Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gasar bai taba ganin jarumai ba kamar wasu mutum 5 wadanda ya hanga atsakiyar filin
Su dai wadannan jarumai sun kasance karfafa ne na gaske
Sannan sun iya yaki da makami sosai duk inda suka gifta acikin filin gasar saidai kaga suna bangaje mazaje kasa
Na farko daga cikinsu ya kasance gabjejen mutum kuma bakar fatane
Ana kiransa da suna warshanu
Wanda ya taho daga nahiyar bakaken fata domin burin lashe wannan gasa
Na biyu kuma shima gabjejen katone amma ba bakar fata bane shi sunansa kuwa shine narkus

Na uku kuwa ta kasance macece ba namiji ba kuma bata da girman jiki
Sannan kuma ta kasance kyakykyawar gaskece don idan ka ganta sai kayi tsammanin ýar sarauta ce
Acikin zuciyarta bata fito wannan gasa ba don samun dukiya bane
Kawai tafito ne domin ta sami soyayyar sarki aryan wannan shine dalilin daya sa ta shiga wannan gasar jarumta
Wannan budurwa ana kiranta da suna jaruma marfuza

Mutum na hudu shima ya kasance matashin saurayine kuma mai natsakaicin jiki
wanda shekarunsa basu gaza ashirin da biyar ba mutane suna yi masa lakabi da sharzan
Mutum na karshe kuwa wani kakkauran mutum ne wanda gaba daya jikinsa amurde yake kamar curin kasa sunan da ýan kallo suke yi masa kirari dashi shine hamukas
Wadannan jarumai guda biyar sune mafiya karfin damtse da iya yaki acikin gaba daya jaruman gasar
Domin duk inda suka durfafa saidai kaga maza suna zubewa kasa
Suna samarwa kansu hanya ta karfin tsiya kai tun ragowar jaruman gasar suna tunkarar su har saida suka daina
Ya zamana su suke shiga cikinsu
Suna fadan ne cikin azababben zafin nama, juriya da bajinta kamar jikinsu bana jini da tsoka baneba
Kafin adau lokaci mai tsawo tuni an zubar da dukkan jaruman gasar
Saura su biyar kacal suka rage sai faman fafata yaki suke
Babu abinda zai baka mamaki face ganin yadda suke ta yakar junansu
Kamar jikinsu bana jini da tsoka baneba
Kuma babban abin mamakin shine yadda jaruma marfuza da jarumi sharzan suke iya kare duk hare haren da wadannan gabza gabzan kartin suke kawo musu har ma suke iya mai da martani ba tareda sun nuna gazawarsu ba
Koda alkalan gasar suka ga tabbas idan aka barsu suka ci gaba da wannan fada to tabbas
Azagaye na biyu za'a gama wannan gasar sabanin zagaye na uku
Kuma yin hakan zaisa su rasa kudade masu yawa
Koda yin wannan tunani sai kurum alkalin gasar ya umarci mai buga kararrawar tsayar da gasar akan ya kada kararrawar
Nantake kuwa ya cika umarni aka tsayar da yakin da sukeyi
Kowa yaja baya acikinsu suna tsuma da hararar juna kamar zakaru
Domin ba'ason ransu aka tsayar da wannan gasar ba
Su so sukayi kawai abasu dama su fitar da raini atsakaninsu
Daga nan sai shima alkalin gasa ya tashi ya dubi jama'a yace yaku mutanen wannan birni mai albarka da kuma bakin mu
Kamar yadda muka tsara ayau gashi mun fitar da zakarun gasa guda biyar
Don haka ayau wasa ya kare sai kuma mu koma gidajen mu mu jira zuwan gobe don fitar da zakara guda daya wanda sai fafata da sarki aryan
Dajin haka sai mutane suka rude da shewa gami da tafi
Kowa yana koda jarumin da yafi burgeshi acikin mutum biyar din
Shi kuwa sarki aryan kawai sai ya mike tsaye da nufin ya koma cikin gidan sarauta
Kawai sai suka hada idanu da jaruma marfuza take kawai tayi masa wani tattausan murmushi
Wanda shi kansa saida ya tsargu da wannan murmushin nata
Ya tambayi kansa shin wannan wanne irin murmushi ne?
Na raini ne ko kuma wani tuggun takeso ta shirya mini?
Tamabayar da ya yiwa kansa kenan kuma ya kasa baiwa amsa
Don haka kawai sai ya murtuke fuska ya kawar da fuskarsa ga barin kallon inda take
Ya tafi gidan sarautar sa dakaru da masu busa da masu yi masa kirari suna biye dashi abaya
Take mutane suka dinga kama hanyar komawa cikin masaukinsu
Jaruma walisa kuwa tana tare da sarkin kasuwa da kuma yaro zaljus wanda ke biye dasu abaya
Suna cikin tafiyar ne sarkin kasuwa ya dubi walisa yace
Shin ke a ganinki acikin wadannan jaruman gasa guda biyar
Wanene zai iya tsallake mataki na biyu ya kara da sarki aryan?
Dajin wannan tambaya sai walisa ta kyalkyale da dariya sannan
Tace ai sakamakon wannan gasa a bayyane yake tabbas ni nasan wanda zai haye mataki na biyu domin duk cikinsu
Babu wanda banyi la'akari da irin salon fadan sa ba da irin nutsuwar da yakeyi yayin wannan fafatawar tasu
Kuma aiki da nutsuwa shima mataki ne na samun nasara
Don haka ka jira gobe kawai zaka ga abinda zai faru da idanunka
A haka dai suka jera su ukun suna tafiya suna hirarrakinsu
Har suka karasa gida da zuwansu masu gadi suka bude musu kofa suka shiga
Shi garsu keda wuya sai sarkin kasuwa yimana ya nufi bangaren da dakinsa yake da nufin yaje ya kwanta
Har ya danyi gaba sai walisa ta kira sunansa cikin sauri ya juyo
Tace dashi ya kuma zaka kwanta alhalin baka karasa mini hikayar hassanul basari ba
Dajin haka sai yayi murmushi yace
Lallai gimbiya akwaiki da zumudi, kawai sai ya canja hanya
Ya shiga dakin ajiyar littattafansa ya dauko littafin
sannan ya dawo gabanta ya zauna
Ya cigaba da bata labari kamar haka

Yayinda gimbiya bahjhat ta samu ta fice daga gidan sarautar
Saita ci gaba da tafiya har saidata isa can bayan gari
Bayan ta boye fuskarta don kada masu gadi su shaida ta
Da zuwa sai ta iske uzumnal a tsaye rike da ingarmun dawakai guda biyu ahannunsa
Koda isowarta saiya rissina agabanta yace ya shugabata sai ki zabi doki guda daya acikin wadannan ki hau domin mu gaggauta zuwa sansanin kabilar banu sudes domin haduwa da sadauki hassanul basari
Ba tare data jinkirtaba kawai ta karbi doki daya a hannunsa ta haye samansa
Suka kama hanyar zuwa sansanin kabilar banu sudes
Sunayin tafiyar ne cikin sauri don suje kuma su dawo da wuri
Suka dinga giftawa ta cikin kananun dajijjika, kuma basu yarda wani mutum ya gansu ba
Suna cikin tafiyar ne bayan sun kusa isa inda sansanin banu sudes yake
Kawai sai suka iso wani dan karamin daji wanda su a saninsu babu wani abin cutarwa acikinsa
Hakika rashin sani yafi dare duhu, abinda su gimbiya bhajaht basu sani ba shine
A can babban dajin da yake yankin birninsu anyi gagarumar gobara wacce tasa dabbobin dajin suka firgice
Kowa ya kama gabansa suka bazama cikin duniya
To adaidai wannan lokaci dasu gimbiya bhajaht ke tafiya acikin dajin ne
Sai ga wani garke guda na zakuna suna gudu saboda gobarar data tashi a dajinsu
Kuma dukkansu a matukar galabaice suke da yunwa muddin suka kara ýan sa'o'i basu ci abinci ba to tabbas mutuwa zasuyi
Kwatsam adaidai wannan lokacin sai suka yi kichibus dasu gimbiya bhajaht
Nanfa sukace yau dame aka hada mu, take suka falfalo kansu da gudun tsiya da nufin su cimmasu koda su bahjaht sukayi arba da wadannan zakuna sai suma suka sakarwa dawakansu linzami suka falfala da gudun gaske
Don su. Tabbatar da cewa indai suka kuskura wadannan zakuna suka riskesu to ba zasu iya ceton rayuwarsu ba
Saboda yawa kuma dadin dadawa ita bahjaht bata iya yaki ba ko kadan bare tayi kokarin ceton rayuwarta
Suna cikin gudun ne kwatsam sai dawakansu sukayi tuntube da wani reshen bishiya
Duk sai suka rikito kasa daga kan dawakan nasu, cikin zafin nama suka mike tsaye uzumnal ya rike hannunta sukaci gaba da falfala gudun akan kafafunsu don su karasa sansanin banu sudes
Amma ina kafin su ankara sai gani sukayi zakunan sunyi musu kawanya sun kewayesu
Ta yadda babu wata hanyar da zasu iya bi su wuce
Take duk suka tsaya suna kallon junansu cike da tsoro
Kuma a lokacin ne wani murgujejen zaki wada yafi kowanne girma da kwarjini acikinsu ya fito
Ya nufo inda su bahjaht suke yana tande bakinsa da harshensa
Sannan yayi wani irin gurnani tareda girgiza jikinsa wanda karar ihun nasa ne ya amsa kuwwa acikin dajin gaba dayansa

A wannan lokaci kuwa shi sadauki hassanul basari yana cikin dajin da wannan abu yake faruwa
Kawai ya sami saman wata katuwar bishiya ya zauna akanta
Yana ta tunanin gimbiya bhajaht da kuma hanyar da zaibi yaje wajenta
Kawai sai ya jiyo sautin gurnanin wannan rikakken zakin
Take yayi sauri ya mike ya kara hayewa saman wannan bishiyar
Ya leko da kansa kasa kawai sai yayi arba da wadannan zakuna
Sun ritsa wasu mutane guda biyu a tsakiya mace dana miji
Kuma wannan zakin ya nufi kan wannan macen gadan gadan tazararsa da Ita bata wuce taku uku ba
Koda ganin wannan abu sai kawai ya daka tsalle daga saman bishiyar da yake
Yana yawo a saman bishiyoyi kamar dan biri adaidai lokacin zakin ya daka tsalle da nufin ya turmushe ta ita kanta alokacin ta gama saddakarwa ta mutu
Don harta rufe idanuwanta
Amma ina kafin ya sauka a jikinta tuni sadauki hassanul basari
Ya bayyana yasa hannunsa guda ya shureta ya hannun hagunsa kuwa ya dankarawa zakin duka a tsakiyar kansa
Take kuwa zakin ya fadi kasa matacce ko shurawa bai yi ba
Sannan ya dauki gawar mataccen zakin ya dinga dukan ýan uwansa dashi
Duk da karfi irin na zakuna sai gashi suna gudun ceton ransu suna komawa can dajin da suka baro sakamakon ganin mutuwa muraran agabansu
HAKIKA MASU IYA MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKA CE
IDAN KAJI ANCE GA KI GUDU TO SA GUDU NE BAIZO BA

Kuma abindaya koro bera daga rami ya fada wuta to hakika yafi wutar zafi
Kafin kace wani abu tuni zakunan sun gama guduwa babu ragowar ko guda daya a gurin
Sai a lokacin ne hassanul basari ya lura cewa gimbiya bhajaht ce wannan budurwa
Kuma sai mamaki ya turnukeshi Baisan sanda ya kalleta yace
Yake wannan gimbiya ma'abociyar daraja da kuma kyawun halitta shin menene ya fito dake daga gidan sarauta a wannan lokaci ba tareda rakiyar dakarunki ba?
Shin bakya tsoron wani abu ya sameki ko a kawo miki harin bazato kamar yadda ya faru yanzu?
Dajin wannan tambaya sai hankalin ta ya dawo jikinta
Ta gane wanene a kusa da ita take taji wani irin farinciki ya turnuketa take ta dago da kanta ta kalleshi cikin murmushi wanda ke faranta zuciyar wanda aka yiwa
Sannan tace
Yakai wannan kyakykyawan jarumi kayi sani cewa ba komai ne ya rabani da masarautar mu ba face tsananin kewarka da tunaninka
Tabbas idan har banzo na sameka ba a wannan lokaci to babu makawa sai dai ajalina ya riskeni
Ka sani cewa tun daga lokacin dana fara arba da kai zuciyata ta fada cikin kogin soyayyarka da begenka
Har naji bazan iya jure zaman rashinka ba na gwammace na bijirewa umarnin mahaifina don nazo na sadu da kai
Kuma wannan tunanin ne yasa na manta da duk wani hatsari da zan iya fuskanta akan hanyata
Atakaice dai ba komai bane ya zautar da zuciyata ba face soyayyarka
Ina fatan zaka karbi tayin soyayyata sannan ka bani gurbi acikin zuciyarka

SHIN SADAUKI HASSANUL BASARI ZAI AMINCE DA SOYAYYARTA?
IDAN MAHAIFIN GIMBIYA BAHJAHT YASAN CEWA TAZO TA HADU DA HASSANUL BASARI WANNE HUKUCI ZAI DAUKA AKANTA?
YAYA KUKE GANIN GASAR JARUMTAR ZATA KASANCE KUMA WAYE ZAI NASARA TSAKANIN SARKI ARYAN DA JARUMAI GUDA BIYAR?
DON SANIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABa
DAGA
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT++++++++++ZUBAR DA JINI

4++++++++++ PART B

LBR

+++++++++++HABIBULLAH KBR

Dajin wannan batu sai fuskar hassanul basari ta fadada da murmushi
Cikin sauri ya dubeta yace
Godiya ta tabbata ga ubangijin daya hada zukatan mu suka zamo daya
Yake wannan ýar sarki kiyi sani cewa
Hakika zuciyata ta kamu da tsananin soyayyarki tun daga farkon haduwa dake
Duk bugun da numfashi na yake yana futane da furucin sunanki
Barci kuwa kauracewa idanuna yayi har ina ji ajikina cewa zan iya sallama rayuwata domin burin mallakarki
Matsala dayace kawai zata tilasta mini rabuwa dake
Wannan matsalar kuwa ba komai bace ba face
A ka'idar addinina haramun ne mutum ya auri wadanda suke addinin tsafi
Ni kuma zan iya hakura da komai muddin zai rusa mini addinina
Kodajin wannan kalamai sai kawai bahjaht ta karaso ta kama hannuwansa
Sannan ta dubeshi tace
Shin kasan irin tsananin soyayyar da nake maka kuwa?
Tabbas akanka a shirye nake dana rasa komai nawa hatta sarauta ta kuwa
Amma da sharadi guda daya
Duk sanda ka nuna mini tsantsar soyayyar da kake mini
To nayi maka alkawarin a ranar zan karbi addininka na musulunci
Amma koda ka gaza nuna mini soyayyarka to ni zan kasance cikin kewarka da begenka
Dajin haka. Sai kawai ya dubi idanunta suna kallon juna. Yace
Matukar zaki karbi addinina nikuma nayi alkawarin sai na yi miki abinda zaki tabbatar da soyayyata
Jin haka keda wuya sai tayi masa wani tattausan murmushi sannan tace
To da wannan kalami nake maka bankwana sai mun sake haduwa akaro na gaba
Tana gama fadar haka saita juya masa baya sannan tayafito hadiminta uzumnal da hannu tana mai yi masa nuni da ya taho su tafi
Take kuwa ya biyota abaya sukabar jarumi hassanul basari atsaye yana ta faman kallon gimbiya bhajaht harsaida suka. Bace masa da gani sannan ya kama hanhar komawa sansaninsu

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU GIMBIYA BHAJAHT BAYAN TAJE SUN GANA DA SADAUKI HASSANUL BASARI
++++++ +++++ +++++++
Acan kuwa gidan sarauta bayan gimbiya bhajaht ta fice gidan bata dade da fita ba
Sai aka sami wani akasi a wannan ranar sarki mayasin ya fito da nufin ya zagaye gidan sarautar nasa
Domin ya dan zagaya cikinsa yaga abubuwan da suke faruwa awannan ranar
Saboda ji yayi gaba daya bashida kwanciyar hankali
Saboda haka yafito yana shiga lungu da sako na gidan sarautar
Da farko bangaren masu kula da bayi ya soma zuwa
Sannan ya wuce bangaren abinci ahaka har ya zagaye gidan sarautar
Sannan ya koma turakarsa, har ya sanya kafarsa abakin kofar
the am at tasa kawai sai ya tuna cewa Bai shiga turakar gimbiya bahjaht ba
Domin ya gani ko tayi barci,
Dayin wannan tunanin sai take ya juya ya koma hanyar turakarta
zuciyarsa na dukan uku uku domin yaji ajikinsa cewa tabbas akwai abinda yake faruwa
Tafiya kadan yayi ya isa bakin turakar da zuwansa sai ya tarar da kofar dakin arufe,
Don haka sai yasa hannunsa a hankali ya bude dakin ya shiga cikinsa
Bisa mamaki saiya ga babu gimbiya bhajaht nanfa hankalinsa ya tashi
Domin saidaya duba gaba daya dakin baiganta ba
Take ya
fito wajen dakin ya tambayi dakarun da suke kula da ita ko sunsan inda ta tafi

Sai dukkansu suka tsaya suna kallon juna koda yaga alamar
suna son boye masa wani abu sai kawai ya zare takobinsa ya sarewa daya daga cikinsu kai

Take kan ya gutsurure jini yayi tsartuwa daga jikin gangar jikin
Koda ganin abinda ya faru ga dan uwansu sai take jikin su ya fara kyarma
Suka fara neman tuba sannan suka kwashe labarin yadda sukayi da ita
Amma basu san inda ta tafi ba kuma itace tace kada su fada masa labarin fitarta
Kodajin wannan batu sai ya kwallara ihu wanda yasa gidan ya amsa kuwwa
Har dakaru suka rugo aguje domin ganin abinda yake faruwa
Da zuwa sukaga halinda sarki yake ciki duk sai sukayi cirko cirko suna kallonsa
Harsaida ya daka musu tsawa sannan suka tarwatse kowa ya koma kan aikinsa
Kawai saiya shige cikin turakar fuskarsa amurtuke kamar an
aiko masa da sakon mutuwa yana jiran dawowar bahjaht
Bai dade da zamaba saiga gimbiya bahjaht ta dawo daga wajen hassanul basari
Alokacin ta gaji likis ta shigo da nufin ta kwanta kwatsam sai
tayi kichibus da sarki mayasin azaune akan gefen gadonsa gaba daya fuskarsa babu annuri ko kadan
Ita kanta da tayi arba dashi awannan lokaci saida taji zuciyarta
ta buga da karfi kuma tsoro ya darsu acikinta
Amma sai ta
dake ta taho gurinsa kamar bata aikata komai ba fuskarta cike da murmushi da nufin ta fada kansa kamar yadda ta saba
Koda ta gama sakin jikinta zata fado kansa sai kawai ya shammaceta ya kauce ta fadi kasa

Cikin daga murya yace
Lallai na fuskanci duk irin biyayyar da kike yi mini yanzu kin daina har ma akwai wani sirri wanda kike boye mini
Ki sani cewa daga yanzu zan kafa miki doka mai tsanani kan ba zaki kara fita daga gidan sarautar nan ba tareda izinina ba
kuma ina mai tabbatar miki cewa akan darajata da karagar mulki
na babu abinda bazan iya aikatawa ba Don haka yanzu zaki
fara ganin misali yana gama fadin haka sai ya fice daga cikin
turakar bayan ýan dakiku kadan sai gashi ya dawo tareda hadiminta
uzumnal adaure cikin sarkoki hannu da kafa Sarki mayasin
ya kalli bahjaht alokacin da take tsugunne akasa yace
Daga yau zan zu zan baki zabi guda biyu
Zabi na farko shine ki fada mini inda uzumnal yayi miki rakiya da
kuma abubuwan da kuka aikatana sirri Ko kuma yanzu nasa takobi na datse masa kai

Koda ma kin fada mini inda kukaje to dolene na yanke masa
hukunci daidai da abin daya aikata Kodajin abinda mahaifinta
ya fada saita taso da sauri tana mai rokonsa akan yayiwa uzumnal afuwa zata fada masa gaskiyar abindaya faru
Awannan lokaci shikuwa azumnal kansa na sunkuye
Take gimbiya bahjaht ta kwashe labarin komai ta fada masa
harda alkawarin dake takaninta da sadauki hassanul basari
Koda jin wannan abu sai nan take kwalla ta zubo masa sannan
ya kwarara wani uban ihu wanda ke firgita maza afilin daga
Baisan sanda ya daga hannunsa sama ba ya kwada mata mari ba wanda saboda karfin naushin saida ta fadi kasa sumammiya
Wannan al'amari ba karamin baiwa uzumnal mamaki yayi ba
Kawai sai sarki mayasin ya kira dakaru ya umarcesu da
su daurawa gimbiya bahjaht sarka dajin haka sai duk suka tsaya suna duru duru kamar ba zasu yi ba
Harsaida ya daka musu tsawa suka razana sannan suka iya
sunkuyawa suka daura mata sarkoki Kamar wacce ta aikata wani babban laifi
Kawai sai sarki mayasin ya shureta akan kafadarsa ya tafi ya kaita gidan kurkuku sannan ya
umarci dakaru dasu kamo uzumnal su biyoshi abaya
Ba tareda gardamar komaiba kuwa suka cika umarni
Suka ciccibeshi suka bi sarki abaya duk inda sarki mayasin
ya gifta saidai kada dakaru da hadimai sun bishi da kallo
zuciyoyinsu cike da mamakin wanne irin laifi gimbiya bahjaht tayiwa sarki
Kafin a jima labarin wannan abu har ya baza cikin birnin gaba daya
Ba karamin mamaki abin ya baiwa mutane ba sakamakon
sanin irin tsananin kaunar da sarki mayasin yake nuna mata
amma sai gashi arana tsaka wannan soyayyar ta rikide ta koma kiyayya alokaci guda
Domin wasu har sun gani da idanunsu yadda sarki ya dauketa
ya nufi wani babban kurkuku birnin wanda aka tanajeshi
don hukunta masu manyan laifuka Shi dai wannan kurkuku an ginashine a saman wani babban tsuburi
Wanda yake karkashin tsaron wasu zaratan jarumai
masu matukar karfin damtse sannan akwai manyan dabbobin daji wadanda suke kewaye da wannan kurkuku
A kasan tsaunin kuwa rami ne mai matukar zurfin gaske wanda duk wanda ya kuskura ya fada cikinsa bazai fito a raye ba
Domin akwai mugayen dodanni masu shan jinin bil'adama
Komai hatsabibancin mutum bai isa ya iya tserewa wadannan dodanni ba
Wannan ne dalilin dayasa akewa wannan kurkuku lakani da darul maut
Lokacin da sarki mayasin ya tafi da gimbiya bahjaht
wannan gidan kurkuku tun daga nesa da masu gadi suka
kula cewa shine da kansa yazo ba dan aike ya turo ba sai nan take suka bude masa kofa
Wacce ta kasance katuwar gaske tayi girman kofar wani babban birnin
Shi kuwa uzumnal wanda dakaru kejansa akasa ko kadan baya tausayin kansa
Ko kuma nadamar abinda suka aikata face gimbiya bahjaht kadai yake jin tausayi
Ganin yadda ta kasance ýar sarauta kuma ýarsa ta cikinsa
Dadin dadawa kuma ga tsananin kyawun da allah ya bata har ake rububin zuwa kallonta
Amma sai gashi yau itace abar wulakantawa agurin mahaifinta
Ta daukota ya kawota gurin da koda wasa bai dace da matsayinsa ba
Kai bama itaba hatta talakawa tsoron rayuwar wannan kurkuku sukeyi
Dayin wannan tunani sai yaji gaba daya ya tsani soyayya kuma yaji cewa ya kamata ya fara neman tsari akanta
Domin ya sami labari daga magabatansa cewa soyayya itace ta hallakar da mazajen jiya
Da kuma manyan sarakuna da dama wadanda suka shude
Dayin wannan tunani sai hankalinsa ya kara dugunzuma yace
Da alama irin yadda ta kasance ga mazajen jiya irintace
Take shirin faruwa akan gimbiya bahjaht ma'ana tarihi yana neman maimaita kansa akanta
Koda yin wannan tunani sai take yaji tausayinta ya kamashi
Yaji dama bata fadawa sarki sirrinta ba in yaso shi sarki yasa takobi ya sare masa kai
Da shigar sarki mayasin gidan kurkuku sai kawai ya kutsa kai da ita ta tsakiyar gidan
Duk inda ya gifta saidai kaga fursunoni suna lekowa ta taga suna leken gimbiya bahjaht wasu daga cikinsu suna tausaya mata
Wasu kuma sai ihu na murna suke saboda ganin cewa ýar sarauta
zata dana irin rayuwar da sukeyi Kai tsaye ya wuce da ita wani
dan karamin daki wanda ko mikewa tsaye mutum bazai iyaba acikinsa
Kuma babu koda makewayi acikin dakin bare abin kwanciya
Wannan daki dai bashi da maraba da gurin zuba shara saboda dattin da yayi
Duk irin bukatar data kamaka saidai kayi shi agefenka
Baka isa ka fita waje ba, da isarsa wannan daki sai kawai ya jiyeta acikinsa ita kadai
Sannan ya fito ya jawo kofa ya saka kwado ya rufe
Shima uzumnal aka kaishi wani dakin daban aka rufe
Bayan nan sarki mayasin ya umarci mai tsaron kurkukun da kada ya kuskura ya saki gimbiya bahjaht
Kuma kada abata kulawa ma'ana abarta tayi rayuwa
irin wacce ko wanne fursuna yakeyi har zuwa sanda zai dawo
Dajin haka sai shugaban kurkukun yace angama ya shugabana
Sannan sarki mayasin ya kama hanyarsa ta komawa gidan sarauta
Awannan lokaci kallo daya zakayi masa kasan cewa acikin tsananin bacin rai yake
Bayan fitarsa daga gidan kurkukun keda wuya sai wani badakare mai
Kula da fursunoni ya debo ruwa mai sanyin gaske yazo ya watsawa gimbiya bahjaht ajikinta
Harsaida gaba daya tufafin jikinta suka jike sharkaf ta farka firgigit daga dogon suman da tayi
Koda ta farka ta ganta acikin wannan daki saita tashi da nufin mikewa tsaye
Sai taji kanta ya gwaru da rufin dakin sai kawai taga wannan badakaren
Ta kyalkyale da dariya yana nunata da yatsa, sai asannan ne ta gane ba'a gidan sarauta take ba

