Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abindaya faru tsakanin sadauki hassanul basari da wadannan aljanu har zuwa sanda ya kashesu gaba daya
Koda gama ganin wannan al'amari sai boka sahibul ukub
Ya takarkare ya kwarara uban ihu wanda yayi matukar razana su gimbiya bahjaht har saida sukaji kamar zuciyarsu zata faso kirjinsu ta fito waje
Dukkansu basu san sanda suka durkushe kasa ba suna masu yi masa sujjada
Koda ganin haka sai ya tsaya ya daina yin ihun sannan kuma ya bushe da dariya yace
Lallai yaro baisan wuta ba sai ya taka yanzu ya tsallake daji na farko saura daji na biyu
Ina mai tabbatar muku da cewa abune mawuyaci ya iya ketare wannan daji araye
*********** *************** ********
Lokacin da hassanul basari ya tunkari daji ma gaba sai yayita tafiya acikinsa
Harsaida yazo iyakar daji na farko sannan ya tsallaka ya shiga cikin daji na biyun yaci gaba da tafiya acikinsa
Koda ya shafe wasu sa'o'i yana tafiya kawai sai yayi arba da wasu rukunin aljanu karo na biyu wadanda suka fi rukunin farko girma ,karfi da kuma yawa adadinsu kuwa yafi na rukunin farko
Su dai wadannan aljanu suna da dogayen hannaye masu matukar tsawo da kuma kaurin gaske koma hannun kowanne daya daga cikin yana kaifi da kuma tsini sai kace takobi
Hakoransu kaca kaca ne masu matukar tsawo da kuma tsini wanda suke karya kashin bil'adama ko aljani wanda badan kabilarsu ba dashi

ME ZAI FARU ACIKIN WANNAN RUKUNI?
SHIN YANA SAMUN NASARAR FITA DAGA CIKINSA?
ADADIN RUKUNI NAWANE YA RAGE MASA YA ISA FADAR BOKA SAHIBUL UKUB?

DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENT****-*****ZUBAR DA JINI

*****************7 PART B

LBR

****************HABIBULLAH KBR

Lokacin da wadannan aljanu sukayi arba da sadauki hassanul basari
Sai kawai wani daga cikinsu ya miko hannunsa daga inda yake da nufin ya cafke shi
Bisa mamaki hassanul basari sai gani yayi wannan hannun yana dadawa kansa tsawo tamkar talashi ake
Inbadon yayi sauri ya sunkuya ba da sai wannan aljanin ya damkeshi ya mutsitstsike shi
Aikuwa sai hannun ya mike yaje ya damko wata katuwar bishiyar kuka
Take ya mutsitstsike ta da hannunsa yadda kai kace biskit ya rike da hannun nasa
Aikuwa sai shima hassanul basarin ya falfala da gudu zuwa inda suke suka kaure da yaki mai matukar firgitarwa
Kafin a jima da fara wannan yaki tuni dajin ya hargitse kura ta tashi sama kamar zata tokare da sararin samaniya
Da zarar hannun wadannan aljanu ya hadu da takobin hassanul basari
Saidai kaga tartsatsin wuta ya tashi tare da kara tamkar sautin haduwar karfe da karfe
Sautin ihu da karajin aljanun ya cika dajin gaba daya
Kasa ta fara girgiza kamar zata juye komai na kanta ya koma karkashinta
Hakika tashin hankali ba abinso bane dole ce take kawoshi
Duk wanda kaga kuwa yana fatan zuwansa to tabbas bai san hatsarin da yake cikinsa baneba
Domin shi farkonsa kawai aka sani ba'a san karshensa ba
Ai kuwa ana fara wannan fafatawar sai hassanul basari ya gane cewa wadannan aljanu ba daya suke da wadanda ya wuce abaya ba
Domin wadannan suna da matukar zafin 8nama sannan aduk sa'adda suka kawo masa hari ya kauce saidai yaga hannun nasu yana kara tsawo har yana zuwa kusa da inda yake
Sai dai yayi amfani da zafin namansa ya kaucewa harin nasu
Ana cikin wannan haline kawai wani zabgegen aljani wanda yafi kowanne daga cikinsu naci
Ya shammaci hassanul basari ya gabza masa dundu agadon bayansa
Saboda tsananin karfin dukan saida yaji kamar zaiyi aman hanjin cikinsa
Harsaidaya fadi akasa da rubda ciki amma sai ya sake mikewa tsaye zumbur tare da tofar da gudan jini daga cikin bakinsa
Ya kara gyara rukon takobinsa suka cigaba da fafata wannan gagarumin yaki
Inda ace kana nan sanda suke fafata wannan yaki sai kayi
Zaton cewa hassanul basari ba mutum bane wani hatsabibin aljanin ne shi ba bil'adama ba
Saboda yadda yake iya jure dukkan hare haren da suke kawo masa
Kuma her suka dauki lokaci mai tsawo ba'a sami wanda yayi nasarar zubar da jininsa ba
In ka dauke dukan da akayi masa a baya kai su kansu wadannan aljanu sun san cewa yau sun gamu da namiji mai dakakkiyar zuciya
Koda suka dauki lokaci mai tsawo suna wannan fafatawar
sai hassanul basari ya fuskanci muddin idan aka ci gaba da wannan fafatawar a haka to tabbas zai iya gajiya kuma idan har ya gaji komai zai iya faruwa dashi
Ai kuwa koda yin wannan tunanin sai take ya shammaci aljanun ya shuri kafar daya daga cikin su
Ai kuwa sai gashi ya daga shi ta dagashi sama ya maka shi da kasa
Cikin bakin zafin nama yasa ya tattara dukkan karfinsa ya kama hannun aljanin ya fuzgeshi da jikin gangar jikin
Take aljanin ya kwarara uban ihu alokaci da jini ya balle daga jikin dungulmin hannun kamar an bude magudanar ruwa
Kawai sai hassanul basari ya maida wannan hannu a matsayin makamin yakinsa
Bisa mamaki sai yaga awannan lokaci duk wanda ya daka ko ya soka da wannan hannu sai yaga ya fadi kasa matacce
Koda ganin haka aikuwa sai ya kara himma cikin aika wadannan aljanun barzahu babu kakkautawa kamar zaki ya shiga garken tumaki
Nantake sai ga dajin ya cika da ihun wadannan aljanu saboda yaune karo ba farko da wata hakitta ta taba kashe koda guda daya daga cikinsu
Amma sai gashi yau bil'adama guda daya ya gagaresu kashewa sai shayar dasu gubar mutuwa yake
Ai kuwa ba'adauki wani lokaci mai tsaho ba sai da hassanul basari ya gama kashesu gaba dayansu

