Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan ranar
Da gama wannan zancen zuci sai kawai tayi murmushi sannan taci gaba da tafiya
HAKIKA RASHIN SANI YAFI DARE DUHU INDA ACE TASAN ABINDA ZAI FARU
DATA HAKURA DA WANNAN RANGADI GABA DAYA TA KOMA GIDA
Aikuwa tana cikin yin tafiyar tatane tare da dakarunta
Ba zato ba tsammani sai taga gari yayi duhu yadda ko tafin hannunka bazaka iya gani ba
Daga can kuma sai kasa ta fara girgiza tana haifar da wawakeken rami
Koda ganin wannan al'amari sai nantake dakaru sukazo sukayiwa gimbiya bahjaht kawanya domin bata tsaro
Daga can kuma sai sukaji an bushe da dariya mai kama da kukan jaki wadda tayi sanadiyar tayar da kura abirnin gaba ki dayansa
Sannu ahankali komai ya lafa gari yayi haske kwatsam sai suka ga wani katon basamuden dodo ya bayyana
Ko'ina ajikinsa a murde yake kamar curin duwatsu, idanuwa
kuwa basa iya ganin karshen tsawonsa Domin ya tokare ko'ina saidai ka gani iya kallonka
Hannunwansa kuwa guda saba'in ne, kowanne daga cikinsu yana dauke da dogayen yatsu masu dauke da kaifi da tsini,
Koda bayyanar wannan dodo sai nantake sarkin yaki ukairu ya nunashi da yatsa da nufin ya jefishi da kibiyoyin tsafi
Take kuws kibiyoyin sukayi fitar burgu daga jikin yatsunsa sukayi kan wannan dodon
Koda saukar kibiyoyin ajikinsa sai take suka kakkarye suka zube kasa
Kafin suyi wani yunkuri tuni dodon ya zuro hannunsa guda daya ya shuri gabaki daya dakarun harda dawakansu
Ya dagasu sama ya watsasu cikin wakeken bakinsa mai girman gaske gaba dayansu ya taunesu,
Kodasu gimbiya bahjaht da kuyanginta da mutanen gari sukaga abindaya faru ga wadannan dakaru
Sai dukkansu suka figice
Suka fara gudun ceton ransu, da ganin haka sai wannan dodon ya bushe da dariyar mugunta
Take kashushuwan mutane dana dawakan nan suka dinga zubowa ta cikin hakoransa,
Da ganin haka sai kowa ya kara firgita suna ihun neman taimako domin sunyi imani da cewa basu isa su tsira daga sharrin wannan azzalumin dodo ba
0=======(:::::::::::::::::::::::::::::::::::::>
Acan cikin kasuwa kuwa sadauki hasanul basari tafiyar sa kawai yakeyi
Ba tareda sanin dalilin dayasa mutane suketa faman rububin kallonsa ba
Har ya isa bakin wata katuwar rumfa wacce ajikinta aka kafe allon sanarwar cewa suna sayen fatun dabbobin daji
Da kyar da makyarkyata mai rumfar ta roki mutane kan suyi hakuri
Idan hasanul basari ya fito sai su hadu dashi acan wajen
Sannan ya zo sukayi cinikin fatun dabbobin ya dauko dinare masu yawa ya bashi
Suka rabu sadauki hasanul basari ya fito daga rumfar ya kama hanyar komawa can kauyensu kenan
Kawai sai yaga bakin hadari ya hado da kuma girgizar kasa acikin garin
Koda aka dan jima sai yajiwo ihun mutane daga can nesa da inda yake
Dajin wannan ihun sai nan take ya falfala da zababben gudunsa
Mai kama dana tauraruwa mai wutsiya ya nufi gurin da yake jiwo wannan ihun

Adaidai wannan lokacin ne dodon ya zuro hannunsa kasa da nufin ya shuri gimbiya bahjaht ya watsata abakinsa ya tauneta kenan
Kwatsam sai ga sadauki hasanul basari ya baiyana agurin
Yana zura sai yayi sulu ya tafi akwance yabi ta karkashin kafafun dodon
Kafin hannunsa ya sauka kan gimbiya bahjaht tuni hasanul basari ya shureta kamar jaririya
Yayi can gefe da ita,
Itakuwa awannan lokacin ta kame domin ta saddakar da cewa ta mutu
Ba tareda bata lokaci ba ya juyo ya fukanci wannan dodon gaba da gaba
Koda dodon yayi arba da shi agabansa sai kawai ya sunkuyo da kansa kasa yace dashi cikin wata kakkausar murya
Kai yaro hakika kayi matukar kuskuren kawo kanka zuwa ga halaka tun kafin lokacin ka ya cika
Ka sani tunda nakeyin bauta ga uban gidana mai girman daraja sahibul ukub
Ba'a taba samun mahalukin daya tsira daga hannuna ba….