Don haka saita kalli badakaren tace kaikuma wanene kuma wanene ya kawo ni nan?
Sannan nan gurin wanne guri ne?
Dajin wadannan tambayoyi sai badakaren yayi dariya yace
Lallai yarinya kinyi kuskure da har kikayi jayayya da mahaifinki
Ki sani cewa shine da kansa ya kawo ki wannan guri kuma nan ba ko'ina bane ba face kurkukun darul maut
Kuma babu wanda ya isa ya kubutar dake daga wannan har zuwa sanda sarki zai nemeki da kansa
Domin yanzu duk isa da takamar da kikeyi ta kare domin kina karkashin ikon mu ne yanzu sai yadda muka sarrafaki
Kodajin wadannan bakaken kalamai sai ta rusa ihu saboda
bakin cikin ganin halin data tsinci kanta Nantake ta dinga buga goshinta da jikin gini
Harsaidaya fashe jini ya zuba sannan ta sami waje ta zauna tayita rusa kuka
Shikuwa wannan badakren babu abindaya dameshi sai murmushi kawai da yayi sannan ya kara gaba abinsa
Babu abindaya fi damun gimbiya bahjaht a wannan rana sai lokacin da dare yayi yayi
Alokacin ne wasu irin sauraye suka dinga cizon fatar jikinta
Sai awannan ranar ne tasan menene sauro, domin tunda tazo duniya bai taba cizonta ba sai awannan dare
Kai saboda tsananin zafin cizon sauron harsaida taji zazzabi mai karfi ya lullubeta
Ahaka ta kwana tana rawar dari, HAKIKA

Please Login or Register in order to submit comment