Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka
Abinda ta manta shine
Shifa dan uwanta ne na jini kuma nono daya suka sha
Hakama horon yaki dana tsafi duk tare aka basu
Duk wani abu da take takama dashi to shima yana dashi
Ballantana kuma yanzu da yake da fifikon karfin damtse dana sihiri fiye da ita
Kuma ya kasance murucin kan dutse wanda bai fito ba saidaya shirya
Abindaya bata mamaki shine ko kadan baiyi motsi ba daga inda yake ba
Da ganin haka sai ya bushe da dariya yace
Lallai yarinya kinyi matukar burgeni amma duk da haka kin cancanci
Mutuwa dalilin da zai hana ni kasheki kawai shine
Duk inda mutum yake anaso ya sami makiyi
Ni kuma yanzu na fuskanci banida makiyin daya fiki
Saboda haka ga fili ga mai doki sai mu zuba muga wanda zaiyi nasara
Yanzu zan hallakar da mutanen garin nan idan ke kuma kin isa saiki hanani
Wannan shine babban kuskurenda ya aikata a rayuwarsa
Domin ya manta cewa komai kankantar makiyi abin tsorone

Yana gama fadin haka sai take taga ya rikide ya zama
Wata bakar guguwa mai karfin gaske, take guguwar ta
Hargitsa birnin gabadaya kura ta turnuke ko ina
Faruwar wannan abu keda wuya sai ta fara jin sautin ihun mutane a cikin wannan guguwar
Daga can sai taga guguwar ta tarwatse saiga sassan jikin su sarki kalkus
Ta zube kasa daga cikin guguwar
Koda ganin haka sai itama ta rukide ta zama bakar guguwa
Ta tafi da gudun gaske ta tari daya guguwar da nufin su kachame da yaki
Koda haduwarsu sai wata iriyar kara mara dadin ji ta tashi
Ta cika birnin gaba dayansa wanda hakan ya kara firgita
Mutane fiye da farko har saida dajijjikan da suke da makobtaka dasu
Suka amsa kuwwa dabbobi kuwa suka dinga faduwa suna mutuwa saboda karfin karar
Daga can saiga guguwar jaruma walisa an jefo ta kasa
Koda faduwarta saita rikide ta koma ainihin siffar ta
Jikinta duk yayi jina jina da jini kuma a lokacin ne
Itama daya guguwar ta rukide ta koma siffar yarima walisu
Jikinsa ko kadan babu wani tabon rauni kawai sai ya kalli
Walisa yayi mata murmushi mai kama dana mugunta
Ko kuma na raini sannan ya sake juyawa ya tashi sama
Ya koma kan jamaa'r gari yana tsinke musu kawuna
Da wannan sarkar tsafin da take hannunsa
Kaico hakika zalunci bashida dadi sai kaga mutum yana gudun
ceton ransa amma an kamashi an kashe Saboda rashin tausayi
Koda walisa taga abinda yake faruwa sai take itama ta daka tsalle ta mike tsaye
Kamar babu wani rauni ajikinta kawai ta shuri wani katon
Bargo wanda zai debi mutane da yawa akansa saboda kawarinsa
Sannan ta tafi daga inda yake wannan barna domin tasan indai
Yana gurin bata isa ta iya tsinana wani abu ba saboda banbancin su abayyane yake
Dolene saita jira wani dan lokaci wanda zata iya samun galaba akansa
Domin ta tabbatar da cewa a yanzu yafi ta karfin sihirin tsafi
Babu yadda zata iya gaba da gaba dashi saidai kawai tayi kokarin ceton rayuwar 'yan yara kanana
Wannan shine dalilin dayasa ta dauki wannan katon bargo
Kawai saita shiga cikin garin ta dinga surar yara tana dorawa akai
Sai dai kaga ta shuri bargon da duk mutanen da suke
Kansa ta tashi dasu sama tamkar tsummokara tana kaisu
Cikin wani dan karamin kauye wanda yake karkashin masarautar madaril adfam ta ajiyesu
Lokacin data dawo cikin wannan birnin kawai saitaga
Walisu har ya gama kashe mutanen birnin saura wani
Yaro guda daya wanda ya zauna agefe daya yanata rusa kuka
Shikuwa walisu ya nufi gurin yaron da nufin ya yi masa kisan farat daya
Kwatsam sai walisa tazo da gudun tsiya kamar daga cikin baka
Aka harbota ta shuri yaron kamar shaho ya shuri dan tsako ta tashi sama tana mai falfala azababbben gudu ta daure yaron a jikin kirjinta
Kamar gudun tauraruwa mai wutsiya
Koda ganin wannan abu sai nantake walisu ya fusata
Ya bude bakinsa
Take wata iriyar bakar wuta ta fito daga cikin bakin nasa
Tabi inda walisa tayi da matsanancin gudun gaske sai
Gashi sunata gasar tsere da ita da wannan wutar inbadon ma tana zulle mata ba da tuni wutar ta kamata ta babbake ta
Amma duk da haka sai gashi wutar taki yarda ta zarce
Ma'ana taki ta daina bin su abaya sai zulle zulle suke yi
Shi kuwa wannan yaron data dauko tuni ya dada rudewa
Domin bai taba ganinsa a sararin samaniya ba kuma
Gashi a wannan lokaci gudun mutuwa akeyi dashi yana
Kallo sunata gifta birane da kuma manyan duwatsu akasansu
Koda aka jima ana wannan faman tseren gudu kuma
Ta tabbatar da cewa wannan wutar ba zata taba daina binta ba
Kuma idan har ta gaji to tabbas karshenta yazo kawai saita
Fara yin tunanin hanyarda zata bi domin tsira da rayuwarta
Kwatsam saita hango wani katon ruwa acan nesa
Da inda take, koda ganin wannan ruwa saita kara zage damtse
Ta tafi inda yake sannan ta sauka kasa cikin ruwan ta nutse gaba dayanta
Take itama wannan wutar ya sauka akan ruwan
Koda faruwar hakan
Sai wata kara mata dadin ji ta tashi sama tareda wani
Irin bakin hayaki
Faruwar hakan keda wuya sai ruwan gaba dayansa ya kafe ya zama tabo
Tamkar dama can haka yake ruwa bai taba taruwa a wajen ba
Amma duk da haka saida tartsatsin hasken wannan wuta ya taba bayanta
Amma ko kadan bai sami wannan yaron ba
Nan fa ta fara kokarin ta fito dasu daga cikin wannan tabon
Koda ta dago kanta daga can karkashinsa zuwa sama
Kawai sai tayi arba da walisu adaidai saman wannan
Tabon yana kallon ko ina na cikin dajin ko zaiga gawar walisa
Koda ya gama nazarin dajin yaga baiga gawarta ba sai
Kawai ya bushe da dariyar mugunta kamar wanda aka yi masa kyakykyawan albishir
Sannan kuma ya murtuke fuskarsa cikin daga murya
Nasan cewa kina raye baki mutuba kuma kina nan kusa dani
To dama ni haka nakeso amma da nayi niyyar hallaka ki da yanzu kin dade da shekawa barzahu
farinciki na dayane shine ganin cewa wannan wutar ta kona miki gadon bayanki
Kuma dolene kiyi jinyar wannan ciwo komai sihirin tsafinki
Bai isa ya warkar miki da wannan ciwon lokaci daya ba
Don haka sai kije kiyi jinya sannan idan kin warke ki dawo
Daga yanzu ba zamu kara haduwa ba ni dake sai bayan
Dan lokaci mai tsawo kuma komai irin kokarin da zakiyi
Domin ba zan sake kai hari wani gurin ba har sai na jira kin sami lafiya
Ba zaki sake ganina ba sai idan ni ne na bukaci haka
Mu ci gaba da farautar juna ina miki fatan samun lafiya cikin kankanin lokaci
Koda gama fadin haka sai nan take ya bude fuka fukansa
Ya tashi sama cikin gajimare ya bace mata da gani