Kafin ya gama fadin abinda yakeson fada fada sai hassanul basari ya saka masa tsawa yace
Kai karya kakeyi ni nayi maka alkawarin daga kai har uban gidanka
Saina rabaku da wannan duniyar gaba dayanta. Yana gama fadin haka ya zare takobinsa ya falfala da azababben gudu
Zuwa kan dodon koda yazo daidai inda yake sai nantake ya daka
Tsalle ya dirga akan cinyar dodon tareda kai masa wani mummunan sara
Koda takobin ta sauka ajikinsa sai yaji kamar ya sari dutse
Kafin shima yayi wani yunkuri tuni dodon ya cilloshi daga kan cinyar tasa sannan yasa kafa da nufin takeshi
Cikin bakin zafin nama ya daka tsalle ya kaucewa harin dodon
Koda kafar dodon ta sauka akan kasa sai gashi ta haddasa wani wawakeken rami
Zurfin gaba dubu don saida kusan kaurinsa ya nutse acikin ramin
Take suka hargitsa wannan filin domin wani irin azababben bakin gumurzu suka dinga yi
Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda sadauki hasanul basari yake iya kaucewa munanan hare haren dodon ba tareda ya sami nasararvkoda taba fatar jikinsa
Su kuwa su gimbiya bahjaht da sauran kuyanginta kamewa sukayi kyam kamar gumaka suna kallon wannan bakin gumurzun
Musamman ma ita gimbiya bahjaht don ita ba yakin take kalloba
Tsananin kyawun sadauki hasanul basari take kallo domin awannan lokaci sai taji ta raina nata kyawun, har ta tambayi kanta tace to wai shin inda ace shi mace ne to wanne irin kyawu zaiyi?
Tabbas inda ace mace ne shi saidai akirashi da sarauniyar kyawawan duniya, kodayin wannan tunani sai nantake taji ta kamu da tsananin soyayyarsa
Har tana fada acikin zuciyarta cewa, tabbas kota halin kaka sai na mallaki wannan jarumi amatsayin abokin rayuwa ta
Kawai sai kuma wata zuciyar tace da ita
Kul ! Kada ki kuskura kice zakiyi haka domin zaki zubar da darajar ki ne a'idon duniya wata kilama yaki amincewa dake
Haka dai ta dinga tunani kala kala,
Can kuwa al'amarinsu sadauki hasanul basari koda yaga sun dauki lokaci mai dan tsawo suna fafata yaki da wannan dodo
Kuma yana ta bata masa lokaci, sai kawai ransa ya baci
Ya kara harzuka fiyeda ko yaushe, ya canja salon fada
Ya dinga hadawa da tsalle tsalle yana hawa jikin dodon kamar kadangare
Shi kuwa dodon saiya dinga kawo masa duka da hannayensa
Amma kafin hannayen su sauka ajikinsa tuni ya daka tsalle yabar gurin ya kara hawa sama
Saidai kaga idan hannuwan suka sauka aduk gurin da sadauki hasanul basari ya bari da zarar hannun dodon ya sauka agurin sai kaga wajen ya dare jini yayi tsartuwa
Wannan itace damar daya dinga samu, don kafin ajima da fara haka har jikin dodon yayi jina jina da jini, kuma kuzarinsa na dada raguwar saboda jinin da yake zuba ajikinsa,
Ana cikin wannan hali ne kawai sai hassanul basari ya daka wani mahaukacin tsalle kamar daga jikin baka aka harbashi
Sai gashi ya sauka akan kafadun dodon sannan ya kara daka wani tsallen akaro na biyu ya dira akan wuyansa
Kawai sai yasa hannuwansa guda biyu ya kama kan dodon da dukkan karfinsa ya murde masa wuya
Take kuwa dodon yayi wani irin mahaukacin ruri na fitar rai
sannan kuma sai nantake ya tarwatse ya bace bat aka daina ganinsa sai ganin sadauki hasanul basari kawai saujayi akan iska yana saukowa kasa
Kamar tsuntsu mai fuka fukai,
Kodaya gama saukowa kasa bisa turba sai kawai suka hada idanu da gimbiya bahjaht
Take anan kowa yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske kamar zata faso kirjinsu ta fito waje

SHIN MENENE TSAKANIN GIMBIYA BAHJAHT DA KUMA SADAUKI HASANUL BASARI?
