Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama kasar saita tashi tabi cikin iska bata sauka ako'ina ba
Sai abayan aljanin sannan kasar ta gade jikinta ta koma sarki aryan tareda dokinsa
Cikin sauri aljanin ya juyo bayansa alokacin da yaji aryan yana kyalkyala masa dariya
Koda suka hada idanu dashi sai ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar yace da aljanin
Ai gashi nan ko yanzu na nuna maka hatsabibancin bil'adama amma duk da haka babu abinda zai hanamu gwadawa da karfin dantse domin abanbance tsakankanin aya da tsakuwa
Koda gama fadin hakan sai ya dako tsalle daga inda yake tsaye ya sauka daga kan dokin sa asama ya kawo wa aljanin mummunan sara
Cikin sauri aljanin yasa wata ýar gajeriyar adda da take hannunsa ya kare saran
Koda makanan nasu suka hadu sai wani irin tartsatsin wuta ya tashi
Nantake suka kachame da azababben yaji atsakaninsu
Tare da kaiwa junansu sara da suka
Wohoho ai kuwa ana fara wannan yakin hankalin komai da kowa dake cikin dajin ya tashi
Tsuntsaye suka fara guje guje acikinsa suna canja suke
Dabbobi kuwa suka dinga chakuduwa da junansu ba tareda sun sani ba
Domin kuwa sai kaga barewa ta shiga cikin garken zakuna ba tareda sun cutar da ita ba
Kura ta tashi ta turnuke sararin samaniya sai a wannan lokaci aryan ya kara nunawa aljanin tsantsar hatsabibancin bil'adama domin kuwa duk da cewa aljanin yafi shi girman jiki
Da kuma karfin damtse amma sai ya zama na banza domin ko kadan ya kasa samun nasarar koda lakutar jikinsa
Ba komai ya janyo hakanba face tsananin zafin namansa
Ana cikin wannnan fafatawar ne aljanin ya shammace shi ya gabza masa duka da kafa saboda karfin dukan sai daya tashi sama ya fado da rubda ciki wani gudan jini yayi futar burgu daga bakinsa
Koda aljanin yaga ya sami wannan gagarumar nasarar sai shima ya kyalkale da tasa dariyar yace
Haba dan saurayi kai wanene ya taba ce maka tsafi yana karya acikin sha'aninsa ?
Koma dai wanene ya fada maka ina tabbatar maka da cewa karyarsa ta sha karya
Domin ga mutuwarka nan a gabanka ai kuwa yana gama fadin haka sai ya kaiwa aryan taku da kafa da nufin ya talitse shi
Koda kafar tazo daidai jikinsa sai ya nuna kafar da tafin hannunsa
Take wani irin haske ya fito ya ratsa jikinsa tun daga kan fafafunsa har kan kwayar kansa
Yaji kamar an zare masa dukkan kuzarin da yake jikinsa
Kafin ya kara yin wani yunkuri tuni aryan ya daka tsalle daga inda yake ya caka masa takobi atsakiyar ruwan cikinsa
Nantake jini yayi feshi daga cikin nasa shi kuwa aryan sai sake daka wani tsallen ya koma can baya kadan
Alokacin ne hanjin cikin aljanin suka zubo kasa daga ruwan cikin nasa
Nanfa yayi wani irin ihu wanda ya cika dajin gaba daya
Sannan ya sulale kasa matacce
Koda ganin haka sai aryan yayi wani guntun murmushi sannan ya mayar da takobinsa cikin kufe
Ya koma can inda dokinsa yake ya kwanto battar ruwansa ya zuba a fuskarsa ya wanke jinin daya fita daga bakin nasa
Ba tareda bata wani lokaci ba ya sake dane kan dokin nasa ya nausa cikin daji domin neman gimbiya walisa
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA SARKI ARYAN BAYAN SUN FAFATA DA WANI ALJANI