Yana gamawa kuwa ya baje akasa yana hutawa sai asannane yaga cewa rana ta fadi
Don haka sai ya tashi ya dauko battar ruwansa yayi alwala
Sannan ya mike yayi sallar magriba bayan ya idar yayi addu'o'insa
Sai ya dauko abincin guzurinsa ya kwanceshi ya ci ya koshi
Sannan ya hangi wata bishiya guds daya acikin dajin don haka
Sai ya tashi ya karasa kasan wannan bishiyar ya zauna yaci gaba da hutawa abinsa
Harsaida yaga lokacin sallar isha'i tayi sannan ya mike yayi sallar
Bayan ya idar sai yayi addu'o'in neman tsari sannan ya kwanta barci abinsa
Ba tareda shakkar wani abu zai iya samunsa ba
Take kuwa sai barci mai nauyi ya daukeshi saboda irin gajiyar da take jikinsa
Duk wannan abu daya faru ga sadauki hassanul basari boka sahibul ukub dasu gimbiya bahjaht suna kallo acikin fadar boka sahibul
Alokacin ne sahibul ukub yaci kunu kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa
Ita kuwa gimbiya bahjaht saita kalleshi suna hada idanu sai tayi masa murmushin mugunta
Tace ai kaga abin dana fada maka tun farko cewa hassanul basari yafi karfin yadda ka daukeshi
Kuma ina tabbatar maka da cewa zai bayyana acikin fadar nan taka kuma babu abinda ka isa kayi masa a wannan lokaci….
Ai kuwa tun kafin ta gama fadin abinda takeson fada sai ji tayi sahibul ukub ya wanka mata mari wanda saida taji kamar kuncinta zai cire
Kawai sai yace da ita karki kara yadda wannan tunanin ya kara shiga cikin zuciyarki domin nine buwayar sadaukai
Wanda ya gagari miliyoyin sadaukai bare kuma ace sadauki dayane zai buwayeni to wannan karyane don haka sai ki jira kiga abinda zai faru
Yana gama fadin haka sai ya rintse idanunsa ya fara karanto wadansu dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya sai kawai kasa ta fara tsagewa kamar zasu rufta ciki
Nantake wata irin zabgegiyar bakar halitta ta bayyana
Ita dai wannan haliitar taja matukar kama da gwaggwan biri
Amma tana da dan karamin kaho atsakiyar goshinta
Faratanta zako zako ne masu matukar kaifi da tsini jikinta a murde yake cike da damatsa kai da ka ganta zaka san cewa dolene ta kasance kakkarfa idanunta jajaye ne kamar garwashin wuta
Koda bayyanar wannan halitta sai su gimbiya bahjaht suka ja da baya a firgice
Saboda tsananin razanar da sukayi sakamakon bayyanar wannan halitta
Take haliitar ta bude bakinta alokacin da yake tartsatsin wuta
Tace ya shugabana menene dalilin kirana da kayi awannan lokaci?
Bayan ka dauki alkawarin bazaka sake nemana ba sai lokacin daka gama mallake wannan duniyar?
Dajin wannan tambayar sai boka sahibul ukub yace dashi
Ai dole ce tasa nayi miki wannan kiran
Yake gidauniyar mutuwa ki sani cewa burin mu yana daf da cika mutum dayane ya zame mana cikas acikin wannan aiki
Duk irin shirin da nayi akansa naga yana iya tsallakeshi
Amma yanzu ke dinnan nake bukatar kije ki hallaka mini shi
Kodajin wannan batu sai wannan batu sai wannan halittar ta bushe da dariya tace wai wanene wannan hatsabibin da kake fada mini?
Take sahibul ukub yayi mata nuni da jikin. Bangon fadarsa
Ya nuna mata hassanul basari wanda yake kwance atsakiyar daji shi kadai
Koda ta kare masa kallo sai tace
Ya shugabana hakika nayi mamaki da naji ance wannan karamar halittar ce tasa ka kirawo ni ka rabani da mijina
Alokacin da muke jin dadin rayuwar auren mu ?
Dajin haka sai boka sahibul ukub yace da ita
Ai wannan ba irin mutanen da ake rainawa bane
Amma ba zaki yarda da zan cena ba
Sai kije ki gwada domin ance dan hakkin daka raina shike tsone maka ido
Dajin haka sai halittar tace an gama ya shugabana take
Kasa ta tsage sannan ita kuma ta shige cikin karkashinta

Kamar yadda haske yake ratsa gilashi, komai na cikin fadar ya koma daidai yadda yake da

Nantake gimbiya bahjaht taji tausayin hassanul basari ya kamata
Ganin cewa kawai duk saboda ganin ya ceci rayuwarta ne
Yasa shi ya sayar da rayuwar sa ya kawo kansa zuwa gurin da zai iya rasa rayuwarsa
Kuma gashi a gabanta aka tura wata shedaniyar halittar wacce zataje ta farmakeshi a daidai lokacin da yake shaka barcinsa bai san halinda ake ciki ba bare ya dauki matakin kare kansa

Al'amarin gidauniyar mutuwa mutuwa kuwa lokacin data fice daga cikin fadar boka sahibul ukub
Bata bayyana ako'inaba face cikin daji na biyu inda hassanul basari yake
Kwance ai kuwa tana bayyana sai ta nufi gurin bishiyar daya ke kwance gadan gadan da nufin tayi masa hadiya guda daya

Aikuwa koda ta isa bakin bishiyar ta kai hannunta da nufin ta daukeshi ta jefa abakinta
Sai taji jikinta ya kamayi mata zafi da radadi kamar gaba daya jikin nata zai tarwatse
Bisa dole ta janye hannunta daga jikinsa arazane taja da baya
Tana mamakin irin wannan abu domin tunda take bata taba jin irin wannan yanayin ba ajikinta