SHIN HASSANUL BASARI ZAI KARBI SOYAYYAR GIMBIYA BAHJAHT?
WANENE YA TURO WANNAN DODO ZUWA BIRNIN FASAWANA KUMA ME YAZO YI?
DON SANIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI MU HADU A KASHI NA GABA
DON JIN KARASHEN WANNAN KAYATACCEN LABARI
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMEN+++++++++ZUBAR DA JINI
++++++++++3 PART C
LBR
+++++++++++++++habibullah KBR
Nanfa suka kurawa junansu idanu kamar gumaka ko kifta idanunsu basa iya yi
Sai daga baya hassanul basari yayi sauri ya kawar da fuskarsa ga barin kallonta
Adaidai wannan lokacin ne mahaifinta sarki mayasin ya karaso gurin bayansa tare da dakaru kimanin dubu biyu a bayansa
Dukkansu sunyi shigar yaki mai bantsoro
Kai kayi zaton duniyar zasu yaka
Sun fito domin suga abin da yake faruwa,
Tun daga nesa ya dinga hango irin kallon da gimbiya bahjhat da hassanun basari suke yiwa junansu,
Harma ya lura da jarumi hassanul basari ya kawar da fuskarsa ga barin kallonta amma ita har yanzu hankalinta yana kansa
Don haka koda ya iso inda suke kawai saiya shiga tsakaninsu da dokinsa sannan yaja linzamin dokinsa ya tsaya
Koda jarumi hassanul yayi arba da sarki agabansa sai kawai ya rissina agabansa domin girmamawa
Ita kuwa har sannan bata lura da abinda yake faruwa saboda gaba daya ruhinta ya fita daga jikinta
Har saida sarki mayasin ya dora hannunsa akan fuskarsa
Sannan ta farfado daga duniyar data shiga don haka
Koda tayi arba da mahaifinta agabanta sai taji kunya ta kama ta don haka sai kawai tayi murmushi
Sannan ta kalli hasanun basari tace ina yakai wannan jarumi ina matukar godiya agareka bisa wannan taimako da kayi mana
Don ba don kaiba da tuni mun dade da zama shekakku
Dajin wannan batu sai hassanul basari ya mayar mata da martanin murmushi
Shikuwa sarki mayasin sai ya hade fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa
Kawai sai ya yiwa hassanul basari godiya bisa taimakon da yayiwa ýarsa
Sannan itama ya umarceta data kama hanya ta tafi gida
Take kuwa aka kawo mata ingarman doki ta hau suka jera da mahaifinta
Har sun danyi nisa sai kawai taja linzamin dokinta ta juyo suka hada idanu da hassanul basari
Take sukayiwa junansu wani irin tattausan murmushi
Kuma duk wannan abu daya faru sarki mayasin ya gani
Don haka sai yaji kamar ya kwallara ihu saboda bakin ciki
Ahaka dai har suka isa cikin gidan sarauta kowa ya koma cikin bagarensa
Adaidai wannan lokacin ne wata kuyanga ta kawo mata kwanukan abinci da kuma na abubuwan sha
Ta ajiye mata su ta kama hanya ta fice
Ba tareda bata lokaci ba ta taso ta zauna akan kujerar da take fuskantar teburin ta mika hannunta cikin kwanon abincin
Kwatsam sai taga fuskar hassanul basari aciki yana yi mata murmushi
Nantake ta mike tsaye zumbur cikin razani ta dan ja baya
Sai asannan ne ta gane cewa bashi baneba gizo kawai yakeyi mata
Amma duk da haka sai ta kasa cin abincin domin duk sanda ta kai hannun shi take gani
Nantake tace acikin zuciyarta wai shin menene yake shirin faruwa dani ne
Domin ban taba shiga cikin irin wannan yanayi ba
ABINDA BATA SANI BA SHINE SOYAYYA CE TA SHIGA CIKIN ZUCIYARTA