Domin karfin gudunsa ya ninka nata sau hamsin
Koda bacewar
sa sai nan take walisa ta doro wannan karamin yaron akan kafadunta
Sannan ta rarrafo da kyar ta fito daga cikin wannan tabon
Alokacin da taji gaba daya jikinta yayi mata tsami saboda
Tsananin wahalar data sha koda ta gama fitowa saita
Sauke yaron daga kan kafadunta sannan ta dauki ruwa ta kafa abakinta ta kwankwada
Saboda tsananin kishirwar da take damunta
Bayan nan ta dauki magani ta zuba akan gurin data kone
Tana gamawa ta sami guri ta kwanta domin huce gajiyar jikinta
Koda ganin haka sai wannan yaron ya karaso gabanta yace
Yake wannan jaruma mai abin al'ajabi ina matukar godiya
agareki bisa ceton rayuwata da kikayi daga hannun wannan
azzalumin amma idan ba zaki damuba inaso na tambayeki
Koda jin haka sai tayi murmushi tace
Inajinka amma kafin ka tambayeni inaso ka fara fada mini sunanka
Yaron yace da farko sunana zaljus agabana wannan azzalumin ya kashe iyayena ke kuma kikazo kika ceceni
Tambayar da zanyi miki itace
Shin dama kinsan wannan mutumin? domin naga yadda yake yi miji magana kamar dama can ya dade da saninki
Dajin wannan tambaya sai kawai ya gyada kai tace
Kwarai kuwa yasanni kuma nima nasanshi
Asalima uwarmu daya ubanmu daya dashi kuma a rana daya
Aka haifemu nice babba sannan kuma shi
Duk wannan abu da kaga yana aikatawa shima ba'a saninsa
Yakeyi ba domin ruhin wani takadirin boka ne ya shiga jikinsa
Wanda ake kiransa da sahibul ukub to shine ya canja masa kwakwalwarsa
Kuma yake saka shi aikata wannan ta'addancin da kaga yana aikatawa
Wannan dalilin ne yasa nahaifina sukayi bincike da manyan bokayensa
Kan yadda za'a shawo kan wannan matsala amma sai biciken ya
Nuna musu cewa dolene nima na fito nemansa domin
Nice kadai zan iya gaba da gaba dashi ba tareda na mutu ba
Kuma yanzu na gamsu da duk abubuwan da suka fada
Domin gashi nazo na tareshi da yaki duk da cewa yafini karfin sihiri
Amma gashi ina raye har yanzu ban mutuba bayan haka
Harma yanzu na sami damar ceton yara kanana wannan babbar shedace
Da ta tabbatar mini da cewa nice zan iya hanashi aikata wannan mummunar dabi'a
Kuma zan cigaba da bibiyar sa har zuwa sanda zai dawo cikin hayyacinsa
Idan kaga na daina wannan aiki to sai dai idan na daina numfashi
Koda jin wannan labari sai zaljus ya girgiza kai saboda tsananin daure masa kai da al'anarin yayi
Kawai sai ya dago kansa kwallar tausayi tana zubowa
Ya dubeta yace
Gaskiya nayi matukar tausaya miki domin ban taba ganin irin wannan al'amari ba
Ni abinda na sani kawai shine a halayyar mutanen wannan
nahiya kana iya samun dan uwa da dan uwa suna farautar juna saboda tsananin kiyayya
Amma ke kuma kina kokarin ki hana naki aikata aikin barna ne amatsayinsa na dan uwanki
Sannan shi kuma yana kallon ki ne amatsayin abokiyar gabarsa
Daga wannan maganar suka tsaya da yin wannan hirar da sukeyi
Kawai sai walisa ta tashi ta rarrafa cikin wani katon kogon dutse
Da fitilar ice a hannunta ta dudduba ko'ina acikin kogon
Ta tabbatar babu wani abu wani abu mai cutarwa sannan
Ta yiwa zaljus shimfida, itama itama tayiwa kanta
Duk suka samu suka kwanta

SHIN MAI ZAI FARU ACIKIN WANNAN KOGON DUTSE?
INA LABARIN SARKI FADARUL MUNNAR MAHAIFIN SU WALISA
SHIN INA JARUMI WALISU YA TAFI?
MY HADU A KASHI NA GABA
DAGA
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++++++ 2PART C

LBR
+++++++++++++++ HABIBULLAH KBR

Kwanciyarsu keda wuya sai duk barci mai nauyi ya daukesu
Saboda tsananin gajiyar da take jikinsu haka sukayita shara barci mai nauyi abinsu
Basu farka ba saida safiya tayi lokacin da hasken rana
Ya fito ya shigo har cikin kogon dutsen ya dallare musu idanunsu, bashiri duk su biyun suka farka
Walisa ce wacce ta fara farkawa,
Tana tashi kawai sai tayi mika sannan ta shuri kwari da bakanta
Da nufin ta fita ta farauto musu abin da zasuci
Kawai sai zaljus ya sha gabanta yace
Haba ya 'yar uwata shin ina zakije ko kin manta da ciwon da yake bayanki?
Kodajin wannan tambaya sai tayi murmushi tace
Haba tayaya zan iya mantawa da ciwon da yake jikina
Wannan fitar da zanyi dolece ta saka zanyita domin nemo mana abincin da zamuci dani da kai
Kafin na sami wani garin da zan ajiyeka
Karka damu babu abinda zai sameni zan fita kuma zan dawo cikin nasara
Ina mai umartarka da ka zauna acikin kogon nan kada ka kuskura kace
Zaka fita ko ina daga cikinsa har naje na dawo
Tana gama fadar haka haka sai ta kama hanya ta fice daga cikin kogon
Koda fitowarta daga cikinsa sai ta kama hanya tana tafiya
Hannunta na hagu na ruke da kwari na daman kuma ruke da kibiya
Tana tafiyane cikin sanda ko zatayi arba da wata dabbar wacce zata farauta
Gaba daya cikin dajin yayi tsit bakajin sautin komai face
Na giftawar iska sai bayan ta shafe ýan lokuta tana tafiya sannan
Ta hango wata katuwar damisa daga can nesa da inda take
Koda yin arba da wannan damisar sai kawai ta dora kibiyarta
Akan baka ta saita tsakiyar cikin damisar ta harba
Cikin rashin sa'a sai damisar ta goce kibiyar taje ta cake ajikin dutse
Take damisar ta juyo sukayi ido biyu da walisa
Kawai sai ta falfalo da azababben domin tazo ta bangajeta
Ta kashe ta domin itama abinci ta fito farauta kuma gashi ta samu abati
Ita kuwa jaruma walisa sai ta tsaya cak ko motsi taki tayi tana jiran karasowar wannan ta
Koda ta iso inda walisa take sai ta daka tsalle sama da nufin ta turmushe ta
Ta kama fuskar ta ta yayyaga, take itama walisar ta sunkuya ta kaucewa harin damisar
Dukkansu su biyun sai suka yi turjiya akan kasa kura ta tashi
Sannan suka juyo suka kara afkawa juna da yaki koda fara wannan gumurzu
Sai gurin ya rinchabe kura ta tashi saboda kokawar da suke
Burin damisar kawai shine ta bangajeta ta fadi
Ita kuwa tana yin fadan ne domin kawai taga iyakar karfin ita wannan damisar
Saboda ta lura cewa damisar a haukace take saboda yunwar da takeji
Kawai hanya takeso ta samu wadda zata cutar da ita amma ta kasa
Koda walisa taga wannan damisar ta kasa cutar da ita kuma tana bata mata lokaci
Sai kawai ta shureta ta dagata sama ta buga kanta ajikin wani dutse
Take kuwa kanta ya dagargaje kwakwalwarta ta zuba akan kasa
Sannan ta dauketa ta dorata akan kafadarta ta kama hanyar
Komawa kogon dutsen da suke zaune, tafiya kadan tayi ta isa bakin kogon
Kai tsaye ta dannan kanta ciki har takai karshensa
Alokacin zaljus yana zaune yanata faman tunanin abindaya faru jiya
Kafin walisa tazo ta ceci rayuwarsa, don haka har ya shigo cikin kogon bai sani ba
Saidata dafa kafadunsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa
Walisa tace dashi kai kuma tunanin me kakeyi ne haka
Dajin wannan tambaya sai zaljus yace
Ina tunawa ne da tsohon birnin mu gaskiya ina mai matukar godiya agareki
Domin badon keba da tuni na dade da zama matacce
Dajin wannan magana sai walisa tayi murmushi tace
Bai kamata ka dinga tunawa da abinda ya riga ya wuce ba
Abinda zai faru nan gaba shi zaka dinga fuskanta Nayi maka alkawarin
Zan kaika wani gurin da zaka ci gaba da rayuwa acikinsa cikin
Kwanciyar hankali kuma anan ne zan rabu dakai inje domin na karasa aikin da yake gaba na
Koda gama fadin haka sai kawai tayi shiru da bakinta
Ta tashi ta dauki wannan damisar ta jata gefe ta fara aikin gyaranta
Cikin kankanin lokaci ta gama gyara naman damisar
Sannan ta hada itatuwa ta kunna kyastu wuta ta kama ta gasa naman da ita
Bayan ta gama gasa naman sai ta juyo ta dawo gurin zaljus
Ta ajiye masa nasa kason agabansa tayi masa izini daya dauka yaci
Sannan itama ta fara cin nata naman sunaci suna hira abinsu
Kamar dama can sun dade da sanin junansu,
Hankali suka gama cinye naman sannan walisa ta tashi ta fara hada kayanta
Domin su ci gaba da tafiyar da suke yi
Cikin lokuta kadan ta gama sanya kayan yakinta ajikinta
Amma bata rufe gadon bayanta ba saboda wannan kunar da take jikin gadon bayanta
Sannan ta tashi ta kama hanyar fita daga cikin kogon dutsen
Babu shiri shima zaljus ya biyota abaya suka fice daga cikin kogon dutsen
Suka kama hanyar da zata kaisu birni
Wanda ake kira da suna shawana, gaba daya mutanen wannan birnin sun kasance zakwakuran mayakane masu matukar karfin damtse da iya yaki
wanda shakkar wadannan mayakance tasa kasahen
da suke makobtaka dasu suke matukar shakkar su duk da cewa sun ninninkasu a yawa
Kasancewar shima shugaban wannan birnin
ya kasance matashine mai jini ajika, gashi ya kasance kyakykyawan matashi
Wanda ýan mata da yawa suke rubibin neman soyayyarsa
Amma bai taba kulasu ba, domin tunda ya taso bai taba ganin wata mace ba wacce ta burgeshi ba

Har yaji ya kamu da soyayyarta, wannan dalili ne yasa shi
ya karyata soyayya cewa ba gaskiya bace ba karyace
Koda ýan majalisarsa sukaji haka sai suka bashi shawara kan cewa
Yayi shiru da bakinsa kada ya bari wannan magana ta shiga kunnen mutanen gari
Don kada wataran yaji kunya saboda wannan maganar daya furta
Kuma wannan sarki ya kasance gawurtaccen mayaki, sannan a fannin karfin sihirima ba'a barshi abaya ba
Domin anan fannin ma shi ba kanwar lasa bane, bayan haka kuma shi bai kasance azzalumi ba
Kuma bai hana zalunci ba
Amma duk wanda ya zalunci wani to wanda aka zaluntar yana da ikon kai kara wajen sarki kuma a bi masa hakkinsa
Lokacin dasu walisa suka kama hanyar tafiya birnin shawana
Sai sukayita kutsawa ta cikin dajijjika iri iri agabansu
Kuma sunayin tafiya suna hira a tsakaninsu
Tazarar inda suke da kuma birnin shawana tafiyar rabin sa'a ce
Don haka basu dade suna tafiyarba suka iso wannan birnin
Tun daga nesa suka hango kofar birnin abude kuma ga dakaru nan
Suna aiki tsaron kofar kai da ganin wadannan dakaru
Kasan cewa dolene su kasance zaratan jarumai kuma gaba daya jikinsu
A rufe yake da sulken yaki koda wadannan dakaru suka
Hango jaruma walisa daga nesa tareda yaro zaljus sai duk suka dora hannuwansu akan kufen takubbansu
Suna masu jiran karasowarta suji me ke tafe da ita
Lokacin da ta karaso bakin kofar wannan birnin sai
Dakarun suka tareta wani daga cikinsu wanda ya kasance
Shine shugabansu yazo ya sha gabanta yace
Yake wannan bakuwa shin ke wacece kuma menene yake tafe dake
Sannan wannan wanne yaro ne atare dake? Munaso ki fada mana iyakar gaskiya
Kada ki boye mana komai dangane da abubuwan da muka tambayeki
Idan har kinason shiga wannan birni namu mai albarka
Kodajin haka sai tayi murmushi ba tareda ta yi musu maganaba
Kawai sai ta zaro hatimin sarautar birninsu na madaril adfam Ta nuna musu
Koda sukaga wannan hatimi sai dukkansu suka rissina
Agabanta cikin girmamawa sukace
Ki gafarce mu ya shugabarmu bamu san kece gimbiya walisa ýa ga mai girma sarki fadarul munnar ba
Muna neman afuwarki sannan munayi miki barka da zuwa bayan haka kuma munayi miki tayin

babbar gasar jarumta wacce aka saba gabatarwa a birnin nan duk sanda shekara tazagayo kamar yanzu
Ahalin yanzu birnin nan ya gama cika da jaruman gasa daga ko ina na wannan nahiyar
Don haka kema zamuso ki shiga wannan gagarumar gasa
Domin ki nanawa kowa jarumtakarki wacce muka saba jin labarinta

Amma kuma ina dan uwan naki ya shiga wato yarima walisu?
Kodajin wannan tambaya sai kawai walisa ta gyada kai tace
Ai yanzu ba tare dashi muke ba, ni kadaice
Wannan kuma yaron da kuke gani na tsinceshi ne a hanya
Tana gama fadin haka sai kurum ta kama hanya ta shige cikin birnin
Koda ta shiga cikin garin sai kawai taga birnin yacika ya batse
Da mutane masu yawan gaske kowa sai tafiyar da harkokinsa
Yake cikin kwanciyar hankali, ko'ina ka kalla saidai ka dinga ganin kabilu kala daban daban
Kuma zaratan karti masu kirar mutanen farko, ruke da mugayen makaman yaki suna aikin wasa su
Wasu kuma saidai kaga suna baiwa kansu horon yaki na daban
Lokacin data shiga cikin birnin shawana sai ta dauko wani
Bakin kyalle ta rufe fuskarta dashi yadda babu wanda zai iya ganin koda kwayar idanunta
Ba komai ne yasa taga mutane kowa yana shirye shiryen wannan gasa ba
Face saura kwana uku kacal a fara gabatar da wannan gasar
Kuma tun daga lokacin da aka fara gabatar da wannan gasar tsawon shekaru takwas
Sarkin garin ne mai suna aryan ne yake cinye wannan gasar ba'a taba samun sabani ba asaboda haka ne ma
Yasa yake yiwa kansa kirarin cewa shine gagara badau
Sadaukin da babu kamarsa a wannan karni
Jin wannan cika baki da sarki aryan yake yine yasa jarumai da yawa suka dauki alwashin cewa
Wannan shekarar sai sun ruguza masa tarihin jaruktakarsa
To a wannan shekara jarumai sun bayyana daga sassa daban daban na wannan nahiyar domin kawai
burin suga cewa sun sami nasarar kawo karshen tarihin jarumtarsa
Shi kuwa sarki aryan ko kadan wannan alwashi da sukaci
Bai dameshi ba domin yayi imani kan cewa shine wanda zai cinye wannan gasar
Komai wuya ko rintsi, don haka nema yasa kyautar dukiya mai yawan gaske ga duk wanda ya sami nasara akansa
Aban garen jaruma walisa kuwa ko kadan bata shigo wannan birnin
Don halartar wannan gasa ba, kawai dai ta shigone don ta sami wanda zata baiwa amanar yaro zaljus ne
Sannan kuma su sami inda zasu yada zango tsawon ýan kwanaki
Sannan ta tashi ta kama hanya tabar wannan garin ta kara gaba
Haka dai sukayita tafiya acikin birnin shawana su biyu rak
Duk inda suka wuce saidai kaga anata kallonsu, kai tsaye ta nufi hanyar da zata kaita gidan sarkin kasuwa
Wanda ya kasance dattijo ne dan kimanin shekaru hamsin
Gidansa yana daga can karshen kasuwa kuma agurinsa
Duk wani bako yake samun gidan da zai zauna domin yin haya a wannan birni
Kuma mutumne shi mai son baki da kuma girmama mutane
Wannan dalilin ne yasa kowa yake yabonsa acikin birnin
Tafiyar dakiku kadan sukayi sannan suka iso gidan sarkin kasuwa
Suna zuwa suka tarar da dakaru kimanin su goma suna gadin gidan
Koda ganin wadannan dakaru sai kawai walisa ta karasa gabansu
Ta tsaya ta dubi shugabansu tace inaso kayi mini sallama da mai gidan ku wato yimana
Kodajin wannan batu sai mai gadin yace
To ke kuma wacece kuma mai yasa kike son ganin yimana?
Dajin wannan tambaya sai tayi murmushi sannan tace
Tabbas ku baku sanni ba, amma shi mai gidan naku da zarar yaji muryata
Nasan zai shaida ni koda bai kalli fuskata ba
Kodajin wannan batu sai badakaren ya girgiza kansa
Sannan ya juya ya shiga cikin gidan, bai dade da tafiya ba sai gashi
Ya dawo tareda sarkin kasuwa yimana, koda fitowar su
Sai yimana ya dubi walisa yace ke kuma wacece kuma
Me kike da bukata a gurina?
Dajin wannan tambayar sai walisa tace
Ni bakuwa ce daga can wata nahiyar daban kuma nazo ne domin ka taimaka mini da masauki
Lokacin da takeyin wannan bayani sai kawai dakarun sukaga yimana ya kame kyam kamar gunki
Yana nazari akan muryar wannan budurwa
Daga can kuma sai sukaga ya bushe da dariya yace
Lale marhaban da zuwan gimbiya walisa kuma basadaukiya
Mai abin al'ajabi nayi matukar farin cikin sake haduwa dake a rayuwa ta
Kuma inayi miki barka da shigowa cikin birnin mu mai albarka
Nandai yayi mata jagora suka shige cikin gidansa tare gabaki dayansu
Ahaka sukayita shigewa ta cikin soraye har suka kai tsakiyar wani babban falo
Sannan yayi mata nuni da wata kujera ya umarceta data zauna akanta
Take kuwa ta sami guri ta zauna ,bayan sun dan jima a zaune dayan su
Baice kala ba, sai yimana ya katse shirun da yake tsakaninsu da fadin cewa
Yake walisa ya akayi na ganki a wannan lokaci ke kadai
Ba tareda dan uwanki yarima walisu ba?
Ki sani nayi matukar kewarku, kuma bazan taba mantawa
Da irin taimakon da kikayi mini ba ke dashi, alokacindana taba shigowa
Yankin birninku domin yin kasuwanci ba,
Har wasu mugayen ýan fashi suka zo suka tare mini hanya zasuyi mana kwacen hajar da mukazo da ita
Ku biyu ne kadai kukazo kuka tarwatsa su da karfin tsiya suka gudu
ki sani cewa inba don wannan taimakon da kukayi mini ba
Da tuni na dade

Please Login or Register in order to submit comment