komai ba
Kowa yasan cewa bai taba fita farauta ya dawo ba tareda ya faruto komai ba
Sai gashi yau ya yini a cikin daji ba tareda ya sami nasarar farauto koda zomo ba
Koda ganinsa sai wani saurayi matashi wanda shekarunsa
Zasuyi daidai dana hassanul basari ya taho da sauri ya tareshi yace
Lale marhaban da zuwan abokina jarumi uban jarumai kuma namijin duniya
Kai kuwa wacce irin bacin rana ka samu yau, kuma menene ya faru da kai naga ka dawo ba tareda ka farauto komai ba?
Dajin wannan tambaya sai hassanul basari yayi murmushi yace
Yakai salban ka sani cewa tunda nake fita farauta ban taba yin farauta wacce na sami riba da yawa acikinta kamar wacce nayi yau
Ka sani cewa ayau ba wai dabba na farauta ba,
Farincikin rayuwata na farauto
Ma'ana ayaune na san soyayya kuma nasan dadinta
Da kuma dalilin dayasa ýan mata da yawa abaya suke neman soyayyata
Amma naki yarda dasu ,tabbas yanzu na gane kuskuren da nayi abaya
Ayaune nasan bakin cikin da masoyi yake kunsa idan ya bayyana soyayyarsa ga wanda baya muradinsa
Yanzu ne na san duk bakin cikin da suka kunsa azuciyarsu idan na nuna bana muradinsu acikin zuciyata
Ka sani a yau ne na hadu da wacce ta sami rinjaye a zuciyata
Kuma ina tabbatar maka da cewa zan iya sallama rayuwata gaba daya don in sata farinciki
Ayanzu haka inaji ajikina bazan iya rayuwaba muddin ita bana tare da ita
Kai nayi imani cewa ko mutuwa ba zata iya rabani da itaba
Idan kuwa har hakan ta faru to babu wanda zan kara mu'amalar rayuwa dashi har zuwa karshen rayuwata
Kuma zan kebance kaina ne a inda babu wani mahaluki da zai iya zuwa har zuwa sanda ajalina zai riskeni
Kodajin wadannan kalamai daga bakin hassanul basari sai mamaki ya kama salban kuma ya bashi dariya yace
Kai da bakinka ka sha fada mini cewa baka san meye soyayya ba
Kuma baka taba ganin macen data burgeka ba tayaya zaka zo mini da wannan labari lokaci guda
Na yarda?
Amma dai bai kamata na karyata ka ba tunda bansanka da karya ba
Zanso ka fada mini wacece wannan mace mai matukar sa'a wacce ta iya tafiya da zuciyar ka lokaci daya?
Dajin wannan tambaya sai yayi murmushi wanda yake kara fito da tsantsar kyawunsa sannan yace
Ba kowa bace ba face gimbiya bahjaht ýa agurin babban sarkin mu wato mayasin
Nandai ya kwashe labarin duk abindaya faru tsakaninsa da ita tun a farkon haduwarsu
Lokacin daya ceci rayuwarta daga hannun wannan maridin dodon
Da kuma haduwar da sukayi yau acikin daji bayan ya fita farauta
Kodajin ya ambaci sunanta sai fara'ar kan fuskarsa ta disashe sannan yace
Yakai abokina shin tayaya zaka mallaki gimbiya bahjaht bayan kasan cewa ita ba musulma bace, haramun ne aure a tsakaninku?
Idan kace ita ta amince zata karbi musulunci kafin aurenku
To tayaya kake tunanin mahaifinta zai amince har ta musulunta
Ba tareda ya dauki matakin hanata ba?
Kodajin wannan tambaya sai hassanul basari ya dafa kafadarsa
yace kada ka damu da wannan ni nayi alkawarin hatta shi
mahaifin nata saina janyo ra'ayinsa zuwa ga addinin gaskiya muddin ina numfashi adoron kasa
Ai kuwa koda gama fadin haka sai hassanul basari ya shige cikin gidansu
Mutane suna ta binsa da kallo domin babu wanda yaji abinda suka tattauna da salban
A wannan lokaci dare ya raba don haka yana shiga dakinsa sai ya shiga bandaki yayi alwala
Sannan ya fito waje duk mutane sunyi sahu sahu acikin wani dan karamin masallaci
Ana jiran zuwan dan uwan mahafinsa wato malan ramadan domin ya ja musu jam'in sallar isha
Ba'a jima ba kuwa sai gashi ya iso ya shiga gaba yayi musu limanci
Sannan kowa ya kama hanya ya wuce gidansa domin haka ka'idar su take
Da zarar an idar da sallar isha to kowa zai shige gidansa ne bazai kara fitowaba sai safiya tayi
Malan ramadan dattijone dan kimanin shekaru hamsin da doriya kuma mutum ne shi wanda yake da tarin ilimin addinin musulunci
Dakuma ilimin fassarar mafarki ga kuma tsoron allah
Wannan dalilin ne yasa mutane suke matukar girmamashi