Ahaka dai ta samu tayi barci amma duk da haka acikin mafarkin nata babu abinda take gani face shi
Har gari ya waye
++++++++++++++++++++++++++++
Shi kuwa sadauki hasanul basari tunda suka rabu da gimbiya bahjaht
Sai yaji gaba daya yanayin sa ya sauya domin in banda tunanin ta babu abinda yakeyi
Ahakane yana cikin tafiya acikin daji kawai sai ya iso bakin wata korama wacce ruwa yake gudana acikinta
Take ya karasa bakin koramar ya sunkuya da nufin ya sha ruwan cikinta
Kwatsam sai ya hango surar jikin gimbiya bahjaht aciki tana sanye da wasu korayen tufafi tana yi masa wani irin tattausan murmushi
Koda ganin wannan al'amari sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske
Yace tabbas a wannan lokaci bazan yaudari kaina ba domin ko shakka banayi soyayyar gimbiya bahjaht ta shiga zuciyata
Kuma dolene nayi kokarin cire soyayyarta daga cikin zuciyata tunda aurena da ita bazai taba yiwuwa ba tunda ita bata kasance musulma ba
Haka dai yayi ta sake sake acikin zuciyarsa har ya isa can sansaninsu
Da zuwansa sai ya iske ýan kabilarsu sun fito sun tsaya suna jiran dawowarsa
gaba daya sun kagu da dawowarsa saboda sunsan dole akwai wani abin daya hanashi dawowa akan lokaci
Koda sukaga dawowarsa sai duk suka kamu da farinciki suka taho suka tarbeshi
Take ya kwashe labarin komai ya shaida musu abindaya faru
Bayannan ya dauko kudadan su gaba daya ya raba musu
Awannan rana dai duk kokarin da jarumi hassanul basari yayi d0n ya cire tunanin gimbiya bahjhat daga zuciyarsa saida yayi amma ya kasa
Domin duk sanda ya rufe idanunsa babu abinda yake gani face fuskar gimbiya bahjhat
Wannan al'amari ba karamin firgitashi yayi ba. Ahaka ya kwana har gari ya waye
Koda gari ya waye yayinda jarumi hassanul basari ya fito daga cikin dakin da yake kwana
Kawai sai sukayi kichibus da wani kanin mahaifinsa mai suna hubairu
Koda suka hadu dashi sai ya kalli idanun jarumi hassanul basari yaga alamun baiyi barci ba awannan daren
Koda ganin haka sai ya kirashi gurinda yake ya tambayeshi kan ya fada masa gaskiyar abindaya faru acikin birnin
Take kuwa ya kwashe labarin komai ya fada masa kodajin wannan labari
Sai fuskar hubairu ta cika da murmushi sannan yace dashi
Yakai dana kada ka damu da wannan al'amari shawarar da zan baka itace duk sanda kuka hadu da gimbiya bahjhat to ka baiyana mata sirrin da yake cikin zuciyarka
Ni kuma nayi imani da cewa ba zata ki amsa maka ba domin kai na daban ne
Bayan haka kuma wata kila ta sanadiyar haka ta karbi musulunci
Kaga idan haka ta faru kamar ka jefi tsuntsu biyu da dutse daya ne
Don haka ka shirya haduwa da ita ako wanne lokaci kar kaji kunyar fada mata sirrin da yake zuciyarka
Da gama fadin haka saiya wuce yabar hassanul basari atsaye kyam domin jin maganar yake kamar tatsuniya
Acan gidan sarautar sarki mayasan kuwa bayan daya shige cikin turakarsa
Sai ya kasa zaune ko tsaye sakamakon fargabar data cika zuciyarsa
Domin babu shakka abinda yake gudu shine yake neman faruwa
Domin ya kula da irin kallon da bahjaht da hassanul basari suka dinga yiwa junansu
Lallai kallone mai cike da alamun soyayya kuma tabbas
Idan har baiyi da gaske ba to yana daf da rasa ýarsa jar abada
