Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsabar kishirwa
Don haka sai ta yanke shawarar ta tsaya a wannan guri domin ta dan huta
Sannan ya sha ruwan cikin koramar da ita da dokin nata kuma tayi wanka
Take ta sauka daga kan dokin nata ta jashi bakin wannan koramar yasha ruwa ya koshi
Sannan ta jashi ta kaishi bakin wata katuwar bishiyar kuka ta daureshii
Tana gama daureshi ta juya ta kalli dajin sosai ta kare masa
Kallo tana yin nazarinsa ko zata sami wani abin mai cutarwa acikinsa
Bayan ta tabbata babu wani abin cutarwar da kuma bil'adama acikin dajin
Sai kawai ta kwabe tufafin jikinta ta fada cikin wannan koramar
Tana wanka abinta kamar a can cikin gidan sarautarsu takeyi ko kadan babu fargaba acikin zuciyarta
Kai harma tana rera baitocin wasu wakoki a bakinta
Koda ta shafe sa'a hudu tanayin wannan wanka sai kurum
Taji koramar da take ciki ta soma girgiza ruwan ciki yana hautsinewa
Kamar zaibar kan doron kasa ya tashi sama koda ta dago da kanta daga cikin koramar Sai tayi arba da wata katuwar kada
Tunda tazo duniya bata taba ganin halitta mai girman wannan kadan ba
Domin girman bakinta kawai yakai girman a hade manyan giwaye guda biyu
Ballantana kuma girman jikinta, idan wannan kadar ta motsa jikinta
Saidai kaga ruwan ya hautsine, nanfa walisa ta tambayi kanta
Shin wannan dabba dama can acikin wannan koramar take rayuwa?
Abinda bata sani ba shine ita wannan koramar reshece daga babban tekun duniya
Kuma wannan kadar ta kasance sihirtacciyace domin bata cin naman dabbobi sai na bil'adama
Shiyasa tana iya gano bil'adama indai ya shiga daya daga reshinan tekun
Kuma taje ta riskeshi cikin 'yan dakiku kadan

WANNE IRIN TASHIN HANKALI WALISA ZATA FUSKANTA YAYIN HADUWARTA DA WANNAN DABBA?
SHIN ZATA TSIRA DA RAYUWARTANE KO KUMA MUTUWA ZATAYI A WANNAN KORAMA?
MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEMENT+++++++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++++++++2 PART A

LBR
++++++++++++++HABIBULLAH KBR
0=====[===============>
Koda gama bayyanar wannan kadar sai walisa ta daka tsalle
Tareda zare takobin da nufin ta fice daga cikin koramar
Ba zato ba tsammani sai kawai taji wannan kadan ya kawo mata duka da jelarta
Inbadon ta tsallakeba da tuni kadan ya raba ta biyu da jelarta
Amma duk da haka sai da jelar kadar ya raba wata bishiya dake gefen koramar
Koda ganin haka sai take walisa ta daka tsalle sama da nufin ta haye tsakiyar kan wannan kadar
Take kuwa kadan ya sa jelarsa ya dokota ta fado kasa cikin ruwa
Cikin sauri walisa ta dago saman ruwan ta fuskanci wannan kadar
Suka ruguntsume da masifaffen fada kamar wasu manyan shedanu
Nanfa suka ruda ruwan da yake cikin koramar saboda
Tsananin gumurzu saidai kaga kifaye suna tasowa sama matattu
Jaruma walisa ta wanzu tana mai kaiwa wannan kadar mugayen hare hare domin taga bayan ta da wuri
Amma ina babu damar hakan domin itama wannan kadar
Irinsu ake cewa murucin kan dutse bai fitoba sai daya shirya
Duk sanda walisa ta sari ko ta yanki jikin wannan kadar saidai taga tartsatsin wuta ya tashi kamar haduwar karfe da karfe
Itama kadar idan ta kawowa walisa hari da zarar ta goce duk abinda ta daka da jelarta
Take yake dagargajewa
Tabbas inba don walisa ta kasance mai tsananin zafin nama ba
Da bata isa ta iya shafe dakiku uku ba suna fafatawa da wannan kadar ba
Kai komai yawan ayarin mutane idan suka yada zango a bakin wannan koramar
To ba makawa sunansu gawa domin ko daya daga cikinsu bai isa yayi rai ba
Kai saida takai ta kawo matafiya sun gane wannan