Bayan hassanul basari ya shige cikin dakinsa wanda yakasance dan kankani ne
Kusan gidan kowa na sansanin yafi nasa girma duk da cewa shine jagoran wannan kabila
Sai ya hau kan shimfidarsa yayi addu'o'i ya kwanta
Kwanciyar sa keda wuya sai barci mai nauyi ya daukeshi

Acikin barcin nasane yayi wani mummunan mafarki wanda ya matukar razana shi
Ba komai ya gani. Ba amafarkin nasa ba face
Gimbiya bahjaht ta fada cikin wani katon tarko ta kasa fita daga cikinsa
Agefen tarkon kuma wasu irin rikakkun damisoshine sukeson ta fito su cinyeta

Daga can kuma sai ya hango wani irin murgujejen zaki mummuna fuskarsa mai matukar ban tsoro yazo
Ya cinye wadannan damisoshin sannan ya cafi wuyan gimbiya bahjaht ya gudu da ita can saman wani dogon tsauni
WANNE IRIN BURINE A ZUCIYAR BOKA SAHIBUL UKUB WANDA YA HANASHI KASHE GIMBIYA BAHJAHT?
SHIN HASSANUL BASARI YANA SANIN HALIN DA GIMBIYA BAHJAHT TAKE CIKI?
MENENE FASSARAR WANNAN MAFARKI DA HASSANUL BASARI YAYI ?
DON SANIN AMSOSHIN WADANN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA TASKAR
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT************ZUBAR DA JINI