Don haka sai ta kara kallon hassanul basari sosai ta kare masa kallo
Tana nazarin hanyar da zatabi taga bayansa tunda taga bata da ikon taba fatar jikinsa
Koda ta tsananta tunani kawai sai dabara fa fado mata
Don haka sai ta rikide ta koma siffar iska sannan ta tashi sama
Jim kadan saiga wannan iskar ta dawo dauke da wani katon dutse
Wanda girmansa yakai girman wani tsuburin
Koda zuwan wannan iskar dauke da wannan katon dutsen
Sai take iskar ta saki dutsen don ya fado akansa yayi daga daga da namansa

Aikuwa koda wannan dutsen yayo kasa daidai wannan bishiyar
Sai take dutsen yayi bindiga ya tarwatse kamar gari yabi cikin iska
Koda ganin wannan abu daya faru sai wannan halittar ta kwallara ihu wanda sai daya amsa kuwwa zuwa dukka ragowar dajijjikan da suke kewaye da fadar boka sahibul ukub
Ba komai ne ya sakata wannan ihu ba face ganin ta kasa samun nasara akansa adaidai lokacin da yake barci
Dole saidai ta zauna ta jira zuwa lokacin da sai farka daga barcin
Take kuwa ta sami guri ta zauna a nesa kadan da inda yake ta tankwashe kafarta ta zauna zaman jiran farkawarsa
Bai farkaba sai da lokacin sallar asuba yayi har asannan bai kula da wannan halittar ba
Don haka kawai sai ya mike zaune ya dauko battar ruwansa
Yayi alwala sannan ya fuskanci alkibla yayi sallar asuba
Sannan ya zauna zaman yin wuridi har zuwa lokacin da hasken rana ya fito
Har a sannan ita wannan halittar kawai tana zaune agefe daya tana kallonsa

Koda hasken rana ya gama fitowa shima ya kammala wuridinsa
Ai kuwa yana juyowa bayansa sai sukayi ido biyu da wannan halittar fuskarta amurtuke
Saboda matukar fusatar da tayi don ganin yadda ya bata mata lokaci acikin ibadar tasa
kafin yayi wani yunkuri tuni halittar ta shureshi ta damfarashj da kasa
KUYI HAKURI DA WANNAN DON ALLAH
KUMA INA BAKU HAKURI AKAN JINKIRIN DA AKA SAMU
SABANIN YADDA AKA TSARA KWANAKIN YINSa
NA SAMI WASU ÝAN MATSALOLI NE

SHIN HASSANUL BASARI YANA SAMUN DAMAR KUBUTA DAGA HANNUN WANNAN HALITTAR?
KO KUWA ITA HALITTAR TANA SAMUN NASARAR KASHESHI?
DON WANNAN AMSAR SAI MU HADU AKASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS
****************ZUBAR DA JINI

**************7 PART C

LBR

***************HABIBULLAH KBR

Lokacin da wannan halittar tayi jifa da hassanul basari da hassanul basari
sai ya fado kasa saboda karfin buguwar da yayi sai da yaji kamar kashushuwan bayansa sun kakkarye
Kafin ya sake yin wani yunkurin tuni ta sake dako tsalle daga inda take ta sake bayyana a inda yake
Ta shureshi sama tayi jifa dashi can gefe
Sannan ta sake bayyana a gurinda zai fado ta hangame katon bakinta tana jiran ya fado aciki
Koda yaga abinda yake shirin faruwa sai take ya juya jikinsa tun a saman bai yarda ya fado cikin bakinta ba
Ya daka wani tsallen yayi alkafira a saman ya dira acan gefe daya da inda take
Ya dira akan hannayensa da kafafuwasan ya fuskanceta suna kallon juna atsakaninsu
Daga can sai ya daka tsalle daga inda yake ya bayyana adaidai saitin fuskarta ya daga takobinsa sama ya kafta mata sara
Aikuwa koda takobin ta sauka ajikinta sai wata irin kara ta tashi ji kake kal !
Kamar karar haduwar karfe da karfe take suka ruguntsume da azababben yaki atsakaninsu
Ya zamana kowa yana kaiwa abokin fadansa mugayen hare hare
Tamkar jikinsu bana jini da tsoka bane
Tabbas inba don hassanul basari ya kasance jarumin gaske mai matukar juriya ba da tuni wannan halittar ta sami nasara akansa
Domin duk sanda ta kawo kasa duka idan ya kauce ta sami kasa
Saidai kaga ta ta haddasa rami agurin data sara ko ta karta da kaifin da yake jikin hannunta
Hakika komai adawar mutum dolene ya sallamawa hassanul basari
Domin yana fadan ne cikin matukar zafin nama, juriya da bajinta
Kuma har. A sannan bai sake bari ta sami nasarar koda taba jikinsa ba
Haka shima idan ya taba jikinta makaminsa baya tasiri
Ahaka har suka shafe sa'o'I masu yawa suna wannan bakin artabu
Asannan ne yayi tunanin tabbas idan aka cigaba da wannan fafatawar a haka zai iya gajiya har ta sami nasara akansa
Saboda haka dolene acikin wannan lokaci ya san yadda yayi ya gudu zuwa cikin rukunin daji na gaba koda kuwa zata biyoshi abaya
In yaso ko menene zai faru sai ya faru a can din
Koda gama wannan tunani sai nantake shima ya shammaceta ya daka tsalle sama ya jera mata kyawawan duka akirjinta
Ai kuwa saboda karfin dukan saida halittar tayi sama sannan ta fado kasa
Kafin tayi wani yunkuri tuni hassanul basari ya falfala da azababben gudun gaske ya nufi hanyar da zata kaishi cikin dajin rukuni na gaba
Ai kuwa koda ganin haka sai itama ta mike tsaye zumbur ta biyoshi da gudun gaske domin ta kamashi kafin ya isa cikin dajin

Wohoho!!! Hakika jarumtaka baiwace domin sai yanzu halittar ta tabbatar da cewa tabbas hassanul basari hatsabibin mutum ne sabanin yadda take tunani abaya
Ba komai ne ya bata mamaki ba face ganin yadda yake tsala azababben gudu kamar zai tashi sama
Duk da irin gudunta sai taga ta kasa riskarsa
Idan yazo giftawa ta cikin daji mai sarkakiyar bishiyoyi saidai taga yana daka tsalle yana hayewa ta saman kansu idan kuwa tsauni ne a gabansa saidai kaga ya kama tsaunin yana gudu akansa kamar kadangare
Hakama idan ruwane zai ci gaba da gudunsa kamar akan kasa yake
Wannan al'amari ba karamin bata mata rai yayi ba domin babu abinda takeso face taga ta kama hassanul basari kafin ya isa daji na gaba
Domin ta samu ta cinyeshi ita kadai
Dalilin dayasa kuwa bata so ya shiga cikin daji na gaba shine
Tsakaninta da shugaban wannan daji basa ga maciji atsakaninsu
Domin kuwa duk sanda suka hadu babu abinda sukeyi face kare jini biri jini
Idan har ta bari ya shiga cikin wannan to dolene ta hakura su raba namansa tareda shugaban wannan daji
Tunda ai ya shigo cikin nahiyarsa
Ai kuwa yana cikin tsala wannan gudun ne ya shiga cikin rukunin daji na gaba
Ahakan yanata faman sharara gudu ita kuma tana biye dashi abaya
Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaci karo da wani katon dutse agabansa
Take kansa ya gwaru da jikin dutsen ya fadi kasa sumamme
Ai kuwa adaidai wannan lokacin ne wannan halittar tazo kansa ta tsaya tanata faman shara haki
Da murnar ganin kamar ta sami dami a akala domin gashi ta shigo yankin da ba huruminta aciki tayi farauta
Nantake ta mika hannunta da nufin ta daukeshi ta jefa abakinta ta cinye
Kafin mai hakkin kula da wannan dajin ya karaso
Ai kuwa kafin hannunta ya sauka ajikinsa sai ji tayi anyi caraf an ruke hannun nata
Take ta dago da kanta don taga wanda ya ruke hannun nata
Koda tayi arba dashi saita cika da tsananin mamaki kuma jikinta yayi sanyi
Ba kowa ga gani ba face shugaban wannan daji mai suna marugas fuskar sa a murtuke
Kamar wanda aka aiki masa da sakon mutuwa
Kawai sai ya dubeta yace
Yake kiyasul ausar menene dalilin shigowarki cikin dajin nan bayan mai girma sahibul ukub ya shiga tsakanina dake?
Dajin wannan tambaya sai kiyasul ausar ta janye hannunta daga cikin nasa
Tace yakai marugas yau ba nazo domin farauta acikin yankinka bane
Nazo ne domin cika umarnin mai girma sahibul ukub
Shi da kansa ne ya umarceni da in zo in kasheshi domin yanzu haka shine babban makiyinsa adoron kasa
Don haka ina mai umartarka daka gaggauta kyaleni na gudanar da aikin da aka umarceni akansa
Wannan shine dalilin shigowata cikin yankinka
Aikuwa dajin wannan batu sai dodo marugas ya bushe da dariya sannan yace
Ke tunda kike kin taba ganin halittar data taba shigowa cikin dajin nan ta fita araye in banda ke?
To ki sani cewa ke din ma darajar mai girma sahibul ukub ce tasa kika fita araye
Don haka yanzu zamu sasanta tsakanin mu a raba shi kowa ya dauki nasa kason
Koda jin haka sai kiyasul ausar ta amince da bukatar sa
Don haka sai ta kai hannu ta kai masa sara da nufin ta rabashi gida biyu
Kafin hannunta ya sauka ajikinsa tuni dodo marugas ya yasa hannu ya janyeshi daga gurin
Cikin rashin yarda kiyasul ausar ta dubeshi tace yakai marugas
Menene yasa ba zaka barni in rabashi ba tun yanzu ko ka manta da yarjejeniyar dake tsakanin mu?
Dajin haka sai yayi murmushi da mummunar fuskarsa sannan yace
Ai wannan bai kamata mu rabashi anan gurin ba zaifi kyau mu karasa cikin gari
Domin mu hada walima wacce zamuyi domin murnar kamashi
Kuma acikin walimar ne zamu rabashi muyi kalaci dashi mu biyu kacal
Kodajin haka sai ta girgiza kanta sannan tace
Lallai na fuskanci bakasan hatsarin da wannan bil'adama na hannunka yake dashi
Ina mai tabbatar maka da cewa yanzu ne muke da damar da zamu kasa shi biyu
Tunda yana cikin halin suma, idan har mukayi ganganci har ya farfado to akwai gagarumar matsala
Dodo marugas yayi gurnani sakamakon jin abindata fada
Yace
Lallai na fuskanci kin firgita da wannan bil'adama kuma kinyi matukar bani mamaki akan haka
Ina so ki sani koda ya farfado ni kadai ma na isheshi babu yadda zai iya dani
Ke bama ni ba hatta jama'a ta idan na barshi dasu babu abinda zai iya yi kansu
Yana gama fadin haka sai ya kama hanya ya shige cikin dajin dauke da hassanul basari a hannunsa
Ita kuma kiyasul ausar sai ta bishi abaya jikinta asanyaye
Ahankali suka isa can cikin tsakiyar dajin inda ya kasance gari ne babba
Ga jinsin dodo marugas nan mazan su da matansu sai gudanar da rayuwar su sukeyi
Tun daga nesa da hangoshi tareda kiyasul ausar sai duk suka kamu da mamaki domin kowa yasan babu shiri atsakaninsu
Koda karasowarsa cikin garin sai yasa wasu dakaru suka dauko wani katon keji na bakin karfe aka saka hassanul basari aciki
Shidai wannan keji ya kasance babbabe mai matukar girma da fadi
Wanda saboda girmansa dodanni ashirin ne suka daukoshi daga ma'ajiyarss
Sannan ya dubi jama'ar tasa yace yaku taron kabilar mutuwa
Dukkanku kunsan irin gabar da take tsakaninsa da kiyasul ausar
To daga wannan lokaci mun daina wannan gabar sakamakon aikin daya hadamu na farautar wannan bil'adama

Take yayi nuni da hannunsa zuwa kan hassanul basari
Kuma shine babban makiyin mai girma sahibul ukub
Yanzu haka ya zo wannan dajin ne da nufin zuws can fadar mai girma sahibul ukub ya yakeshi
Wannan shine babban kuskurensa arayuwa domin kuwa gashi tun kafin ya karasa can ya hadu da ajalinsa

Don haka a wannan ranar zamu shirya walima ta musamman
saboda samun nasarar kama wannan bil'adama kuma acikin walimar ne zamu rabashi gida biyu mu cinye namansa ni da kiyasul ausar
Yana gama fadin haka sai suka kama hanya ya nufi can wani katon kogon dutse
Take kiyasul ausar tabishi abaya sannu a hankali sai kiyasul ausar taga sun shiga cikin wata katuwar fada mai girman gaske
Wacce aka kawata ta kamar masarautar wani babban sarkin
Har suka isa wani guri da aka ajiye kwanon abinci guda biyu da kuma abin sha
Kowanne kwano ko kofi zurfinsa yakai a jefa mutum biyar acikinsa
Ba tareda bata lokaci ba suka zauna sukaci suka Cinye
Ana cikin haka ne kawai sai kiyasul ausar yaji ba zata iya yin shiru da bakinta ba
Don haka sai ta dubi marugas tace
Lallai kana jin dadinka domin na fuskanci ba karamin kaunarka sahibul ukub yake yi ba
Dubi irin daular da kake ciki da kuma jama'ar daya baka kake shugabanta
Tabbas ka gama jin dadin rayuwar ka saboda wannan daular da kake ciki
Dajin haka sai marugas ya girgiza kansa cikin alamun damuwa yace
Yake kiyasul ausar ki sani cewa duk wannan abubuwa
Da kika lissafa basa burgeni kuma basa bani sha'awa
Rayuwarki tafi bani sha'awa fiye da wacce nake ciki
Ni yanzu burina guda dayane shine ganin na sami dama nayi aure kuma na sami magaji
Amma gashi har yanzu ba'a bani damaryi ba
Hatta tarawa da wata macen ya hanani dukda cewa kuwa muna da ýan mata kyawawa
Ke kuwa gashi har yana baki dama kije ki tara da mijinki na lokaci mai tsaho
Haka dai sukayita atsakaninsu,
Can kuwa gurin da aka ajiye kejin da aka rufe hassanul basari aciki
Tuni gurin ya cika makil da jama'a
Domin wannan ne kari na farko da suka fara ganin bil'adama
Wasu ma har zuwa suke suna shafa fatar jikinsa
Suna cikin wannan haline wani daga cikin manyansu ya fito ya daka musu tsawa yace
Shin bakusan irin ganganci kukeyi bane taba wannan halittar?
Ina mai tabbatar muku da cewa wannan abune mai hatsari agaremu tunda har kukaga an sakashi acikin wannan keji
Aikuwa sunajin haka sai kowannensu ya fara ja da baya a razane
A hankali duk suka watse akan bar wasu tsiraru suna gadinsa kadai a tsaye agurin su dinma duk sun gama firgita
Ba tareda bata lokaci ba kowa ya fara shiryeshiryen wannan walima
Ana cikin wannan halin ne kawai sukayi arba da dodo marugas tareda kiyasul ausar sun fito daga cikin fadarsa
Koda ganinsa sai kowa ya nutsu ya koma cikin hayyacinsa
Ba tareda bata lokaci ba ya umarci wasu dodanni dasu shiga cikin wannan kejin su daurawa hassanul basari sarkoki sannan su fito dashi daga ciki
Aikuwa take suka garzaya makera aka taho da wasu irin murtukekiyar sarka mai kaurin gaske tana jan kasa
Suka shiga cikin kejin suka daura masa sarkokin a hannunsa, wuyansa da kuma kafafunsa
Amma dukda sun san cewa yana cikin halin suma hakan duk a tsorace suke
Kamar ace kyat su ruga da

Please Login or Register in order to submit comment