Domin idan yayi sake soyayyarsa ta shiga zuciyar ta to shi kansa bai isa ya iya sarrafata ba
Saboda aurenta da hassanul basari bazai taba yiwuwa ba face ta karbi addininsa na musulunci
Shi kuwa bazai taba bari hakan ta faru ba domin zai zama abin yi masa gori acikin ýan uwansa sarakai
Kuma da hakan ta faru gwanda ya rasa ýar tasa gaba daya
Koda yaga zuciyarsa bata sami nutsuwa ba
Sai kawai ya tashi da kafafunsa ya nufi can bangaren da take
Koda zuwansa sai kawai ya danna kansa cikin dakin kai tsaye ba tare da neman izini ba
Da da shigarsa cikin dakin sai kawai yayi arba da ita a zaune agaban kwanukan abincin da aka kawo mata
Ta zauna tayi tagumi kawai tana kallon abincin ba tareda tayi koda loma daya ba
Tana kallon abincin kawai tana murmushi kamar tana tattaunawa da wani,
Koda ganin wannan al'amari sai kawai ya girgiza kansa kuma yaki yayi mata magana
Sannan ya juya ya fice daga cikin turakar tata ya kama hanyar komawa tasa turakar
Ita kuwa gimbiya bahjhat gari na wayewa saita tashi
Ta kira wani amintaccen badakarenta mai suna uzumnal
Shidai uzumnal yakasance amintaccen ta ne kuma abokintane domin tare suka taso
Kuma sun shaku dashi sosai don haka babu wanda ta yarda dashi aduk cikin hadimanta kamar sa
Saboda haka ne ma duk wasu aiyukan sirri take nemansa idan tanaso tayi su daidai
Da zuwansa sai ya tsugunna har kasa ya gaisheta sannan yace
Ya shugaba ta me kike da bukatar nayi miki yanzu take na aiwatar
Dajin wannan batu sai tayi murmushi sannan tace dashi
Inaso ne kayi mini rakiya zuwa can sansanin kabilar banu sudes
Domin na gano saurayin daya ceci rayuwata kuma nayi masa godiya
Dajin haka sai ya dago kansa arazane yace ya shugabata
Wannan aiki da kike shirin yi ganganci ne babba arayuwarki ina mai rokonki da ki hakura da zuwa wannan guri
Domin idan har mahaifinki ya gano cewa kinje wannan guri to babu shakka kasheni zaiyi
Ina rokonki da darajar iyayenki daki hakura da wannan tafiya
Kodajin wannan batu sai take ta daka masa tsawa akaron farko na rayuwarta sannan tace
Shin kasan irin halinda ni zan shiga idan har na rasa hassanul basari?
Dolene kayi mini wannan aiki, kuma ina mai tabbatar maka da cewa koda asirinmu ya tonu to bazan bari mahaifina ya cutar dakai ba
Saidai duk irin hukuncin da zaiyi maka ni yayi mini shi, saboda haka saika shirya ka jira fatowata awajen gidan sarauta
Dajin haka sai nantake ya tashi ya fice daga cikin turakar tata
Sannan ita kuma ta tashi ta kewaye tayi wanka ta fito sannan ta caba ado na gani na fada
Tana gamawa saita fito ta nufi hanyar fita daga gidan sarautar
Duk inda ta gifta sai dai kaga dakaru suna gaisheta sannan kuma kaga sun kura mata idanu suna mamakin fitarta a daidai wannan lokaci don basu taba ganin ta fita a wannan lokaci ba
Har gimbiya bahjhat ta fice sai kawai tayi wani dan tunani saita juyo
Ta dawo wajen shugaban masu gadin tace dashi
Kada wanda ya kuskura ya sanar da mahaifina wannan fitar tawa
Duk wanda kuwa ya kuskura ya sanar dashi wannan sirri sai na sa an kasheshi
Tana gama fadin haka sai ta fice daga cikin gidan ta nufi bayan gari inda zata hadu da hadiminta uzumnal………… .