********;***6 PART B

LBR

****************HABIBULLAH KBR

Adaidai na hassanul basari ya farka daga barcin da yake
Afirgice ya mike zaune tareda karanta wasu addu'o'i a zuciyarsa
Nan fa ya zauna ya fara tunani akan mafarkin da yayi
Koda yazo daidai inda wannan zakin ya cafi wuyan gimbiya bahjaht
Sai ya takarkare ya kwarara uban ihu baisan sanda yasa hannunsa
Ya naushi katangar ginin dakinsa ba saboda karfin dukan saida katangar ta burma hannunsa ya bullo ta bayanta
Duk da cewa kaurin katangar yakai kamu ashirin ba tareda hannunsa yayi koda kwarzane ba
Nantake ya dauki kayansa na yaki ya sanya ajikinsa
Sannan ya dauki rantsatstsiyar takobinsa ya rataya ya fito daga cikin gidan nasa
Da yake a wannan lokaci dare ne to sai yankin nasu gaba daya yayi tsit babu sautin da kunne yakeji face na karnuka
Kuma gaba daya yankin babu mai gadi ko guda daya wanda baiyi barci ba
Saboda tsananin zaman lafiyar da yake tsakaninsu da kuma amana
Amma wani ikon allah shine duk da cewa basa zuba masu gadi
Wani mugu bai isa ya kawo musu harin bazato ba face asirinsa ya tonu
Lokacinda hassanul basari ya fito daga cikin gidansa sai kawai ya kama hanya bisa kafafunsa ba tareda ya hau kan doki ba
Domin shi bai yarda da hawansa yafi ganewa duk inda zaije kuma duk nisan tafiya yayita akan kafafunsa
Domin aganinsa hawa kan doki alamace ta lalaci da rashin jarumta
Bayan haka kuma hawa doki yana bata masa lokacine don karfin gudunsa yafi na doki
Har ya kama hanyar tafiya birnin shawana sai kawai yaji zuciyarsa bata kwanta da tafiyar ba
Domin tunda ya taso lokacin da mahaifinsa yake shugabantar wannan kabila
Bai taba fita daga cikin ayarinsu cikin dare ba, kuma tun wannan lokacin yake gargadinsa akan kada ya kuskura ya aikata hakan
Amatsayinsa na shugaba, domin mutane zasuyi ta zarginka idan suka ga ka aikata haka
Kuma kai da kanka sai kayi nadamar aikata hakan da kayi
Kuma har a lokacin daya mutu wannan itace wasiyyar daya bar masa
Koda yin wannan tunani sai jikinsa yayi sanyi yaji kamar ya fashe da kuka
Don haka sai ya koma gida ya zauna ya kasa zaune ko tsaye
Sai sunturi yakeyi yana tunani akan wannan mafarki nasa
Ahaka ya kwana ba tareda ya rintsa ba babu abinda yake face
Tunani akan gimbiya bahjaht da kuma mafarkin da yayi akanta
Ai kuwa wani ikon allah safiya nayi sai hassanul basari ya yanke jiki
Ya fadi kasa cikin matsanancin ciwo a wannan lokaci koda dan yatsansa ma baya iya dagawa
Har rana ta take ya kasa koda fitowa daga cikin dakin da yake kwance
Wannan al'amari ba karamin mamaki ya baiwa mutanen kabilarsu ba
Domin a kullum shine yake riga kowa fitowa daga gida
Da zarar ya fito to zai wucene gidan malan ramadan ya gaisheshi
Daga nan kuma sai ya wuce cikin daji dashi da wasu tsirarun abokansa domin yin farauta
Koda ýan kabilarsu suga fuskanci cewa hassanul basari bai
fito daga gida ba a wannan rana sai hankalinsu ya dugunzuma
Suka fuskanci lallai akwai matsalar da take faruwa acikin gidan
Koda yin wannan nazari sai kawai mutane suka taru suka sakawa kofar gidan nasa duka
Har saida ta karye ta rufta ciki
Dukkansu suka dunguma cikin gidan don su ga halin da shugabansu yake ciki
Da shigarsu sai suka tarar da hassanul basari cikin wani irin mawuyacin hali mai kama da suma ko mutuwa
Take hankalinsu ya dugunzuma suka tura wasu daga cikinsu da su tafi su kirawo malan ramadan wasu kuma su nemo likitoci domin su duba lafiyarsa
Cikin kankanin lokaci malan ramadan da likitoci suka hallara
Nanfa aka sallami duk mutanen da suke cikin dakin suka koma waje suka zauna
Sannan likitoci suka fara gwada jikinsa kafin su fara bashi magani domin su san irin ciwon da yake damunsa

Saida suka shafe sa'o'i suna bincike sannan suka dago da kansu jikinsu a sanyaye suka dubi malan ramadan sukace
Yakai babban malami ka sani cewa binken da mukayi ba komai bane yake damun hassanul basari ba face tunani mai yawa
Wanda sanadiyar hakan ne ya haddasa masa ciwon zuciya mai karfi
Kuma da alamu a daren jiyane kawai ya Hana idonsa barci ya sakawa zuciyarsa tunani mai yawa
Domin da zarar ka kalli kwayar idanunsa zakaga alamar rashin bacci acikinsu
Sannan kuma abinda zai kara tabbatar maka da maganar mu shine
Kayan yakin da suke jikinsa, kai da kanka ka sani kayan yaki ba kayan kwanciya barci bane
Dole akwai wani burin da yake zuciyarsa wanda yake da burin saduwa dashi a kurkusa sai anyi da gaske sannan za'a iya shawo kan wannan ciwon nasa
,amma yanzu zamu bashi magunguna wadanda zasu taimaka masa
Take suka debo wasu magunguna suka dura masa abakinsa ya kurba da kyar ya hadiyesu
Sannan suka tashi suka barshi acikin dakin daga shi sai malan ramadan
Kai abu dai kamar wasa duk maganin da akayi masa sai yaki yayi tasiri domin koda yaushe jikinsa kara rikicewa yake
Al'amarin salban kuwa hankalin sa yafi na kowa tashi game da halin da abokinsa ya shiga
Don haka sai ya yanke hukunci kawai ya tafi birnin shawana domin ya sanarwa da gimbiya bahjaht halinda yake ciki
Koda kuwa zai rasa rayuwarsa gaba daya, koda yin wannan tunani
sai kawai ya faki idon mutane ya dauki dokinsa sannan ya
fice daga cikin sansanin gaba daya Yadda babu wanda saiga tafiyarsa bare ya tambayeshi inda zaije
Take ya danna kansa cikin daji yana mai tsala azababben gudu tamkar zai bar nahiyar gaba daya saida ya shafe ýan dakiku yana tafiya
Kawai sai ya hadu da wasu fatake akan hanyarsu ta dawowa daga birnin shawana
Har ya dan ratse zai kauce musu kawai sai yaji wani daga cikin su
Yana kiransa cikin sauri yaja linzamin dokinsa ya adaidai inda suke
Kawai sai wanda ya kirashi yace dashi yakai wannan matashi
Naga Alamu kaima birnin shawana ka nufa ko. Ba haka bane?
Dajin wannan tambaya sai salban ya amsa musu da hakane
Kawai sai bafataken yace dashi
To ina baka shawara daka koma da baya domin muma
da kyar muka samu aka barmu muka fito daga cikin birnin
domin yanzu haka sarki mayasin ya kafa dokar hana shiga da fita acikin birnin
Koda jin haka sai salban ya tambayeshi ko ya san dalilin wannan sabuwar doka
Dajin wannan tambaya sai bafataken ya amsa masa da cewa
Na sami labari abakin wani hadimin gidan sarauta cewa
Yanzu haka gimbiya bahjaht ta kamu da soyayyar wani jarumi mafarauci wai ana kiransa da hassanul basari
Shi kuma mahaifinta baya son wannan soyayyar saboda hakane ya dauki mummunan mataki na wulakantata ta a gaban jama'a
Nan dai ya kwashe labarin duk abindaya faru tsakanin gimbiya bahjaht da sarki mayasin ya fada masa harda ma maganar gidan kurkukun darul maut ya fada masa
Kodajin wannan labari sai zuciyar salban ta buga da karfin gaske
Saboda ya fuskanci kamar yadda shi hassanul basari yake
cikin matsanancin hali saboda soyayya to haka itama gimbiya
bahjaht take awannan lokaci kawai sai ya juya linzamin dokinsa baya cikin sauri
Ba tareda yayi musu koda sallama ba ya kama hanyar komawa gida da sauri
Nanfa wadannan fatake suka kara kamuwa da tsananin
mamaki dalilin dayasa shi komawa da baya da sauri haka sakamakon jin wannan labari
Ai kuwa a wannan karon cikin lokaci kankani ya isa sansaninsu
Saboda yadda ya kagu akan ya kawowa hassanul basari labari akan halinda gimbiya bahjaht take ciki
Da isarsa sai ya wuce kai tsaye zuwa dakin hassanul basari ya iskeshi a kwance har sannan babu alamun lafiya ajikinsa
Sannan malan ramadan yana zaune agefensa yana faman lazimi
Koda ganin haka sai ya yiwa malan ramadan inkiya akan ya fito waje su yi magana
Take kuwa malan ramadan ya tashi ya biyoshi
Ba tareda bata lokaci ba ya bashi labarin abinda suka tattauna jiya shida hassanul basari
Da kuma labarin daya je ya samu a bakin wadannan fatake ya fada masa

Ashe duk wannan magana da suke tattaunawa hassanul basari yanaji daga inda yake kwance
Nantake ya mike zumbur daga kwanciyar da yake kamar bai taba wani ciwo ba
Yana mikewa babu abinda ya fara ambata face sunan gimbiya bahjaht
Sannan ya falfala da gudun gaske ta gabansu malan ramadan ya wuce
Koda sukaga yadda ya sami lafiya lokaci guda sai duk suka cika da mamaki domin basu taba ganin irin wannan ciwo ba
Abinda basu sani ba shine ciwon soyayya babu abinda baya haddasawa
Malan ramadan da salban sukayita kwala masa kira amma ina shi ko kadan baya jinsu zuciyarsa gaba daya ta tafi cikin tsananin tunanin gimbiya bahjaht
A wannan lokaci gudun da yakeyi ya zarce irin wanda ya sabayi abaya
Don haka cikin kankanin lokaci ya karaso bakin birnin shawana
Saidai kash !!
An sami sabani domin a wannan lokacin har boka sahibul ukub
Ya gama baje birnin tareda sihirtattun mikiyoyinsa
Babu sauran wata halitta wacce take numfashi acikin birnin
Koda ganin wannan danyen aiki saiya canja hanya ba tareda ya koda tsaya ba
Ya nufi hanyar da zata kaishi can kurkukun darul maut
Domin ya tarwatsa kurkukun ya dauko gimbiya bahjaht da karfin tsiya
Aikuwa kafin cikar dakika sittin har ya isa tun daga nesa jikinsa yayi sanyi
Domin hango kurkukun yayi an rugujeta kai bama ita kadaiba
Hatta tsaunin da take kansa anyi daga daga dashi kuma tun daga inda yake
Yana iya hango yadda jinin mutane yake gangarowa kasa
Kamar an ruwa ta cikin matse matsin duwatsu,
Take ya kara karfin gudunsa don yaje yaga abinda yayi musu wannan kisan gillan
Sannan yaga halin da masoyiyarsa take ciki
Isarsa keda wuya sai ya fara laluben gimbiya bahjaht kai tun da hasken rana
Har saida rana ta fadi duhu ya shigo amma bai tsaya da lalube ba
Kai saidaya bincike ko'ina hatta kasan tsaunin inda katangu suka daddan ne mutane sai daya bincika baiga gimbiya bahjaht ba
Ko kuma gawarta ba, wannan ne ya tabbatar masa dacewa
Lallai gimbiya bahjaht bata wannan wuri kuma saceta akayi
Koda gama yin wannan tunani sai ya takarkare ya kwarara uban ihu
Nantake ya fara diban manyan duwatsu yana jifa dasu kamar wanda ya dauki lomar abinci
Duk da cewa kowanne dutse inda za'a tara samari majiya karfi mutum ashirin ba zasu iya koda rabashi da kasa ba
Amma sai gashi mutum daya tak yana jifa dasu saboda tsananin fusatar da yayi
Tun yanayi a tsaye har saida yaji kamar kafafunsa ba zasu iya daukar nauyinsa ba
Yana cikin wannan haline kawai sai ya tuna da mafarkin da yayi acikin daren jiya
Koda yin wannan tunani sai ya daga muryarsa cikin fusata
Karar sautin muryar tasa ce tasa tsuntsaye suka fara guje guje suna sauya sheka
Dabbobin da suke dajin kuwa suka gigice suka fara gudun ceton
ransu domin duk dabbobin da suke nahiyar babu wacce bata san sautin muryarsa ba
Domin jinta suke kamar saukar aradu acikin kunnuwansu yace
Na rantse da ubangijina kowanene ya aikata wannan danyen kuskure
Saina dandana masa dacin mutuwa da hannuna
Yana gama fadin haka saiya juya ya kama hanyar komawa gida
Domin ya baiwa malan ramadan labarin mafarkin da yayi kuma ya fassara masa shi ko zai sami bayanin da zai gamsar dashi
Daga kurkukun darul maut zuwa inda sansanin banu sudes yake tafiyace ta kimanin sa;'o'i uku amma sai gashi ya shafe wannan tafiyar cikin sa'a daya kacal
Koda karasowarsa kai tsaye sai ya wuce gidan malan ramadan
Ta tsakiyar sansanin ai kuwa sai kowa yabishi da kallo cike da mamakin yadda akayi ya sami lafiya alokaci guda haka
Koda zuwansa gidan sai ya tarar da malan ramadan zaune yana jan cazbaha
Take ya gaisheshi sannan ya kwashe labarin komai ya fada masa
Tun daga farkon haduwarsu da gimbiya bahjaht da kuma alkawarin dake tsakaninsu
Kai harda mafarkin da yayi jiya akanta har zuwa abinda yake ya gano yanzu
Ma'ana saceta din da akayi, kodajin wannan labari sai malan ramadan ya cika da tsananin mamaki domin jin al'amarin yayi kamar wasa
Don haka saiya dago kai yace
Lallai wannan al'amari akwai ban al'ajabi acikinsa
Don haka sai ka saurara kaji fassarar mafarkinka da kuma wanda ya sace gimbiya bahjaht

Da farko dai inaso ka sani shi wannan tarkon daya kama gimbiya bahjaht ba komai baneba

Face kurkukun da mahaifinta ya tsareta Su kuma wadannan
damisoshin da suke gadinta sune dakarun da suke tsaron kurkukun
Sai kuma abu na karshe wanda shine babban tashin hankali
wato wannan murgujejen zakin daya zo ya hallaka wadannan
damisoshin ya cafi wuyan bahjaht ya haye da Ita saman dogon tsauni
Ba kowa bane ba face BOKA SAHIBUL UKUB

Shidai wannan boka ya kasance takadirin gaske kuma mara
imani wanda ya gagari duk sauran nahiyoyin da suke makobtan wannan nahiya tamu
Babban burinsa shine yaga ya mallaki duniya gaba dayanta yadda komai da kowa zai dawo karshen mulkinsa
Kai yanzu haka ma maganar da muke wadancan nahiyoyin duk sun mayar dashi abin bauta
Yanzu haka duk shi suke bautawa saboda tsananin tsoronsa da sukeji
Kai bama mutane hatta aljanu da dabbobi suna tsananin tsoronsa
Da kuma yi masa biyayyar dole, badon komai. Ba sai don tsananin rashin imaninsa da kuma rashin son zaman lafiyarsa
Kai yanzu haka duk nahiyoyin da yake mulka ba a zaman lafiya acikinsu
Domin ya halattawa kowa zalunci, ma'ana duk wanda yafi wani karfi to shine a sama
Babu wanda yake da kwanciyar hankali tun daga kan talakawan gari har zuwa kan masu mulki
Saboda kowa farautar rayuwar kowa yake
Yanzu haka duk duniya babu matsafi mai tarin sirrikan tsafinsa
Saboda haka kusan shi yake sarrafa dukkan sarakunan duniya da kuma matsafansu
Nahiya dayace kawai ta rage masa ya zamana ya mallaki duniyar nan gaba dayanta
Wannan nahiyar kuwa itace nahiyar nan wacce muke ciki
Ita dinma ya kawo mata hari ta hanyar turo sihirtaccen maridinsa
Ya fara kawowa birnin shawana hari da nufin ya bajeta daga doron kasa
Tunda itace masarautar datafi kowacce masarauta girma acikin wannan nahiyar tamu
Amma sai allah ya kaika ka ruguza masa shirinsa ta hanyar kashe
Wannan maridi daya turo
Saboda wannan dalilin ne ya taho da kansa yaci birnin shawana da yaki
Sannan yaje har cikin kurkukun darul maut ya dauke gimbiya bahjaht
Ya tafi da ita can fadarsa domin ka kai kanka ya hallaka ka
Ya kai hassanul basari ina mai tabbatar maka da cewa
Sai kayi da gaske sannan zaka iya zuwa wannan fadar tasa
Domin akwai tsaro mai tsauri akan hanyar zuwa wanda allah ne kadai zai kareka daga sharrinsu bawai sadaukantaka kadai na
Wadanda bansan adadinsu ba dole sai kayi da gaske sannan zaka iya tarwatsa su ka shiga cikin fadarsa ka isa har inda gimbiya bahjaht take tsare ka daukota ka taho da ita
Yanzu haka fadarsa tana can nahiyar kudancin duniya
Cikin wani kungurmin daji wanda akewa lakabi da duniyar sihiri
Babu wata halitta wacce ta isa ta shiga wannan daji ta fito a raye
Saboda hatsarin dayake cikinsa, na sihirtattun aljanu da halittu kala daban daban
Inaso ka sani cewa duk wannan abubuwa nagansu ne acikin barcina jiya da daddare
Idan har kanason gimbiya bahjaht araye dolene kayi shiri ka tafi nemanta

SHIN HASSANUL BASARI YANA TAFIYA NEMAN GIMBIYA BAHJAHT?
WANNE IRIN TASHIN HANKALI NE ACIKIN DAJIN DUNIYAR SIHIRI?
WANNE HALI GIMBIYA BAHJAHT TAKE CIKI?
SHIN ANA SAKE KAFA BIRNIN SHAWANA KUWA?

DON JIN KARASHEN WANNAN LABARI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT***********ZUBAR DA JINI

*******************6 PART C

LBR
*****************HABIBULLAH KBR

INDA MUKA TSAYA
Yanzu haka fadarsa tana can nahiyar kudancin duniya
Cikin wani kungurmin daji wanda akewa lakabi da duniyar sihiri
Babu wata halitta wacce ta isa ta shiga wannan daji ta fito a raye
Saboda hatsarin dayake cikinsa, na sihirtattun aljanu da halittu kala daban daban
Inaso ka sani cewa duk wannan abubuwa nagansu ne acikin barcina jiya da daddare
Idan har kanason gimbiya bahjaht araye dolene kayi shiri ka tafi nemanta
INDA ZAMU CI GABA
Bansan tazarar nisan tafiyar dake tsakanin mu da wannan nahiyar ba
Amma zan hadaka da wani hadimin aljani na wanda zai daukeka daga nan har zuwa farkon dajin duniyar mutuwa
Anan ne shi zai ajiyeka yayi zaman jiranka har zuwa sanda zaka dawo
Sannan ya sake daukoka ya dawo dakai nan fadar tawa
Shi dai wannan aljanin ya kasance ma'abocin addinin musulunci ana kiransa da suna hadimul islam
Wannan aljani ina tabbatar maka da cewa yana da matukar karfin gudu kamar yadda kaima kake dashi
Duk da cewa kaima nasan kana da karfin gudu, zan hada ka dashine saboda ya debe maka kewar tafiya tun daga nan har zuwa can farkon dajin duniyar mutuwa
Abu daya kawai zan baka shawara akansa, kasan ace kowa agidansa sarki ne
To dan haka dolene ka mike tsaye ka yi amfani da dukkan sadaukantakar da allah ya baka da kuma addu'o'i
Domin neman nasara daga mahalicci, shi kansa aljani hadimul islam
Nasan yana da burin shiga cikin wannan duniyar koda kuwa zai rasa rayuwarsa
Amma lokacin hakan baiyi ba, kuma ayau zan baka ajiyar da mahaifinka ya bani ita don na ajiye maka ita tun kafin ya rasu
Yana gama fadin haka sai ya tashi ya shiga cikin gida bai fito ba saida ya dan jima kadan sannan ya fito
Dauke da wani farin kyalle wanda aka lullube wani dogon abu ajikinsa
Da kallo daya zakayi kasan cewa abune mai matukar mahimmanci aciki
Koda ya karaso gaban hassanul basari sai ya zauna suna kallon juna sannan ya mika masa wannan farin kyallen tareda umartarsa daya bude yaga ko menene aciki
Aikuwa take hassanul basari ya yaye kyallen
Take yayi arba da wata siririyar sanda wacce aka sana'anta ta da zallan azurfa
Tana da maruki daga tsakyarta sannan a samanta kuwa kaifi ne kamar na takobi
Daga kasanta kuwa tsini ne da ita kamar mashi
Sai sheki da walwali take, kamar zata kashe ido, sannan ajikinta
An yi rubutun wasu addu'o'i na neman tsari masu karya sihiri
Da kuma sunayen allah dari ba daya,
Malan ramadan yace dashi kaga wannan sandar tana da matukar tasiri
Wajen karya sihiri kayi amfani da ita a sanda ka isa fadar boka sahibul ukub
Dajin wannan batu sai hassanul basari ya kara damke wannan sandar da hannunsa
Daga can kuma sai ya daureta akan gadon bayansa
Ba tareda bata lokaci ba hassanul basari ya fito sukayi bankwana da abokansa da mutanen gari kan alkawarin yanzu lura da wannan kabila yabar hannunsa ya koma hannun malan ramadan
Awannan rana mutanen wannan kabila sunsha kukan bakin ciki saboda rabuwa dashi musamman ma salban domin saida kyar ya iya hakura suka rabu da hassanul basari
Sannan ya shiga gida ya dauko abincin guzuri dan kadan da kuma ruwa wanda

Please Login or Register in order to submit comment