******* ******** *********
Al'amarin gimbiya walisa kuwa lokacin da dakarun sarauniya suzaila suka ja dokinta suka shiga da Ita cikin birnin durgan har a wannan lokaci tana cikin halin barci bata farka ba
Duk inda dakarun suka ratsa da ita idan mutane suka ganta sai su tausaya mata
Ba komai ne ya janyo haka ba face tsananin kyawunta da suke gani
Domin babu da namijin da zai yi arba da ita ba tareda yaji sha'awarta ba acikin zuciyarsa

Kai hatta ni habibullah kbr da na ganta a wannan lokaci sai da nayi kwallah saboda tausayinta

Domin duk inda ake bukatar mace mai kyau gimbiya walisa zata iya shiga sahunsu
Su kansu dakarun da suke dauke da ita babu wanda baiji ajikinsa cewa
Dama abar masa ita ya tafi da ita can gidansa domin ta zama kuyangarsa ba
Kawai dai sunajin tsoron furta hakan ne don kada sarauniya suzaila tayi musu hukunci mai tsanani

Ahaka suka dinga ratsawa da ita ta cikin gari har sukazo daidai gidan sarauta
Suna zuwa daidai kofar gidan sai dakarun dake tsaron kofa
Suka bude musu kofa suka shige ciki sannan suka maidata suka rufe
Ýar kankanuwar tafiya sukayi suka iso bangaren da bayi suke acikin gurin ne aka ware wani bangaren daban ake ajiye duk wanda aka kama yazo ketarewa ta bakin birnin har sai sarauniya suzaila tazo ta yanke masa hukunci da kanta
Aikuwa suna zuwa bakin dakin sai suka sa makulli suka budeshi
Sannan suka daura mata manyan sarkoki ahannuwanta, kafafunta da kuma wuyanta sannan suka sauke ta daga kan dokinta aka fice dashi
Makaman da suke jikinta ma sai suka debe su suka rayaye ajikin wata kusa wacce aka kafe a wajen dakin idan an fita daga cikinsa sannan suka mai da kofa suka rufe
Suka kama gabansu
Fitarsu keda wuya sai suka wuce zuwa wajen sarkin fada suka sanar dashi cewa sunzo da wata sabuwar fursuna mai tsananin kyawun gaske
Shi kuma kai tsaye ya zarce turakar sarauniya suzaila ya sanar da ita halin da ake ciki

Koda jin labarin wannan bakuwar fursuna sai sarauniya suzaila ta bushe da dariya tace ai na fika sanin halinda ake ciki
Ayanzu domin kuwa wannan fursuna itace wacce na dade ina nema ruwa a jallo
Dajin haka sai mamaki ya kamashi ya dubeta yace shin dama kin santa ne?
Kodajin wannan tambayar sai tayi murmushi tace kwarai kuwa
Inaso ka sani ita wannan bakuwar fursuna mutum ce mai hatsari kuma itace
wacce ta shiga tsakanin ýar uwata wato jaruma marfuza da sarki aryan ta hanashi karbar soyayyarta
Duk da cewa kuwa ýar uwata tana matukar kaunarsa fiye da rayuwarta
Sanin kanka ne duk saboda shi ta bar birnin nan namu ta tafi can nahiyar su
har ta isa cikin birnin shawana birnin da sarki aryan yake mulki
Ta shiga gasa mai matukar hatsari duk da tasan cewa wannan gasa daidai take da gasar mutuwa amma
ta shiga cikin jaruman gasar duk don ta sami nasarar nunawa sarki aryan soyayyarta agareshi
Kuma tayi nasara akansa
Saidai kuma wannan bakuwar fursunar da kike gani
itace tazo ta rusa duk shirin da ýar uwata tayi
Ni kaina na rasa abinda tafi ýar uwata marfuza
don haka zan ajiyeta anan harsai shi sarki aryan din yazo da kansa ya yarda zai auri ýar uwata marfuza sannan zan saketa