koramar sun daina tsayawa abakinta domin sun san sakamakon tsayawa agabar tata
Koda suka shafe wasu dakikun masu yawa sai fadan nasu ya zama abin tsoron kallo
Domin saida gaba daya reshinan wannan koramar suka amsa wannan fafatawa da akeyi
Kai harma saida takai zuwa ga babban cibiyar wannan korama wato tekun bahar zus
Sai gashi gaba daya dabbobin cikinsa sun haukace
Suna neman gurin buya, kai wasuma har tsalle sukeyi suna fadowa kan doron kasa
Ba tare da sun sani ba, saidai suyita kokarin komawa cikin tekun amma su kasa
Ahaka har ransu ya fita,
Acan bangaren su walisa kuwa lamarin yafiyin tsamari
Domin dukkansu sun san cewa yau sun hadu da gamonsu
Kuma a wannan yanayi kar ta san kar ce a tsakaninsu
Ana cikin wannan bakin artabun ne kadar ta sammaci walisa
Ta kawo mata hadiya da nufin ta tauneta gaba daya
Cikin tsananin zafin nama ta daka tsalle ta kaucewa harin wannan kadar
Inbadon tayi saurin kaucewa ba da tuni shi kenan an gama da shafinta
Amma duk da haka saida kadar ta doketa da kafarta ta gaba
Take tayi sama ta fice daga cikin koramar ta gwaru da wani katon dutse
Wanda yasa har jini ya fita daga cikin hancinta ta fara ganin taurarin wuya acikin idanunta
Cikin tsananin juriya ta mike tsaye rukeda takobinta a hannunta
Tana jiran karasowar kadar domin alokacin itama kokarin fitowa daga cikin koramar take
Sai bayan ta gama fitowa ne walisa ta karewa wannan kadar kallo sosai
Sannan ta gane lallai wannan ba irin kadar da ta saba gani bace
Ita gaba daya jikin wani irin santsine dashi kamar an shafa masa
Kubewa sannan kuma yana da tsananin daukar ido,
A tsakiyar gadon bayanta kuwa akwai wani dan karamin kaho
Tana cikin wannan nazarin ne kawai taga kadar ya kawo mata wani irin harin bazato
Cikin zafin nama ta daka tsalle cikin shammace ta dira
A gadon bayan wannan kadar kuma ta kama wannan kahon ta rukeshi da hannunta guda daya
Nan fa wannan kadar ta haukace ta fara kokarin wullo ta daga gadon bayanta, itakuwa sai taki yarda ta fado kasan
Ta ci gaba da ruke wanna kahon,
Wohoho hakika idan kaji ance ga ki gudu to sa gudu ne baizoba
Sai gashi da wuya tayi wuya kadar ta dinga zuwa tana gwara jikinta da jikin bishiyoyi
Suna karyewa da faduwa kasa,
Ganin wannan al'amarine yasa walisa ta fahimci cewa tabbas
Ruwa baya tsami banza dole akwai dalilin dayasa kadar bata son a ruke wannan kahon na bayanta
Gama wannan tunani keda wuya sai ta tattara karfinta
Guri guda ta daga takobinta sama ta sara a tsakiyar wannan kahon
Take kuwa kahon ya rabe gida biyu kamar an tsaga lemo
Faruwar hakan keda wuya sai kadar tayi wani irin gurnani mara dadin saurare
Jini yayi fitar burgu daga jikin wannan kahon ya kwarara
Zuwa cikin wannan koramar yana gudu kamar ruwan famfo
Take ta fara mirgine mirgine tana tumurmushe abubuwan da suke cikin dajin
Aciki harda dokin da walisa take hawa koda walisa ta ga abinda yake faruwa saita daka tsalle ta sauka daga kan kadar
Ta sauka can gefe guda tana kallonta tun tanayin motsi har ranta ya gama fita daga jikinta
Bayan kadar ta mutune sai walisa ta dawo bakin koramar ta sake shiga cikinta ta wanke jinin daya bata mata jikin nata
Tana cikin wanke jinin da yake jikintane kawai sai taji wata irin guguwar iska mai karfin gaske ta wuce
Ta saman kanta cikin sauri ta dago da kanta sama take tayi arba da dan uwanta
Walisu da wasu irin manyan fuka fukai a cikin sararin samaniya yana zabga gudu kamar tauraruwa mai wutsiya
Ya nufi bangaren gabas, domin shi baima kula da Ita ba
Koda ganin wannan al'amari sai tayi sauri ta fito daga cikin koramar ta debi kayanta da makamanta ta sanya ajikinta
Sannan ta falfala da azababben gudu ta nufi bangaren da shi walisun yabi
Domin itama ta tabbatar da cewa zaijene domin ya aikata ta'addanci
Nanfa ta dinga tsala azababbben gudu acikin dajin
Kai saboda ma karfin gudun har tashi sama zakaga tanayi
Tana tsallake kananan bishiyoyi da ramuka sai a sannan nema ta kula da cewa
Ta ma fi dokin nata karfin gudu saboda cikin lokuta kadan ta dinga
Shafe tafiya mai nisan gaske gaba daya cikin zuciyarta
Tana tunanine akan inane jarumi walisu sai nufa domin tayi gaggawar dakatar dashi ga barin yin wannan mummunan aikin da yakeyi
Kai wani lokacinma idan bishiyoyi suka tare mata hanya
Sai dai kawai kaga ta daga tsalle sama tana kama reshinan
Bishiyoyin tana tsalle akansu kai sai kayi zaton cewa ita ba mutum bace
Gwaggwon biri ce ahaka ta dinga wucewa ta dajijjika masu yawa
Idan kuwa tazo gaban ruwa da zarar ta karanta wadansu
Dalasiman tsafi saidai kaga tana tafiya a saman ruwan kamar akan doron kasa takeyi
Saida ta shafe sa'o'i tana gudu sannan ta iso bakin wani babban birni
Da ganinsa saita cika da tsananin mamaki sakamakon ganin garin da tayi cikin nutsuwa babu alamar ana tashin hankali acikinsa
Take ta tambayi zuciyarta cewa
Anya kuwa yarima walisu yazo wannan birnin kuwa ?
Ko dai canja hanya yayi ya tafi wani bangaren daban?
Amsoshin data kasa baiwa kanta amsarsu kenan don haka
Kawai sai ta yanke shawarar shiga cikin birnin koda kuwa baya ciki
Da gama wannan tunani kawai saita rikide ta koma saurayin mafarauci
Dauke da mataccen murgujejen zaki akafadarsa
Kai da ka ganta a wannan lokaci ba zaka taba tunanin ba mace baceba
Saboda komai na siffar jikinta ya rikide ya zama na maza
Take ta nufi wannan babban birni wanda tun daga nesa ta fara
Hango dakarun cikinsa dauke da miyagun makamai sai zare idanu sukeyi kamar saci babu kai da ganinsu kasan babu sauran tausayi acikin zukatansu
Kowannensu ya bada hankalinsa wajen kallon kan hanya
Domin su ga wanda zai shiga cikin birnin ahankali walisa taci
Gaba da tafiya tana kara kusantar wadannan dakarun
Kuma ko kadan babu tsoro acikin zuciyarta a haka harta karasa wajen masu tsaron kofar
Daya daga cikinsu wanda ya kasance murgujejen gaske
Mai kirar mutanen farko ya dakawa saurayin mafaraucin tsawa
Yace kai kuma wanene kuma daga ina kake inason ka fada mini
Iyakar gaskiya idan ba haka kuwa yanzu nasa takobina na raba
Jijiyoyin da suke jikin wuyanka biyu domin tasha jinin jikinka ta kuma barwa kasa ragowar ta shanye
Kodajin haka sai saurayin mafaraucin ya russinar da kansa
Yace ka gafarceni ya kalmaru nine jamwar daga marugayi sarkin mafarauta na wannan birnin namu mai albarka
Abinda yasa baka san da fita ta ba shine
Ka sani cewa ni bata wannan kofar da kuke gadinta na fitaba
Na fitane ta wata kofar daban akan hanyata ne na hadu da wannan murgujejen zakin
Inda muka kasa tseren gudu dashi har saida muka iso wajen
kusa da wannan kofar da kuke tsaronta Sannan na samu na iya cimmasa na kamashi

Muka fafata yaki dashi daga baya na sami nasara akansa
Dajin wannan bayani sai sarkin kofa yayi shiru yana dan nazari
Yana cikin yin tunanine sai wani badakare dake bayansa
Ya matso gabansa yace ya shugabana tabbas wannan shine jamwar daga marugayi sarkin mafarauta
Don haka inaganin abindaya fada gaskiyane badon komaiba sai don ya zo da hujja
Ga zakin nan a kafadarsa, dajin haka sai sarkin kofa yayi murmushi
Ya kalle badakaren yace waya fada maka kowa abin yarda ne?
Idan har sun fafata yaki da wannan murgujejen zaki dolene
Za'a sami tabo ajikinsa don haka ba zan yarda dashi ba har sai na duba na gani
Yana gama fadar haka sai ya yafito jamwar da hannu
Yana mai yi masa nuni da yazo inda yake
Cikin sauri kuwa ya matso gabansa ya tsaya
Sarkin kofa ya kalli fuskar sa ya kare mata kallo sannan ya kalli kan damtsen sa da kan wuyansa
Kawai
Saiyaga yankan farce harma yankan ya danyi zurfi da ganin haka
Sai sarkin kofa yayi murmushi yace to yanzu zaka iya shiga cikin birnin nan
Amma ka sani idan nayi bukatar ganinka zan nemeka
Da gama fadar haka sai ya umarci dakarun dake bayansa da su bude kofa
Take kuwa suka cika umarnin shugaban nasu, cikin girmamawa jamwar yace nagode
Ya kama hanya ya shiga cikin birnin mai suna teheran
Da shigarsa cikin birnin sai ya kama hanyar da zata kaishi cikin gari
Bayan ya danyi nisa da barin kofar birnin yadda masu tsaron kofa
Ba zasu ganshi ba sai ya sake rikidewa daga wannan siffar
Zuwa ta dan yaro dan kimanin shekaru goma sha biyu
Matalauci wanda ko kaya masu kyau babu ajikinsa kuma a hannunsa ruke yake da kokon bara
Take ya kama hanyar shiga cikin gari ya dinga bibiyar guraren da mutane
Suke yanayin bara acikin barar tasa yana hada mutane da darajar abin bautarsu kan su taimaka da abin da zaici
Amma sai yaga duk wanda ya kalleshi saiya kyalkyale da dariya
Sannan su koreshi daga inda suke wannan halayya tasu
Ba karamin bashi mamaki tayi ba yace acikin zuciyarsa
Wai dama haka ala'dar gaba daya mutanen duniya take babu wanda yakeda tausayin nakasashshe?
Abin da bata saniba shine duk duk mutanen wannan zamani haka suke
Itama abinda yasa bata san da hakaba shine mahaifinsu
Ya hana aikata wannan dabi'a acikin birninsu tun kafin a haifesu
Wannan dalilin ne yasa ake zaman lafiya acikin birninsu har mutane suke sha'awar rayuwa acikinsa
Yana cikin wannan tunanin ne ta iso bakin wani gidan abinci
Wanda ya cika da mutane maza da mata kowa yana ciye ciyensa
Da zuwa gurin saiya fara yi musu bara kan su taimaka masa da abinda zaici koda kuwa loma dayane
Yana cikin yin barar ne kawai wani murgujejen kato ya dauke abinci ya taho gurin da yake
Hannunsa ruke da kwanon abinci
Da zuwa gurinda yake saiya kalleshi kamar yana jin tausayinsa
Yace kai yaro yanzu yaushe rabonka da cin abinci?
Cikin karamar murya irin ta yara yace
Rabona da cin abinci tun jiya da rana ina mai rokonka daka
Taimaka mini da wannan abincin don kaima wataran ubangiji ya taimakeka
Dajin haka sai saurayin ya murtuke fuska take ya saki kwanon abincin agabanta
Ya zube sannan yasa kafa ya tattakashi yace
Lallai ma yaran nan kai da ganin irin siffata nayi maka kama data masu tausayi?
To ka sani ko zaka mutu bazan taba taimaka maka da abinci ba
Yana gama fadar haka yasa hannu ya zabga masa mari
Ganin abindaya faru ga wannan almajiri sai ya baiwa mutanen da suke cikin wannan rumfar dariya har suna yabon wannan saurayin akan abin da yayiwa almajirin
Almajirin ya tashi fuskarsa na zubar da hawaye ya tafi daga wannan rumfar ya kara nausawa cikin gari
Koda ya bar jikin wannan rumfar ya kara shiga tsakiyar kasuwa
Kawai sai yayi arba da dakarun sarki kalkus suna tafiya acikin tsakiyar kasuwar
Adadinsu yakai dubu uku kuma sarki kalkus dinne akan gaba
Har sun dan gifta ta inda almajirin yake sai kawai akaga sarki kalkus
Ya ja linzamin dokinsa sannan ta dawo daidai inda wannan almajirin yake
Ya kare masa kallo sama da kasa sannan ya bushe da dariya yace
Wai dama har yanzu akwai irin wadannan kaskantattun mutanen acikin wannan duniya?
Gaskiya da ace ban fito farautar boka sahibul ukub ba to da sai na sa an kama mini kai
An kaika masarautata domin ka dinga debe mini kewa saboda
Babu abinda nakeson gani a rayuwata kamar makaskantan mutane irinka
Duk ragowar dakarun da suke bayansa sai suma suka bushe da dariya
Sannan sarki kalkus ya kada linzamin dokinsa ya kara gaba dakarun sa na biye dashi
Ana cikin wannan yanayi ne kawai sai ya jiyo sautin wani yaro yana tsallara ihun neman taimako inda wani gabjejen kato
Ya sakashi agaba yana zabga masa wata katuwar bulala
Wacce ko doki idan aka dakeshi da ita sai yaji zafin dukan
Idan wajen ya kumbura sai kaga ya debo gishiri yana shafawa akan shatar bulalar
Yaron sai rusa ihu yake kamar ransa zai fita amma duk da haka
An rasa mutum daya wanda zaije ya ceci wannan yaron
Kowa idan yazo sai kaga ya kauda kansa ya kara gaba
Abinsa domin sam wannan abu ba komai baneba su awajensu
Domin sun saba ganin zaluncin daya wuce wannan har almajirin ya kauda kansa zai kara
Gaba sai yaji shifa ba zai iya tafiya ya bar wannan yaron ba
Cikin bakar wahala ba don haka sai ya juya ya tafi inda ake azabtar da wannnan
Da isarsa sai ya fara yiwa wannan gabjejen katon magiya akan ya yi hakuri ya kyale
Yaron yayi tafiyarsa amma sai yaki ya hakura daga bayama
Sai ya daga bulalar da nufin shima ya hada dashi ya azabtar
Koda ya daga bulalar sama da nufin zabgawa wannan almajirin sai kawai yaji an shureshi an dagashi sama sannan
An dokashi da kasa saboda karfin dukan saida yaji kamar kashushuwan bayansa
Sun kakkarye take ya mike tsaye tareda zare takobinsa da nufin
Ya sare kan wannan almajirin
Kafin ya aikata haka sai yaga wannan almajirin ya rikide daga
Wannan siffar ya koma zuwa ainihin siffar jaruma walisa
Koda ganin wannan abin al'ajabi sai wannan ya wullar da takobinsa
Ya falfala da gudun gaske saboda firgitar da yayi da lamarinta
SHIN INA YARIMA WALISU YA TAFI?
KUMA ME WALISA TAKE NEMA ACIKIN WANNAN BIRNIN?
ME SARKIN GARIN ZAIYI MATA SABODA TA WULAKANTA DAN CIKIN BIRNINSA AMATSAYINTA NA BAKUWA ?
SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
DAGA
HABIBULLAH KBR
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT++++++++++++++ZUBAR DA JINI

+++++++++++++2 PART B

LBR

+++++++++++++++HABIBULLAH KBR

Jaruma walisa ta sanya hannayenta ta tashi wannan yaron tsaye
Sannan ta nuna inda tabban bulalar jikinsa yake
Take ya daina jin radadin bulalar jikin nasa
Ya dago da kansa ya kalleta yace
Yake wannan ma'abociyar taimako ina matukar godiya agareki
Bisa kulawar da kika bani kuma ina addu'a agareki ubangiji
ya baki nasara kan dukkan abubuwan da kika sanya agabanki
Dajin haka sai tayi murmushi agareshi sannan tace
Kaikuwa wanne irin laifi ka aikata masa wanda yasa yaketa faman azabtar dakai?
Dajin wannan tambaya sai yaron yace ni kaina bansan laifin da nayi masa ba
Saidai kawai nasan al'adar duk wani wanda yakeji da karfi
A wannan nahiyar idan yana da bukatar yin nishadi sai
Kawai ya kama wanda yafi karfi yayita zaluntarsa su kuma mutane
Idan suna ganin haka sai suyita jin dadi
Koda jin bayanin da wannan yaron yayi mata sai kawai
Tausayinsa ya kamata kuma taji ta tsani zama acikin birnin
Don haka sai ta debo dinare dari ta baiwa wannan yaron
Sannan tace ga wannan sai kaje dashi ka baiwa iyayenka
Ni kuma zan kama hanya domin na bar wannan birnin in kara
Gaba saboda ba zan iya zama a garinda mutane da dabbobi basu da banbanci ba
Yaron ya kalleta yace yake wannan jaruma shin waike wacece
Kuma menene ya kawoki wannan birni namu saboda naga alamun kamar ke bakuwace
Dajin wannan tambaya sai tayi murmushi sannan tace
Nice gimbiya walisa ta birnin madaril adfam
Kuma ba komai ne ya raboni da gidaba face neman dan uwana yarima walisu
Wanda ruhin wani takadirin boka ya shiga jikinsa yake sarrafashi
Tana gama fadin haka saita juya zata tafi kawai sai taji an ruko
Gefen rigarta koda ta juya bayanta sai kawai taga wannan yaron
Ya mike tsaye siffar jikinsa shima tana rikidewa zuwa ta saurayi
Kakkarfa sannu ahankali sai gashi ya koma siffar dan uwanta
Yarima walisu amma kuma sai taga gaba daya ya sauya daga yadda ta sanshi
Ga wasu irin manyan fuka fukai ajikinsa launin fatar kirjinsa kuwa
Itama ya sauya gaba daya gashi ya lullubeshi sai kace tsuntsu

Hannunsa na dama kuwa ruke yake da wata iriyar zabgegiyar sarkar tsafi
Cikin sauri walisa ta dubeshi tace
Ka ganeni kuwa nice ýar uwarka walisa yanzu haka mahaifinmu ne ya turo ni nemanka
Take ta kai hannu da nufin ta rungumeshi
Koda hannuwanta suka sauka akan fatar jikinsa sai taji
Wani irin zafi mai radadi yaratsa jikinta kamar wacce ta kama garwashin wuta
Cikin sauri ta cikashi tareda ja da baya taku uku tana mai fuskantarsa
Shi kuwa sai kawai ya kyalkyale da dariyar mugunta
Wacce tasa taji kamar gabaki daya kunnuwanta zasu fashe
Harsaida tasa hannayenta ta toshe kunnuwanta dasu
Kasar gurin kuwa ta fara girgiza kamar za'ayi girgizar kasa
Saida yayi dariyarsa ta isheshi sannan kuma yaci kunu tareda murtuke fuska
Sannan ya daka mata tsawa yace
Ke karamar yarinya karya kikeyi baki isa ki raina mini
Hankali ba domin duk duniya bani da ýan uwa ni kadaine
Sannan inaso ki sani ina sane dake tun sanda kika biyo bayana
Kina nemana saidai duk wannan abinda kikeyi kina yaudarar kanki ne
Ina mai tabbatar miki cewa duk duniya babu wanda ya isa
Ya hanani aiwatar da abinda nayi niya balle ke karamar yarinya
Ni kadai fasa tarone don haka babu yadda za'ayi mutum daya ta iya hanani cika burina
Inaso ki sani cewa inda ina da burin kasheki to babu makawa yanzu take
Zan hallakaki sannan na tafi can birnin ku na hallaka mahaifinku
To amma bakune agabana ba nafiso sai na gama razana mahaifinki
Sannan zanje shima nayi masa irin kisan da nake bukatar yi masa
To a lokacin ne duniya zasu tabbatar da cewa
Boka sahibul ukub ya dawo sannan kowa ya dawo ya cigaba
Da bauta mini kamar yadda akeyi abaya
Koda yazo daidai nan azancensa sai itama ta bushe da dariya
Sannan tace karyarka tasha karya baka isa ka aikata abinda kakeso ba
A wannan duniyar sa'arka dayace shine nayiwa mahaifina
Alakawarin zand dawo masa da kai a raye amma badon hakaba
Kasheka kawai zanyi
Koda gama fadin haka saita zare takobinta ta daka tsalle sama
Da nufin tayi masa fashin albasa, koda takobin ta sauka
Ajikinsa sai wata kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe tareda tartsatsin wuta
Cikin bakin zafin nama ta sake daka tsalle sama ta dinga jera masa
Kutufo da naushi akan fuska saboda karfin dukan saida taji
Kafafun nata da hannuwanta suna radadi amma duk da haka sai taga ko motsi baiyiba daga inda yake
A ka'ida idan tayi irin wannan dukan ko bishiya ta daka
Sai bishiyar ta fadi komai girmanta da kuma nutsewar da tayi acikin kasa
Sai kaga ta bubbugo daga cikin kasa har jijiyoyinta
Sun zube akasa ba'a taba samun akasi ba, don haka saita kamu da tsananin mamaki akan

Please Login or Register in order to submit comment