Adaidai wannan lokaci ne wani hadimi ya shigo cikin turakar sarkin kasuwa yimana
Ya rissina yace ya shugabana lokacin gudanar da wannan gagarumar gasa yayi
Dajin wannan batu sai sarkin kasuwa yayi murmushi sannan ya dubi
Walisa yace
To kinji lokaci yayi kamar yadda na fada miki cewa da zarar lokaci yayi zamu katse wannan labari mu tafi kallon wannan gasar jarumta
Sai bayan mun dawo zamu cigaba da wannan labari
Dajin haka sai walisa tayi murmushi sannan tace kada ka damu ni zan jira daga nan har a kammala wannan gasa
Yana gama fadin haka saiya tashi ya shiga bangarensa yayi shiri
Ya fito sannan su walisa suka tashi suka biyoshi abaya
Amma saida walisa ta dauko bakin kyalle ta sake rufe fuskar ta dashi saboda tabbatar da tsaro
Da fitowarsu daga cikin gidan sai sukaga awannan ranar birnin ya cika ya batse fiye da ko yaushe
Da jaruman gasa da kuma baki maza da mata daga sassa daban daban
Ahaka dai suka dinga ratsawa ta cikin mutane har suka isa filin
Da kyar suka samu aka budawa walisa hanya ta shiga cikin filin ta zauna
Shikuwa sarkin kasuwa yimana saiya wuce izuwa cikin
Wata katuwar rumfa wacce take can karshen filin gasar
Akasanta an jera kujeru na alfarma wadanda manyan mutane zasu zauna acikinsu
Acikin jerun kujerun kuwa an ware wata guda daya wacce tafi kowacce girma da kawatuwa
Kuma ita kadaice babu kowa akanta sai kuma wacce sarkin kasuwa ya zauna akanta amma ragowar duk an zauna akansu
Akasan filin gasar kuwa mutanene birjik suketa tururuwar shigowa domin kallon wannan gasa
Wasu kuma da suka zo da wuri sun sami kujeru sun zazzauna
Wadanda kuwa suka makara sai kan katangu suka dinga hawa don kallon gasar
Domin sunsan cewa dolene kowa ya morewa idonsa kallo
Ana cikin hakane sai aka fara jiyo sautin bugun ganguna da busar sarewa suna tashi daga can hanyar tahowa daga gidan sarauta
Nanfa kallo ya koma can hanyar da wannan sauti yake tahowa
Daga can kuma sai ga dakaru masu dumbun yawa suna tahowa daga ta wannan hanyar
Rike da makaman yaki masu matukar ban tsoro, suka firfito suka kewaye gaba daya hanyar da sarki aryan zai wuce
Awannan lokaci gaba daya jaruman gasa sun gama hallara afilin jira kawai suke sarki ya fito afara wannan gasa
Duk wanda ka kalla acikinsu kasan dolene ya kasance jarumin gaske
Bayan lokaci kadan sai ga sarki aryan ya taho cikin shigar kayan sarauta masu kyawun gaske, da tsada
Kalar kayan da yasa kuwa sun kasance shudin launi mai haske
Kuma kayan sun matse jikinsa ta yadda suka nuna tsantsar kyawun surar jikinsa da kuma murdewar jikinsa
Ya sanya wata hula akansa wacce aka kerata da zallan zinare
Kuma anyi mata alamar hannun mutum rike da takobi a samanta
A jikin kugunsa kuwa ya daura wata takobi wacce aka kera kubenta da zallan dutsen lu'u lu'u
Tun daga nesa haskenta ya dinga dallarewa mutane ido
Koda mutane sukayi arba dashi cikin wannan kyakykyawar shiga sai suka rude da ihu suna koda shi tareda yi masa kirari
Har sai da yaje kan kujerarsa ya zauna sannan akayi tsit ana jiran jawabinsa
Bayan kowa ya gama bada hankalinsa sai kawai ya mike ya fara bayani kamar haka
Yaku mutanen wannan birni namu mai tarin albarka da kuma wadanda sukazo daga wasu kasashen
Domin shiga ko kallon wannan gagarumar gasar jarumtaka inayi muku barka da zuwa wannan birni namu
Sannan bayan haka kowa ya sani nima ina daga cikin jaruman wannan gasa
Don haka banida ikon gabatar da jawabi a wannan lokaci sai munji abinda alkalan gasa suka yanke game da wannan gasa
Saboda haka yanzu sai mu saurari bayani daga bakinsu
Yana gama fadin haka sai ya sami guri ya zauna akan karagarsa
Sannan alkalin gasa shima ya mike tsaye ya fara nasa jawabin da cewa
Ina yiwa jaruman gasa barka da zuwa wannan gasa mai albarka
Bayan haka kamar yadda kuka sani wannan gasa anayintane da zallan karfin damtse
Ba'a yadda wani yayi amfani da sihirin tsafi ba acikinta
Duk wanda aka kama kuwa za'a ci shi tara mai yawan gaske
Acikin wannan gasa ni kaina inajin akwai wani babban abin al'ajabin da zai faru
Domin naga yadda jaruman gasa suka cika wannan fili da kuma ýan kallo wadanda ba'a taba samun masu yawansu ba
Duk jarumin daya lashe wannan gasa sarki yayi masa alkawarin zai bashi dukiya mai tarin yawa sannan zai bashi kambun wannan gasar da hannunsa
Saboda haka ina mai shawartar jarumai dasu kara zage damtse domin ganin sun sami nasara akansa
Ita dai wannan gasa zamu kasata kaso uku ne ayau zamu gudanar da zagayen farko
Wadanda suka haye shi to sune zasu zo kuma su hadu a zagaye na biyu
Sannan duk wanda ya zama zakaran gwajin dafi acikin su
To shine wanda zai kara da mai girma sarki aryan a rana ta uku
SHIN YAYA WANNAN GASA ZATA KASANCE?
WANENE ZAI LASHE WANNAN GASA?
WANNE IRIN ABIN AL'AJABI NE ZAI FARU ACIKINTA ?
INA LABARIN JARUMI WALISU DAN UWAN JARUMA WALISA?
DON SAMUN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU.
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEM+++++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++++++++ 4 PART A

LBR

++++++++++++++HABIBULLAH KBR

Acikinsu ne zamu fitar da zakaran wannan gasa saboda haka yanzu muna da bukatar jaruman gasa gaba daya su hallara acikin fili
Bayan haka kuma a wannan karon ba'a yarda kowa yayi amfani da makaminsa ba
Amma zamu bashi irin makamin da ya iya amfani dashi
Yana gama fadin haka take yasa aka budewa jaruman gasa hanya suka shiga tsakiyar fili suka yi layi sahu sahu
Sannan wasu dakaru suka shigo da makaman yaki masu yawa kala daban daban suka ajiye
Bayan nan aka umarci kowa da yaje ya dauki kalar makamin da ya iya amfani dashi ba
Take kuwa koya yaje ya dauki kalar nasa na ainihin kuwa ya ajiyeshi agefe
Hikimar yin haka itace anaso kowa yayi amfani da zallan karfin damtsensa da iya yakinsa ne
Don ba'aso wani yayi wani sihirin ajikin makaminsa
Koda suka gama karbar makaman yaki sai take shugaban alkalan gasar ya fito ta daga katon bututu yace
A ka'idar wannan gasar da muka tsara awannan shekara
Ba'a yarda wani ya kashe wani ba acikin zagayen farko ba
Amma zaka iya yi masa dukan da zaiji jiki matukar dai bazai mutu.ba
Koda gama fadin haka sai ya juya ya kalli wani katon badakare wanda ke ruke da katuwar guduma ahannunsa ya tsaya agaban wata ganga
Take kuwa badakaren ya daga wannan gudumar ya buga ajikin gangar alamar a fara gasa
Nan da nan kuwa jaruman suka ja baya tareda zare makamansu
Dukda yawansu kuwa saida filin ya cinyesu domin babban filine kuma an tanaje shi ne kawai saboda wannan gasar
Sannan suka afkawa junansu da yaki cikin wani irin azababben salo
Wohoho nanfa mutane suka rude da ihu gami da shewa
Sakamakon ganin irin wannan bakin artabu da akeyi
Wanda ana iya kiransa da turnuku fadan iblisai babu abinda idanu suke gani face
Yadda mazaje suke bangazar kirazan juna duk wanda aka fishi karfi saidai kaga kafin aje ko'ina an zubar dashi kasa
Saidai dakaru su zo su daukeshi daga cikin filin don kada a hallakashi
Karafkiyar karafa tareda ihun mazaje suka cika dodon kunnuwa
Jini ya dinga fantsama ako'ina kananan jarumai kuwa suka fara nadamar kawo kansu wannan fili
Su kuwa ýan kallo in banda ihu babu abinda sukeyi
Kafin cikar dakiku masu yawa anzubar da sama da rabin jaruman
Hakika komai rashin imanin mutum saiya tausayawa kananun jaruman gasar
Su kuwa mutanen da suke gurin kawai ihu suke suna dada koda jaruman su
Acan bangaren sarki aryan kuwa kawai ya zauna ne yana murmushi
Sannan yana karewa jaruman gasar kallo yana nazarin salon fadan kowanne daga cikinsu
A sannan ne ya fahimci cewa lallai acikin wannan shekarar sai ya kara zage damtse acikin gasar domin tunda aka fara gudanar da

Please Login or Register in order to submit comment