Amma kuma dolene nayi taka tsantsan akan gimbiya walisa domin itama macece mai hatsarin gaske
Domin muddin muka kuskura ta farka daga dogon barcin da takeyi
To abune mai matukar wahala mu iya kamata koda kuwa zamu hada karfi da karfe ni da jaruma marfuza
Tana gama fadin haka sai ta karanta wasu dalasiman tsafi
Nantake ta bace daga inda take bata bayyana ako ina ba face gidan kurkukun dake cikin gidan sarautar
Alokacin duk fursunonin suna cikin tsananin yunwa da kishirwa sai koke koke suke
Amma koda sukaga sarauniya suzaila ta bayyana sai sai duk suka nutsu
Saboda tsananin tsoronta da suke ji cikin sauri ta dafa kofar dakin da hannunta take kofar ta bude kanta
Itakuma ta shige ciki kawai ta kwanto wata farar hoda daga aljihunta ta hurata a daidai hancin walisa
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai barcin nata ya kara karfi har tana minshari
Koda ganin haka sai ta bushe da dariya mai karfin gaske
Wacce sai data ratsa ko ina acikin gidan sarautar amma gimbiya walisa batajin sautin komai saboda dadin barcin da takeyi
Koda ta gama kyalkyala dariyar ta ta isheta sai ta sake bacewa
Bata sake bayyana a ko ina ba face turakar jaruma marfuza
A wannan lokaci tana zaune akan wata kujera agabanta an zube mata kayan ciye ciye kala da ban da ban amma ta kasa cinsu kawai dai ta saka su agabane amma zuciyarta cike take da tunanin sarki aryan
Bayyanarta keda wuya sai ta karasa gabanta ta dafa kafadunta
Cikin sauri marfuza ta dago da kanta don taga ko wanene
Bisa mamaki sai taga ýar uwarta sarauniya suzaila atsaye akanta tana yi mata murmushi
Cikin mamaki ta dubeta tace yake ýar uwata shin menene ya kawo ki a wannan lokaci kuma murmushin me kikeyi mini domin na kasa gane kansa
Dajin wannan tambayar sai sarauniya suzaila tayi murmushi tace
Ki kwantar da hankalin ki domin yanzu kina daf da mallakar wanda zuciyar ki ta mutu acikin soyayyarsa
Dajin haka sai mamaki ya turnuke marfuza tace har yanzu ban gane manufarki ba
Kodajin haka sai nantake ta kwashe labarin komai ta zayyanewa marfuza
Data gama sauraron sarauniya suzaila sai kawai ta girgiza kai cikin alamun takaici tace
Indai kuwa hakane to gaskiya kin tabka babban kuskure
Ki sani cewa ko kadan gimbiya walisa bata da hannu wajen hana sarki aryan karbar soyayyata
Sai daima taimako na da tayi a lokacin da yake daf da hallakani
Inaso ki sani wannan tarko da kika yiwa walisa ba zai sa sarki aryan ya fada cikin soyayyata ba
Saidai ma ya kara tsanata
Ke har yanzu abu dayane baki fuskanta ba wannan abu kuwa shine
Shi so ba'a taba sayensa da kudi komai yawan dukiya
Kuma babu ruwansa da kyau ko nasaba atakaice dai shi so gamo na jini ne
Ba'a iya yi masa dole duk wanda yace yana sonka to babu mai rabaka dashi
Hakama duk wanda ya nuna baya kaunarka to baka isa ka tilasta masa ya soka ba
Don haka ina shawartarki daki saki gimbiya walisa tun kafin wata matsalar ta kunno kai

Koda jin wadannan kalamai sai sarauniya suzaila ta fusata akaron farko ta dakawa marfuza tsawa

ME NENE ZAI SHIGA TSAKANIN JARUMA MARFUZA DA SARAUNIYA SUZAILA?

SHIN SARKI ARYAN ZAI YARDA YA KARBI SOYAYYAR JARUMA MARFUZA?

ME XAI FARU GA GIMBIYA WALISA?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYIN SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment